shagwaɓe fuska, ɗago kai tayi ta dubesa. Rau-rau yayi da idanunsa, tare da yi mata alama kancewar
"Tayi haƙuri karta ce zatayi fushi da shi." gane hakanne yasa Ummi ta sake haɗe fuska, tare da ɗan kau da kanta gefe, cikin haɗe fuska tace.
"Idan ma nayi fushi dakai ae kai ka nema, meyasa zanta maimaita maka magana ɗaya, amma ka kasa aiwatarwa, tunjiya naketa binka, akan maganan key ɗin ɗakin Zaleeha, sannan ga kuma maganar rakata ta bawa Babanta haƙuri, amma gaba ɗaya ka share maganta, bansan yaushe kazama haka ba Saifuddeen, bansan kuma meke damunka da har yasa ka kasa jin tausayin Zaleeha acikin ranka ba, To Wallahi matuƙar ba ɓacin raina kakeson gani ƙiri-ƙiri ba, tun wuri kaɗauki yarinyarnan kuje ku bawa Baba Malam haƙuri, tun da dai idan har dakai taje, baban nata zai iya yafe mata."
Idanunsa ya rumtse, lokaci guda yaji zuciyarsa na bugawa da ƙarfi, ɗanjan kekensa baya yayi, tare da zamewa ya durƙusa akan guiwowinsa, sake kamo hannun Ummin nasa yayi, lokaci guda ya shiga girgiza mata kai, sosai rauni ya bayyana akan fuskarsa, cikin body language ɗinsa yace. "Dan Allah Ummi kiyi haƙuri, ki bani ko wani irin umarni ne zan bi, sannan kuma bazan taɓa bijiremiki ba, amma dan Allah kada ki tursasani kan cewa na raka Zaleeha ta bawa Baba Malam haƙuri, idan nayi hakan Ummi zan cutu, tunda batasan ina da ƙima ba sai yanzu da matsala ta taso mata? kuma ma Ummi lokacin da tayi lefinta tare dani tayi ne? ai ita kaɗai tayi lefinta, da tazo guduwa kuma bata shawarceni ba, tanajin cewa ta isa shiyasa ta gudu alokacin da takeso, ta kuma dawo alokacin da takeso, ni nasan sam bata shirya yin nadama ba, kawai dan rasuwar Adda Maryam ne, amma bacin haka ai bazata dawo ba."
Dubansa Ummi tayi tare da ɗan girgiza kai, sam bata taɓa tunanin cewa wai Saifuddeen zaiyi fushi akan maganar Zaleeha ba, amma babu komai tayi masa uzuri, saboda tasan ba har zuciyarsa maganar da yake faɗi take fitowa ba, gyara zamanta tayi, cikin son nusar dashi da kuma yanda zai fahimta tace.
"Koma me Zaleeha ta maka, bai kamata kayi irin wannan fushin da ita ba, sannan kuma kaima shaida ne akan irin damuwar da take ciki, ca nake jiya anan gabanka ta suma, ko so kake mu barta haka, mu zuba mata idanu ciwon zuciya ya kamata? ko kuwa so kake mubar rayuwarta cikin garari?, kakuwa san halin da take ciki? bata da wani abunyi sai kuka dare da rana, bata da wani sauran farinciki, da wanne zataji, mutuwar ƴar uwarta ko kuwa ƙunci da baƙin cikin rayuwa? ko Allah ma muna masa laifi me girma, amma damunyi kyakkyawan tuba yake yafe mana, saboda meyasa to mu bazamu yafe mata ba?."
Rumtse idanunsa yayi da ƙarfi tare da tattauna lips ɗinsa, sosai yakejin wani abu azuciyarsa, wanda shikansa bazai iya fassara sa kaitsaye ba.
Raleeya wanda tuni idanunta sun ciko da ƙwalla ne ta ɗan matsa kusa da Ahmad, cikin sanyi tayi masa alamar cewa.
"Ya taimaka yasa baki, Hamma Saifuddeen ɗin ya raka Zaleeha ta bawa Baba Malam ɗin haƙuri, saboda rashin agaza mata zai iya sawa ta kamu da wani ciwon, musamman ma idan akayi la'akari da yanda take wuni kuka."
Jinjina mata kai Ahmad ɗin yayi alaman
"Yaji kuma zaiyi wa Saifuddeen ɗin magana. Hayatuddeen dake zaune shikansa saida yaji hawaye sun cika masa ido.
Ummi kuwa gaba ɗaya ranta ya gama ɓaci, domin shirun da Saifuddeen ɗin yayi, alamace dake nuna cewa, har yanzu yana kan bakansa, hakan ne yasa cikin fushi ta tashi ta nufi ɗakinta.
Cikin sauri Zaleeha dake tsaye jikin ƙofa ta koma ɗakinta, dan batason wani daga cikinsu ya ganta, saboda tunda suka fara magana'n harzuwa yanzu tana jinsu, duk da cewa Saifuddeen ɗin baya magana, amma ayanayin yanda yake gudanar da body language ɗin nasa, yasa ta fahimci komai dake zuciyarsa, ga kuma alaman fushin da yakeyi da ita da ya bayyana ƙarara, zamewa tayi anan jikin ƙofar ɗakin ta saki wani irin kuka mai taɓa zuciya, dama shi kaɗaine hope ɗinta, kuma shima gashi yaƙi amincewa, shikenan bata da wani me taimakonta ayanzu ta tabbata fushin uba dana mijinta yana kanta, kuka ta shigayi sosai, sanin cewa yanzu bata da wani madafa, ya zatayi mijinda a ƙarƙashin shi aljannarta yake yana fushi da abinda ta aikata a baya,kana babanta mahaifi yana fushi da ita ya zatayi, ta ina zata fara neman tafiyar mijinta.
Saifuddeen kuwa ganin Ummi ta tafi cikin fushi, yasa yaji gaba ɗaya jikinsa yayi masa sanyi, sosai zuciyarsa ta karye, damuwa me tarin yawa ya ɗarsu acikin ransa, sam bai saba da fushin Ummi ba, asanyaye ya hau saman wheelchair dinsa, ahankali yake tura keken har ya fice daga cikin ɗakin, part ɗinsa ya nufa, yana shiga kuwa ya laluɓo wayarsa dake cikin aljihu, numbern Ummin nasa ya laluɓo, asanyaye ya shiga rubuta mata text message, sai ya faɗi maganar acikin zuciyarsa, kafun yake rubutawa, kalamaine naban haƙuri, ya turawa Ummin nasa inda yace
_"Kiyi hakuri Ummina, akullum bana fatan na zamo me ɓata miki,ko yanzu ma ba'a son raina bane nakasa bin umarninki, kawai dai naga abun da Zaleehan tayi ne bai dace ace an roƙa mata yafiya ba, ta gujemu tayi tafiyarta, sai yanzu da duniya da kuma ƴan uwanta suka juya mata baya shine ta dawo garemu, wato mu gidanmu ya zama gidan ƴan iska kenan, da zata tafi ta kuma dawo alokacin da take so, nayi hakanne bawai dan na ɓata miki ba, kiyi haƙuri Ummi ki yafemin"_
Yana gama rubutun yayi sending message ɗin, tare da ɗan kifa kansa ajikin keken nasa, kana ya lumshe idanunsa.
Ummi na zaune akan gado, saƙon ya shigo, koda ta gama karanta saƙon nasa murmushi tayi, dama ita ba fushi tayi dashi ba, tayi hakanne kawai saboda yayi mata abun da takeso.
amsa ta shiga rubuta masa, tare da jaddada masa cewar
_"Yayi abun da takeso kawai, idan kuma baso yake, damuwa yayi sanadiyar taɓa zuciyar Zaleehan ba, dan jiya kwana tayi kuka, bakin cikin rayuwa sunyi wa Zaleehan yawa, da wanne zataji mutuwar ƴar uwarta ko kuwa fushin da Babanta keyi da ita? sannan gefe guda kuma ga fushin ƴan uwanta, ga kuma shima da ya kamata ace yazame mata garkuwa fushi yakeyi da ita, meyasa bazaiji tausayin Zaleeha'n ba, wanda har yanzu yasan cewa, ita yarinyace, sannan kuma tayi nadama har acikin zuciyarta."_
tura masa saƙon Ummi tayi tare da aje wayarta.
Shi kuwa Saifuddeen yana gama karanta saƙon Ummin sake lumshe idanunsa yayi, zuciyarsa duk ba daɗi. Cikin sanyi ya rubuta cewa.
_"Kiyi haƙuri Ummi banso na ɓata ranki ba, shikenan naji na amince zan rakata, amma dan Allah Ummi kiyi haƙuri zuwa gobe idan anyi sadakan uku saina kaita kafin nan mutane sun ɗan ragu a gidan nasu"_
Murmishin farinciki da samun nasara Ummi tayi, bayan ta gama karanta text message ɗin daya turo mata, nan tace dashi.
"Allah ya kaimu goben." Sai alokacin ya ɗanji sanyi acikin ransa, saboda yasan zuwa yanzu, zuciyar Ummin nasa zata ɗanyi sanyi.
Can ɓangaren Zaleeha kuwa kuka tasha sosai har taji babu daɗi, dan kanta haka ta share hawayenta saboda koma menene tasan ita ta jawa kanta, ko ahaka suka barta ma, tasan sunyi mata gata tunda suka bata muhallin zama, abun da ƴan uwa da mahaifinta suka kasa yi mata kenan saboda fushin da sukeyi da ita.
Ganin kukan bazai kaita ba yasa ta tashi ta wuce toilet tare da wanko fuskarta wanda tayi ja sosai saboda kukan da tayi, fitowarta daga toilet ɗin kuwa yayi dai-dai da shigowar Ummi cikin ɗakin, ganin fuskar Zaleehan da kuma idanunta sunyi luhu luhu, yasa Ummi kamo hannunta suka zauna anan bakin gado. Cikin kulawa Ummi tace. "Kuka kikayi ko?" Sadda kanta ƙasa tayi, saboda bazata iya musawa Ummi'n ba, kanta Ummi ta shafa, tare da cewa.
"Ki kwantar da hankalinki kinji, Insha Allah gobe Hammanku zai kaiki kuje ku bawa Baba Malam haƙuri, kuma Insha Allah Baba Malam zai yafe miki, ki daina kukan nan kinji!."
Ummi tafaɗi maganar cikin lallashi, jin cewa Hamma Saifuddeen ɗin ya yarda zai kaita yasa taji wani irin farinciki ya lulluɓe Zuciyarta, hakanne yasa ta faɗa jikin Ummi ta saki kuka. Rarrashinta Ummin ta somayi tare da sanya hannu tana shafa bayan Zaleeha'n, cikin kukan tace.
"Nagode sosai Ummi, haƙiƙa kin zame min uwa, nagode sosai..."
saurin rufe mata baki Ummi tayi, cikin kulawa tace.
"Kamar ƴa haka na ɗaukeki Zaleeha, saboda haka bama saikin min godiya ba, duk wani burina bai wuce farincikin ku, Allah Ubangiji ya muku al'barka, ungo wannan kayan ɗazun Hayatuddeen ya sayo miki su."
Ummi ta faɗi maganar tana me miƙawa Zaleehan ƙatuwar ledan dake hannunta.
Amsar ledan tayi cikin farinciki tace.
"Nagode sosai Ummi." har cikin ranta taji daɗin kayan, saboda itama kayan jikin nata sun isheta, yau kwanansu biyu kenan ajikinta, abunda tunda take aduniyarta bata taɓayi ba kenan, dama haka rayuwa take tana juyawa da abubuwa kala-kala, wai ita Zaleeha me yawan ado da kwalliya uwa uba ƙwalisa, itace ke sanye da kaya ɗaya ajikinta har tsawon kwanaki biyu, bacin da arana ɗaya saita sanja kaya kusan kala uku, amma yau gashi komai ya juya mata, damuwa ya mata yawa, wani lokacin har takan manta wasu abubuwan da suka shafeta.
Ummi kuwa tashi tayi inda da kanta ta shiga toilet ta haɗawa Zaleehan ruwan wanka me ɗumi, cikin kulawa Ummi tace da Zaleehan ta shiga tayi wanka, babu musu kuwa ta shiga rage kayan jikinta, ganin haka yasa Ummi fita daga cikin ɗakin, tare da jawo mata ƙofa.
Jikinta aɗan sanyaye haka tayi wankan, ba laifi kuwa taɗanji damuwarta ta ragu, nan cikin kayan da Ummin ta kawo mata ta zaɓo wata doguwar abaya gown me kyau ta sanya, sam damuwar da take ciki kuwa bai hana zallan kyawunta fitowa ba, gashi rigar ta amshi jikinta tayi mata ɗas, mayafin doguwar rigar ta yafa, sannan cikin yanayin sanyi ta fito zuwa falo.
Nan ta iske Raleeya da Hayatuddeen zaune, Raleeya karatun littafin hausa take, shikuwa Hayatuddeen game ya haɗa yakeyi.
Yana ganinta ya ɗan waro idanunsa, tare da cewa.
"Wow Adda Zaleehan mu kinyi kyau, yeah ashe dai niɗin gwanine wajen iya zaɓen kaya." Murmushi tayi masa, tare da zama anan kusa da Raleeya.
Duban Raleeya tayi cikin kulawa tace.
"Sister sannu da gida." cikin sakin fuska Raleeya tace.
"Yauwa sannu my kyakkyawar Auntyn mu, halan wannan kwalliyan duk na hamma ne" Raleeya ta ƙare maganar cikin yanayi naɗan tsokana, murmushi Zaleehan tayi wanda har saida fararen haƙwaranta suka bayyana, nan ta sadda kanta ƙasa tana tunanin. Uhum Hammanku kam ko kallo ban isheshiba ba ai. Hayatuddeen kuwa tashi yayi ya wuce ɗakinsa, mintuna kaɗan sai gashi ya dawo da leda ahannunsa, nan kan cinyarta ya ajiye mata, cikin kulawa yace. "Aunty roasted fish ne da cake, please kici kinji, nasan kinaso." murmushi tayi tare da cewa.
"Nagode auta." Dukansu murmushi sukayi sannan suka shiga ɗan taɓa hira, ita dai haryanzu akwai damuwa kwance aƙasan zuciyarta, hakanne ma yasa maganarta bai wuce.
"Eh, ko A'a ba".
Suna nan azaune Ummi ta fito ta samesu, zama tayi acikinsu, itane ma take ƙoƙarin jan Zaleehan da hira.
Saifuddeen ne ke tura wheelchair ɗinsa, yana son ƙarasawa part ɗin Ummi, dai-dai lokaci Ameena wanda dawowarta daga aiki kenan ta shigo cikin gidan, ganin Saifuddeen ɗin yasa ta ƙaraso da sauri tana sakar masa murmushi, shiɗinma murmushin ya sakar mata, tare da miƙa hannu ya karɓi Adeel dake rungume akafaɗanta. Ɗan ranƙwafowa tayi tayi mishi kiss a forehead ɗinsa, cikin kulawa tace. "Nayi kewarka Mijina." murmushinsa me kyau yayi mata, tare dayi mata alaman cewa shima haka, nan ta riƙe saman wheelchair ɗin nasa, tana turasa shikuwa yana riƙe da Adeel haka suka nufi part ɗin Ummi.
Ahankali suka tura ƙofar falon suka shiga bakin Ameena ɗauke da sallama, hakanne yasa gaba ɗayansu suka ɗago kai suka kallesu, Ummi ne ta fara amsa sallaman, kafun suma suka amsa, kallo ɗaya Zaleeha tayi musu ta duƙar da kanta ƙasa, cikin kulawa Ummi tace. "Mutanen asibiti kun dawo."
Murmushi Ameena tayi, wanda ganin Zaleeha cikin shiga me kyau yasa duk taji zuciyarta ba daɗi, ɗan durƙusawa tayi tare da cewa.
"Ummi barka da gida." Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Yauwa Ameena ya wajen aikin naki?" tana murmushi ta amsa da lafiya lau, Raleeya da Hayatuddeen ne sukayi mata sannu da dawowa, baki awashe haka ta amsa musu, duk dama dai aranta sam bataji dadin ganin Zaleeha ba, gashi kuma Zaleehan tayi kyau sosai, Ɗago kai Zaleeha tayi tare da ɗan kallon Ameena'n, cikin sanyin murya tace.
"Ummu Adeel barka da dawowa."
Cakwai haka Ameena taji muryan Zaleehan acikin kunnuwanta, take kuwa taji kaman an watsa mata ruwan zafi ajikinta, wani irin haushin Zaleehan ne ya cika mata zuciya, amma ganin idon su Ummi yasa ta ɗanyi yaƙe tare da cewa.
"Yauwa Sannu." Ɗan ɗago kai Zaleeha tayi ta saci kallon Adeel dake kan cinyar Saifuddeen, Gani tayi Adeel ɗin na kallonta, hakan yasa ta sakar masa murmushi wanda har saida dimples ɗinta suka lotsa, shima yaron murmushi yake ta mata yana wangale mata haƙora tare da mutsu-mutsu har yana zamowa tare da miƙo mata hannu alamun ta ɗaya shi.
Cikin dariya Hayatuddeen yace.
"Aunty Zaleeha ke yakeyiwa hakafa".
murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Ae wannan ɗan naku saiku yaron ba dai ƙirniya ba abinda ya iya".
Murmushi sukayi baki ɗaya su.
Ita kuwa tashi tayi daga zaunen da take, gaba ɗaya ta gama mantawa cewar ma yaron akan cinyar Saifuddeen ɗin yaƙe, ƙarasawa tayi tare da ɗan ranƙwafawa tasa hannu zata ɗauki Adeel ɗin, daddaɗan ƙamshin turarensa ne ya daki hancinta, cikin tsautsayi kuwa hannunta ya gogi nasa, wani irin shock sukaji su duka biyun, ahankali ta ɗauki Adeel ɗin, sannan ta ɗagashi sama tana sakar masa murmushi,
baki ya wangale mata harda tsalle shi, Allah ya sani tana son Adeel har cikin ranta kuma shima yaro yana sonta.
Baki buɗe Ameena ke kallonsu, kishi kuwa haka takeji kaman zai fasa ƙirjinta, ƙwarai tazo iya wuya, dan kasantuwar Zaleeha akusa da Saifuddeen ɗin baƙaramin dacewarsu ta gani ba.
Ummi kuwa jin wayarta dake cikin ɗaki na ƙara yasa tatashi ta bar musu falon, Raleeya ma miƙewa tayi ta haura sama.
Nan falon ya rage daga Hayatuddeen, Zaleeha, sai su Saifuddeen ɗin, Zaleeha kuwa rungume Adeel ɗin tayi tana yi masa wasa, Saifuddeen kuwa ahankali yake ɗan satan kallon Zaleeha'n, saboda tayi masa kyau sosai, duk da kasancewar ma ya lura cewa idanunta aɗan kumbure suke kuma gaba ɗaya yanayin rayuwarta ta sauya ta zama mai sanyi, hakan yasa shi jin wani abu na tausayi acikin ransa. Ameena kuwa ganin cewa Saifuddeen ɗin na ɗan satan kallon Zaleehan ƙasa-ƙasa ne, yasa taji gaba ɗaya ranta ya ɓaci, wani irin matsanancin kishi ne ya taso mata, amma saita dake, cikin kirsa ta tashi ta dawo kusa da Saifuddeen ɗin, ɗan durƙusawa tayi tare da tallafo haɓarsa cikin son nunawa Zaleeha matsayinta tace. "Mijina Mekakeso na kawo maka kasha?" Shikuwa sanin cewa Zaleeha na falon, yasashi jawo hannun Ameenan kusa dashi, kissing ɗinta yayi, tare da nunata da
Showing 114001 words to 117000 words out of 237945 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39 Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80