Murmushi kawai tayi masa, tana ɗan satan kallonsa, cikin ranta kuwa moment dinsu na ɗazu take tunowa, tabbas yasata acikin wata duniya me daɗin gaske, batasan cewa sex na da daɗi ba sai ayau, duk da cewa ta ɗanji zafi, amma zafin ɗan kaɗanne daɗin da taji yafi zafin yawa. Hannunta dake cikin nasa ya kama suka fita daga cikin ɗakin, kaitsaye sashin Ummi suka nufa, ganin sun kusa kaiwa falon Ummi yasa ta janye hannunta daga nasa, suna shiga falon kuwa suka iske Ummi da Raleeya da kuma Ahmad azaune suma cikin shirgarsu ta alfarma da shirin fita, gefe Hayatuddeen ne ke zaune yasaka roban Ice cream agaba sai sha yake, yana jujjuya kai, dan earpiece ne akunnensa.
Ummi na ganinsu haka ta saki murmushin jin daɗi, dan tabbas sunyi kyau sosai, ga kayansu kala ɗaya, sunfito ras dasu gwanin burgewa. Saida Ahmad yaɗan tsokane su sannan sukayiwa Ummi sallama, har bakin mota Hayatuddeen ya rakasu, saidai awannan karon ba Saifuddeen ɗin bane zaiyi driving, Sule driver ne Ahmad kuwa da Raliya suma motarsu suka shiga,
saida Hayatuddeen yaga tashinsu sannan ya koma cikin gida shima ya ƙarisa shirinsa dan Khamis zai biyoshi suje suda Imran, Sulaiman, Isma'il Zakariyya.
Suna ɗaukan titi taɗan jinginar da kanta akan kafaɗansa, lumshe idanunta tayi tana shaƙan ƙamshin jikinsa, ganin haka ne yasa shi zura hannunsa a ƙugunta ya rungumota, ahankali yake ɗan hura mata iskan bakinshi akan fuskarta, hakan kuwa sosai yayi mata daɗi, gaba ɗaya sun shagala hannunta tasa tanata shafa sajenshi, ahaka suka ƙaraso wajen da za'ayi diner'n, wato Madugu Guest Palace, sosai wajen ya ƙawatu da decoration me kyau da burgewa, gaba ɗaya wajen cike yake da jama'a, kusan kowa yazo, amma Ishaq yakafe kan cewar baza'a fara gudanar da diner ɗin ba, har sai anjira Amininsa wato Saifuddeen ya ƙaraso.
Da isowarsu kuwa MC yafara shelan zuwansu, nanfa jama'a suka zubawa ƙofar shigowa ido, dan ganin wanene shi Aminin Ishaq ɗin, da kusan inbashi babu biki. Cikin nutsuwa suka raso cikin hall din, hannunsu sarƙafe acikin na juna, sunyi wani irin fitinannen kyau da dacewa.
Suna shigowa kuwa waje ya ɗinke da surutu, dan kowa ganinsu yake tamkar taurari ne suka sauƙo ƙasa, saboda tsabar haɗuwa, kyau, da kuma dacewa, har wani irin yanayin kama sukeyi, wanda hakan yasa suka ƙara ƙayatarwa. Har suka ƙarasa wajen zaman da aka tana da musu na musamman, MC baidaina wasa suba, mutane da yawa saidai kawai suce.
"Masha Allah." dan kuwa su Saifuddeen ɗin sunyi kyau matuƙa. Suna zama kuwa aka soma gudanar da diner ɗin, sosai abun ya ƙayatar, dan babu laifi Ishaq ya kashe kuɗi sosai, hakama Saifuddeen kusan komai shiyayi, dan wani abun ko Ishaq yace bazaiyi ba, saboda kashe kudin zaiyi yawa, Saifuddeen ne ke tuburewa, yace sai anyi, babu wani nuƙu-nuƙu kuma ya buɗe bakin al'jihunsa, dan yanason bikin abokin nasa kuma amininsa yayi armashi. Alhamdulillah anyi diner lafiya, taro yayi daɗi, haka kuma anci ansha ankuma yi ɓarin naira, biki dai saidai ace masha Allah.
Ƙarfe 10 dai-dai aka tashi awajen diner'n, saida amarya da ango suka tafi, kafun suma su Saifuddeen suka kamo hanyar gida.
Tun acikin mota takejin cikinta na hautsunawa, ga kuma wani irin jiri dake ɗan sanɗanta, haka duk takejin bakinta ba daɗi ita sai lokacin ta tuna rabonta da jin wani abu tun jiya da dare sai dai in taji yunwa tasha ruwan tea to kuma yanzu tun rana bata kuma cin komai ba.
Suna shigowa cikin gida, direct sashin Ummi suka nufa, afalon kuwa suka tarar da ita, tana zaman jiran dawowansu, dan bazata taɓa iya bacci, batare da taga dawowansu ba, saida safe suka mata, suna fitowa daga sashin Ummi, ya riƙo hannunta, dan yaga kaman gaba ɗaya gauraya hanya take, shiyasa yayi tunanin ko bacci ne yaci ƙarfinta, direct part ɗinsa ya nufa da ita, har cikin bedroom suka ƙarasa, sakinta yayi ta zauna akan gado, ɗan jingija bayanta da jikin gadon tayi, tare da lumshe idanunta, tun rana rabonta da abinci, amma kuma batajin zata iya sawa cikinta wani abu, wani irin tashin zuciya da amai takeji, saidai abun beyi ƙarfi ba ga wani fitinenne gajiya da takeji. Shikuwa cikin nutsuwa yaɗan rage kayan jikinsa, ganin ta lumshe ido kaman me bacci ne yasashi wucewa toilet, ya sakarwa kansa shower, har ya fito daga wankan tana nan zaune a inda ya barta, still idanunta arufe suke, saboda jirin da takeji, shirya kansa yayi, cikin wasu riga da wando na bacci, masu taushin gaske, wanda suke da kalan navy blue, sunkuwa yi masa kyau. Ahankali ya turo wheelchair ɗinsa, har zuwa inda take, hannunta ya kamo, tare dasa ɗaya hannunsa ya shafi gefen fuskarta, hakanne yasa taɗan bude idanunta wanda suka ɗan soma lumshewa, giransa ɗaya ya ɗaga mata, tare da yi mata alaman "Kingaji ne?."
Kanta taɗan jinjina masa, tare da karyar da wuyanta gefe, dan gajiya takeji ajikinta sosai, jawota jikinsa yayi, cikin kulawa ya zuge zip din rigar dake jikinta, sam bata hanasa ba, dan dama tana da buƙatar hakan, kawai dai kuzari ne da bata dashi, anutse ya cire mata doguwar rigan, tare da ɓalle mata maɓallin bra ɗinta, wani farin towel ya ɗaura mata, shida kansa ya kama hannunta suka shiga toilet, ruwan wanka me ɗan ɗumi ya haɗa mata, tare da zaunar da ita acikin bathtube, duk yanda yabi da ita haka take binsa, wanka yayi mata sannan ya kuma ya ɗauka mata towel, yana riƙe da hannunta suka fito daga cikin toilet ɗin, shida kansa ya zura mata doguwar rigan bacci, irin me lafewa ajikin nan, wanda take sak kala da nasa, ganin yanda jikinta duk ya sake ne yasashi ɗanjin tausayinta ya kamashi, akan gado ya kwantar da ita, tare da zama akusa da ita, yana shafa lallausan gashin kanta. Cikin abun da baiwuce 15 minute ba kuwa bacci ya ɗauketa, ganin hakane yasashi ɗan janye jikinsa daga nata, laptop ɗinsa ya jawo, cikin nutsuwa ya soma gudanar da binciken da aka basa, wanda zaiyi akan wani riƙaƙƙen robber, wanda yake ta bawa manyan jami'an tsaro wahala, dan duk yanda suka kai ga ƙwarewa sun kasa kamashi, hakanne yasa suka damƙa aikin ahannunsa, dan sunyi matuƙar yabawa da ƙwazonsa, kasancewar idan yasa aiki agaba, sai ya cimmasa. Yajima yana aikin sosai, sai kusan ƙarfe 12 sannan ya kwanta, bayan yayi nasaran samun duk wani imformation da yake so ya tattara ya turawan shugabansu, abayanta ya kwanta tare da jawota jikinsa, yayi hugging ɗinta, sannu ahankali yake shaƙan daddaɗan ƙamshin jikinta har bacci ya ɗaukesa. 2:00 am, ahankali take ɗan bude idanunta, har ta gama waresu tas, ahankali taɗan zare jikinta daga nasa, tare da tashi zaune, wani irin amai da tashin zuciya na murɗar yunwa ne, suka taso mata, take taji kaman ana sukan ƴaƴan hanjinta, cikin sauri ta diro daga kan gadon, har tanayin tuntuɓe wajen shiga toilet, tana isa bakin sink kuwa ta soma kakarin amai, saida ba komai a cikinta sai aman ruwan takeyi, aman tayi sosai sannan ta wanke bakinta, awahalce ta jingina bayanta da jikin bango, tana meda numfarfashi ahankali, saida ta ɗauki kusan mintuna 10 tana maida numfashi, jin ɗan dama dama yasa ta fito daga cikin toilet ɗin, komawa tayi ta zauna, ai ko wasu mintuna goman ba'a ciki ba, taji sabon amai yasake zuwar mata, nan ma dai toilet ɗin ta shige ta dinga kakari kamar zata amayo da ƴaƴan hanjinta, tana gamawa kuwa ta sake wanko bakinta, saidai kuma tunkan takai ga fita daga toilet ɗin, ta kuma sake sakin wani ama'n. Cikin baccinsa yake jiyo ƙaƙarin amai, tun yanajin abun sama sama, har ya maye jinsa, aɗan zabure ya tashi daga baccin, jiyo sautin aman Zaleeha'n acikin toilet yasashi jawo kekensa cikin sauri ya hau, jikinsa na rawa ya nufi toilet ɗin.
Zuwa lokacin kuwa gaba ɗaya ta galabaita, dan har ta durƙushe akan ƙafafunta, dan kuwa amai ɗinta na uku kenan. Da sauri ya ƙaraso cikin toilet ɗin, hannayensa yasa duka biyu ya ɗagota jikinsa, dai-dai lokacin kuwa wani sabon amai ya sake zuwar mata, saida ta amayar da duk wani abu na cikinta, faɗawa jikinsa tayi tana me fitar da nishin wahala, dan ta jigata ƙwarai, hankalinsa ne yayi matuƙar tashi, tallafo haɓarta yayi, cikin body language ɗinsa yace.
"I'am sorry my happiness, am so sorry, sannu ko kinji, dama baki da lafiya ne? tun yaushe kika fara amai? please tell me what happened dear?." Idanunta wanda sukayi narai narai dasu ta ɗan juya, awahalce tace. "Wayyo Hamma Saif jiri nakeji, sannan inajin kaman zan amayar da ƴaƴan hanjina, please helf me."
Cikin matsanancin tausayinta in boddy language yace.
"Oh My God am sorry kinji, zaki samu sauƙi insha Allah, taso na wanke miki jikinki kinji My Love ɗina, yanzu 2am, da sasssfe zan ƙira Dr. ya dubamin ke." Kanta kawai ta iya jinjina masa, cikin kulawa kuwa ya ɗagota, inda ya wanke mata jiki da kuma bakinta, ɗagota yayi jikinsa kaman ƴar baby, haka suka fito daga bathroom ɗin tana liƙe ajikinsa, jin jikinta da zafi ya sa ya shumfuɗeta akan gado, tare da bin bayanta ya kwanta, acikin jikinsa ya sata, yana me shafa bayanta ahankali, kasancewar yaɗanji jikinta da zafi. Sake lafewa ajikinsa tayi, tare da sakar masa sassanyan kukan shagwaɓa. Jin sheshsheƙan kukan nata ya sashi hugging ɗinta tide, ahankali ya zura harshensa acikin kunnenta yana ɗan lasa. Hakanne yasa tun tan kukan ahankali, har tayi lub ajikinsa, wani wahalallen bacci ne ya ɗauketa, ganin tayi bacci ya sashi shima ɗan lumshe idanunsa.
Ai kuwa baccin nata baiyi nisa ba, wani sabon amai ya sakota gaba, da sauri ta yunƙura ta sauƙa daga kan gadon, saidai tun kafun ma ta ƙarasa toilet ta riga da ta sheƙasa akan tiles.
Hankalin Saifuddeen ne yayi masifar tashi, dan yaga yanda take kwara ama'n, gaba ɗaya babu ƙarfi ajikinta, duk tayi weak, saida ya bari ta gama, sannan ya gyara wajen, ɗaukanta yayi ya maida ita kan gado, zama yayi sannan ya ɗaura kanta akan cinyarsa, sosai yakejin wani irin matsanancin tausayinta.
Itakuwa zuwa yanzu ko ƙarfin kirki bata dashi, hakanne yasa take ta faman sauƙe ajiyar zuciya akai akai, tana kuma ɗan numfasawa awahalce.
Suna nan zaune ahaka har aka ƙira sallan asuba, da ta fara bacci amai zai taso ta gaba, dole kuma saitayi take ɗan samun relief, ganin ta soma bacci ne yasashi janye jikinsa, toilet ya shiga yayi alwala, yana fitowa kuwa jallabiya ya zura ajikinsa, saida yayi kissing ɗin goshinta, sannan ya fice daga cikin ɗakin. Kaitsaye sashin Ummi ya nufa, ba kowa afalon sai sautin A/C dake tashi, ƙarasawa jikin ƙofar Ummin yayi, tare dayi mata knocking, Ummi wanda fitowanta daga toilet kenan ta ɗauro alwala, jin ana buga ƙofar ɗakinta yasa ta ƙarasowa ta bude, ganin Saifuddeen yasa tayi mamaki ƙwarai, dan tasan baya taɓa zuwa gaisheta sai ya dawo daga masallaci, cikin yanayin mamaki tace. "Saifuddeen lafiya kuwa, naganka adai-dai wannan lokacin?." Ɗan shagwaɓe fuskansa yayi, cikin bayyana damuwarsa yace. "Ummi Zaleeha ne bata da lafiya, tun cikin dare take ta amai, gashi jikinta duk ya ɗau zafin zazzaɓi." Idanu Ummi taɗan zaro, cikin jimami tace. "Subahanallah amai kuma? dama bata da lafiya ne?."
Narke fuska yayi akasalance yace.
"A'a Ummi lafiyanta fa ƙalau har muka dawo daga wajen diner." Ɗan jim Ummi tayi tare da cewa.
"To bari nayi sallah sai naje na duba ta ko, amma kafun nan kaƙira Dr. yazo ya duba ta." Kansa ya jinjina, sannan ya juya ya koma cikin falon, wayarsa ya ciro tare da dannawa number'n Dr.Adnan ƙira, ringing biyu kacal Dr.Adnan ya ɗaga wayan. Bayan sun gaisane Saifuddeen ɗin keyi masa bayanin rashin lafiyan Zaleeha'n, cikin tausayawa kuwa Dr.Adnan ɗin yace idan ya idar da sallah zaizo saiya duba ta, da haka sukayi sallama Saifuddeen ɗin ya wuce masallaci. Koda aka idar da sallan baiwani tsaya acikin masallacin ba, dan bayaso yayi nisa da Zaleehan, koda ya koma ɗakin nasa har yanzu tana nan ayanda ya barta, har yanzu kuwa sama sama take fitar da numfashi.
Akusa da ita ya zauna, cikin lallami ya tasheta, ahankali taɗan bude idanunta, kanta ya shafa, cike da soyayyarta ya mata mgna da yarensu. "Sannu ko dear, tashi kiyi sallah kinji, ya jikin naki?."
Kai kawai ta iya gyaɗa masa alaman.
"Da sauƙi." Hannunta ya kama suka wuce bathroom shi ya taimaka mata ta ɗauro alwala, shida kansa kuma ya sa mata hijab ta tada sallah, koda ta idar da sallan jingina kanta tayi ajikinsa, har yanzun dai jiri take ji, ga kanta dake ɗan sarawa, kamo hannunta yayi ya maida ita kan gadon, tare da rufa mata blanket, kallon agogon dake saƙale jikin bangon ɗakin yayi, ganin ƙarfe 5 ɗin asuba, ya sashi sauƙe ajiyar zuciya, dai-dai lokacin kuwa yajiyo knocking ɗin ƙofar falonsu, take kuma wayarsa ta kawo haske alaman shigowar saƙo, koda ya duba saƙon Dr.Adnan ne, inda ya rubuta masa cewa.
"Na iso."
ahankali yake sarrafa wheelchair ɗinsa, har ya fice daga cikin ɗakin, dakansa ya ƙarasa jikin ƙofar falon ya buɗe, ganin Dr Adnan tsaye yasashi ɗan sakin murmushi tare da bashi hannu sukayi musabaha, iso yayiwa Dr.Adnan ɗin har cikin ɗakin nasa, Ƙarasawa jikin gadon Dr.Adnan yayi, anutse ya ƙira sunanta, jin muryan Ya Adnan ɗin yasata ɗan ɗago kanta, kansa yaɗan jinjina cikin kulawa yace.
"Sannu ko, ya jikin naki?." Kanta taɗan jinjina masa alaman da sauƙi, ɗan ƙaramin jakan dake hannunsa ya ajiye, yana ƙoƙarin saka hand clobes ahannunss yace.
"Ina da ina ke miki ciwo?."
awahalce taɗan karyar da wuyanta, murya asanyaye tace.
"Amai da jiri nakeji, sai kuma tashin zuciya da zazzaɓi, gashi bakina duk ba daɗi".
Idanu yaɗan zuba mata, lokaci guda kuma sai ya ɗan saki murmushi, bargon da take rufe dashi yaɗan yaye, hannunta ya kamo tare ɗa ɗaura mata wani abu kaman igiya, ganin ya fito da allura ne yasata rumtse idanunta da ƙarfi tare dasa hannu ta riƙo hannun Hamma Saif ɗin.
Jininta yaja sannan yayi mata wata allura, wanda yasan zata ɗan taimaka mata, dai-dai lokacin Ummi da Raleeya suka shigo cikin ɗakin, amutumce suka gaisa da Dr.Adnan ɗin, nan yace musu zai koma asibiti dan yanaso ya gwada jininta daya ɗiba,
"to" sukace sannan ya fita.
Ummi ne ta ƙaraso jikin gadon, kan Zaleehan ta shafa, cikin kulawa tace. "Ayya Zaleeha sannu kinji, ya jikin naki?."
Jin muryan Ummi ya sa ta buɗe idanunta ashagwaɓe tace.
"Da sauƙi, amma Ummi jiri fa nakeji kuma har da amai".
dagajin yanayin maganan nata kasan ba iya zafin ciwo bane, harda zallan shagwaɓa ne da raki.
Sake shafa
Showing 222001 words to 225000 words out of 237945 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75 Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80