kallonta, ganin tana ƙoƙarin fitowa batare da ta saka turare ba, yasashi kamo hannunta suka koma cikin ɗakin, turaren daya saya mata ya ɗauka ya ƙara fesa mata, murmushi ta saki tare da cewa.
"Kaidai Hayatuddeen rigima ne dakai, ɗazu fa na fesa turaren kuma har yanzu akwai ƙamshin ajikina."
Kansa ya jinjina tare da cewa.
"Eh naji ai, amma so nake ki ƙara".
Murmushi kawai tayi sannan tabi bayansa suka fice daga cikin ɗakin.

Daddaɗan Ƙamshin turarenta shiya fara ziyartan hancinsu, ahankali yaɗan lumshe idanunsa tare da haɗiyan wani yawu daya tsaya masa amaƙoshi, Ameena kuwa da sauri ta juyo dan bakaɗan ba ƙamshin ya tafi da ita, idanunta na sauƙa akan Zaleeha taji gabanta ya faɗi, saboda wani irin kyau da taga Zaleehan ta ƙara, kau da kanta tayi tare da ƙara matsaya kusa da Saifuddeen, har jikinsu na gogan na juna, Zaleeha kuwa cikin nutsuwa ta ƙaraso kan dining ɗin, fuskarta ɗauke da ɗan murmushi tace.
"Ummi barka da dare." Murmushi Ummin tayi, tare da cewa.
"Yauwa dai Zaleeha sannunki, dan kema yau kinsha aiki, daga samun sauƙi kuma sai shiga kitchine".
ɗan murmushi Zaleehan tayi tare da miƙa hannu ta karɓi Adeel, dai-dai lokacin Saifuddeen ya buɗe idanunsa ya sauƙesu akanta, murmushin daya bayyana dimples ɗinta tayi, tare da ɗan manna fuskar ta da ta Adeel ta sakar masa kiss akan bakinsa, cike da ƙaunar yaron tace.
"I miss you my sweet papy na."
Baki Adeel ɗin ya wangale yana yi mata dariya.
Ɗan lumshe idanu Saifuddeen yayi, tare da lasan lips ɗinsa, dan kiss ɗin da Zaleehan tayiwa Adeel haka yaji kaman shi tayi wa, a ranshi yace.
"Uhummm da yadda akeson Adeel haka akeson Abbanshi da duniya tai mana daɗi, kalli yadda take son yaron kamar tana son ubanshi".
Kujera Zaleehan taja ta zauna, wanda kuma hakan yasa suke facing ɗin juna ita da Saifuddeen ɗin, ɗan kallon Ahmad tayi cikin muryarta me ɗauke da sanyi tace.
"Barka da dare Ya Ahmad."
Hakanan yaɗanji tausayinta ya kamasa, fuskarsa yaɗan saki sannan ya amsa mata.
Fuskarta ɗauke da murmushi ta kalli Ameena wanda keta ƙara shigewa jikin Saifuddeen, murmushi tayi mata tare da cewa.
"Ummun Adeel sannunki da dare."
Duk yanda Ameena taso daure kishinta akan Zaleeha abun naneman fin ƙarfinta, dole haka ta daure ta ƙaƙalo murmushi, cikin muryarta da ta maƙale tace.
"Yauwa."
Ummi ne tasa hannu ta amshi Adeel ɗin, cikin kulawa tace.
"Kawo sa yanzu saiki fa ke dashi kiƙi cin abinci, nasan halinki sarai, tashi ma kiyi seving ɗin mu."
Murmushi Zaleehan tayi tare da miƙewa tsaye, food flasks da kuma plates ɗin ta jawo gabanta, cikin nutsuwa tashiga zubawa kowa abincin,
Kyawawan idanunsa ya zuba mata, a ƴan kyawawan yatsunta yake kallo, komai tanayinsa ne acikin nutsuwa.
Ameena da gaba ɗaya haushin Zaleehan ya cika zuciyarta, ɗan kallon Saifuddeen ɗin tayi, ganin ya ƙure hannun Zaleehan da ido, yasa taji kaman ta tashi awajen, wani baƙinciki da kishine suka tokare maƙoshinta, gaba ɗaya da zuwan Zaleehan sai duk taji ta raina kanta, hakanan taji babu ma irin ƙamshin da ta tsana kamar ƙamshin oud ɗin da ke jikin Zaleeha'n.
Zaleeha kuwa sam hankalinta ma ba akansu yake ba, cikin nutsuwa ta gama seving ɗin kowa, ɗan matsowa gabansa tayi ta ajiye masa nasa abincin, komawa tayi ta zauna, tare da jawo plate ɗin da ta zubawa kanta abinci aciki, dubanta Ummi tayi cikin kulawa tace.
"Zaleeha ɗan wannan abincin shi zaki ci kuma har ki ƙoshi".
Murmushi ta ɗanyi, tare da cewa.
"Eh Ummi, amma idan ban ƙoshi ba zanci na Hayatuddeen."
Kai Hayatuddeen ya jinjina, murmushi kawai Ummi tayi, haka suka shiga cin abincin.
Loman farko da yayi, ya lumshe kyawawan idanunsa, dan kuwa sosai yaji ɗanɗanon abincin abakinsa, tabbas Zaleeha ta iya girki sosai, wanda har yau yana mamakin a ina ta koyo girki kala kala haka.
Abinda bai saniba ƙabilar su mama sunyi zarra a iya girki kuma Zaleeha Mama ta gado a iya girki kana ta samu horon Mamy iya sarrafa abin da za'aci.

Ameena ma tun aloman farko da tayi, gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, dan kuwa taji ɗanɗanon abincin ya banbanta da wanda Raleeya ta saba girkawa, maganan Hayatuddeen ne ya katse mata tunani, inda yace.
"Kai Adda Zaleeha wallahi kin iya girki."
Jin cewar Zaleehan ne tayi girkin yasa duk taji abincin yafita aranta, domin Zaleehan iya girki nesa ba kusa ba.
Ahmad shi kansa yau ya yaba da abincin dan buɗe cikinsa yayi yaci sosai.

Zaleeha kuwa ahankali take ɗan tsakuran abincin tana kaiwa bakinta, yanayin yanda take tauna abincin cikin nutsuwa shi yasa Saifuddeen yake ta faman satan kallonta.
Ganin haka yasa Ameena tsaida cin abincin tayi shiru, hakanan taji idanunta na neman kawo ruwa, ɗan juyowa Saifuddeen yayi ya kalleta, ganin yanda tayi shiru ne, yasa ya ɗan tsiyayi drinks acikin cup, hannunsa yasa miƙa mata cup ɗin,
Rau-rau tayi da ida nunta hawayen kishi na gab da zubo mata,
Tuni Saifuddeen ya karanci Ameena tanada masifar kishi, har ga Allah yasan ta tsananin sonshi amman yana mata addu'a Allah ya sassauta mata zafin kishinta.
Gani tana gabda zubda hawayene yasa yayi niyar bata abu mai sanyi tasha zataji sassaucin abinda takeji a ranta.
A hankali yakai cup ɗin drinks ɗin bakinta, ɗan shagwaɓe masa tayi, tare da buɗe baki ya bata drinks ɗin, saida tasha rabin cup ɗin sannan ya ajiye, da ido ya nuna mata filet ɗin alamun taci abincin,
kai ta sunkuyar cikin sanyi tasa hannu ta ɗauki spoon ɗin madadin taci sai tayi ta wasa da cikalin.
Numfashi ya ɗan fesar kana yasa hannunshi akan nata,
hannu dake gefenshi murza hannu yake ɗanyi a hankali alamun taci. itakam dama abun da take nema kenan, saboda haka saita biye masa, duk dan saboda tanason kawar da hankalinsa akan Zaleeha, Kallo ɗaya Ummi tayi musu ta watsar tare da girgiza kanta, dan ta fahimci cewa sam Saifuddeen bayajin kunyarta, Ahmad kuwa murmushi kawai yayi yaci gaba da cin abincinsa.
Raleeya ma ƙasa tayi da kanta, hakanan taji wani iri, sam batason abun da zaisa Zaleeha taji babu daɗi aranta.
Hayatuddeen kuwa baki ya sake yana kallonsu, har acikin ransa yana mamakin dalilin dayasa ayanzu Hamman nasa ke ƙoƙarin nunawa Ameena kulawa agaban kowa.

Itakam Zaleeha kallo ɗaya tayi musu ta maida kanta ƙasa , kwata kwata abun nasu baya damunta, wani lokaci ma sai abun da sukeyi ɗin yana bata dariya, dan ta fahimci kamar Ameena'n bata iya sirranta soyayyarta ba, amma ganin ba huruminta bane, shiyasa ma takeyin kamar bata gani ba.

Saifuddeen kam har acikin ransa da yakeyin hakan dan sassauta kishin Ameena, kana a wani sashin kuwa da gaggan yakeyi dan kawai Zaleehan taji wani abu aranta, Ameena kuwa gaba ɗaya ta sakankance, shiya dinga yi mata wani irin kallo, tana mejin wani irin daɗi acikin ranta, hakanan idan Saifuddeen na mata hakan agaban Zaleeha take jin kanta kaman tafi kowa a duniya.
ganin ta girgiza mishi kai alamun ta ƙoshine yasa ya sake bata abin sha.
Ɗagowan da Zaleeha zatayi ta gansu ahaka, take taji ƙirjinta ya buga. Cikin sauri ta kauda kanta wani sihirtaccen murmushi tayi kana ta miƙe a hankali hannu ta miƙa ta karɓi Adeel dake hannun Ummi, kana ta juya ta nufi cikin falon,
sam Ummi batayi yunƙurin hanata ba.

Wani irin murmushi Saifuddeen yayi, tare da ɗan cije laɓɓansa, cikin zuciyarsa yace.
*"Ƴarinya yanzu aka fara wasan."*

Hayatuddeen ne ya miƙe yayi ɗakinshi,
Hakama Raliya ta miƙe tabi bayan Ahmad.

Ido Ummi ta zubawa Saifuddeen ko ƙibtawa batayi,
ganin haka yasa itama Ameena ta miƙe ta nufi side ɗinsu dan taje ta sake wonka dan ta lura yau Saifuddeen a matsaye yake.

Shiru falon ba motsin kowa,
gaba ɗaya Ummi ta hana Saifuddeen motsi dan yasan tun yana yaro in ya mata laifi taka hukunta shi da hakan, cikin fargaba ya ɗan gyara zama tare da yin rau-rau da ida nunshi wanda da gaske sun cicciko da ruwa dan bai fahimci abinda yayi yanzu bane ya ɓata mata rai.
kai ya rangwafar tare da mata mgna da yarensu.
"Ki gafar ceni Ummi ban san me nayiba, na tuba gaya min laifiba?".
Kwaffa tayi tare da cewa.
"Uhummmm yayi kyau Saifuddeen kaci gaba da cusawa ƴar mutane baƙin ciki".
Kanshi ya jujjuya cikin alamun mgnarsu yace.
"Ummi me kuma nayi, na kaita gidan su na tayata bada haƙuri, duk sun yafe mata nima na yafe mata, kuma yanzu meya rage?".
miƙewa tsaye tayi tare da cewa.
"Key ɗin ɗakinta zaka bani, ta koma ɗakinta,kuma ka raba musu kwana kamar yadda shariya ta buƙata".
Wayarshi ya zaro tare da rubuta mata.
"Wlh Allah Ummi na mance inda na ɓoye key ɗin amman insha Allah zan neme shi in na ganshi zan bakishi".
kai ta jinjina tare da cewa.
"Tom yayi kyau".
Daga nan ta juya ta nufi ɗakinta.
Shiru Saifuddeen yayi yana saƙa da warwara a ranshi, wani irin munafikin murmushi yayi kana ya wuce side ɗinshi, yana tafe yana rubuta wa Ameena saƙo ya tura mata kana kai tsaye ya wuce ɗakinshi.




Wasa farin girki sannu-sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba jeba, muna gab da shigo wani sashi mai ɗan karen zaƙi a littafinsa biya ɗarinki uku ki karanta ba tare da haƙƙin kowa a kankiba, in kina buƙata ga number ta 09097853276 ki turo katin mtn na 300 ko kimin transfer na 300 ta asusuna na 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa.



By

*Garkuwan Fulani*
10/4/20, 7:04 PM - Mmn Khalid: Ngs Bayan duk sun gama fita daga falon Ummi kaitsaye ɓangarensa ya nufa, ahankali yake tura wheelchair ɗin nasa, wayarsa ƙiran Samsung ya ciro tare da laluɓo number'n Ameena ya tura mata text, ganin saƙon ya tafi ne yasa ya maida wayar cikin al'jihunsa, ahankali ya murda handle ɗin ƙofar ɗakin nasa ya wuce ciki.
Yana shiga kuwa yaɗan rage kayan jikinsa, tare da hayewa saman gadon ya kwanta.
Can ɓangaren Ameena kuwa tana nan zaune taga saƙon text ɗinsa, koda ta karanta ɗan murmushi tayi tare da lumshe idanunta, ita dai dama tun ɗazu da suke cin abincin tagane take takensa, miƙewa tayi tare da ƙarasawa gaban mirror, turare ta ɗan fesa ajikinta, sannan ta fice daga cikin ɗakin, dan dama tun shigowarta ma bata shigo da Adeel ba, yana can wajen Zaleeha.
Ahankali ta tura ƙofar ɗakin ta shiga bakinta ɗauke da sallama, duk da tasan cewar bayaji, amma ako yaushe idan zata shigo ɗakin nasa saitayi sallama, kamar yanda addini ya koyar.
Ganinsa kwance akan gado ya sa taɗan saki murmushi, ahankali ta ƙaraso jikin gadon, anan bakin gadon ta zauna. Idanunsa ya zuba mata, ganin haka yasa tace. "Naga message ɗinka, shiyasa nace bari nazo ko kana da buƙatar wani abu ne."
Ɗan lumshe idanunsa yayi, ahankali ya ɗago hannunsa ya nuna ta, alaman cewa.
"Ita yake da buƙata."
Ɗan murmushi tayi, dan har acikin ranta taji daɗin hakan, amma abayyane kuwa gyara zaman ta tayi, tana ɗan murmushi tace.
"Indai nice ae kagama samu, saidai kuma banso shigowa wajenka yau ba, saboda nayi tunanin banice dakai ba yau Zaleeha ce, shiyasa har na kwanta ma ganin message ɗinka ne yasa na fito."
Tafaɗi maganan, tana me zuba masa idanu, dan ƙwarai ta ƙagu tafahimci abun dake wakana atsakaninsa da Zaleeha, wanda yasa bata zuwa ɗakinsa, da kuma zaman da taga tanayi a ɓangaren Ummi.
Take yanayin fuskarsa ya sauya, lokaci guda yaji ransa ya ɓaci, sam baiso jin sunan Zaleehan abakinta ba, dan kwata kwata atsarinsa babu irin wannan rayuwan, da wata daga cikinsu zata kawo zancen abokiyar zamanta agabansa, sam bayaso kwata-kwata, domin yin hakan shikesawa Namiji ya zama kamar munafuki a tsakanin matanshi, shi kuma ko kusa baya fatan haka wa kansa.
Jikin Ameena ne yayi matuƙar sanyi, musamman ma yanda taga ya haɗe gabas da yamma, lokaci ɗaya annurin fuskarsa ta gushe, gaba ɗaya jin zuciyarta tayi babu daɗi dan kwata kwata bataso ɓata masa ba, saidai kuma azuciyarta tana mamakin abun da zaisa ransa ya ɓaci dan kawai ta ambaci sunan Zaleeha, wanda ita kuma tayi hakanne dan ko zataji wani ƙarin bayani daga garesa ta samu ta gwaggwafi sirrin Zaleeha.
Ɗan matsowa kusa dashi tayi tare da kama hannunsa, cikin sanyin murya tace.
"Kayi haƙuri, bansan maganan dana faɗa zai ɓata ranka ba."
Ɗan kawar da kansa gefe yayi, dan yanason nuna mata cewar ko gaba bayason irin hakan. Ganin ya kau da kansa gefe ne, yasa Ameena ta saki ɓoyayyen murmushi, cikin ranta tace.
"To kodai dama bayason zaleeha'n ne? sannan idan da ace ma yana sonta, ai da zaina ƙiranta part ɗinsa, to amma kuma mayataccen kallonta da nake yawan kamasa yanayi mata fa? da kuma zamanta asashin Ummi duk me hakan ke nufi?."
Ɗan jim tayi tare da sauƙe ajiyar zuciya. " kodai Wataƙila Ummin ne tace ta zauna a part ɗin nasu saboda rashin da akayi mata, dan hakan zai ɗebe mata kewa." Duk acikin ranta take maganan, yarda da abunda zuciyarta ta faɗa mata ne, yasa ta sake kamo hannun Saifuddeen ɗin, tare da tallafo haɓarsa ya zamana suna fuskantar juna,
murmushi ta sakar masa tare da sanya hannu ta kama kunnenta, cikin sanyi tace.
"Kayi haƙuri kaji please." Idanunsa yaɗan lumshe, tare dayi mata alaman cewa.
"Kada ta sake yi masa irin hakan."
cikin ɗanjin daɗi tace. "Insha Allah." rungumesa tayi tare da haɗe bakinsu waje ɗaya. Kasancewar dama tun haɗuwarsa da Zaleehan na ɗazu a cikin mota yakejin kansa amatuƙar buƙace, hakan yasa bai ƙi biye mata ba, haka suka sha romance ɗinsu, bayan komai ya wakana, ya tashi daga kwancen da yake, tare da hawa kan wheelchair ɗinsa, kai tsaye ya wuce banɗaki yayi wanka, yana fitowa itama Ameenan ta shiga, sai sakin ɓoyayyen murmushi take, dan ƙwarai taji daɗin kasancewarsu na yau ɗin.
Koda ta fito ta samu har ya koma ya kwanta, yana ƙoƙarin rufawa jikinsa blanket, kayan baccinta ta sanya sannan itama ta hawo gadon, idanu ya zuba mata, cikin body language ɗinsa yace. "Ina Adeel?"
tana me ƙulle gashinta tace.
"Ai tun ɗazu yana can wajen Amminsa." Ɗan jinjina kansa yayi tare da lumshe idanunsa, dan ya gaji ƙwarai so yake yayi bacci. Ganin baice komai ba yasa ta ce.
"Na karɓoshi ne?" akasalance cikin body language ɗinsa yace. "No idan bazaiyi kuka ba, ki barshi kawai." idanu ta ɗan zaro tare da cewa.
"Chab aikuwa zaiyi kuka kam, halan dai kamanta Adeel ne, abunda kusan kullum da dare sai ya tashi shan nono, ba naje na karɓosa kada ma ya tashi tsakiyar dare ya hanasu bacci."
ta ƙare maganar tana me sauƙowa daga kan gadon, ficewa tayi daga ɗakin, shikuwa blanket yaja ya sake rufe jikinsa, kasancewar har wani sanyi sanyi yakeji saboda gajiya, waist ɗinsa kuwa ciwo yake mai, shikansa yasan me raunine shi awannan ɓigeren, zaiyi ƙoƙarin jurewa, amma fa da za'aran komai ya kammala zaiji gaba ɗaya gaɓɓan jikinsa nayi masa ciwo hakan kuma baya rasa nasaba da larurarsa. Ameena kuwa saida ta fara biyawa ta ɗakinta ta ɗauko hijab kafun ta wucewa sashin Ummi'n, koda taje haka ta samu falon shiru, sai Hayatuddeen kawai dake zaune yana ta faman latsa wayarsa, yayinda ya saƙala earpiece akunnensa, hakanne ma yasa ko shigowan Ameenan bai ji ba, murmushi kawai Ameena tayi, sannan ta wucesa, kai tsaye ɗakin Zaleehan ta nufa, anan bakin ƙofan ta tsaya tare da ɗan ƙwanƙwansawa, jin shiru babu amsa yasa ta ɗan tura ƙofar ɗakin ahankali tasaka kanta ciki. Hango Zaleehan tayi kwance akan gado, yayinda ta ɗaura Adeel asaman cikinta, baccinsu suke cikin kwanciyar hankali, bisa duk kan alama ma Adeel ɗin ya riga Zaleehan bacci, dan yanayin da suke cike ya nuna, kaman cewa Zaleehan na shafa bayansa ne bacci ya ɗauke ta.
Ɗan tsayawa ajikin ƙofar tayi, tana tunanin yanda za'ayi ta tashe su.
Showing 129001 words to 132000 words out of 237945 words