yayinda hawayenta ke ɗiga akan kafaɗansa.
Ahankali yaɗan jingina bayansa da jikin kujeran motar, tare da lumshe idanunsa, numfashinta dake sauƙa akan wuyansa, shiya sanya yaji gaba ɗaya jikinsa ya sake, yayinda tsikar jikinsa keta faman mimmiƙewa, dama akan Zaleeha shi namiji ne me yawan feelings, yanzu da take ajikinsa kuwa shikaɗai yasan me yake ji.
Zaleeha kuwa daɗin jikinsa da kuma sassanyan ƙamshin turarensa dake shiga hancinta, su suka taimaka wajen bata wani irin nutsuwa na musamman, sake lumshe idanunta tayi, tana me busa masa iskan numfashinta akan fatar wuyansa.

Gaba ɗayansu sun shagala, babu wani wanda yake cikin tunaninsa, musamman ma Saifuddeen daya tafi izuwa wata duniya ta daban, tsayuwar motar ne yasasu buɗe idanunsu, gani sukayi har sun iso gida. Akunyace taɗan janye jikinta daga na Saifuddeen ɗin, nan ta ɗan gyara mayafinta dake ƙoƙarin zamewa. Sule driver kuwa cikin hanzari ya zagayo ya buɗe mawa Saifuddeen ƙofar motar, bayan ya buɗe bot ya zaro masa kekensa.
Cikin nutsuwa kuwa ya hau kan keken nasa, Zaleeha ma jikinta asanyaye ta fito daga cikin motar, idanu ta zuba masa ganin ya nufi part ɗinsa, kanta ta ɗan sunkuyar ƙasa, sannan ta share ɗan gun hawayen dake maƙale ƙasan idanunta, cikin ɗan sassarfa ta nufi part ɗin Ummi, tun kafun ta ƙarasa shiga falon, take ƙiran sunan Ummi, Raleeya dake zaune acikin falon ne ta ƙurawa ƙofar shigowa ido, musamman yanda taji Zaleeha nata faman ƙiran sunan Ummi.
Murɗa handle ɗin ƙofar falon tayi ta shiga, fuskarta ɗauke da murmushi da kuma hawaye, ganin Raleeya yasa ta tafi da gudu ta faɗa jikinta, ganin murmushi da dariya akan fuskan Zaleehan yasa, Raleeya itama ta saki murmushi, ɗago kai Zaleehan tayi, tace. "Raleeya Baba Malam ya yafemin, haka Ya Ahmad dasu Mamy ma duk kowa ya yafemin, Raleeya Hamma Saifuddeen ya zama garkuwa agareni, ayau ya bani duk wani farinciki, sanadiyarsa Baba Malam ya yafemin, yanzu Baba Malam baya fushi dani." ta ƙare maganan hawaye na zuba daga cikin idanunta.
Itama Raleeya Idanunta ne suka ciko da ƙwalla, murmushin jin daɗi ta saki, tare da ƙara rungume Zaleehan, cikin farinciki tace.
"Masha Allah Zaleeha natayaki murna ƙwarai, yanzu kema zakiyi rayuwa cikin farinciki."
Dai-dai lokacin Ummi ta fito daga ɗaki, dan tun tana banɗaki takejin ƙiran da Zaleehan keyi mata,
ganin Ummi yasa cikin sauri tatashi daga jikin Raleeya, ƙarasawa tayi da sauri kaman wata ƴar ƙaramar yarinya ta raɓa jikin Ummi, tana sakin dariya me haɗe da hawaye.
Cikin nuna farin cikinta tace.
"Ummi Baba Malam ya yafemin, hakama su Mamy, Ummi har Ya Ahmad ɗina ma ya yafemin, kuma yanzu basa fushi dani, Ummi Hamma Saif ne yayi min komai, saboda shine duk kowa ya yafemin, shikenan yanzu Baba Malam ɗina baya fushi dani."
taƙare maganan tana me sake rungume Ummi, sam ita bata ɗauki Ummi mazaunin suruka ba, ko yaushe amatsayin uwa take ɗaukanta, dan abun da za tayiwa Mama da Mamy shi zatayiwa Ummin, saboda acikin jininta soyayyar Ummin take.
Cikin farin ciki Ummi ta shafi fuskarta, tare da cewa.
"Alhamdulillah, tabbas kinzo da labari me daɗi, kuma naji daɗin hakan sosai, dama nasan ke ta gaban goshin Baba Malam da ya Ahmad ne, saboda haka yanzu kuka ya ƙare, idan kuma nasake ganin hawaye akan wannan fuskar to fa zamu ɓata, kindai ji kam."

Murmushi me kama da dariya tayi, kamo hannun Ummin tayi cikin sanyi tace.
"Nagode sosai Ummi haƙiƙa kin cika uwa tagari, samun irinki awannan duniyar zaiyi wahala, Inasonki Ummi na, dan Allah ki ƙara yiwa Hamma Saif godiya, duk ta dalilinshi ne Baba Malam ya yafemin, ku ɗin kunzama majingina agareni, sannan kunzaman to mini lema, wanda daku ne zan kare ruwa da zafin rana, nagode sosai!".
tafaɗi maganar tana sakin wasu hawayen farinciki, tare da sake rungume Ummin.
Murmushi Ummi tayi, sosai takejin soyayyar Zaleehan acikin ranta, tabbas tasan Zaleeha mutumiyar ƙwarai ce, kuma tasan bazata taɓayin danasanin samunta amatsayin suruka ba.
Hayatuddeen wanda tun ɗazu ya shigo falon, ƙarasowa garesu yayi, tare da haɗasu su duka ya rungume ta gefen Ummi cikin farinciki yace.
"Nima Inasonki Adda Zaleehan Hamma, saidai kuma zan iyayin kishi dake ako da yaushe, dan naga kaman kinason maidamin Ummi na taki ke kaɗai."
Murmushi su dukansu sukayi.
ɗan ɗagowa Zaleeha tayi, tana share hawayen dake kan fuskarta tace.
"Ai dai kuma indai ina cikin gidannan Ummi tawa ce dan kai kayi ƙato. Ko Ummi?".
ta faɗa tana mutsutstsuka idanunta, hakan yasa tadawo kaman wata ƙaramar yarinya.
Ƴar dariya Ummi tayi tare da cewa.
"Ƙwarai kuwa, amma fa saidai in kin ɗauki al'ƙawarin cewa bazaki sakeyin kuka ko abayan idanuna ba, sannan kuma kada kice zaki sakeyiwa Adda Maryam kuka, nasan kinsan cewa mamaci bayason kuka, addu'a kawai yake buƙata, saboda haka Adda Maryam addu'a take buƙata awajenki ba kuka ba, daga yau kuma banso na ƙara ganinki cikin ƙunci, tun da Baba Malam ya yafe miki, inason ki saki jikinki, ki zauna acikin ƴan uwanki, sannan kuma daga yau banason naga kina takura kanki kinji ko." Kanta ta jinjina alaman. "To." Murmushi Ummi tayi tare da shafa kanta, cikin kulawa tace. "Allah yayi muku al'barka, ya kuma baku zaman lafiya keda abokiyar zamanki."
sunkuyar da kanta ƙasa tayi tana wasa da ƴan yatsun hannunta tace "Ameen"
Hayatuddeen ne yaja hanunta suka dawo cikin falon, nan kusa da Raleeya suka zauna, kallonta yayi cikin nuna jin daɗinsa yace.
"Wallahi Adda Zaleeha kinfi kyau idan kina murmushi, yanzu da kina murmushi bakiga yanda kikayi kyau ba, sannan kuma nasan yau da dare zamu buga game sosai tunda naga kina cikin farinciki ko?."
Murmushi tayi tare da cewa.
"Ni dai bazan buga game da kai ba, abunda duk nasan halinka, rinto kakeyi, ranan ai naga kanata yiwa Raleeya rinto."
Ummi da Raleeya wacce waya takeyi da Raihana ne sukayi dariya, shikuwa Hayatuddeen murmushi mugunta yayi, cikin son tsokan Raleeyan yace.
"Adda Zaleeha bakisan wacece Adda Raleeya bane, itace fa bata iya game ɗin ba, shine kuke ganin kaman rinto nake mata."
Hararansa Raleeya tayi tare da cewa.
"Faɗawa wanda baisan waye kai ba yaro,kowa ya sanka da rinto."
Nan dai dukansu suka ɗanyi murmushi, daga haka kuma suka shiga ɗan taɓa hira.

Acan ɓangaren Saifuddeen kuwa, yana isa part ɗinsa, kai tsaye bedroom ya wuce, yana shiga ya soma rage kayan jikinsa, cikin nutsuwa ya cire riga haɗi da wandon dake jikinsa, wani farin towel ya zaro daga cikin wani ɗan ƙaramin drawer, tare da ɗaurawa akan waist ɗinsa, ahankali yake tura wheelchair ɗin nasa, har ya kawo bakin ƙofar shiga bathroom, hannunsa ya ɗaura ajikin handle ɗin ƙofar sannan ya tura kansa ciki, komai na cikin toilet ɗin nasa tsab yake, ƙamshi ne kawai ke tashi, sanin cewa kwata kwata bayason ƙazanta yasanya Ameena ke ƙoƙarin gyara masa toilet ɗin nasa kullum dan Ameena akwai tsabta, cikin nutsuwa ya haɗawa kansa ruwan wanka me ɗan ɗumi, tare da zuba wani irin turaren wanka me daɗin ƙamshi acikin ruwan, kunce towel ɗin jikinnasa yayi, ahankali yaɗan matso da kekensa kusa da bathtube ɗin, kamar yanda ya saba, cikin nutsuwa yake komansa, koda ya shiga cikin bathtube ɗin, ɗan zamewa yayi ya kwanta, tare da jingina kansa da jikin saman bathtube ɗin, hakanne yabawa ruwan ɗumin daman ratsa ko ina najikinsa, ɗan lumshe idanunsa yayi tare da sakin wata irin ajiyar zuciya me ƙarfi. Ahankali moment ɗinsu da Zaleehan ke dawowa cikin tunaninsa, wani irin sabon yanayi ya samu kansa aciki, laɓɓansa ya ɗan lasa, saboda tunawa da sweet mood ɗinsu da yayi, musamman ma yanda ɗazun bakinta ke gogan ƙirjinsa, samun kansa yayi cikin wani irin shauƙi, baisan wani irin so yakewa Zaleeha, da har yakejin wani irin feelings na musamman akanta ba, Ameena ce ta fara faɗo masa arai, hakanan yaji gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi, sam bai taɓajin abun dayaji ayau dangane da Zaleeha, akan Ameena'n ba, saidai kuma koma miye itama tana da nata matsayin acikin rayuwarsa, saboda itace mace ta farko daya fara sani acikin rayuwarsa, itace kuma wacce ta fara haifa masa ɗa, sannan tasoshi amatsayinsa na nakasashshe, nakasarsa baisa taƙisa ba, ta kuma rungumesa amatsayin miji, duk da tasan cewar baya sonta, amma hakan baisa taƙi yi masa biyayya ba, ko yaushe so take ta faranta masa, saboda haka ko kusa Ameena bata cancanci wulaƙanci daga garesa ba, koba komai tayi masa halacci, haƙiƙa Zaleeha itace mace ta farko daya fara so, kuma yakejin soyayyarta acikin jininsa, sannan itace zaɓinsa, Saɓanin Ameena da ta kasance zaɓin Ummi, sai-dai kuma duk da haka tana da nata matsayin awajensa, wulaƙanta ta kuma tamkar budulci ne ga Umminshi.
Sake gyara kwanciyansa yayi, yana mejin kasala nasake sauƙar masa, gaba ɗaya abun da Zaleehan tayi masa, ya hautsuna tunaninsa, haka yayi wanka jikinsa duk amace, koda ya fito acikin bathtube ɗin wata rubber bathrobe yasanya, saida ya ɗauro al'wala kafun ya fito daga cikin toilet ɗin.
Nan ya kimtsa kansa cikin wasu riga da wandon jeans masu kyau da tsada, feshe jikinsa yayi da turarensa me dadin ƙamshi, ɗan ɗaga kansa yayi ya kalli agogon dake saƙale ajikin bangon ɗakin. Ganin 3:30 pm yasanyashi ɗaukan wayansa da kuma laptop ɗinsa, ahankali yake tafiyar da wheelchair ɗinsa har ya fice daga cikin ɗakin, sam bayaso ya makara dan ƙarfe 4:00 pm daidai zasu gudanar da meeting acan ƙungiyarsu ta JONAPWD.

Cikin nutsuwa ya fito compound ɗin gidan, nan ya iske Sule driver da kuma Bala megadi suna al'walan sallan la'asar, cikin body language ɗinsa yayiwa Sule driver alaman cewa yafito da mota zasu fita, kai Sule driver'n ya jinjina masa alaman "To." saida ya jira suka gama alwalan, sannan sule driver ya fito da motar, ya shiga ayarinsu suka wuce masallaci.
Koda suka idar da sallan azkar yayi, sannan ya tashi ya hau kan kekensa, ganin haka yasa shima Sule driver miƙewa tsaye.
Shi ya buɗewa Saifuddeen ɗin murfin motar ya shiga, sannan shima ya zaga ɓangaren driver ya zauna, Bala mai gadi ne yayi musu adawo lafiya, sannan sule yaja motar suka tafi, kai tsaye ƙungiyar Jonapwd ɗin suka nufa.

Acan ɓangaren Ummi kuwa, bayan sunyi Sallan la'asar, Raleeya ne ta wuce kitchine dan ɗaura dinner.
Zaleeha kuwa koda ta idar da sallan falo ta fito, ganin Raleeya a kitchine yasa itama ta nufi kitchine ɗin, amsan girkin tayi tare da cewa. "Raleeyan taje ta huta." duk yanda Raleeya taso suyi aikin tare Zaleeha taƙi, dole haka Raleeya ta koma falo ta zauna ita kuma Zaleeha ta ci gaba da aikin.
Tana nan acikin kitchine ɗin, Ameena ta dawo daga wajen aiki, ɗakin Ummi tafara zuwa ta gaishe da ita, sannan ta wuce ɓangarenta.
Zaleeha kuwa ana ƙiran sallan magriba ta gama girke-girken nata, nan kan dinning ta jere abincin wanda gaba ɗaya ƙamshinsu ya cika falon, Hayatuddeen dake zaune afalo kuwa sai faman haɗiye yawu yake, koda tana girkin ya shigo kitchine ɗin yafi sau uku, duk shigansa kuwa sai ya buɗe tukunya ya ɗanɗani stew ɗin da Zaleehan ta haɗa, wanda yaji naman kaji, ganin yanda yake lashe mata tukunya ne yasa ta saki murmushi, nan ta zuba masa pepper meat acikin wani ɗan plate, tare da kama hannunsa ta turasa falo, dan yaƙi ya barta tayi aikinta cikin nutsuwa.
Hayatuddeen kuwa dama abunda yake nema kenan, haka ya bararraje ƙafafu yana cin pepper meat ɗin, sai faman kaɗa kai yake yana santi.
Yana gamawa kuwa ya wuce masallaci.
Itama Zaleehan ɗaki ta wuce, wanka tayi sannan ta ɗauro al'wala, wani body lotion ta shafa, tare da fesa turaren white oud ajikinta, take kuwa gaba ɗaya jikinta ya gauraye da ƙamshi.
Wata ƴar siririyar pencil gown me stones ta sanya ajikinta, sosai kuwa rigan tayi mata kyau, dogon gashinta wanda ya kwanto har gadon bayanta ta ɗaure da ribbom sannan ta ɗaura hijab akan kayan, nan kan darduma ta hau tare da tada Sallah.

Acan ɓangaren Saifuddeen kuwa, kusan awa biyu suka ɗauka a Jonapwd suna meeting, koda suka kammala kowa ya watse, hira suka ɗan taɓa shida Ishaq kafun ya shiga mota suka kamo hanyar gida, anan masallacin dake jikin gidan sukayi sallan magriba, koda suka idar da sallan zama yayi acikin masallacin, har lokacin sallan isha ya cika, bayan sun idar da sallan ne ya sanya hannuwansa ya dafa ƙasa, ahaka yake ɗan jan jikinsa har ya ƙarasa bakin ƙofar shigowa masallacin inda anan yake aje wheelchair ɗinsa, yana hawa kuwa controlling wheelchair'n yayi, inda ta soma tafiya da kanta, dai-dai zai shiga gida ne suka haɗe da Ahmad, wanda shima daga masallacin yake, yawan jama'a shiyasa basuga juna ba, saman keken Saifuddeen ɗin ya kama, haka suka nufi cikin gidan, cikin body language ɗinsa ya ke bawa Ahmad ɗin labarin meeting ɗin da sukayi yau.
Ahaka har suka ƙarasa part ɗin Ummi, anan cikin falon kuwa, Ummi ne da kuma Raleeya, sai Hayatuddeen dake faman turo baki, waishi adole yunwa yakeji, kuma Ummi tace bazaici abinci ba sai yajira kowa yazo sun haɗu a dining area, dan daga yau gaba ɗaya ahalin gidan atare za suna cin abinci, daga kan break fast har zuwa dinner, lunch ne dai kowa zai iyayi aɗakinsa.
Shigowar su Hamman nashi ne yasa ya ɗanji sanyi aransa, dan yasan yanzu Ummi zatace suje suci abincin, shikansa yasan idan aka tsananta bincike ba yunwa yake jiba, kwaɗayine kawai ke damunsa, musamman ma yanda yaga yau Adda Zaleehan ta girka musu abubuwan daɗi kala kala.

Cikin girmamawa Ahmad yaɗan rusuna ya gaishe da Ummi, dan yau tun safe daya fita agidan baidawo ba sai yanzu, fuska asake Ummi ta amsa masa, tare da tambayansa ya aiki.
Ya amsa mata da "Alhmdlh."
Saifuddeen kuwa ƙarasowa wajen Ummin nasa yayi, tare da ɗan shafa gefen fuskarta, cikin kulawa haɗi da tsantsar soyayya yaɗan ɗaura kansa agefen kafaɗanta, murmushi Ummin tayi tare da shafa lallausan sumar kansa, tabbas yau yafaranta mata rai daya kai Zaleehan gida, har kuma Baba Malam ya yafe mata, cikin kulawa tace. "Ya meeting ɗin naku?" idanunsa yaɗan lumshe tare da jinjina kansa alaman,
"Komai ya tafi yanda akeso."

Jin sallaman Ameena ne yasasu duk suka ɗago kai suka kalleta, sanye take da riga da sket na atamfa, yayinda ta zuba meckup akan fuskarta, babu laifi ta kyau sosai, sannan kayan ma sunyi mata kyau, Adeel ne ɗauke a kafaɗanta, haka ta ƙaraso cikin falon, sai baza ƙamshi take, dan wani turare me shegen ƙarfi tasa, hwanda yasa gaba ɗaya falon ya ɗauka, murmushi ta sakarwa Saifuddeen wanda ke kallonta, shiɗin ma murmushin yayi mata, Ummi ne ta amshi Adeel tana yi masa wasa, Ameena kuwa nan kusa da Raleeya ta zauna, bayan ta gaishe da Ahmad, cikin sakin fuska kuwa ya amsa mata, harma da tambayanta ya aiki, tana murmushi ta amsa da "Alhamdulillah."

Hayatuddeen ne ya miƙe tsaye, tare da duban Ummi, cikin shagwaɓa yace.
"Ummi shikenan ai tunda dai kowa yazo ai sai muje muci abincin ko?".
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"To acici."
Shiya fara zama akan dinning ɗin, sannan Ahmad da Saifuddeen suka rufa mishi baya dan duk yunwa sukeji, babuma kamar Ahmad wanda tun lunch da yayi baisake sa komai abakinsa ba sai ruwa.
atare Raleeya da Ameena suka ƙarasa kan dining ɗin, nan kujeran dake kusa dana Saifuddeen Ameena ta zauna, Raleeya kuma ta zauna akusa da Ahmad ɗinta, wanda keta jifanta da wani irin mayataccen kallo, ƙasa-ƙasa yake lumshe mata idanu, murmushi tayi tare da ɗan sa hannu ta muntsineshi, dan sarai ta gane me yake nufi, takarance sa tsab, da ta ga yana mata irin wannan kallon, to matsanancin feeling ɗinta yakeji.

Ummi ne ta ƙaraso nan kan dining ɗin, rungume da Adeel ajikinta, cikin kulawa tace. "Hayatuddeen jeka ƙira Zaleeha tazo taci abinci." Jin cewa Zaleeha zai ƙira yasa batare da ya musa ba ya nufi ɗakin nata, nan Ummi taja kujera ta zauna.
Ameena kuwa jin an ambaci sunan Zaleeha yasa taji wani abu ya tokare mata ƙirji, Allah ma yasani tana matsanancin kishin Saifuddeen, shiyasa ko sunan Zaleeha bataso taji anƙira, bawai tsanan Zaleeha takeji aranta ba, zallan kishine kawai sai kuma haushinta da takeji.

Zaleeha kuwa tunda tayi sallan isha tana nan zaune akan sallayan bata tashi ba, suratul falaq take karantawa acikin ranta, dan nemawa Adda Maryam dama duk wani musulmin daya rigayemu gidan gaskiya gafara awajen Allah.
Shigowar Hayatuddeen ne yasa taɗan ɗago kanta ta kalleshi, cikin kulawa yace.
"Adda Zaleeha kizo muyi dinner inji Ummi."
Kanta ta jinjina masa, sannan ta soma ƙoƙarin tashi daga kan sallayan, hijab ɗin jikinta ta cire, nan cikin drawer'nta ta ciro wani ɗan mayafi mai kauri, ta yafa ajikinta, sosai tayi kyau, dan kalan mayafin ya karɓi kyakkyawar fuskarta, duk Hayatuddeen na tsaye ajikin ƙofa yana
Showing 126001 words to 129000 words out of 237945 words