cikin ɗakin tare da faɗawa jikinsa ta ruggumeshi gam-gam kamar mai tsoron a kwace mata shi, cikin tsananin farin ciki tasaki wani irin kukan farinciki, sam ta ma manta da su Dr.Adnan dake cikin ɗakin.
Hannunshin yasa ya dai-dai ta kanta dake kanshi cikin sanyin murya tace.
"Aminatu Zaki ƙara ɓalle bayan ki rasa na yin lilo gaba".
Cikin wata irin yar salama da jin daɗi tasa hannu ta shafi gefen fuskarsa, cikin matsanancin farinciki tace.
"Alhamdulillah Ya Allah, Alhandulillah." Murmushin ƙarfin hali yaɗan sakar mata, tare da sanya hannu ya amshi Adeel, dake ta dariya yana wutsil-wutsil da ƙafafunsa kamar yasan farin cikin da sukeyi.
Rungume yaron nasa yayi, yanajin wani matsanancin farinciki acikin ransa.
Ameena kuwa ɗan sharce hawayen dake cikin idanunta tayi, tuna cewa su Dr Adnan na ɗakin yasa ta ɗan janye jikinta baya, tare da cewa.
"Abban Adeel yaushe ka fara magana?." Kasa amsa mata yayi saboda yanda yaji bayansa na wani irin duka, idanunsa ya rumtse da ƙarfi sosai, Dr Adnan ne yaɗan riƙe masa hannu, tare da zaro wayarsa, numbern Dr Aleeyu ya laluɓo, sannan ya danna masa ƙira. Bugu ɗaya kuwa ya ɗauka.
Bayan sun gaisane Dr Adnan ya ɗan gyara zamansa.
Cikin nutsuwa yacewa Dr Aleeyu.
"Sir jikin Saifuddeen ne fa ya tashi sosai fa, amman kunnuwansa kuma sun buɗu yanzu duk wani motsi yanaji, sai-dai amma tun ɗazu yake ta complain cewar bayansa ya riƙe, yanzu haka ko zama da kyau baya iyawa, nakasa gano kan matsalan nasa, dan harma yace wai ko zamu koma India ne." Sosai Dr.Aleeyu yaji daɗin buɗuwar kunnuwan Saifuddeen ɗin, saidai jin wata matsala da ta kunno kai duk sai yaji babu daɗi acikin ransa, sai-dai yasan hakan ma wani matakin nasara ne a jinyar tasa dogon numfashi yaja cikin kulawa yace.
"Ai dama lokacin komawarsa india yayi harma ya wuce, bansan me yasa bayason komawa asibiti ba, lalle ya zama dole amaidashi india, dole anjima zan biyo jirgi nazo, zan taho da wasu allurai da magunguna wanda xasu ɗan rage masa pain kafin a samu wucewa dashi India, ka gayawa Ahmad ya fara nema musu damar tafiya tun daga yanzu yayi musu bukin ta online."
Cikin jin daɗin hakan Dr. Adnan yace.
"Okay Sir shikenan sai kazo".
da haka sukayi sallama, yana ajiye wayar kuwa Ummi ta shigo cikin ɗakin.
Ganin Ummi yasa Ameena tashi da sauri ta ƙarasa jikin Ummin cikin tsananin farinciki tace. "Alhamdulillahi Ummi, kunnuwan Abban Adeel sun buɗe ya fara jin magana, Alhamdulillah Ummi, tabbas Allah abun godiya ne."
Kai Ummi ta jinjina tare da cewa.
"Tabbas Ameena Allah abun godiyane, gashi cikin ikonsa ya buɗe masa kunnuwansa." Murmushi Ameenan tayi tana kallonsa, ji take kaman ta maidashi cikin jikinta tsabar murna.
Dr Adnan ne yayiwa Ummi bayanin yanda sukayi da Dr Aleeyu, sosai Ummi taji zuciyarta, ta gamsu da zuwan Dr Aleeyun saboda, yanda taga Saifuddeen nacije laɓɓansa, tasan yanajin ciwo sosai.
Ameena ne ta kalli Umm'in, cikin kulawa tace.
"Ummi ina Zaleeha?" Ɗan jim Ummi tayi cike da tausayawa tace. "Zaleeha bata da Lafiya, yanzu haka tanacan sashin Saifuddeen, akwance sai rawan sanyi take, zazzaɓi ne me zafi ya sauƙar mata, so nake idan Dr Adnan ya gama da Saifuddeen, sai muje yaɗan duba ta."
Idanu Ameena ta zaro tare da cewa. "Subahanallah, Allah sarki bari naje na duba ta, ko akwai wani taimakon da zan iya bata".
Kai Ummi ta jinjina, sannan Ameenan ta juya nufin fita,
sai kuma ta tsaya jin an riko hannunta ganin Saifuddeen ne yasa ta matsoshi cikin lumshe ido yace.
"Aminatu Kada ki ce mata kunnena ya buɗu kuma ina iya mgna, kinji ko Ummu Adeel".
Cikin jin daɗin yadda yake yawan kiranta da yadda yake kiranta Aminatu kana da mmki ta gyaɗa kai a ranta tace.
"To meyasa za'a ɓoye mata wannan abin farin ciki, to ko dan bata da lfy ne".
Kai kawai ta gyaɗa kana ta juya ta fita daga cikin ɗakin.

Kamar yanda Ummi ta faɗa mata kuwa, kaitsaye sashin Saifuddeen ɗin ta wuce, ganin bata ganta afalo ba, yasa tayi tunanin cewa tana ɗaki.
Tana shiga kuwa ta samu Adda Rahama zaune agefenta, dan har yanzu Zaleehan bata daina sakin sheshsheƙan kuka ba.
Ƙarasowa cikin ɗakin tayi, cikin kulawa ta zauna abakin gadon tare dakai hannu taɗan taɓa wuyan Zaleehan, jin jikin Zaleehan zafi zau yasa tace.
"Subahanallahi Ammin Adeel sannu ya jikin naki?".
Kai kawai Zaleeha ta iya jinjina mata dan batajin zata iya wani dogon magana.
Ɗan sake taɓa jikin Zaleehan tayi, tare da duban Adda Rahama, tace.
"Adda Rahama miyene yake damunta bayan zazzaɓi?."
Ajiyar zuciya Adda Rahama tayi, asanyaye tace.
"Tace min tanajin jiri da kuma ciwo acikin jikinta, danko tafiya ma batayi da kyau, nadaiyi mata sit bath, amma gashi nan dai sai rawan sanyi take." Wani irin ƙaton abune ya daki ƙirjin da ran Ameena, har saida taji kanta yaɗan juya mata duhu ya gilmawa ganinta, take ta gano matsalan Zaleeha'n, murmushi taɗanyi tare dayin ƙasa da kanta tana jin wani sassanyan abu a ranta da zuciyarta da sauri ta katse shaiɗan da yin tasbihi, gaba ɗaya ji tayi jikinta yayi sanyi, sai-dai kuma yauɗin ranace ta daban agaresu ranace ta farin ciki su budurcin Zaleeha ya zame musu abin al'fahari tunda sanadin ƙarɓarsa a samu gagarumar nasara a rayuwar mijinta abin soyuwa.
Wayarta ta ciro inda ta laluɓo numbern wata ogarsu Dr Fateema, wanda take nan kusa dasu dan gidanta baida wani nisa, Dr Fateeman na ɗagawa, ta matsa ɗan gefe tare dayi mata bayani, kan cewa suna da patient agida, sannan tayiwa Dr Fateeman bayani, kan cewa ita bazata iya aikin ba.
Da yake Dr Fateema'n, macece mai sauƙin kai hakan yasa tace wa Ameenan gatanan zuwa, dan dama tana gida bata fita ba. Babu wani jimawa kuwa, saigata tazo, ganin yanda jikin Zaleehan yayi zafi sosai yasa tace su bata waje, zata dubata.

Babu musu kuwa Adda Rahama da Ameena suka koma falo.
Duba Zaleehan tayi, sosai, ganin babu rauni sosai aƙasan nata yasa ta bata wasu magunguna tasha, wata alluran kashe zafi da zogi tayi mata, sannan ta ɗaura mata drip tare dasa alluran zazzaɓi.
Cikin abun da baiwuce 10 minute ba bacci ya ɗauki Zaleeha.
Dr Fateema na fitowa daga ɗakin su Ameena suka nufota cikin sauri. Ameena ce tace.
"Dr Yajikin nata?." Ɗan murmushi Dr Fateema'n tayi, tare da cewa.
"Ku kwantar da hankalinku, jikinta da sauƙi, dan harma ta samu bacci, kuma bawani babban damuwa bane, kunsan dama yawanci irin haka yana faruwa idan akayi dis virgin ɗin mace, mussamman idan ya zamana namijin yaje mata da ƙarfi, ko kuma manhood ɗinsa ya zamana, yafi ƙarfin privet part ɗinta, wanda sai ahankali ne kuma zata saba, thank god ma babu rauni sosai ajikinta, yanzu dai tana da buƙatar hutu, so please abarta taɗan huta." Jinjina kai sukayi su dukansu cike da gamsuwa,
Ameena kuwa ido ta rumtse jin hawayen kishi zasu zubo mata a ranta tace.
"Ashe da kam duk kishin banza nakeyi nagodewa Allah dayasa bai kusanceta tun ina kan jahilin kishin nanba na sani da mutuwa zanyi. Har waje kuwa Ameena ta raka Doctor ɗin.
Saida taga tafiyarta sannan ta dawo gida tana tafe tana mgnar zuciya da share hawaye.
"Ai kam dole taji azaba dan Abban Adeel ingarman namiji ne".

Ganin Zaleehan na bacci, yasa Adda Rahama jawo ƙofan ɗakin ta rufe, sukuma suka koma sashin Ummi.

Suna zuwa kuwa suka samu Raleeya ta kammala breakfast, da ƙyar Adda Rahama tasa Saifuddeen ya ɗanci wani abu acikinsa, dan yace musu ji yake bayansa na harbawa. Ɓangaren Zakariyya kuwa suna gama waya da Hayatuddeen, cikin gida ya wuce, anan falon Baba Malam yasamu Mama da kuma Mamy, harma da Ya Ahmad, anan yake sanar musu cewa, jikin Saifuddeen ɗin ya tashi.
Sosai Baba Malam ya shiga damuwa, nan yace su Mama su shirya idan akayi sallan azahar zasuje su dubashi.


Ameena ma ta kira Daddy ta sanar mishi batun jikin Saifuddeen kuma yace yana nan tafe gobe,
hakama ta kira Mamanta ta sanar mata, inda ta haɗata da Ummi suka gaisa, ta jajanta mata jikin Hamma Saif ɗin kana tace suma in Allah ya nufa gobe zasu taho.

Kusan atare motocin Su Wareesu dana Ishaq Salisu suka shigo cikin gidan.
Dan dukansu Ahmad ya ƙira ya sanar musu. Koda suka shiga cikin gidan, Raleeya ce tayi musu jagora zuwa ɗakin Hayatuddeen ɗin.
Lokacin da sukaji muryan Saifuddeen wanda ganinsu ne ya sashi buɗe muryarshi ya amsa Salllamarsu da ƙarfi yadda duk zasuji muryarshi ai kuwa dukansu babu wanda bai ji muryar tashiba.
Hannu yasa ya kamo hannun Ishaq dake ƙoƙarin kamo nashi cikin tsanyi yace.
"My Ishaq gani nan kusa da kai".
Wani irin riƙo Ishaq yayiwa hannun Saifuddeen cikin tsananin farin ciki yace.
"Allahu akbar Allah mai iko da girman buwaya. Buwayi gagara misali Alhamdulillah ko yanzu na mutu Allah ya cika min burina laruran Aminina sun ragu".
Wani irin raunine ya baiyana a fuskar Saifuddeen murya na rawa yace.
"Ni kuwa ina roƙon Allah ya aramin rai da lfy, ya nuna min lafiyarka inga kaima kana gani da idanunka".
Kusan a tare Ahmad da Salisu ds Mudassir da Warisu sukace.
"In sha Allah, shima Allah zai bashi lfy".
Salisu kuwa tuni hawaye sun wonke mishi ido sai yake tuno irin gogormoya da suka sha shida Saifuddeen a cikin bulayin neman halal ɗinsu a lokacin badon ƙarfin imaniba sai su kauce hanya, sabida tsananin uƙubar talauci da wahalar rayuwa
hannu Saifuddeen yasa yana share masa hawayenshi, shi kuwa sai maimaita kalmar Alhamdulillah yake tayi.
Warisu kuwa murmushi yayi tare da cewa.
"Ya Allah ka nuna mana randa zaka tsaya da kafafunka kamar yadda ya jiyar damu mgna da muryarka".
Amin Amin yace kana ya kalli Salisu tare da cewa.
"Haba Salisu godewa Allah zamuyi ba kuka ba".
Cikin sauri duk suka rinƙa maimaita Alhamdulillah,
Ahmad ne yayi dariya tare da cewa.
"Daga dare ɗaya Zaleeha tayi sanadin dawo mana da bakinshi da kunnenshi, a dare na biyu kuma ƙugu kam zai ida ɓalgawacewa in mutun bai jira kanshi ba".
Dariya sukayi baki ɗaya dan sun gano kurman baƙin da Ahmad ya musu,
shi kuwa Saifuddeen mare ƙeyan Ahmad yayi,
lokaci ɗaya kuma ya riƙe hannun Ishaq da karfi dan sarawar da yaji ƙugunshi nayi cikin dakiya yace.
"To mugaye masu cewa Allah yasa ƙuguna ya ida ɓalgacewa, kunji daɗinku ya ɓalgace ɗin".
Dariya sukayi baki ɗayansu.
Ganin alamun yana cikin ciwo ne yasa suka sarara mishi suka koma falo.

Kafun sallan Azahar tuni gidansu Saifuddeen ɗin ya cika da jama'a, ƴan uwa da abokan arziki da maƙota, harma dasu Bappa Ali da suka samu isowa, acikin gidan fuskar kowa ka kalla zaka ganta ɗauke da zallan farinciki, da kuma jindaɗi.


Kusan ƙarfe 3 na yamma, su Baba Malam suka samu isowa gidan. Tarba me kyau Ummi tayi musu, inda Baba Malam yashiga har ɗakin Hayatuddeen ya gaishe da Saifuddeen ɗin. Mama ma haka ta gaishesa tana ta faman sunne kai, dan kunyansa takeji.
Ahamad ne yaja Baba Malam gefe ya sanar dashi buɗewan kunnen Saifuddeen.
Sosai Baba Malam yaji daɗi, sam baiga laifin Saifuddeen ɗin ba kuma da yace a ɓoyewa Zaleeha hakan, dan yasa komai Saifuddeen yana yinsane cikin hikima da kuma dalili tabbas yasan yanada dalilin da yasa yace a ɓoye matan.

Jin cewar Zaleeha na kwance bata da lafiya, yasa Mamy zuwa ta dubata, Mama kam da Baba Malam basuje ba, saboda abun akwai nauyi sosai.

Har zuwa tafiyansu kuwa Zaleeha bacci take batasan ma da zuwansu ba.

Haka gidan nasu ya cigaba da amsan baƙi har kusan dare.
Sai Bayan sallan la'asar Zaleeha ta farka daga nannauyan baccin da take.
Dai-dai lokacin kuwa Adda Rahma da Raleeya suka shigo, da taimakonsu tayi wanka, dan taɗanji dama daman jikinta, sai-dai tafiyan natane har yanzu bai dawo dai-dai ba.
Da taimakon Adda Rahama ta koma ɗakinta, sallan Azahar da la'asar tayi.sanna Ta kwanta.

Ƙarfe biyar dai-dai Dr Aleeyu yaso daga Abuja kai tsaye gidan su Saifuddeen ɗin ya Adnan ya kawoshi, ya dubashi yayi da kyau kana yayiwa Saifuddeen allurai da kuma magunguna, ba laifi kuma yaɗanji sauƙi.

Bayan sallan isha ne Ya Ahmad da Aunty Lubna suka zo suma dan dubashi da jiki

Bayan sun gaishe da Saifuddeen ɗinne. Raleeya tayiwa Aunty Lubna jagora xuwa ɓangaren Zaleeha. Zaune suka sameta akan sallaya, tayi jigum, ganin Aunty Lubna yasa ta kwaɓe fuska, sai kuma ga hawaye sun soma tsiyaya daga cikin idanunta.
Ƙarasowa cikin ɗakin Aunty Lubna tayi tare da zama akan wani ɗan stoll ɗin dake gefen gado, a hankali ta kamo hannun Zaleehan cike da kulawa tace.
"Sannu Zaleeha ya jikin naki".
Kasa amsa mata tayi, saima samun kanta tayi da ɗan jan jikinta, ta ɗaura kanta tayi akan cinyar Aunty Lubna'n, lokaci ɗaya ta kwaɓe fuska cikin zallan shagwaɓa tai rau-rau da ido.
Ganin haka yasa Aunty Lubna ta ɗanyi murmushi dan tasan mai neman kukane aka jefa da kashin awaki, ahankali ta soma shafa kanta, cikin sanyi da kuma lallashi tace.
"Ya isa haka Zaleeha kada kiyi kukan, ciwon me kuma yake damunki harda kuka?" ɗago kanta daga cinyar Aunty Lubnan tayi cikin naƙe murya tace.
"Zafi nakeji Aunty duk jikina ciwo yake min, sabida muguntar da Hamma Saif yamin."
Danne dariyarta tayi tare da cewa.
"Kenan nima sai ince ya Ahmad ɗinki ma mugunta yaita min".
Kai ta jujjuua tare da cewa.
"Allah nasan da kinyi ta magiya da roƙon ya Ahmad ya barki yadda nai ta mishi jiya da dare nasan zai barki.
Shi dai mugune, babu irin kuka da roƙon da banyi masa ba, amma yaƙi jina, zafi nakeji sosai Aunty ko tafiya mai kyau bana iyawa, gashi ma harda zazzaɓi nakeyi."
Sosai Aunty Lubna ta gane sanadin ciwon Zaleeha'n, ɗan sake shafa kanta tayi.
Cikin kulawa tace.
"Kiyi haƙuri Zaleeha kowa ma yaji hakan, amma da sannu yake wucewa, banaji Ummi tace likita ta dubaki ba." Ashagwaɓe ta gyaɗa kanta, cikin lumshe ido tace.
"Amma Aunty Lubna meyasa zaimin haka, yanzu fa ko ƙarfi banaji ajikina."
Ɗan guntun murmushi Aunty Lubna'n, tayi, tare da cewa.
"To yanzu ai yayi mgnin guduwa da bakin tsiwa.
Ai haƙuri kawai zakiyi , shima dakike magana akai ai ba daɗi yakeji ba, yanzu haka ma fa shi mukazo dubawa, jikinsa babu daɗi, ciwonsa ya tashi, ko ɗazu ma su Baba Malam harma da Mama sunzo dubashi." Idanunta ta zaro waje, cikin yanayin damuwa da fargaba tace.
"Bashi da lafiya kuma Aunty, to me ya sameshi?." "Bayansa ne ke ciwo, dan ma naji ance sai an fitar dashi India, yanzu dai ki lallaɓa kije ki duba shi, yana can sashin Umminsa."
Hakanan taji wani irin matsanancin tausayinsa ya dirar mata azuciya, take taji zuciyarta ta karye taji tana son ganin shi.
Miƙewa tsaye Aunty Lubna tayi tare da cewa. "Ni kam zan wuce, dan tare ma muke da Yayanki, nace bari na shigo naɗan dubaki." Hannun Aunty Lubnan ta kama sannan ta miƙe tsaye, cikin yanayin shanye ciwon da takeji, tace.
"Aunty muje na gaishe da Ya Ahmad, tunda dai yaƙi shigowa."
A cikin ranta kuwa cewa tayi.
"Daga nan zan ganshi ai, in banda Hamma Saif kai kamin fyaɗe kuma kaima wai baka da lfy mu duka mun zama majinyata".
Murmushi Aunty Lubna tayi, tace.
"Baƙin shigowa yayi ba, suna tare da me sunansa ne."
(Wato Ahmad mijin Raleeya.) Kaita ɗan jinjina, sannan ta kama hannun Aunty Lubna'n, haka suka fito daga cikin sashin nata, ahankali take tafiya, sai faman ciccije baki take, kasancewar tana ɗanjin zafi acikin jikinta.
A compound ɗin gidan, suka iske Ya Ahmad da kuma Ahmad atsaye, suna ɗan tattaunawa, wanda kuma duk akan matsalan Saifuddeen ɗinne, kana anan Ya Ahmad ke ce mishi suma gobe zasu koma Abuja.
Ganin Zaleeha yasa Ya Ahmad ɗin sakin murmushi, cikin kulawa yace.
"Ha'a marar lafiyance da kanta, har kin warke kenan?."
Ɗan shagwaɓe fuska tayi tare da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba, asakalce tace.
"Nidai Ya Ahmad
Showing 198001 words to 201000 words out of 237945 words