abincin kinji." Cikin sheshsheƙan kuka tace.
"Ummi bazan iya ci ba, ko tea ɗin ɗazu dana sha haka najisa kaman maɗaci, gaba ɗaya kaman yanda zuciyata take babu ɗanɗano acikinta, haka bakina ma, banajin daɗin komai."
cikin tausayawa Ummi tace.
"To akawo miki fresh milk kisha ko kaɗanne?"
Batason yawaita yin musu da Ummi hakan yasa ta ɗan gyaɗa kanta, dai-dai lokacin kuwa Raleeya ta shigo, nan Ummi tace da ita, ta kawowa Zaleehan fresh milk.
Babu ɓata lokaci kuwa takawo fresh milk ɗin me sanyi.
Karɓan cup ɗin Hayatuddeen yayi, cike da tausayinta yace. "Adda Zaleeha, ki tashi kisha kinji."
bazata iya janye jikinta daga garesa ba, saboda tanajin ya zame mata kamar majingina, hakan yasa ahankali taɗan ɗago kanta dake masifar sarawa, cikin kulawa Hayatuddeen ya shiga bata fresh milk ɗin abakinta, sam kwata kwata batajin daɗi ko ɗanɗano abakinta, jima take kamar magani take sha, kurɓo huɗu kawai tayi ta janye bakinta daga jikin ƙofin, har yanzu sheshsheƙan kuka take, gashi jikinta ya sake ɗaukan zafi sosai, komawa jikin Hayatuddeen ɗin tayi ta kwanta, tana ta faman fusgar numfashinta dake neman ƙwace wa. Ummi, Adda Rahama, Raleeya, har zuwa kan Hayatuddeen babu wanda ya gusa da ga kusa da ita, wani irin kulawa haɗi da tattali na musamman suke bata, sosai suke faɗa mata kalaman dazai kwantar mata da hankali..
Suna nan azaune har aka ƙirayi sallan la'asar, Ummi ne tace da Adda Rahama da kuma Raliya su shiga kitchine su ɗaura abinci, kasancewar tunda akayi rasuwa'n kullum sai sunkai abinci gidan su Zaleeha.
Nandai Hayatuddeen ma ya tashi ya wuce massallaci, itama Zaleehan sallah tayi, nan kan carpet ta kwanta tana masassara saboda zazzafan zazzaɓin ya soma cin ƙarfinta.
Su Adda Rahama kuwa suna kammala girkin, nan cikin wasu manyan food flask suka juye abincin.
Kamar kullum dama Hayatuddeen da Raleeya ne ke kai abincin, to yau ɗin ma dai hakanne, ta kasance dan sune suka kai abincin, Hayatuddeen ne ke driving, kasancewar yanzu hannunsa yaɗan faɗa wajen iya tuƙin mota, saboda Khamis na koya masa tuƙin time to time, babu laifi kuma yaɗan iya.
Koda suka ƙarasa gidan su Zaleehan bayan sun sake yi musu gaisuwa, Hayatuddeen ne ya kamo hannun Zakariyya da Imran ƙanin Ishaq wanda da Babansu yazo, zagawa sukayi wajen da babu yalwar mutane. ɗan karyar da wuya Hayatuddeen yayi, cikin sanyi haɗi da damuwar dake bayyane akan fuskarsa yace. "Zakariyya Adda Zaleeha taje gida bata da lafiya sosai, gaba ɗaya jikinta zafi kaman wuta, har suma tayi, dan Allah abawa Baba Malam haƙuri ya yafe mata, tana cikin matsanancin damuwa, kuka yazama tamkar abinci agareta."
Idanun Zakariyya ne suka cicciko da ƙwallan tausayin ƴar uwartasa, ɗan lumshe idanunsa yayi, yana mejin tausayinsu su dukansu, tabbas yasan akwai ƙauna me zafi atsakaninsu, wanda koda ace babu auren Hamma Saifuddeen akan Zaleeha, idan Hayatuddeen yaganta cikin damuwa zai ji ƙanta, kuma gashi nan damuwa ta bayyana ƙarara akan fuskarsa, sunyi imani cewa duk wani damuwan ɗayansu nasune su duka.
Cikin sanyi yasa hannu ya share hawayensa, muryarsa asanyaye yace. "Hayatuddeen nima bansan ya zanyi ba, Baba Malam yace. Bayason sake ganinta, yana fushi da ita sosai, kuma ta basa haƙuri ma yaƙi haƙura."
Sosai jikin Hayatuddeen da Imran yayi sanyi, dole da addu'a kawai zasu taya ta, dan basu da wani zaɓin daya wuce hakan.
Fitowar Adda Raleeya daga cikin gidan ne, yasa sukayi shiru da zancen, ƙarasowa wajen da su Zakariyyan suke tayi, ganinta yasa Hayatuddeen duban Zakariyya murya asanyaye yace.
"Mu zamu wuce."
Har bakin mota Zakariyya da Imran suka rakasu, saida yaga tafiyarsu sannan suka komawa cikin gida, zuciyarsa gaba ɗaya ba dadi, sosai tausayin Zaleehan ke damunsa.
Koda su Hayatuddeen suka koma gida kuwa kai tsaye ɗakin Ummi suka wuce. Har yanzun Zaleeha na duƙunƙune waje ɗaya, gefenta Ummi da Adda Rahama ne zaune.
Ƙarasowa cikin ɗakin Hayatuddeen yayi tare da zama akusa da ita, hannunta ya kamo, hakan yasa ta ɗago ta dubeshi da idanunta wanda sukai jajur, murmushi yaɗan ƙaƙalo akan fuskarsa, cikin kulawa yace.
"Adda Zaleeha kukan ki ya kusa ƙarewa Insha Allah, Baba Malam zai yafe miki nan bada jimawa ba, kuma Ya Ahmad ma da kansa yace agaisheki."
Zabura tayi tare da matsowa gab dashi, idanunta ta zuba masa, kansa ya jinjina mata alaman dagaske yake, idanunta ta lumshe, take kuma wasu sabin hawaye suka zubo mata, matsawa kusa dashi tayi tare da ɗaura kanta akan kafaɗansa, hannunsa ta riƙe ƙam tana sauƙe ajiyar zuciya.
Ganin haka yasa su Ummi sakin ajiyar zuciya suma, dan gaba ɗayansu burinsu bai wuce ganinta cikin nutsuwa ba.
Da misalin ƙarfe 6:20 pm Ameena tashigo cikin gidan, wanda dawowarta daga wajen aiki kenan, kai tsaye falon Ummi ta nufa bakinta ɗauke da sallama,
saidai rashin ganin kowa acikin falon yasa taɗan shiga mamaki, saboda yawancin lokuta falon Ummin bai rabuwa dasu Raleeya ko kuma auta Hayatuddeen, gashi yau kuma falon shiru babu motsin kowa.
Ganin haka yasa kaitsaye ta nufi ɗakin Ummi'n, hannunta riƙe da Adeel. Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin tayi, Adda Rahama dake zaune gefen Zaleehan ne ta bada izinin shigowa, nan ta tura ƙofar ɗakin ta shigo, bakinta ɗauke da sallama. Kusan dukansu ne suka amsa mata sallaman cikin kula, ƙarasowa cikin ɗakin tayi tana me mamakin ganin yanda suka taru su duka acikin ɗakin, cikin nutsuwa ta gaishe da Adda Rahama, amsa mata tayi tare dasa hannu ta karɓi Adeel, idanunta ne suka sauƙa akan kyakkyawar matashiyar budurwar dake zaune ta jingina jikinta dana Ummi, kanta kuwa na kan kafaɗan Hayatuddeen, wani irin bugawa taji ƙirjinta yayi, cikin nutsuwa tace. "Ummi sannu da gida." cikin kulawa da so Ummi tace.
"Yauwa Aminatu sannu, ya wajen aikin naku?" Ummi tayi mata tambayar batare da ta ɗago kai ta kalleta ba, saboda gaba ɗaya hankalinta naga Zaleeha, magungunan zazzaɓin da Hayatuddeen ɗin ya seyo, shi take ƙoƙarin ɓallewa dan bawa Zaleehan tasha.
Ƙurawa Zaleehan idanu Ameena tayi, cikin ranta tace.
"Ina su Ummi suka samo wannan balarabiya'n?" Tabbas tasan Zaleeha a hoto sai dai ashema rage kyanta hoto keyi, tabbas ita kallon balarabiya tayiwa Zaleeha'n, saboda kwata-kwata yanayinta baiyi kama dana mutanen Nigeria ba, musamman idan akayi duba da yanda dogon gashin kanta ya kwanto har zuwa gadon bayanta, ga kuma farin fatarta wanda yake na musamman ne, bawai irin farin fatar nan bane da wasu ke mutane ke ƙarawa da mai, natural fari ne me kyau da ɗaukar hankali, uwa uba matsanancin kyawun da tagani atattare da Zaleeha'n.
Cikin zuciyarta ta ƙara tambayar kanta, ko itaɗin wacece. Tunaninta ne ya katse alokacin da taji Ummi tace.
"Zaleeha tashi kisha maganin kinji, nasan zuwa anjima kaɗan zafin zazzaɓin zai sauƙa."
Wani irin luguden duka Ameena taji ƙirjinta nayi, cikin ranta ta maimaita sunan Zaleeha, take tunaninta ya bata cewa, itace Zaleeha matar Saifuddeen, ƙura mata idanu Ameena tayi, take kuma sai taji wani irin abu ya tokare maƙoshinta, wani irin haushin da tsanar Zaleehan ne taji ya cika mata zuciya, duban Hayatuddeen dake riƙe da hannun Zaleehan tayi, gani tayi idanunsa sunyi rau-rau kamar zaiyi kuka, tunda ta shigo ma ko ɗago kai baiyi ya kalleta ba, Raleeya da Adda Rahama ta kuma kallo, suma gani tayi rabin hankalin na kan Adeel gaba ɗaya rabin hankalinsu nakan Zaleeha'n, Ummi kuwa dama tuni hankalinta akan Zaleehan yake. Laɓɓanta ta cije, tare dajin wani abu na zazzafan kishi akan Zaleeha'n, bakomai kuwa yasa hakan ba, face tsananin kyawun Zaleehan da ta gani, ga kuma yanda su Ummi ke nan nan da ita, ganin cewa gabaki ɗayansu hankalinsu a tashe yake hakan yasa taja da baya, tana sakin murmushin dayafi kuka ciwo, ta fice daga cikin ɗakin, sam su hankalinsu ma ba'a kanta yake ba, shiyasa basusan cewa ta fita daga ɗakin ba.
Zaleeha kuwa asanyaye ta karɓi maganin tasha, lokacinne kuma aka soma ƙiraye ƙirayen Sallan magriba. Ameena kuwa tana shiga ɗakinta, tayi wurgi da jakanta ranta amatuƙar ɓace.
Iska ta furzar ta bakinta, tare da sanya hannu ta kama ƙugunta, ahankali ta taka ta ƙarasa gaban mirrror, tsayawa tayi tare dayin shiru tana ƙarewa kanta kallo, idanunta ta rumtse da ƙarfi, sam koda wasa, koda kuwa makaho bazai taɓa haɗa kyawun Zaleeha da nata ba, ita kamma mecece akyau? idanunta ne suka sake hasasho mata Zaleeha, take taji gabanta ya faɗi, tabbas hanyar jirgi daban haka ma kuma ta mota daban, zamewa tayi ta zauna akan gadonta, wani irin haushin Zaleeha da matsanancin kishinta ne ke tokare mata maƙoshi, taɓe baki tayi abayyane tace. "Jiyanda suke wani nannan da ita saikace wata ƴar gold, gaba ɗayansu kulawa suke nuna mata, jiyanda duk Hayatuddeen ya wani liƙe mata, hmmm."
kanta ta jinjina ganin zancen zuci bazai kaita ba, yasa ta miƙe tsaye kai tsaye ta wuce toilet. Gaba ɗaya ta mance a fagen kishi da aurataiya ba'a surka kyau a mizani ta mance cewa kowa ya iya Allonsa ya wonkene mata nawane munana na bugawa a mujalla kuma sune star a gidajensu
Can ɗakin Ummi kuwa ƙiran sallan magriba da akayi ne yasa Hayatuddeen tashi ya wuce masallaci, Raleeya ma ɗakinta ta koma don yin sallah, Adda Rahama kuwa shirye-shiryen tafiya ta somayi, sam bama da niyan kaiwa dare tazo ba, saidai ganin halin da Zaleeha take ciki yasa bata tafi da wuri ba.
Zaleeha kuwa babu laifi ta ɗanji sauƙin zazzaɓi da kuma ciwon kan daya rufeta.
Hakan yasa ta ɗauro alwala tazo ta gabatar da sallah, koda ta idar da sallan bata tashi akan sallayan ba, jingina tayi da jikin gadon Ummi, tare da lumshe idanunta, wasu siraran hawaye ne suka biyo ta gefen idanunta suka sauƙa akan fuskarta. Dai-dai lokacin Ummi ta shigo cikin ɗakin, ƙarasowa jikin gadon tayi ta zauna.
Cikin kulawa ta ƙira sunan Zaleeha'n, ahankali taɗan ɗago kanta ta kali Ummi'n. kafaɗunta Ummi ta dafa cikin son sake bata karfin guiwa tace.
"ki kwantar da hankalinki, Insha Allah gobe zamuje za'a bawa Baba Malam haƙuri, kuma nasan zai haƙura ya yafe miki, sannan kuma Baba Malam ba tsanarki yayi ba, hakama ƴan uwanki, kawai dai suna fushi dake ne, saboda abun da kikayi baki kyauta ba sam, bawai dan kina auren Saifuddeen bane yasa nace haka, a'a ina faɗa miki hakane dan ni matsayin ƴa na ɗauke ki, ke macece Zaleeha, duk kuwa mace me tarbiya irinki ba a santa da gudu ta bar gida ba, haka kuma ɗabi'ar guduwa ma sam bai kamata ace mace ta ɗaukesa ba, bazan tursasaki faɗamin dalilin dayasa kika gudu ba, saboda nasan dama tuntuni bakyason auren ki da Saifuddeen, bakya sonshi dole akayi miki amma kuma duk da haka bai kamata ki tsalleke iyayenki ki tafi can wata duniya ba, nasan kinyi nadama kwarai, kuma insha Allah Allah Zai karɓi tubanki, kuma Baba Malam ma nasan zai yafe miki, kawai dai yana fushi ne saboda yanda kikayi watsi dasu, amma nasan da zaran anbasa baki zai yafe miki, saidai kuma ina fatan zaki kiyaye gaba, sannan kowata kikaga zata aikata irin abun da kika aikata zaki haneta." Tuni hawaye sun gama wankewa Zaleeha fuska, tabbas tasan bata kyauta ba, kunyar Ummi ta rufeta yadda ta gane cewa bata son ɗanta ita kuma duk da haka bai hanata so taɓa. wanda dalilin hakanne kuma kowa ke fushi da ita, ƴan uwanta sun ƙita saboda abun da ta aikata, Babanta mahaifi ya koreta duk akan abun da ta aikata, tabbas Ummi ta cika uwa ta gari, abun so ga kowa, ta aikata musu laifi amma sun ƙaunace ta, alokacin da kowa ya nuna mata tsana, su kuma sunjawota jikinsu, Babanta ya koreta, su kuma sun amsheta duk da laifin da ta aika ta musu suka bata mafaka, tayaya zata fara misalta girman halaccinsu agareta? abune me girma da bazai kwatantu ba, kukane ya ƙwace mata sai kawai ta kifa kanta akan cinyar Ummi, ta saki kuka'n.
Awannan karon Ummi batayi yunƙurin hanata kukan ba, saboda ko ba komai shi kukanne zai rage mata zafi da raɗaɗin zuciya.
Saida Ummi taga kukan yayi yawa sannan tashiga ɗan bubbuga bayan zaleehan tana shafa kanta.
Sannu ahankali ta rage sautin kukan nata, shiru tayi tana sakin ajiyar zuciya.
Ganin haka ne yasa Ummi kamo hannunta suka fice daga cikin ɗakin, kai tsaye ɗakin dake gefen na Ummi'n, Ummi takaita, wanda yake ɗakin su Raleeya ne wanda sukai budurci acikinsa, kuma nanne masauƙin Goggo Dada da Aunty Meena in sun zo, akimtse ɗakin yake sannan babu wani hargitsi acikinsa, akan gado Ummi ta zaunar da ita, toilet ɗin ɗakin ta shiga ta haɗawa Zaleehan ruwan wanka me ɗan ɗumi. Dubanta Ummi tayi cikin kulawa tace.
"Kishiga kiyi wanka, zuwa gobe an gane key ɗin side ɗinki, dan yanzu na tambayi Hammansu key ɗin yace baisan inda key ɗin yakeba sai ya nema,
shiga na kiyi wonka sai kizo ki kwanta, ko za ki ci abinci nasa Hayatuddeen ya kawo miki."
Asanyaye ta girgiza kanta alaman
"A'a" jinjina kai Ummi tayi sannan ta fice daga cikin ɗakin, tana mai tuna za'ayi daga da Saifuddeen dan tasan batun wai shi baisan inda key ɗin side Zaleeha yakeba duk cikin fushine ta lura ya fusata sosai da Zaleeha.
Ita kuwa Zaleehan cikin sanyi ta tashi ta shiga toilet ɗin, wanka tayi sannan ta ɗauro al'wala'n sallan isha, rigar da ta cire shi ta sake mayarwa, wanda dama doguwar rigar atamfa ce ajikinta. Koda tayi sallan ta jima akan sallaya tana addu'o'i, har kusan ƙarfe tara na dare tana nan zaune akan sallaya'n, daga ƙarshe kuwa anan kan sallayan ta kwanta tare da lulluɓe jikinta da bargo, luf tayi tana sakin ajiyar zuciya, hawaye kuwa na tsiyaya daga cikin idanunta.
A ɓangaren Saifuddeen kuwa dawowarsa daga sallan isha kenan, kai tsaye bathroom ya nufa, wanka yayi haka ya fito jikinsa sai tashin ƙamshin turaren wanka yake, tura wheelchair ɗinsa yayi zuwa gaban dressing mirror, cikin nutsuwa ya shafawa jikinsa mai me daɗin ƙamshi, body spray ya fesa, sannan yaja wheelchair ɗinsa ya ƙarasa gaban drawer'nsa, wani 3 quater jeans ya sanya tare da wata blue ɗin t-shirt me kyau, sake feshe jikinsa da turare yayi sannan ya ƙarasa inda laptop ɗinsa yake, ɗauka yayi tare da ajesa akan cinyarsa, cikin nutsuwa ya soma ɗan daddanawa. Ahankali ta turo ƙofar ɗakin ta shigo, tasha kwalliya cikin wata sleeping dress me kama jiki, kana ta sake ɗan gashinta wanda iya kansa ya kwanto kan wuyanta, tsaye tayi ajikin ƙofan tana kallonsa, sosai yayi mata kyau, akullum indai ta ɓangarenta ne ƙara kyau yakeyi tana masifar sonshi shiyasa take tsananin kishinsa ji take tamkar dan ita ɗaya aka halicceshi, shikuwa Saifuddeen sam ma baisan da zuwanta ba, saboda ya bawa ƙofar shigowa ɗakin baya sannan kuma gaba ɗaya hankalinsa akan laptop ɗinsa yake. Murmushi ta ɗanyi tare da takowa ta ƙaraso inda yake, hannuwanta tasa ta bayansa kana ta rungumesa, ɗan lumshe idanunsa yayi, tare da cije laɓɓansa, dama yasan aje azo dole saitazo ta katsesa daga abun da yakeyi.
Ameena kuwa zagayowa ta gabansa tayi ya zamana suna fuskantar juna, wani irin annuri ta hango akan fuskar tasa, take taji ƙirjinta ya buga, shikuwa Saifuddeen ganin yanda ta ƙuresa da ido ya sashi ɗan sakar mata murmushi. Itaɗinma murmushi ta mayar masa, tare da ɗan duƙowa tayi kissing ɗinsa akan forehead ɗinsa, ɗago kyawawan idanunsa yayi ya kalleta, ɗan lumshe idanunsa yayi tare da miƙa mata hannunsa, kama hannun nasa tayi, shikuwa ya jawota cikin jikinsa ya ajiyeta kan cinyoyinshi ya zama suna fuskantar juna da kyau, wani sakalin murmushi yayi mata tare zaro harshensa waje yana ɗan karkaɗa mata wani irin abu taji ya ratsa jiki da zuciyarta, ido ta zuba mishi ganin ya sanya lips ɗinsa yaɗan yiwa kumatun ta kiss, wani irin sanyi taji acikin ranta, hannayensa ya sanya ya tallafo haɓarta, haɗe fuskarsu waje ɗaya
Showing 105001 words to 108000 words out of 237945 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36 Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80