kiyi salla lokaci yayi kar kije ki tasashi gaba kuyita dariya."
Kai ta jinjina kana a hankali tace.
"Uhum Hamma Saif".
Ido ya zuba mata dan duk duniya ita ɗaya yaji tana kiranshi da wannan sunan".
Ganin tayi shirune ya sashi ɗaga mata hannu alamun lfy dai ko?
Cikin inda-inda tace.
"Uhum dama gobene za'ayi sadakan bakwai ɗin Adda Maryam to kuma ina son zuwa in ka amince ka yerje min?".
Karo na forko kenan da Zaleeha ta nemi izininshi akan abu, shiyasa yaji kanshi tamkar wani sarki,
ita kuwa ganin yayi shirune yasa ta rumtse idanunta da suka cika da hawaye,
Cikin sanyi tace.
"Dan Allah kayi haƙuri, ka bani izinin zuwa inaso inje inga ƴan uwana".
Kanshi ya jinjina mata alamun
"Allah ya kaimu".
Cikin jin daɗi tace Amin Amin kana ta sunkuyo ta karɓi Adeel sannan ta wuce tayi ciki, shi kuma ya wuce ya nufi ƙofar gida.

Amina kuwa dake tsaye bakin falon Ummin ta cika tayi fam tuni sheiɗan ya shiga ingizata, sunkuyowan da Zaleeha tayi ta bashi Adeel ɗin nan sai takega kamar, sumbatar ta Saifuddeen yayi, hakan kuma sheiɗan ya raya mata.
"To ai dai duk iyayinta yau dai kam girkinkine, tunda taci kwana biyunta ai sai ta bar miki mijinki yau kam".
Wani irin kishi da tsanar Zaleeha ne suka cika mata ciki da zuciya.
gaba ɗaya ta hautsine a haka ta nufi side ɗinta dan yin sallan magriba.

Koda sukaci abincin dere suka ɗanyi hira,
ganin yadda Ameena ke watsa mishi harara ya sashi sanin lallai yau akwai aiki,


A can gidan Baba malam kuwa,
Ziyada ne ke zaune gaban Baba Malam a cikin falonshi sai ya Ahmad da Malam Adam , da kuma ya Ameenu,
shiru sukayi baki ɗayansu,
cikin tattausan lafazi Baba Malam ya kira Ziyada.
"Ziyada".
Cikin nitsuwarta irin ta Adda Maryam tace.
"Na'am".
A hankali yace.
"Wata al'farma nake nema a wurinki in Allah yasa kin amince zanji daɗin hakan,
Amman fa bawai umarni nake bakiba al'farmace nake nema".
Ɗago kanta tayi wanda ida nunta tuni sun cika da kwalla cikin sanyin murya tace.
"Baba malam al'farma kuma?".
Kai ya gyaɗa mata alamar eh,
da sauri tace.
"A a baba ka bani umarni kawai, ko wanne irine zan bishi domin nasan bazaka sani yin abinda ya saɓawa shariya ba".
Cikin jin daɗi ya fuskaceta da kyau, murya a tausashe yace.
"Ga ɗan uwanki Ameenu mijin yayarki Maryam, ko zaki amince in aura masa ke in mishi madadin Maryam dake? Kije ki zauna ki raini ɗan ƴar uwarki?."
Kai ta sunkuyar hawaye na zuba murya na rawa tace.
"Na amince Baba Malam na yarda in dai Ya Ameenu ya amince nima na amince".
Wani irin sassanyan ajiyan zuciya Baba Malam ya sauƙe,
Ya Ameenu kuwa ido ya zuba wa Baba Malam cikin tsananin mamaki da kaɗuwa,
Ya Ahmad da Malam Adam kuwa sosai sukaji daɗin wannan batun.
Shiru ya Ameenu yayi jin Baba Malam na ce mishi.
"Ameenu ga Ziyada na baka ita, gobe da asuba in sha Allah za'a ɗaura muku aure in ka amince ta koma ɗakin ƴar uwarta".
Kai ya jinjina hawaye na zuba yace.
"Nagode Baba Malam Allah ya saka da al'khairi ya jiƙan Maryam".
Amin Amin sukace baki ɗayansu kana Baba Malam yace Ziyada ta tafi cikin gida.

Nan suka ajiye batun ɗaura auren gobe da asuba.


Ƙarfe tara dai-dai Mamy ta shigo falon Mama ta sanar mata kiran Baba Malam, wanda tunda ta dawo gidan bai kulata ba,
Don tuni ya dai-dai ta larin aurenshi da ita.

Jiki a mace ta nufi side ɗinshi.
Ganin baya falo ne yasa tayi sallama a bakin ƙofar bedroom ɗin shi,
A hankali yace mata.
" Wa alaikissalam,shigo".
Jiki da zuciyarta cike da kunya da nadama da dana sani ta shigo.
Gefen ta zauna cikin zubda hawaye tace.
"Gani". Ido ya zuba mata domin gaba ɗaya ta zama wata jibiri-jibiri ta zama abar tausayi.
kanshi ya kawar tare da cewa.
"Batun auren Ziyada da Ameenu na haɗa kuma duk sun amince, gobe da asuba za'a ɗaura auren me kikace a kai".
Cikin sanyin murya da nadama tace.
"Allah ya sanya al'khairi ya basu zaman lfy, ya kuma jiƙan Maryam da Rahma".
Cikin mmki da tsananin jin daɗi yace.
"Amin Amin,kin amince kenan ba fitina da masifa?".
Cikin jin kunya tace.
"Eh".
Gyara zamanshi yayi tare da cewa.
"To sai kuma batun yayarki Ruda, bana son zuwanta gidana".
Da sauri tace.
"Nima nace mata bana so".
Kanshi ya jinjina tare da cewa.
"To Allah ya kyauta ya shirya min ke".
Amin Amin tace cikin jin kunya,
kana ta miƙa zata fita,
jin ya kamo hannunta ne yasa ta koma gareshi.


Ƙarfe goma duk suka watse kowa yayi side ɗinshi,
Koda ya gama shirin baccinsa, a tsastsaye ya leƙa Zaleeha yayi mata saida safe dan tunima ita ta fara bacci ji shine yasa ta ɗan ɗago ta kalleshi ganin ta zarro mishi ido alamun mmki ne yashi mata alamun ta konta saida safe.
Yana fita ta meda kanta ta konta taci gaba da baccinta.


11 dai-dai Saifuddeen ya shiga ɗauki Ameena, hasken wayarshi ya kunna dan tuni ta kashe wutan ɗakin dan bata da niyar zuwa ɗakinshi.
kan gadon ya hau ya konta tare da sa hannu ya ɗauki Adeel ya maidashi kan gadon shi dake kusa da nasun.
Matsowa jikinta yayi tare dasa hannunshin ya juyata suna fuskantar juna.
Da sauri ta sake komawa ta juya ta bashi baya....!






By
*GARKUWAR FULANI*
10/4/20, 7:04 PM - Mmn Khalid: Ngs,eɗɗ Sake ɗan mirgino ta yayi, tare da sanya hannunsa ya kama waist ɗinta, da sauri ta ja baya, tare da ɗauke hannunsa daga jikinta, fushi takeyi sosai dashi, saboda haka batajin zata iya biye masa awannan daren.
Asanyaye ya kuma kai hannunsa yana ƙoƙarin cire mata rigar baccin dake jikinta, ƙanƙame jikinta waje ɗaya tayi, tare da riƙe rigartata, fuska ta haɗe sosai tare da ɗan girgiza masa kai alaman bataso. Hannunsa ya zare daga jikinta, tare da zubawa bayanta idanu, dan dama ta bashi baya ne,
shi kam yarasa meke damun Ameenan kwana biyu, yasan duk bai wuce zafin kishi ba.
Ɗan lumshe idanunsa yayi, tare da gyara kwanciyarsa, cikin ransa yace.
"Bazan taɓa takura miki ba, zanjira harsai kinyi ra'ayi dan kanki." Ameena kuwa ranta ne keta ƙuna, baki kawai take ta cijewa, da ace kuka zaizo mata ma da tayi, ko zata ɗanji salama acikin ranta da zaran ta rufe idonta sai taga lokacin da Zaleeha ta sunkuyo kanshi dan bashi Adeel ita kuwa a zatonta kissing ɗinta yayi.
Suna ahaka bacci ya ɗaukesu dukansu. Washegari kuwa da sassafe ta wuce wajen aiki, ko gaisuwa ma, haka tayi masa fuskarta babu wata cikakkekiyar fara'a.
Shidai idanu kawai ya zuba mata, dan yasan fushin nata na babu gaira babu dalili ne.
Zaleeha kuwa ita da Raleeya sukayi komai na breakfast, kusan atare suka yi break fast ɗin inbanda Ameena da tatafi wajen aiki.
Suna kammalawa kuwa, Zaleeha ɗaki ta wuce ta kwanta, dan anjima kaɗan ne tafiyarsu gidan Baba Malam. Saifuddeen kuwa anan falon Ummi suka zauna shida su Hayatuddeen yana ƙoƙƙofanshi kan sabon abokinshi da tuni ya dasa mishi ayar tambaya, kuma tuni ya liƙa bincikansa kan wayar ƙanin nashi.
hira sukayi sosai, kasancewar yau ɗin jumma'a ne yasa dukansu ba da wuri zasu fita ba, Hayatuddeen kamma sai kusan ƙarfe 11 yake da lecture, nan ma kafin ƙarfe 2 zai dawo bawai wani jimawa zaiyi ba. Ƙarfe 12 Zaleehan ta dawo sashin Ummi, dan ɗaura abincin rana, zuwa lokacin kuwa su Saifuddeen din basa falon, kowa yayi ɓangarensa, dan shirin masallaci, ita da Raleeya ne sukayi lunch ɗin, sannan suka juye acikin manya manyan food flasks.
Koda suka kammala ɗaƙi ta koma, inda tayi wanka, tare da ɗauro alwala'n sallan azahar tana tunanin zaman gidan na mata yawa da zata samu dai a barta ta koma aikinta, to amman ta inama zata fara maganar.

Can ɓangaren Saifuddeen kuwa, kwalliya yasha cikin wata haɗaɗɗiyar shadda ƴar mita me kyaun gaske, wacce take da kalan dark greeen, sosai tayi masa kyau, ga kuma hulan zanna bukar daya kafa akansa, wani tsadadden agogo ya ɗaura atsintsiyar hannunsa, sosai yayi kyau, yayinda sajen fuskarsa ta kwanta lub-lub, turare ya fesa, wayansa kaɗai ya ɗauka, sannan ya fice daga cikin ɗakin, bayan yasawa ƙafansa takalma flat shoe irin na maza me tsadan gaske.
Anan compound ɗin gidan ya haɗu da Ahmad wanda ya jiƙu da ƙyau shima cikin shigar shadda milk colour, atare suka wuce masallaci. Zaleeha kuwa koda ta fito daga wankan sama sama taɗan shafa lotion ajikinta, wata haɗaɗɗiyar powder ta shafa akan fuskarta, wanda tayi mata kyau sosai, kajol da kuma lipstick kawai ta shafa, bata wani cika kwalliya akan fuskar tata ba, wani haɗaɗɗen riga da sket na atamfa tasanya ajikinta, sket ɗin irin pieces ɗinnan ne, yayinda rigar kuwa ta kasance fitted, sosai kayan sukai mata kyau, kasancewar atamfar nada kalan ja ajiki, yasa ta yafa wani haɗaɗɗen mayafi me kalan ja, wani ɗan hill ta sanya aƙafanta me masifar kyau, waya da kuma ɗan jakanta ta ɗauka, tayi kyau matuƙa sai faman baza ƙamshi take, kallon kanta taɗanyi amadubi ta numfashi ta ɗan sauƙe ita kanta taga ramarta.
Juyawa tayi cikin nutsuwa, ta fice daga ɗakin nata, kai tsaye sashin Ummi ta nufa, zuwa lokacin kuwa har sun dawo daga masallaci.
Saida Numfashinsa yakusan ɗaukewa alokacin daya ganta, tayi masifar kyau, gashi skin ɗinta ya ƙara haske. Ummi ne tayi musu fatan al'khairi da kuma adawo lafiya, sannan suka fita, yana gaba yana me sarrafa wheelchair ɗinsa, ita kuma tana biye dashi abaya.
Haka suka ƙaraso har wajen mota, Sule driver ne ya buɗe musu motar cikin hanzari suka shiga. Anan gidan baya suka zauna.
Cikin nutsuwa kuwa Sule driver ke tafiya dasu, gaba ɗaya daddaɗan ƙamshin turarensu ne ya cika cikin motar, hakan kuwa ya bada wani irin yanayi me daɗi.
Ɗan lumshe idanunta tayi tare da jingina bayanta da jikin kujera, shikuwa Saifuddeen wani aiki yake shiyasa gaba ɗaya hankalinsa nakan wayarsa ƙiran Samsung S20.
Ahaka suka isa gidan Baba Malam ɗin, jin tsayuwar motar ne yasa duk suka ɗago idanunsu, wani ajiyar zuciya Zaleeha ta sauƙe, sannan ta buɗe murfin motar ta fito, Saifuddeen kuwa Sule driver ne ya buɗe masa murfin motar ya fito, bayan ya ware masa wheelchair ɗinsa. Kusan atare suka jera, sashin Baba Malam ɗin suka nufa.
Zaleehan ce tafara tura ƙofar falon ta shiga bakinta ɗauke da sallama.
Baba Malam, da kuma su Mamy sai Ya Ahmad da kuma Ya Ameenu ne zaune afalon, can gefe kuwa wasu ayarin mutane ne wanda aƙalla zasu kai su 15, Ciki kuwa hadda Uncle Solomon da kuma matarsa Elizabet, ga kuma Baffa wato baban Aisha.
Cike da mamaki Zaleeha ta ƙaraso cikin falon tana ɗan rarraba idanunta, ganin Baffa yasa tace.
"Laa Baffa kaine agarinmu?"
ɗan murmushi Baffan yayi tare da cewa. "Ƙwarai kuwa ƴata nice." Nan ta durƙusa har ƙasa ta gaishesa, sannan ta gaishe dasu Baba Malam, wannan karon kam har Ya Ameenu ta gaisar kuma ya amsa mata.
Ƙarasowan Saifuddeen cikin falon ne yasa, Baba Malam faɗaɗa fara'ar dake kan fuskarsa, cikin kulawa haɗi da mutuntawa ya tarɓi Saifuddeen ɗin. Cikin girmamawa kuwa Saifuddeen ɗin ya gaishe dasu Baba Malam ɗin, harma da Baffa'n Aisha. Haka Baffan Aisha ya amsa fuska asake yana yabawa da kyau haɗi da kwarjinin yaron. Anutse kuwa Saifuddeen ya gaishe dasu Mamy da kuma Mama.
Fuska asake duka suka amsa masa, Mama kam sai faman sunne kai take, dan kunyar Saifuddeen ɗin takeji, uwa uba kuma kwarjinin da yake dashi. Zaleeha kuwa bayan ta gaishe dasu Mama, kusa da Ya Ahmad ɗinta taje ta zauna, zuciyarta fari tas, wani irin dadi takeji, musamman ma da take hango fariniki akan fuskar gaba ɗaya ahalin nata.
Bayan sun ɗan nutsane Baffa keyi mata bayanin cewa.
"Ai su Solomon musulunta sukazo yi, dan zamanta awajensu yasa sunji kwaɗayi da sha'awar addinin musulci, sun kuma gano cewa shine haske dake haskaka rayuwar duk wanda ke cikinsa, saboda haka suma suna so su musulunta, zasu musuluntan ne kuma ba saboda kowa ba, saidan suma su samu dacewa da rahamar Allah, sukuma samu daman ɗanɗana ni'ima da kuma baiwar dake cikin musulunci, saidai ance dama komai nada sanadi, to ita ce ta kasance sanadiyar musuluntar su Solomon ɗin wanda harda fastonsu suka zo wanda shima zai musulunta, shiyasa basu musulunta tun tana canba dan sunce sai sunar mishi koda suka gaya mishi ko shima yace zai musuluntan."
Wani irin daɗi da farinciki ne suka cika zuciyoyin gaba ɗaya ahalin, wani irin ni'im taccen daɗine ke ratsa zuciyar Baba Malam da kuma Saifuddeen, Allah mai iko yaugashi asanadin Zaleeha mutum ɗai ɗai har goma shabiyar zasu musulunta, tabbas zuwanta garin Numan yazamanto al'khairi, zuciyar Baba Malam ne tayi wani irin haske, take yaji duk wani abu dake ransa ya kau, ƙaunar ƴar tasa ne ya shigesa, har takai ga yanajin kamar ma bata taɓa yi masa wani abu na laifi ba. Saifuddeen ma yaji daɗin haka, take kuwa Baba Malam da kuma Baffa'n, suka shiga bawa su solomon da kuma sauran maƙotansu da suka biyosu dan suma suna son musulunta, kalman shahada, wasu suyi dadai wasu kuma su kwaɓa harsai angyara musu, ahaka dai har dukansu suka musulunta, su Ya Ahmad ne suka ce.
"Allahu Akhbar, haƙiƙa Allah da girma yake, yau gashi Zaleeha ta jawo sanadiyar musuluntan mutane 15, gaskiya wannan abun farinciki ne acikin zuri'arsu dama musulunci baki ɗaya." Haka dai duka zuciyoyinsu suka cika da farinciki da kuma jin daɗi.
Daga nanne Saifuddeen ya basu kuɗi masu yawa, dan su saya ƙaton fili acan garin nasu, sukuma yi ginin masallaci da kuma makaranta, Baba Malam ne yace.
Shi zai ɗauki nauyin ginin masallaci da kuma makarantar, sannan kuma zaiyiwa babban shugaban malaman izala dake can numan ɗin, akan cewa asama musu malamai waƴanda zasu riƙa koyar dasu addini. Ya Ahmad ma take yace zai bada gudumowarsa 1mil.
A nan Man Lima ya nemi keɓawa da Baba Malam ya sanar mishi dukkan abubuwan daya samu a jikin Zaleeha na sihiri,
Tabbas sihiri gsky ne yana kama ɗan adam tunda ya kama fiyeyyen halittama badon gazawar shiba ko tawayar darajarta ba a a sai dan nuna mana cewa zai iya kama mutun, sai dai tasirinsi ƙalilan ne, sosai Baba Malam yayi mamakin wannan al'amari, kana yayiwa Man Liman godiya mai tarin yawa.

Kana anan take ya kira shugaban ƙungiyan izala reshen Adamawa dake cikin numan ya shaida musu abin Al'khairi daya samu,
su kuma sun ɗauki niyar koyar dasu dukkan wani abinda ya kasance na addini,
babban farin cikinsu ga masallaci da islamiyar da za'a gina a yankin da da babu hasken musulunci sai warin kafurci dana burkutu da kashin aladu.


Zaleeha kam farin cikinta bazai misaltuba, kayan da tayi budurci dasu kab ta kwashe ta basu, dan ta san basu da wadattun suturu daya dace suke sawa, Mamy ma da Aunty Lubna sun basu kayayyaki da manya-manyan hijabai,
Mama kuwa saida tayi kuka wato Allah yaso wasu da rahma ne yasa ita da kanta ta tura ƴarta can da nufin watsa sunnar manzo sai gashi sanadin haka addini ya samu ƙaruwa.

Sune dai basu tafiba sai bayan sallan al'asar.

Bayan tafiyan sune Baba Malam ke sheidawa Zaleeha batun an ɗaura auren Ziyada da Ya Ameenu,
wannan al'amari yasata ƙara nitsuwa da jin tsoron Allah.

Shi kuwa Saifuddeen sallamansu yayi cewa zaije wurin Ishaq, sai bayan magriba zaizo su tafi gida.

Baba Malam kuwa shida kanshi ya ɗauki Ziyada da Ya Ameenu da Ayman ɗan Adam Maryam ya kaisu gida.
Sosai ya zauna yayi musu nasiha mai ratsa jiki da zuciya,
gaba ɗayansu kuka sukeyi sabida al'amarin ubangiji ya wuce wasa ko a zato ko a mafarki basu taɓa zatawa kansu zama mata da mijiba inba mutuwaba mai zai raba Adda Maryam da Ya Ameenu har ya aureta.

Bayan tafiyan Baba Malam ne, ya Ameenu ya ari jarumtar dole dan kukan da Ziyada keyi ya tsananta dole ya fara rarrashinta da nuna mata suyi haƙuri ƙaddar suce haka kums kowa da irin tasa.


Sai bayan sallan magrib Saifuddeen ya dawo shida Sule dan ɗaukan Zaleeha su koma gida,
nan
Showing 147001 words to 150000 words out of 237945 words