Rahama yayi, tare da ɗaukan wayansa, cikin message ɗin Ummi ya shiga, nan ya nuna mata fuskar wayar, tare da yi mata alaman tambaya, kan cewa.
"Wacece? Ina take?".
Murmushi Adda Rahama tayi masa tare da cewa.
"Miye abun tada hankalinka haka ne Saifuddeen? da ka nutsu ma don amaryar taka ba ɓoyayya bace awajenka kasanta."
Cikin son ƙarin bayani ya zubawa Adda Rahama'n fararen idanunsa.
Duban tsab Adda Rahama tayi masa, kana cikin nutsuwa tace.
"Nasan kasan Ameena ae, wannan nurse ɗin da ta baka kulawa, lokacin da kake jinya a Abuja, kafun ku wuce India, to ita ce dai Ummi ta zaɓa maka, nima kuma nayi na'am don yarinyar akwai hankali, Masha Allah.
Ka tuna har gida tazo itada Mamanta suka dubaka da jiki."

Idanunsa ya zazzaro waje tare da jujjuya kai da ƙarfi sosai yashiga mamaki, lokaci ɗaya yaji kaman an watsa masa ruwan zafi, amamakance ya ɗan ƙanƙance idanunsa, cikin yanayin maganarsa wanda ya saba, wato body language yace.
"Allah ya sauwaƙe ni dai na auri wannan Ameenan, mezanyi da ita bazawara ce fa!."
Cikin tsananin mamaki Adda Rahama ta dubeshi,  kallonsa tayi da kyau tare da faɗin.
"Kai Saifuddeen banda sharri bazawara kuma? wa ya faɗa maka cewar bazawara ce?".
Murmushin gefen baki yayi, tare da jijjiga kansa, in a body language ɗinsa yace.
"Impossible!, nine zan auri bazawara? chab hmmm Allah ma ya sauwaƙe, sam banason sauran wani wlh Allah ya kiyasheni suɗe ƙashin da wani ya rigani tsotsa."
Baki Adda Rahama ta buɗe fuska cike da tarin mamaki sauƙe a jiyan zuciya tayi tare da cewa.
"Wai nikam wayace dakai itaɗin bazawara ce?."
A shagwaɓe ya rubutawa Addan nasa.
"Ae basai an faɗa min ba, duk ckekken Namiji in dai ya nitsu idan mace bazawara ce zai gane ta ido, kuma nayi imani cewa Ameena bazawara ce, saboda haka ni dai bana sonta wlh bazan iyaba, ba kuma zan aure ta ba."
Ahmad da Ishaq kam dariya sukeyi sosai fahimtar abinda yake faɗin.
Baki Adda Rahama ta taɓe, inda ta gyara zamanta, dubansa tayi da kyau,ido cikin ido tace.
"Naji koma dai bazawara ce, ita Ummi ta zaɓa maka a matsayin mata, sannan da kake ta maganar cewa, ita bazawara ce, kai ɗin dakake magana saurayi ne kai? inace kaima bazawarinne tunda dai kayi aure."
Bakinsa ya turo gaba, a shagwaɓe ya narke fuska, cikin body language yace.
"Wallahi ni banason Ameena, yarinyar da idanunta abuɗe suke, ta fa riga da tasan Namiji, sannan kuma har yanzu ni matashin saurayi ne, tayaya ma zan yarda na auri Ameena."
Duban Adda Rahaman yayi tare da kamo hannunta, cikin yanayin daya saba musu alaman magana yace.
"Kin sanni tun ina ƙaramin yarona ma ko ta yaya bana amfani da tsohon abu, hatta kaya idan ya kasance gwanjo ne bana sawa, sannan idan yakasance wani ya taɓa amfani da abu, bana kuma amfani da abun, a iyaka tsawon rayuwata nafison komai sabo, koda wajen zama ne nafison sabo, banason wanda wani ya taɓa amfani dashi, harta mota ko wayar hannu, ban taɓa sayan second ba, komai na nafison yakasance sabo, ko lokacin da nake makaranta, ko yaushe ni nake zuwa first a acikin aji, bana taɓa yarda nazo second akomai na, to me yasa yanzu zan yarda na auri mace second hand? sauran wani, wanda wani ya cakalkala ya bari, ragowar wani fa Adda tunda nake gidannane kawai nataɓa sayan abu second hand kuma kin san shima saida na sabunta mana shi, bazan iya auren sauran waniba kinfa san inada kishi."
Kansa ya girgiza tare da cije laɓɓansa.
Baki buɗe Adda Rahama ke kallonsa, sosai take mamakin ƙarfin hali irin na Saifuddeen ɗin.
Shikuwa Ahmad da shaq dake gefe sai ƙyalƙyala dariya suke tayi, don sosai show ɗin na Saifuddeen keyi musu daɗi.
Ajiyar zuciya Adda Rahama ta sauƙe tare da cewa.
"Koma menene dai Ummi ta gama magana, kuma ta yanke hukunci, wanda mu dukan mu mun gamsu, ta kuma ce zata sanar wa Bappa Ali, don asamu ayi bikin cikin gajeren lokaci, kaman yanda Baba Malam ya buƙata, kai da za'ayi maka auren gata ma, miye na damun kanka, sadaki, kayan aure, komai da komai, duk fa Baban Zaleeha yace ya ɗauke ma, wannan kaɗai bai isa saka farinciki ba, auren huce haushi fa zaiyi maka."
Jan kujeransa baya yayi, inda ya kwaɓe fuska, nan ya dubi Ahmad yace dashi.
"Su tafi." kana ya ja hannun ishaq
Shidai Ahmad dariya kawai yake, har hakan yaso ƙular da Saifuddeen.
Haka dai suka dawo gida, bayan sun sauƙe ishaq ko amota Saifuddeen fuskar nan tasa aɗaure take tamau.
Suna isowa gida, kai tsaye part ɗin Ummi ya sake komawa.
Ganinsa yasa Ummi kafesa da ido, cikin sanya fuskar tausayi, yayiwa Ummi alaman cewa.
"Shi bayason Ameena, saboda bazawara ce, sannan kuma shi tsoronta ma ya keji, gata da kallon tsiya, sai kace mayya, gaba ɗaya idanunta abuɗe suke."

Dubansa Ummi tayi, tare dayin dariyar zuci batayi mamakin jin cewa Ameenan bazawara bace, saboda kafun isowarsu Adda Rahama ta kirata tasanar mata.
gyara tsayuwa tayi tare da cewa.
"Allah mai iko, yau kuma Saifuddeen  kai ne me tsoron mace? uhmm saboda bakason auren ta  shiyasa kake tsoronta ko?"

Sake shagwaɓe fuska yayi, duk yanda yaso Ummi ta fahimce sa, ƙiyawa tayi, daga ƙarshe ma juyawa tayi ta koma cikin ɗaki.
Ganin haka yasashi komawa part ɗinsa, ransa duk ba daɗi, wani haushin Ameenan nema duk ya cika masa zuciya, wannan rana haka dai yayi bacci zuciyarsa duk ba dadi.

Washegari.

Yana gamayin break fast ya shirya kansa, inda ya ɗauki Sule driver suka nufi gidan su Ishaq, don tun adaren jiya ya tsara cewa zai je yasamu Dirankaɗi da maganar, wato Baban Ishaq kenan."
Koda yaje Ishaq ne yayi masa jagora zuwa falon mahaifin nasa,  bayan sun gaisane Saifuddeen yayi masa bayanin duk wani abun daya kawosa, ta hanyar yi masa rubutu a laptop ɗinsa.
Koda Dirankaɗi ya karanta murmushi yayi tare da duban Saifuddeen ɗin.
Cikin son basa ƙarfin guiwa yace.
"Tayaya kake tunanin cewa, bazaka iya auran mata biyu ba? Kai jarumi ne Saifuddeen, saboda haka kada kasa wani damuwa aranka zaka iya."
Nan fa Saifuddeen ya tubure masa kan cewar lallai shi bazai iya ba, ganin haka yasa Dirankaɗi ɗaukar wayarsa, inda ya ƙira Bappa Ali, shi kuma Ishaq dariyan Saifuddeen ɗin kawai yake.
Gaba ɗaya abun da Saifuddeen ɗin ya faɗa, shi Dirankaɗi ya maidawa Bappa Ali, nan Bappa Ali yace da Dirankaɗi, ya faɗawa Saifuddeen ɗin, aure babu fashi, tunda Baba Malam da kansa ya yanke hukunci.
Koda Dirankaɗi ya faɗawa Saifuddeen ɗin, take yace.
"To Baba nifa banida kuɗin auren ma in da ba sadakanta iyayenta zasuyi ba".
Nan Dirankaɗi da Ishaq suka saka dariya, dubansa Dirankaɗi yayi tare da cewa.
"Ae dama ba kaine zaka sayi komai na auren ba, auren gata za'ayi maka ae."
Haka duk yanda Saifuddeen yaso ya kaucewa auren, Dirankaɗi da Bappa Ali sunƙi basa dama, dama shi Baba Malam baisan wainar da ake toyawa ba.
Dole haka Saifuddeen ya dawo gida, zuciyarsa cike da tunani kala-kala.

Haka akayi ta kai ruwa rana da Saifuddeen inda yaketa cemusu wai aifa Dr yace bazai iya zama da mata biyuba, Ya Adnan kuma yace a a ba wani Dr daya faɗi hakan.

Ɓangaren Baba Malam kuwa, tuni ya turawa Yaya Ahmad kuɗi, kan cewar ya bawa Aunty Lubna ta shiga cikin shoprite na Abuja, tayi musu sayayyan kayan lefe,  wanda za'aiwa Saifuddeen sabon aure dashi.
Yaya Ahmad  ne yace da Baba Malam ya amshi kuɗinsa,  shi zai haɗa lefen da kansa,  nan Baba Malam yace "a'a so yake komai na auren yayi da guminsa, da kuma haƙƙinsa, don ya ƙudurta aransa cewa, auren huce haushi da kuma gata zai yiwa Saifuddeen ɗin."

Can ɓangaren Zaleeha kuwa, rayuwarta mai sauƙi take gudanarwa acan garin na Numan, zuwa yanzu bata da wani abinci sai kayan fruits,  dangin su apples da kuma ayaba, goiba dabina sai su water meloon, acikin ƴan kwanki kaɗan ɗin, tuni abubuwa da yawa sun sau ya mata, zuwa yanzu abu biyu ne ke damunta, wato tana jin can ƙasan zuciyarta bata son gudowan da tayi tana kewan kowa hatta su Ummi tana kewansu, ji take kamar ta koma amman da zaran ta tuna ta koma ɗin sai taji kanta yana juyawa sai taji ta gigice lokaci ɗaya taji kamar an ɗaure mata zuciyarta.

Sai kuma nata soyayyar mutumin da har yanzu takasa sake sanyashi acikin idanunta, sosai soyayyarsa ke ƙara ninkuwa acikin zuciyarta, dashi take kwana kana dashi kuma take tashi, yayi mata tsaye acikin rai.

Yanzu ma zaune take akan katifarta, laptop ɗinta ne agabanta, inda ta saka earpiece akunnenta, wani series film take kallo acikin laptop ɗin nata, don tahakane take samun rage kewa, wayarta dake gefe ne ta soma ƙara alamar shigowar ƙira, sunan Balkeesu ne ke yawo akan screen ɗin wayar, saida ta kusa katsewa ta ɗauka tare da kara wayar akan kunnenta.
Daga can ɓangaren Balkeesu tace.
"Mutanen ƙauye."
Baki Zaleeha ta taɓe tare da faɗin.
"Ya akayi ne."
Balkeesu kuwa dariyar dake cinta arai ta danne tare da faɗin.
"Lafiya lau, ya kike kwana biyu ina ƙiran number ki baya tafiya."
Ajiyar zuciya Zaleeha ta sauƙe, cikin halin rashin kulawa tace.
"Maybe matsalan network ne."
Dariya Balkeesu tayi inda cikin zuciyarta tace.
"Ko kuma matsalan wuta ba." Afili kuwa cewa tayi.
"Dama Rabeel ne yace nayi miki magana, yana ta ƙiran wayarki amma bakya ɗauka, sannan yayi miki text duk babu reply, meyasa bazaki ɗauki wayarsa ba, ko kin manta cewar abokin aikin ki ne?."
Baki Zaleeha ta taɓe tare da cewa.
"Tayaya kike tunanin zan ɗaga ƙiransa, halan ya manta cewar ina da aure ne? igiyoyin auren wani ne fa akaina, to me yasa zan ɓata lokacina nakuma ɗaukarwa kaina zunubi wajen magan, da Rabeel wanda kuma bai zama lalle dole sai munyi magana ba."

Hararan wayar Balkeesu tayi, kamar Zaleehan na ganinta, taɓe baki tayi tare da faɗin.
"Uhummm su aure manya, dama naƙira ne kawai don naji ykk, da kuma dalilin ƙin ɗaga wayar Rabeel da kikayi."
Ɗan jim Zaleeha tayi tare da cewa.
"Bani da wani dalili naƙin ɗaga wayarsa sai na darajar auren dake kaina, kuma ma koda zai ƙira sau 100 bazan ɗaga wayarsa ba, saboda ina da aure, kuma shi ba muharrami na bane babu yadda za'ayi nayi magana dashi ina matar aure."
"Okay." Balkeesu ta faɗa ataƙaice tare da kashe ƙiran,
ita so take taga rayuwar Zaleeha tazama lalatacciya ta yadda zata samu damar maye gurbinta a ma'aikarsu da kuma gidan Saifuddeen, amman ta kaicinta ɗaya Zaleeha nada riƙo da mutuncinta na ɗiyamace musulma tana kare budurcinta da lallaɓashi tamkar ranta ga ibada.

Ita kuwa Zaleeha aje wayar tayi tare da maida hankalinta akan laptop ɗinta.

Itan kuwa Balkeesu tana kashe wayan, ta saki dariyan mugunta, inda a fili tace.
"Ko ahaka aka tsaya awasan nasamu kaɗan daga cikin abun danakeso tunda ko yanzu shirinki na mushaƙata ya dawo hannuna."

Can ɓangaren su Baba Malam kuwa, gaba ɗaya sun fita daga sha'anin Zaleeha, ko zancenta ma Baba Malam baiso ayi masa.
Maryam kuwa sosai take cikin damuwa, domin kullum da tunanin ƴan uwa da kuma mahaifiyarta take wuni, ganin yanda ta damu sosai ne, yasa Ya Ameenu ɗaukan ta ya kaita wajen Baba Malam, nan Baba Malam yayi mata kalamai irin na mahaifa masu kwantar da zuciya, tare da sa mata al'barka, hakan kuwa yasa zuciyarta ta saki, kaɗan daga cikin damuwarta ya kau.

Rayuwar Mama a Ɓilliri kuwa abun yazo mata cikin wani irin yanayi, komai ba yayi mata daɗi, zaman takura kawai takeyi agarin nasu, yayinda Zahira kuwa kullum bata da wani aiki, sai ƙworafi da mita, kan cewar ita lallai saida Maman ta maida ita gida, ita kuwa Mama har yanzu gani take kamar Baba Malam ɗin zai sauƙo yace su dawo gidan, don tasawa kanta aƙidar cewa bazata taɓa ƙiransa ta basa haƙuri ba, har sai shida kansa ya gaji yace su dawo.
To gatanan dai rayuwar batayi mata daɗi, abinci ma bata samun wanda takeso, gaba ɗaya komai yayi mata duhu, badon komai ba kuwa saidan tana rayuwa acikin mutanen da gabansu da kuma bayansu duk duhu ne, basa ɗauke da haske ko kaɗan, zaman Ɓillirin sam baya yi mata daɗi Babanta kuwa duk da kafurine yaga rashin kyauta warta, shiyasa ya tsananta mata yace gata ga ƙauyen ta zauna kuma damuna na dawowa noma zatayi, Zahiri kuwa ji take kamar a rami take gida ba wuta bare fanka ko AC ba Radio bare tv babu firij bare kayan more rayuwa babu gado bare lafiyayyan katifa babu ƙamshin komai sai warin burkutu, rayuwa dai ta masu tsamari gashi ita Zahira an katse mata karatu ta. Ruda kuwa Addan Mama daɗi hakan taji dan ko yanzu ta samu sun zama dai-dai da ƙanwar tata, itama ta wahalan dai.

Bayan Kwana Uku, da turawa Ya Ahmad kuɗin lefe, Baba Malam da kansa ya kimtsa, inda ya tsara tafiyarsu Abuja, shi da Dirankaɗi, da kuma Bappa Ali, yayinda za suje nemawa Saifuddeen auren Ameena, Alhaji Naseer Maichanji shine mariƙi ga Ameena, wanda yake ɗan kasuwa ne sosai, hakan yasa mafi yawancin mutane sun sanshi, koda zasuyi tafiyar tasu ta yanzun da expriance ɗinsu zasu tafi, kasancewar Dirankaɗi yasan Alhaji Naseer wanda a binciken da Dr Adnan yayi akan Amina a wurin Dr Aliyu ne sukaji komai na Amina.
ananne Dirankadi ya gane ɗiyar tsohon abokin kasuwancishi shiɗin, har ma number'n wayarsa yana dashi, domin sun sha haɗa busineess dashi Alhaji Naseer ɗin tun shekarun baya.
To kuma bisa jagorancin Dirankadin zasuyi tafiyar da tuni sun sanarwa Alhaji Nasir Daddy kenan zuwan nasu.

Ɓangaren Saifuddeen kuwa shi har yanzu ganin abun yake, kamar almara, musamman idan ya tuna da cewar.
"Ameena ɗin bazawara ce." Sai yaji sam shi bazai iya mu'amala da ita ba.

Ƙarfe 10 na safiya dai-dai jirgin da zai ɗaga zuwa Abuja, ya kwashi su Baba Malam da Bappa Ali. Inda suka tafi da niyar cewa bazasu dawo nan Gombe ba sai an tsaida lokaci da kuma ranan aure, don suna sa ran cewa.
"Insha Allah Alhaji Naseer ɗin bazai hanasu ɗiyarsa ba."

Sun isa garin Abuja lafiya, inda Ya Ahmad da kansa yaje ɗauko su a airport, nan fa dukansu suka shiga motar, kaitsaye unguwar Asokoro suka nufa, wanda anan gidan su Ameena yake.

Yayinda duk abinda akeyi Amina bata da labari.

Maigadi ne ya wangale musu gate ɗin gidan, nan cikin parking space ɗin gidan Ya Ahmad yayi parking, dai-dai lokacin wani ɗan Dattijon mutumi me cike da kamala, wanda yasha adonsa cikin manyan kaya, yafito daga cikin wata ƙofa, ganinsu da yayi yasa ya nufosu cikin sauri, fuskarsa ɗauke da fara'a ya miƙa musu hannu, nan suka shiga gaisawa cikin mutunta juna, kai tsaye yayi musu jagora zuwa ɓangarensa, wani babban falo ne mai kyau, inda anan yake tarban baƙinsa masu mahimmanci.
Zama sukayi, tare da sake sabon gaisuwa.
Duban Dirankaɗi Alhaji Naseer yayi tare da cewa.
"Alhaji Ma'aruf ashe rai kan ga rai?."
Murmushin manya Dirankaɗi yayi tare da cewa.

"Ƙwarai kuwa Alhaji Naseer, gashi bayan lokaci mai tsawo da muka ɗauka gashi kuma mun sake haɗuwa."

Shima Alhaji Naseer ɗin murmishi yayi tare da cewa.
"Allah Mai iko, gashi kuwa harda Malam Bashir Sulaiman Dukku kuka zo, a gaskiya yau gidana yana ɗauke da manya manyan baƙi, masha Allah sannunku da zuwa."
ya ƙarishe maganar yana miƙawa Baffa Ali hannu

Dai dai lokacin masu aiki suka shigo, nan suka cika musu gaba da kayan ciye ciye harma da dangin su snacks.

Drinks ɗin kaɗai suka ɗan taɓa, nan Baba Malam da kansa ya gyara zama, duban Alhaji Naseer yayi tare da cewa.
"Nasan zakayi mamakin ganinmu, to amma ance wanda yake da buƙata shi yake zuwa, ko ba haka ba?."
Nan dukansu suka jinjina kai, inda Alhaji Naseer yace.
"Ƙwarai haka ne."
Ajiyar zuciya Baba Malam ya sauƙe tare da cewa.
"To kamar dai yanda ka ganmu dukan mu nan al'khairi ne ya kawo mu, dan kuwa munzo newa ɗan mu auren ɗiyar ka Ameena, muna fatan Allah yasa ba ai mata miji ba."

Ajiyar zuciya Alhaji Naseer ya sauƙe, tare da ɗan numfasawa, cikin murna haɗi da farin cikin ganin manyan malamai sunzo neman haɗa zuriya dashi a hankali yace.
"Masha Allah, Haƙiƙa naji daɗin wannan zancen naku ƙwarai, sannan kuma ba aiwa Ameena miji ba, saidai kuma bazan ɓoye muku ba, magana ta gaskiya banine mahaifin Ameena ba, nine dai mariƙinta, dani da mahaifinta kuwa uwa ɗaya uba ɗaya muke, sannan kuma magana ta biyu dai ita ce, Ameena ba budurwa bace, bazawara ce, don kuwa ta taɓa aure, ta auri ɗan wajena Amir, sai-dai kuma da yake Allah bai tsara zamansu tare ba, sati ɗaya kacal auren yayi Allah ya kawo ƙarshensa, sannan ahalin yanzu dai babu wani wanda ta tsayar mazaunin wanda zata aura."

Ajiyar zuciya suka sauƙe su dukansu, cikin gamsuwa Baba Malam ya gyara zama, inda ya fuskanci Alhaji Naseer, cikin yanayin dattako yace.
"Alhamdulillah, duk da kafun muzo bamusan da wannan magana ba, koda muka jita yanzu kuwa bazaisa mu fasa niya da kuma ƙudurin dake ranmu ba, saidai kuma muma zamu faɗa muku cewar ɗan mu na ɗauke da laluri, wanda idan akayi dubida ƙaddara ce wanda zata iya hawa kan kowa, sannan kuma duk cikinmun nan babu wanda baisan cewa, Lafiya da rashinta duk na Allah bane, sannan shike sawa bawa cuta, kuma shike yaye masa, sannan lalurar da ɗan mu kedashi, bai tauyesa daga zama cikakken ɗa namiji ba, domin yana da lafiyar da zai iya kusantar mace, sannan yana da wadatar da zai iya zama da mace, saboda haka muna fatan hakan bazaisa ku hanamu ƴarku ba, saboda shi aure nufi ne na Allah, matar mutum kuma ance kabarinsa."

Bappa Ali ne ya gyara zama tare da soma yiwa Alhaji Naseer ƙarin bayani, dan gane da larurar Saifuddeen ɗin, bai ɓoye masa komai ba, ya fayyace masa komai yanda zai fahimta.

Jinjina kai Alhaji Naseer yayi tare da cewa.
"Nafahimce ku, ƙwarai kuma ai nakasa ba kasawa bace, kana nakasashshe zai iyayin abun da wani mai lafiyan ma bai iyawa, tabbas kuma idan na fahimta kune iyayen Saifuddeen ko?."
Cikin Mamaki suka kalli juna, Dirankaɗi ne yace.
"Ƙwarai kuwa, amma dama kasan Saifuddeen ɗinne?"
Murmushi Alhaji Naseer yayi inda yace.

"Ƙwarai kuwa, ai sanadiyar ita Ameenan nasanshi, don ita ta kula dashi lokacin da yayi jinya anan, sannan kuma koda suka koma india, danaje wani business ɗina naje har New Delhi na dubasa, gaskiya ni kaina na yarda da ƙwazon sa, don dagani matashi ne mai tsayayyar
Showing 54001 words to 57000 words out of 237945 words