yi mata kyau sosai, hijab ta sanya sannan ta tada sallah, saida tayi raka'atanul fajir, sannan tayi sallan asuban, koda ta idar Azkar tayi sannan taɗan taɓa karatun Alƙur'ani.
Tana kai karshe kuwa miƙewa tayi, wani ɗan ƙaramin vail ta yane kanta dashi, sannan ta fesa turarenta me dadin ƙamshi, wayarta ta ɗauka, sannan ta nufi hanyar fita daga ɗakin, cikin nutsuwa ta murɗa handle ɗin ƙofar ta fice. Kanta tsaye sashin Ummi ta nufa, bakowa afalon, hakan yasa ta nufi ɗakin Ummi kaitsaye, tana knocking kuwa aka bata izinin shigowa, murɗa handle ɗin ƙofar tayi ta shiga, anan kan sallaya ta samu Ummi najan carbi, durƙusawa tayi ta gaisheta cikin girmamawa, fuska asake Ummi ta amsa, mata. Bata wani jima aɗakin Ummin ba, ta miƙe tsaye, kaitsaye ɗakin Goggo Dada ta shiga, nan ta iske goggo dadan itama najan carbi, cikin girmamawa ta gaishe da goggo dada'n, haka goggo Dada ta amsa mata cikin kulawa da sakin fuska.
Koda ta fito daga ɗakin goggo dadan, anan falo suka haɗu da Raleeya, bayan sun gaisane, suka nufi kitchine saboda ɗaura breakfast, Raleeya ne me fere dankali, ita kuwa Zaleeha ferfesu take haɗawa, sai kuma sandwich, aikin suke cikin nutsuwa suna ɗan taɓa hiransu. Koda Ummi ta fito falo, ganinsu a kitchine suna aiki,yasa tayi murmushi, nan kan kujera ta zauna, tare da maida hankalinta ga TV inda take kallon Sunnah tv. Saifuddeen kuwa tunda ya tashi da asuba ya wuce masallaci bai dawo ba sai yanzu, tafe suke Hayatuddeen na riƙe masa saman kekensa, sai zuba yake yana basa labarai kala-kala, ahaka suka ƙaraso falon Ummin.
Ummi naganinsu haka ta saki murmushi, har acikin ranta tana godewa Allah daya haɗa mata kan ƴaƴanta, kana yasanya musu soyayyar juna azuƙatansu, wannan haɗin kan nasu shine matakin nasaran rayuwarta.
Ƙarasowa gabanta Saifuddeen yayi, cikin body language ɗinsa ya gaisheta, amsa masa tayi tana murmushi. Hayatuddeen ne yazo ya zauna akusa da ita, cikin kulawa ya kamo hannunta yace.
"Ummi kinsan me?" dubansa Ummi tayi da kyau, dan duk atunaninta serious magana ce, cikin nutsuwa tace.
"A'a saika faɗa." pink ɗin laɓɓansa wanda suke shige dana Hammansa ya lashe, tare da cewa.
"Wallahi Ummi ƙamshin girki nakeji tun fa kam mushigo cikin falon nan, tun da ga gate, to ni narasa a ina ƙamshin yake fitowa."
ya kare maganar yana ɗan kallon ƙofar kitchine. Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Ehem aikin kenan, to su Raliya ne suke dafa break fast."
Murmushi yayi tare da suɗe bakinsa, dan dama yunwa yakeji.
Dai-dai lokacin kuwa Zaleeha ta fito daga kitchine din hannunta ɗauke da food flask, lumshe kyawawan idanunsa da suka sauƙa akanta yayi, sosai tayi masa kyau cikin jan rigar saikace wata sarauniya, Raleeya ne ta fito da sauran kayan abincin da suka girka, nan suka shiga jerawa akan dinning table. Ameena ce ta shigo cikin falon, Adeel rungume akan kafaɗanta. Sanye take da uniform ɗinta na aiki tayi kyau sosai cikin shigar nasu.
Ƙarasowa cikin falon tayi, tare da durƙusawa ta gaida Ummi.
Cikin kulawa Ummi ta amsa, tare da tsare Ameenan da ido, cikin kulawa hankalinta a tashe, tace. "Subahanallahi Ameena me ya samu idanunki haka naga sunyi ja?". Ɗan sadda kai ƙasa Ameenan tayi, murya aɗan sanyaye tace. "Babu komai Ummi, kawai dai mura ne keta damuna jiya kusan kwana nayi banyi bacci ba, saboda tari da atishawa."
Kai Ummi ta girgiza cikin tausayawa haɗi da kulawa tace.
"Allah sarki, sannu kinsha magani kuwa?" Kaita jinjina alaman "Eh" Hayatuddeen ne yace. "Ayya Aunty Ameena sannu ko."
Ɗan murmushi tayi masa tare da jinjina kanta, Saifuddeen kuwa idanu ya zuba mata, yana me mamakin ƙaryar da ta zabga, yanayin yanda yaga fuskarta yasa shi gane cewa kwana tayi batayi bacci ba, shikam yarasa irin kishin Ameena, dan kishine da takeyinsa babu wani dalili. Zaleeha dake tsaye nan kan dinning area, jin cewar Ameenan bata da lafiya ne yasata ɗan ɗago kanta, cikin sakin fuska tace.
"Ummu'n Adeel barka da safiya, ya jikin?" Jin muryan Zaleehan yasa ta ɗago dakai ta kalli inda taji muryar Zaleehan na fitowa, wani irin bugawa kirjinta yayi, take taji wani irin masifaffen kishi ya sake rufeta, musamman ma ganin yanda Zaleehan tayi kyau cikin doguwar rigan jikinta, haushi da takaicin Zaleehan ne suka turnuƙe mata zuciya, gudun kada su Ummi su zargi wani abu, yasa ta ɗan danne zuciyarta, murmushin yaƙe, wanda yafi kuka ciwo ta saki, can ƙasan maƙoshi tace.
"Yauwa barka, jiki Alhmdlh."
Kai Zaleeha ta jinjina cikin sanyin da ta dawo ɗabi'arta tace.
"Masha Allah, Allah Yaƙara sauƙi."
Kasa amsa mata tayi, dan kuwa wani abune yazo yayi mata tsaye acikin rai, jin muryar Zaleehan acikin kunnuwanta yasa taji kaman ta kurma ihu, ƙasa-ƙasa ta watsawa Zaleehan harara, cikin zuciyarta tace.
"Shegen iyayi, koma menene ai duk sanadinki nasamu kaina ahaka, wallahi da ace ina da yanda zanyi Saifuddeen ya daina ganinki acikin gidan nan da nayi, lokacin da bakyanan ai hankali akwance yake, yanzu kuma da dawowarki da shegen farar fuska kaman mayya duk kin wargaza min nitsuwa ta."
Ta ƙare maganar tana me sakarwa Zaleehan harara ƙasa-ƙasa, Zaleehan, ko zataji sanyi aranta.
Ummi kuwa ganin su Zaleehan sun gama shirya break fast ɗinne yasa tace.
"Dukansu su tashi suje suci abinci." Anan kan dinning suka zauna, yauma kamar kullum Zaleeha ne tayi seving ɗinsu, inda take komai nata acikin nutsuwa. Saifuddeen kuwa gaba ɗaya yau yakasa ɗauke idanunsa akan matan nasa Zaleeha'n, tayi matuƙar kyau, ga fresh skin ɗinta dake ta shinning,
Ameena kuwa tausayinta yakeji da yanada hali da ya yaye mata wannan kishin ta huta, ahankali yake tauna abincin bakinsa, yana wani irin lumshe ido, sosai yakejin daɗin abincin Zaleeha'n, dan zai iya cewa agidan bayan Umminsa babu wanda yakai Zaleeha iya girki duk da yasan Ameena ma ba tayar bayaba bace. Ameena kuwa gaba ɗaya ko daɗin abincin ma bataji abakinta, cuccusawa kawai take, komai bayayi mata daɗi, saboda zafin kishin da ta sawa kanta, ɗan ɗagowa tayi ta kalli gefen Saifuddeen, dan tun da suka zauna bata ɗago kai ta kalleshi ba, kasancewar har yanzu fushi take dashi. Ganin yanda yake sakin murmushi da kuma yanda ya ke kallon Zaleeha wanda take tauna abincin bakinta cikin nutsuwa, yasa taji gaba ɗaya ranta ya ɓaci, wani irin maƙaƙi ne ya zo maƙoshinta, hakan yasa batasan lokacin da ta ƙware ba, take kuwa tasoma tari, kumburarrun idanunta suka kaɗa sukayi ja.
Hankalin Ummi a tashe tace. "Subahanallahi Ameena tarin ne?".
Kai ta jinjina alaman "Eh." tana me riƙe ƙirjinta dake mata zafi. Saifuddeen kuwa hannunsa yasa yana ɗan bubbuga bayanta cikin kulawa.
Zaleeha da Raleeya kuwa atare suka haɗa baki wajen cewa. "Sannu."
kasa amsa musu tayi saboda matsanancin kishi da kuma ɓacin ran dake cinta, Hayatuddeen cikin kulawa yace.
"Ayya Aunty Ameena sannu, kisha ruwa kinji." Yafaɗi maganar yana me miƙo mata goran ruwan faro me sanyi. Babu musu ta amsa tasha, saida tasha sosai kafun take kifa kanta ajikin dinning ɗin tana meda numfashi. Ahankali Saifuddeen ya aje spoon ɗin dake hannunsa, tare da ɗanjan kujeransa baya, ƙoƙarin barin dinning area ɗin yake, Ummi tace.
"Inakuma zaka ana tsaka dacin abinci?" Ɗan shagwaɓe fuska yayi, tare da sanya hannu ya shafi lafaffen cikinsa alaman ya ƙoshine. Kai kawai Ummi ta girgiza tare da maida hankali ta cigaba da cin abincinta, shikuwa Saifuddeen kai tsaye yafice daga cikin falon. Koda ya fita compound ɗin gidan, nan inda motar Ameena take ya nufa, yana zuwa kuwa yayi sa'a batayi locked motar ba, buɗe murfin motar yayi yashiga, anan ɓangaren me zaman banza ya zauna, tare da jawo ƙofar motar ya rufe. Ameena kuwa jin ta soma dawowa cikin hayyacinta, yasa ta miƙewa tsam, dan batajin za'a iya ƙare cin abincin da ita, tsayuwarta awajen kuwa dai-dai yake da hawan jini ya kamata. Ummi tayiwa saita dawo, tare da ɗansa hannu taja kumatun Adeel dake jikin Ummi'n, dan idan za'aci abinci kullum Ummin ne ke karɓan Adeel ɗin ta ɗaurasa acinyarta. Adawo lafiya Ummi tayi mata, haka ma su Zaleeha, al'barkacin Ummi yasa ta amsa musu fuska asake, jakarta ta ɗauka sannan ta fice daga cikin falon, sukuwa ci gaba sukayi da cin abincinsu. Haka ta fito compound ɗin gidan sam fuskarta babu alaman walwala, kaitsaye wajen motarta ta nufa, tana zuwa kuwa ta buɗe tashiga, ƙoƙarin ajiye jakar hannunta takeyi, idanunta ne suka sauƙa akan Saifuddeen wanda ya zuba mata kyawawan idanunsa, wanda ke masifar tafiya da duk wani tunaninta. Sosai ta ɗan tsorata da ganinsa, amma tunawa cewar fushi takeyi dashi yasa ta shiga ta dake tare da kawar da kanta gefe, can ƙasan maƙoshinta tace.
"Lafiya?." Gane abun da tace yasashi girgiza kansa, kana ya gyara zamanshi da kyau yadda zasu fuskanci juna, dubanta yayi da kyau cikin body language dinsa yace. "Wannan itace sabuwar gaisuwar da kika koyo?." Sake haɗe fuska tayi, tare da ɗaura hannunta akan steering motar, ganinsa akusa da ita, da kuma tunowa da irin kallon da yake jifan Zaleehan ɗazu, da tayi yasa taji gaba ɗaya ma haushinsa takeji. Ganin haka yasashi ɗan lumshe idanunsa tare da kamo hannunta ya rumtseshi cikin nashi hannayen, sam baisan menene damuwar mata ba, akan Ameena kuwa bayaso ace ya sani, kwata-kwata baya ƙaunar abun da zai kawo masa matsala arayuwarsa, tabbas ya fahimci cewa tunanin Ameena ƙaramine, dole saiya nusar da ita kuma ya bita a hankali yasan zata gane zata kuma fahimceshi.
gyara zamansa yayi akasalance cikin body language ɗinsa yace. "Azamana dake ina iya ƙoƙarina wajen ganin na sauƙe haƙƙin ki dake kaina, bansani ba Ameena, bansan mekikewa fushi ba, bansan me namiki ba, ban kuma san dalilin dayasa kika ɗauki kishi da zafi har haka ba, azamana dake bana cutar dake, ba kuma na musguna miki, kinsani na sani Zaleeha matatace kamar yanda kema kike matata, to menene aibuna dan nashiga wajenta na jima? kada ki manta ba haƙƙinki na ɗauka na kai mata ba, saboda ba ranan girkin ki bane nata ne, ashe kenan banyi haka dan na cutar dake ba, meyasa dole kikeson sawa rai da zuciyarki damuwa? ko kusa banason Ummi ta zargeni da rashin yi muku adalci ku biyun, bana kuma fatan ranan da zanyi rashin adalci atsakanin ku, amma saidai naga kaman haƙurin ki naneman gazawa, akullum ƙoƙarin bayyanar da kishinki afili kike, meyasa Ameena? meyasa bazaki daure zuciyarki ba? tunjiya kike fushi dani batare da wani dalili ba, me nayi miki? faɗamin ina jinki laifin me nayi miki?. " Gaba ɗaya jikinta ne yayi sanyi, hakan yasa ta sadda kanta ƙasa, lokaci guda kuwa saiga hawaye sun kwaranyo daga cikin idanunta, tabbas ita kanta tasani fushin da takeyi dashi bashi da dalili, saboda ba laifi yayi mata ba, bai kyareta ba, bai kuma zageta ba, babu abun da yayi mata asalima ya ninka kulawarshi a kanta ne ita kanta tasan baya son damuwarta, kawai dai zallan kishi ne ke ɗawainiya da ita, har yasa take ganin kaman yayi mata rashin adalci. Ɗago kanta tayi da idanunta wanda sukayi luhu luhu, cikin sanyin murya irin ta rashin gaskiya tace.
"Kayi haƙuri, nima bansan me yasa nakejin hakan ba."
Ta ƙarashi mgnar tare da manna kanta a ƙirjinshi. Idanunsa yaɗan lumshe tare da cije laɓɓansa, asanyaye cikin body language yace. "Banason irin wannan halin, ina dalilin ta kura kanki da kikayi? kinsa kanki cikin ƙunci, sannan kin kwana kuka, kin tashi kuma kina fushi dani, bayan ban tauye ɗaya daga cikin haƙƙoƙinki dake kaina ba, banason Ummi tafara tunanin cewa ina tauye miki haƙƙi, idan wani abu nayi miki ki faɗamin, kinsa kanki aɗaki kin kwana kuka, saboda kina yarda da abun da zuciyarki da shaiɗan ke raya miki, sannan sun tambayeki kince musu mura ne ke damunki, su mahaukata ne da bazasu gane cewar kuka kikayi ba, ki dubi fuskarki, ki dubi yanda idanunki suka bayyana alamun kuka, meyasa ba zaki nutsu ki maida hankalin ki ba? Meyasa kike haka?". Hawayen da suka zubo daga cikin idanunta ta sharce, murya na rawa tace.
"Dan Allah kayi haƙuri."
Kansa yaɗan jinjina mata alaman yaji, sannan kuma ta kiyaye, dan abun da tayi ɗin ya sosa ransa, bai kamata ace tana fushi batare da ƙwaƙƙwaran dalili ba, Allah Ma yasani yana iyaka ƙoƙarinsa wajen ganin bai tauye mata haƙƙinta ba.
Buɗe murfin motar yayi ya fice, kaitsaye part ɗinsa ya nufa, dan yanaso yaje yaɗan huta. Itakuwa Ameena gaba ɗaya jikinta amace yake, dan tasan bata da gaskiya, gefe guda kuwa ga wani irin soyayyarsa dake ratsa ta, ita har ga Allah tasan Zaleeha batayi mata komaiba kuma itama bawai tsanar Zaleeha takeyi ba, sai dai tana jin kishinta, haka tayiwa motar key, asanyaye ta fice daga cikin gida. Ta tafi tasan in taje wurin aiki ƙawarta Samira zata ƙara kwantar mata da hankali, ita kanta tasan Samira ƙawace ta gari.

Acan falon Ummi kuwa cikin nutsuwa suka kammala break fast ɗin, Zaleeha da Raleeya ne suka kimtsa dinning area'n, inda Raleeya ta zuba kwanukan da suka ɓata acikin injin wanke wanke, nan falon Ummi suka zauna suna ɗan taɓa hira. Ganin lokaci na ɗan jane, yasa suka sake komawa kitchine ɗin, lunch suka ɗaura, basu wani yi girki me wahala ba, hakan yasa cikin mintuna kaɗan suka kammala, Raleeya ne ta haye sama dan agajiye take jinta sosai, itama Zaleeha part ɗinta ta nufa, Adeel ɗauke akan kafaɗanta, koda ta isa ɗakinta, akan gado ta aje Adeel ɗin sannan ta jefa masa ɗan ƙaramin pillow dan yayi wasa dashi, kayan jikinta ta rage, sannan ta shiga wanka, koda ta fito wata ƴar riga marar nauyi tasanya, sannan ta haye saman gadon, jawo Adeel jikinta tayi tare da ɗaurasa
Showing 141001 words to 144000 words out of 237945 words