kullum sai Ameena tabarwa Zaleeha Adeel, awajenta yake wuni harta dawo daga wajen aiki. Hakanne yasanya shaƙuwa me ƙarfi ta shiga tsakanin Adeel ɗin da kuma Zaleeha tana jin yaron har cikin ranta.
Saifuddeen ne zaune kan wheelchair ɗinsa, wayarsa ya jawo sannan ya turawa Raleeya, text akan taƙira Hayatuddeen suzo tare yana son ganinsu, kasancewar yau Hayatuddeen ɗin baida lecture'n safe shiyasa baije school ba.
Suna shigowa cikin part ɗin nasa ya miƙowa Hayatuddeen key tare da cewa.
"Karɓi key ɗin part ɗin Zaleeha ne."
cikin yanayin zumuɗi Hayatuddeen yace. "Nakai mata." Hararansa Saifuddeen ɗin yayi, cikin body language ɗinsa yace. "To sarkin azarɓaɓi bahaka nakeson cewa ba."
Ɗan zumɓura baki Hayatuddeen ɗin yayi, cikin shagwaɓa yace.
"To me za ayi dashi."
Duban Raleeya Saifuddeen ɗin yayi, cikin body language ɗinsa yayi mata alaman cewa.
"Su shiga ɓangaren Zaleehan, suɗanyi share share."
Murmushi Raleeyan tayi, har acikin ranta taji daɗi, saboda hakan alama ne dake nuna cewa Zaleehan ta kusa dawowa ɓangarenta, jan hannun Hayatuddeen tayi suka wuce sashin Zaleehan, shikuwa Saifuddeen laptop ɗinsa ya ɗauka ya cigaba da aikinsa.
Raleeya da Hayatuddeen kuwa suna shiga sashin Zaleehan, suka soma ƴan share share da goge goge, kafun awa biyu tuni sun tsab tace ko ina sun gyara komai, haka falon yadawo sabo fil sai sheƙi yake, inda suka fesa turaren air feshener,
suna tsaka da aikin ne Ahmad ya ƙira Raleeya dan tun ɗazu ya dawo baiganta ba, ya kuma sauƙo har ƙasa bai ganta ba.
Nan take sanar masa cewa tana ɓangaren Zaleeha Hamma Saifuddeen yaɗan sasu suyi mata share-share da gyare-gyare.
Ƙwafa Ahmad yayi tare da cewa.
"Lalle ma Saifuddeen so yake ya maidamin da mata baiwa ko? yarasa wazai sa yayiwa Zaleehan share-share sai ke, zanyi maganinsa ne badai yayi mata biyu ba yaseen zamu ƙaura." Dariya Raleeya tayi sannan ta kashe wayan, nan dai suka kammala komai suka fice daga sashin.
Washe gari ne Goggo Dada taturowa Saifuddeen saƙon godiya, da kuma fatan al'khairi kala-kala, dan sosai taji daɗin kyautar nasa.
Nan yake ce mata. "Bakomai, Goggo Dada ai kema uwace agareni kuma uba".
ananne ma yake ce mata.
"Lafiya ko batazo tayi ta'aziyyan rasuwar Adda Maryam ba".
cewa tayi.
"Itama tana tason zuwa to amma Allah ne baiyi ba."
take kuwa yace washe gari zai turo sule driver ya ɗaukota, haka dai tayi ta masa godiya, daga nan sukayi sallama . Murmushi yayi bayan ya aje wayar, cikin zuciyarsa yace.
"Awannan karon Goggo Dada dake zanyi amfani wajen dawo da Zaleeha ɗakinta, tun alokacin da Ummi ta bini akan na bada key ɗin ɗakinta ban nemeshiba, yanzu kuwa dana ga key ɗin bani da wani ƙarfin guiwan da zan iya tunkaran Ummi nace mata ga key ɗin ɗakin Zaleeha, amma yanzu tunda dai zakizo nasan lokacin dawowan Zaleeha ɗakinta yayi, zanyi komai asauƙaƙe tayanda Ummi bazata zargeni ba."
Haka dai yayita saƙawa da kuncewa, sosai ƙudurinsa ke ƙara ƙarfafa acikin zuciyarsa.
Kaman yanda ya faɗa kuwa washe gari yasa Sule driver yaje har Dukku ya ɗauko Goggo Dada'n, Raleeya ne ta rakata gidan su Zaleehan tayi musu ta'azziyya, daga nan kuma suka dawo gida.
Yauma kamar kullum Zaleehan ne tayi musu girkin abincin dare, kusan atare sukaci abincin, koda suka kammala cin abincin, nan cikin falon ta koma ta zauna akan sofa tare da tanƙwashe ƙafafunta, sama sama take ɗan kallon tv, ahaka taɗan jingina kanta da jikin kujeran falon, bacci takeji sosai, saidai sanin cewa Goggo Dada na cikin ɗakin nata yasa bata shiga ta kwanta ba, saboda kallon suruka takewa Goggo Dada'n.
Ɗan sake jingina bayanta da jikin kujeran falon tayi, tare da lumshe idanunta, ta kuma sake riƙe Adeel dake jikinta ƙam, bacci takeji tare da gajiya, amma sam tanajin bazata iya shiga ɗakin nata ba, saboda Goggo Dada dake ciki, kunyanta takeji, musamman ma da takeson kafun ta kwanta tayi wanka. Hayatuddeen ne ya lura da yanda Zaleehan keta lumshe idanunta, alaman bacci.
Hannu yasa ya ɗan taɓa kafanta cikin kulawa yace.
"Adda Zaleeha bacci kikeji, kije ki kwanta mana."
ɗan buɗe idanunta tayi, tare da sakin sassanyar murmushi. Raleeya dake jinsu ne taɗan ɗago kai, tare da duban Hayatuddeen ɗin tace.
"Ai tun ɗazu Goggo Dada na ɗakin." Ɗan marairaice fuska Hayatuddeen yayi yace. "To Adda Zaleeha ki tashi ki hau saman kujera mana."
Ummi da fitowarta daga ɗaki kenan, duk taji abun da suka faɗa, duban Raleeya tayi, cikin kulawa tace.
"Raleeya tashi kije kicewa Goggo Dada ta dawo nan ɗakina mu zauna tare, duk ai zai ishe mu, abu ba yaro ba ba komai ba." "To" Raleeya tafaɗa tana me miƙewa tsaye. Saifuddeen da tun shigowar Ummin yake kallon yanayin yanda bakinta ke motsi, hakan yasa shi danna madannanin wheelchair ɗinsa ya nufi hanyar fita daga falon, dama tuntuni wannan damar yake jira shiyasa koda suka kammala dinner bai tafi ba.
Kai tsaye ɓangarensa ya nufa, yana shiga kuwa ya zaro wayarsa, text ya turawa Hayatuddeen akan cewar "Yazo yana son ganinsa." Hayatuddeen na zaune yaga saƙon Hamman nasa, tsam ya miƙe ya fice daga cikin falon, kai tsaye sashin Hamman nasa ya nufa.
Anan falo ya iske Saifuddeen ɗin, yana shan Maltina, ƙarasowa cikin falon yayi tare da cewa.
"Hamma gani." Kai ya jinjina tare da sanya hannunsa acikin al'jihun rigarsa ya zaro key, miƙawa Hayatuddeen key ɗin yayi, nan cikin body language ɗinsa yace. "Ka kaiwa Zaleeha, ta dawo ɗakinta tabarwa Goggo Dada wannan ɗakin."
Yanayin yanda yayi maganan yana wani basarwa, shine abun daya sanya Hayatuddeen yaji wani irin dariya ta kamasa, amma sai ya share, da murna ya karɓi key ɗin, tare da cewa.
"To zan kai mata." juyarda akalan kekensa yayi ya nufi bedroom, Hayatuddeen kuwa binsa yayi da kallo yana murmushi, yana ganin ya shige ɗakin, yayi ɗan tsalle tare da cewa. "Yess yanzu itama Adda Zaleeha zata koma ɗakinta."
juyawa yayi cikin sauri ya fita daga falon. Anan falon Ummi kuwa har yanzu suna nan a zazzaune, gefe kuwa ga Ameena da zuciyarta keta raya mata abubuwa iri iri.
Da murna Hayatuddeen ya shigo cikin falon, yana ɗan rawa, harda su shaku shaku, baki Ummi dasu Raleeya suka buɗe suna kallonsa, da mamaki Ummi tace.
"Kai Hayatuddeen lafiyanka kuwa?." Murmushi mai ɗauke da dariya yayi, tare da miƙowa Raleeya hannu, cikin jin daɗi yace.
"Adda Raleeya maza maza taso muyi rakiya ."
Hannunsa ya miƙa ya karɓi Adeel dake kan cinyar Zaleehan, ɗaga Adeel ɗin yayi sama tare da cewa.
"Adeel kaima kayi murna yau Amminka ta zama zata bar mana side ɗin Umminmu ta koma can ɗakinta."
Ya faɗi maganar yana me cilla Adeel ɗin sama. Jin abunda Hayatuddeen ɗin ke faɗa yasa Ummi sakin murmushi tare dayin ƙwafa, dama ai ita ta jima dagane shirin Saifuddeen ɗin, kuma zatayi maganinsa ne. Ameena kuwa kalaman Hayatuddeen ɗinne suka zuciyarta tsananta bugawa, wani irin fitinannen kishin Zaleehan ne ya taso mata, take taji komai na duniya ya daina yi mata daɗi, ashe duk adacan baya ba kishi takeji ba haukan banzane kawai takeyi, ayanzu yanda ƙirji da zuciyarta ke tafasa, nanne ta tabbatar da cewar kishi take, idanunta ne suka kawo ruwa, sakamakon wani irin ɗaci da takeji azuciyarta, lokaci ɗaya ta shiga cikin yanayi marar daɗi, miƙewa tayi jiki asanyaye ta fice daga cikin falon.
Tana fita Ummi ta gyara zama tare da cewa.
"Babu inda Zaleeha zataje, ai ɗakina zai ishemu nida Goggo Dada'n, saboda haka bama sai taje ko ina ba." Goggo Dada wanda duk taji abun da suke faɗa ne ta fito daga cikin ɗakin, cikin kulawa tace.
"A'a Ya zakiyi haka kuma, ki hana yarinya komawa ɗakinta, ai baiyi ba."
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"A'a Goggo Dada barta dai anan ɗin".
Kai Goggo Dada ta girgiza tare da cewa. "Sam baza'ayi haka ina gidan nan ba, ki barta ta koma ɗakinta, ai babu ma inda zatafi sakewa kamar ɗakin aurenta." Murmushi Ummi tayi, tare da cewa. "Shikenan, Zaleeha tashi ki koma sashinki, Allah ya muku al'barka." Wani irin kunyane ya lulluɓe Zaleeha'n, hakan yasa tayi ƙasa da kanta, Raleeya ne ta miƙe cikin jin daɗi tace.
"Yauwa Aunty Zaleeha tashi mu rakaki." Akunyace ta tashi tsaye, Raleeya ne ta kama hannunta, Hayatuddeen na biye dasu abaya, kafaɗansa rungume da Adeel, suka fice daga cikin falon, Goggo Dada da Ummi suka bisu da kallo suna murmushi. Ummi kam bataso ace Zaleehan ta koma cikin sauri ba, so tayi ta bashi wahala sosai akan komawar Zaleeha'n, tun da dai da farko babu yanda batayi dashi ba akan ya kawo key ɗin ɗakin Zaleehan ta koma, amma yaƙi, sai yanzu daya ga dama zai zo ya wani ce ta koma. Su kuwa koda suka ƙarasa part ɗin, Hayatuddeen ne ya sanya key ya buɗe ƙofar falon, nan suka shiga, Raleeya harda sata ta shiga da bismillah da kuma ƙafar dama, saikace wata sabuwar amarya, har cikin bedroom ɗinta suka wuce, wanda ko ina keta tashin ƙamshin airfreshener, anan kan gado Zaleehan ta zauna, tare da war ware gyalen da ta yane kanta dashi. Wayar Raleeya ne ta fara ƙara alaman shigowar kira, koda ta duba ganin sunan Raihana yasa ta ɗaga wayan tare da karawa akan kunnenta, bayan sun gaisane Raihana da yaji kaman Raleeyan na cikin farinciki tace.
"Mekuka samu ne haka keda Hayatuddeen, kuketa nishaɗi, daga nan mafa ina iya jiyo muryar Hayatuddeen." Murmushi Raleeya tayi tare da cewa.
"Mun rako Adda Zaleeha ne yau ta dawowa ɗakinta."
tsuka Raihana tayi daga can cikin wayar tace.
"Aikin banza akan wannan shine kuketa wani farinciki? ai ni wallahi tunda tace batason Hamma nima banasonta."
ɗan murmushin yaƙe Raleeya tayi, dan batason kowa ya fahimci abun da Raihanan ke cewa.
Dai-dai lokacin kuwa Zaleeha ta ɗago kai ta kalli Raleeya, cikin sanyin muryarta tace.
"Raihana ce ko?".
Gyaɗa mata kai Raliya tayi alamar eh itace.
Cikin yanayin sanyi tace. "Kice ina gaishe ta." Murmushi Raleeya tayi, take kuwa tace wa Raihana'n.
"Aunty Zaleeha tace na gaisheki."
A gyatsine Raihana tace.
"Banaso ta riƙe gaisuwarta."
jin hakanne yasa Raleeya ta fice daga cikin ɗakin, falo ta koma, nan cikin son nusar da ƴar uwarta ta tace.
"Wallahi kedai Raihana kincika masifa, kuma kidaina ganin baƙin Zaleeha, wallahi tana da daɗin zama, saidai idan baki fahimceta ba, kuma koda da tace batason Hamma Saifuddeen me ta taɓayi mana? tana zaune damu lafiya, sannan kuma bata taɓa raihana mana mahaifiyar muba, kullum biyayya ne atsakaninta da Ummi, aganina ai hakan baizama abun da zaisa muƙita ba koda albarkacin hallacin mahaifinta."
Baki Raihana ta taɓe tare da cewa.
"Ohon muku dai, nidama naƙiraki ne dan naga tunjiya bamu gaisa ba, sai anjima ki gaishemin da Ummi na da autanta da Hamma na."
da haka sukayi sallama, Raleeya ta koma ɗakin Zaleeha'n.
Sun ɗan taɓa hira kafun suka tafi, inda suka barta ita da Adeel.
Ummi kuwa da Goggo Dada ɗakin Ummi suka shiga suna hirarsu ta manya kuma ƴan uwa suna cikin hirane kiran Adda Rahma ya shiga wayar Ummi,
da sauri ta ɗaga bayan sun gaisa ne Adda Rahma tace.
"Ummi ni kam yaushe ne Saifuddeen zai koma India a yaga likita?".
Ajiyan zuciya Ummi taja tare da cewa.
"Uhummm ke dai barni da Baba na Rahma, kingafa wancan karonma da kyar na sashi yaje bayan aurenshi da Ameena da wata shida kinga lokacinma watanshi takwas da dawowa kafin yaje, wai shi ya worke me sai yayi ta bin kan likitoci ai haka Allah ke son ganinsa kuma shi yama worke gara harda cemin shifa lafiyar shi lau."
Cikin sanyi Adda Rahma tace.
"To Amman kuma ai in anyi dace zai sake miƙewa tsaye fa suke cewa.
Ni yanzu nema Ya Adnan ke cemin Dr Acash prasat ya mishi mgna kan cewa, date ɗin kowanshi fa yayi har ya ɗan wuce, shine yake cemin in gaya miki kisashi ya fara shirin zuwa".
Ɗan gajeren tsaki Ummi taja tare da cewa.
"Bazai yarda bafa, mu barshi kawai tunda yaji ya gani yace shi ya godewa Allah a hakanma tunda yana iya yiwa kanshi komai, in na matsa mishima sai dai yaje don dole badon yasoba, shiyasa ni kuma ban fiye son takurashi ba."
Kai Adda Rahma ta ɗan jinjina tare da cewa.
"Uhum lfy yakeji ai in yaji ciwo ba sai ance ya komaba, Allah ya ƙara bashi lfy, dan na lura shi jin wannan kujerun nasa yakeyi kamar kujerun mulki".
Dariya suka ɗanyi kana Ummi tace.
"Ga Goggo Dadanku ma tazo".
Cikin kula tace.
"Bata waya".
Cikin kula ta gaita kana ta ƙara da cewa.
"Goggo Dada zamu kwana biyu ko?".
Dariya tayi tare da cewa.
"Tab ai gobema da safe zan koma".
Cikin shaƙuwarsu tace.
"Ayyah dai Goggo Dada zaki idoni ko?".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Eh kafin in tafi zansa Ahmad ya kawomin".
cikin happy tace.
"To sai kinzo".
Da haka sukayi sallama, sukuma sukaci gaba da hirarsu.
Acan ɓangaren Saifuddeen kuwa ya riga daya gama tsara yanda rayuwar gidan nasa zata kasance, inda ya rabawa kowaccensu kwana bibbiyu, duk kuwa randa yake ɗakin ɗaya daga cikinsu ne kedashi, to zai na zuwa part ɗin wanda ya kasance ba itace ke dashi ba yayi mata saida safe.
Yanzuma fitowansa daga wanka kenan, bayan ya gama shirya kansa tsab cikin wasu haɗaɗɗun kayan bacci, masu kalan pink da ɗigo ɗigon fari, sosai kayan sukayi masa masifar kyau, tare da bayyana zallan hasken fatarsa, kasancewar wandon irin mai tsayawa aɗan gaba da guiwa ɗinnan ne kaɗan, sai kuma rigar dake da hannu wanda shima ta wuce guiwa, sosai kayan sukai masa kyau, ga lallausan sajensa daya kwanta lub-lub akan fuskarsa. Kaitsaye ɗakin Ameena ya nufa, danyi mata saida safe kaman yanda ya tsara. Yana shiga cikin falon nata yaji shiru kaman babu kowa acikin
Showing 135001 words to 138000 words out of 237945 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46 Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80