na bawa su Mamy dasu Aunty Lubna haƙuri, dan suma fushi sukeyi dani."
Kyawawan idanunsa ya ɗan lumshe, tare da jinjina mata kai, alaman "To."
Hannunta dake cikin nasa ya ɗan murza, sannan suka nufi ɓangaren Mamyn.
Har zuwa yanzu kuwa bata daina sakin sheshsheƙan kuka ba, hasali ma amaimakon kukan nata ya tsaya, ƙaruwa yayi, saboda wani irin yanayi da takejin kanta aciki.
Anan bakin kofar shiga sashin Mamyn ya tsaya, saboda aganinsa bai kamata ya shiga musu kai tsaye ba tare da an masa iso ba.
Ganin ya tsaya ne, yasa ta juyowa ta kalleshi, gani tayi ya zuba mata kyawawan idanunsa, wanda da zaran ta kalli cikinsu, to sai taji wani iri ajikinta.
Ɗan lumshe idanun nasa yayi tare kuma da buɗe su alokaci guda, wani irin abu ne taji yabi jikinta, hakan yasa ta zare hannunta daga cikin nasa.
Ahankali ta murɗa handle ɗin ƙofar falon, ta shiga bakinta ɗauke da sallama, wanda muryarta ko fita da kyau bayayi tsabar kukan da tayi.

Mamy, Aunty Lubna, da kuma Goggo Maryama, da Ziyada, sai kuma su Zainab da Ubaida ne zaune a cikin falon, jin sallaman Zaleehan ne yasa su duka ɗago kai suka kalleta, ahankali take takawa har ta ƙaraso cikin falon, da ɗan sassarfa taje ta faɗa jikin Mamy, tare da sakin sabon kuka me sauti, rungume Zaleehan Mamy tayi, tana mejin matsanancin tausayinta aranta, jin Mamyn ta rungumeta ne, yasa ta ƙara volume ɗin kukan nata, haka falon ya ɗauki shiru ba abun dake tashi cikinsa sai sautin kukan Zaleeha, hakanne yasa hawayen dake cikin idanun Mamy suka samu daman gangarowa.
Cikin sheshsheƙan kukan ta ɗago daga jikin Mamyn, muryarta na rawa tace.
"Mamy dan Allah ki yafemin, kinga Baba Malam ma ya yafemin, kuma yace na koma ɗakin mijina na zauna, fushin Baba Malam ya tsoratani sosai Mamy, wallahi bazan sake gudun ku ba, nasan nayi kuskure me girma dana tafi na barku, bayan kuma aduniya bani da wasu sama daku, dan Allah Mamy kema kiyi haƙuri kinji, Ya Ahmad ɗina ma ya yafemin."
ta ƙare maganar tana me kamo hannun Mamyn ta riƙe.

Murmushi Mamy tayi tare da share hawayenta, tabbas taji daɗin jin cewa Baba Malam ɗin ya yafewa Zaleeha, dan ko itama adole taƙi kula Zaleehan, bawai dan tana fushi da ita ba, duk da ma tasan cewa abun da Zaleehan tayi bai dace ba, amma fushin da aka yi da ita yayi yawa, ba a fushi me tsanani ga ƴa mace irin haka.
Ɗan shafa bayan Zaleehan tayi, cikin kulawa tace.
"Kukan Ya isa haka Zaleeha, tabbas naji daɗi ƙwarai da Baba Malam ya yafe miki, nidama tuncan Zaleeha ba fushi nake dake ba, kuma na yafe miki, sannan dan Allah kada ki sake kamanta irin kuskuren da kikayi abaya kinji, sam guduwa ga ƴa mace ba ɗabi'a bace me kyau, ki zauna agidan aurenki kiyi zama me kyau, kada ki saɓawa mijinki, tasanadiyar hakan da zakiyi saikiga kin samu aljanna da yardan Allah."

Cikin kuka ta jinjina kanta alaman gamsuwa, da kalaman Mamyn, ahankali taɗan janye jikinta tare da tashi ta ƙarasa gaban Goggo Maryama, durƙusawa tayi tare da, ɗaura kanta akan cinyar Goggo Maryama'n, cikin sheshsheƙan kuka tace.
"Dan Allah Goggo Maryama ki yafemin, nasan kema kina fushi dani, dan Allah Kuyi hakuri, yanzu al'barkanku nake nema."
Goggo Maryama kuwa Ɗan share hawayen dake cikin idanunta tayi cikin sanyi tace.
"Babu komai Zaleeha na yafe miki, Allah ya yafe mana baki ɗaya, fatana dai shine ki nutsu kiyi zaman aurenki, insha Allah saikiga Al'barka nata bibiyan rayuwarki."
Kanta ta jinjina, cikin sanyi tace.
"Nagode sosai Goggo ." tashi daga jikin Goggon nata tayi, kai tsaye jikin Aunty Lubna ta faɗa, rungumeta tayi ƙam, tana ɗan sakin sheshsheƙa, itama Aunty Lubna'n hawayene cike a idanunta, saida sukayi kuka sosai kafun, Zaleehan ta sake riƙe Aunty Lubna'n, cikin dashashshiyar muryarta tace.
"Aunty dan Allah ki yafemin, kidaina fushi dani, kinga Ya Ahmad ma ya yafemin."
wani irin tausayin Zaleehan ne ya cika zuciyar Aunty Lubna, cikin kulawa tace.
"Ni dama ban ƙullaceki da komai ba Zaleeha, wallahi na yafe miki har acikin zuciyata."
Ziyada dake zaune agefe ne ta taso tare da ƙarasowa ta rungume Yayarta ta, nan tasaki kukan tausayinsu, juyowa Zaleeha tayi ta rungume Ziyada'n, wanda ayanzu take ganinta kamar Adda Maryam, dan sanyin zuciyar Ziyada dana Adda Maryam ɗin iri ɗaya ne.

Acan ƙofar shigowa falon kuwa Saifuddeen ne zaune ya sunkuyar da kansa ƙasa, Zakariyya wanda shigowansa gidan kenan, hango Hamma Saifuddeen zaune akan wheelchair ɗinsa yasa shi ƙarasowa cikin sauri, fuskarsa ɗauke da ɗan murmushi ya taɓa kafaɗan Saifuddeen ɗin, tare da cewa.
"La Hamma Saifuddeen kaine."
murmushi Saifuddeen yayi tare da miƙawa Zakariyya'n hannu suka gaisa, fuskar Zakariyyan ce taɗan fidda rauni, asanyaye yace.
"Hamma da Adda Zaleeha kuka zo?". ahankali ya jinjina masa kai alaman "Eh" wani irin daɗi Zakariyyan yaji acikin ransa shikenan yasan Baba Malam ya yafewa Zaleeha, cikin zumuɗi ya kama saman wheelchair ɗin Saifuddeen ɗin, tare da cewa.
"Hamma mu shiga ciki to."
Haka suka shigo cikin falon na Mamy, bakin Zakariyya ɗauke da sallama.
Har tsakiyan falon Zakariyya ya ƙaraso da Saifuddeen ɗin, nan cikin body language ɗinsa ya gaishe da Mamy, da kuma Goggo Maryama, fuska asake haka suka amsa masa, gaishe da Aunty Lubna yayi itama ta amsa tanayi masa murmushi, dan Allah ma yasani itakam Saifuddeen ɗin na burgeta, mutum ne shi me mutunci da kamun kai, komai nasa daban, babu ruwansa da cewar shi nakasashshe ne, abunda ta fahimta ma shine shi nakasar tasa ado ta zame masa, dan idan yana kan wheelchair ɗinsa zaka ɗauka cewa wani sarkine mai cikakken iko,,
sosai abun keyi masa kyau.
Zainab da Ubaida ne suka gaidashi, cikin body language ɗinsa ya amsa yana ɗan murmushi, sukam daganinsa mamakine yakusan kashesu, sunsan dai Zaleehan gurgu kuma kurma ta aura, amma ko kusa basusan haɗuwa da kyawunsa har yakai haka ba, dan idan ma ba dan sunsan cewar shi gurgu bane, to zasuce ya hau keken ne kawai dan ƙarawa kwalliyarsa armashi, Ubaida ne ta jinjina kanta, acikin zuciyarta tace.
"Lallai Zaleeha bata da hankali, wace macece zata samu wannan santalelen namijin sannan ta gudu ta barsa? hmmm ai irinsu Saifuddeen koda na kasarsu mata wawansu suke, saboda koba komai akwai kyau da cikar haiba."
Ziyada ne ta taso daga jikin Zaleehan tare da taƙarasowa gabansa, ɗan durƙusawa tayi, cikin sanyinta tace.
"Hamma Saifuddeen ina wuni."
Murmushi yayi wanda yaɗan bayyana fararen haƙwaransa, hannu yasa ya ɗan shafa kanta, cikin kulawa ya jinjina mata kai alaman "Lafiya" Zakariyya kuwa ƙarasawa wajen Zaleeha wanda kanta ke jikin Aunty Lubna tana ta faman sakin sheshsheƙan kuka yayi, cikin sanyi yace.
"Adda Zaleeha." ɗago kanta tayi ta kalleshi, sai kawai ta faɗa cikin jikinsa, tana sakin sabon kuka, shikansa Zakariyyan saida yayi ƙwalla, da ƙyar ya saitata ta iya tsaida kukan nata, hannunta ya kamo sannan ya haɗa dana Saifuddeen cikin kulawa yace.
"Muje na rakaku part ɗin Mama."
Hakan kuwa akayi har part ɗin Maman ya kaisu, anan falo suka iske, Mama, Aunty Ruda, da kuma Aunty Aisha, da Maman Mama da dai sauran ƴan uwanta arnataku,
gaba ɗaya sunyi jigum dasu.
Jin motsin shigowarsu, da kuma ƴar siririyar sallaman Zaleehan ne ya sasu ɗago Idanu suna kallonsu, Zaleeha na tafiya asanyaye, yayinda Zakariyya kuwa ke tura saman keken Saifuddeen ɗin, ahaka suka ƙaraso cikin falon, anan gaban Mama Zaleeha ta durƙushe tare da ɗan ɗaura kanta akan cinyar Maman, haƙiƙa uwa uwace komin munin halinta kuwa tana nan a mazaunin ta na uwa, sannan kuma ba'a taɓa sanjata, idanu Zaleeha ta lumshe, hakanan taji wani sabon kuka nason zuwar mata.
Su Mama kuwa gaba ɗaya tun shigowarsu idanunsu akan Saifuddeen suke, musamman ma Aunty Ruda da Mama dan tunda suke basu taɓa ganinsa ba sai yau ɗin, ganin hakanne yasa Saifuddeen sakin ɗan murmushi tare gaidasu cikin body language ɗinsa da Aunty Ruda'n, da kuma Aunty Aisha, fuska asake kuwa Aunty Aisha ta amsa masa, Aunty Ruda kam idanu ta zuba masa, tana mamakin tsantsar kamala kwarjinin da kyaun sa.
Juyowa yayi ya ɗan kalli Mama, cikin yanayin girmamawa ya gaisheta, idanu taɗan zuba masa, asanyaye da muryarta wanda ta dashe saboda tsabar kukan da tayi na rasuwar Adda Maryam ɗin ta amsa masa, lokaci guda kuma tayi ƙasa da kanta, saboda hakanan taga yayi mata kwarjini, acikin idanunta kunya mai ƙarfi da dana sani suka rufeta, dan kwata-kwata bata ɗauka haka yake ba, ta ɗauka irin musakan nan ne masu matacciyar zuciya wanda sun kele sun yaɗe sun shanye irin waɗanda ba zasu iya smfanan kansu Bama bare wani.
Ɗago kai Zaleeha tayi ta kalli Maman, ɗan lumshe idanunta dake zubar da ƙwalla tayi, asanyaye tace.
"Mama." Dubanta Maman tayi, tare da ƙura mata idanu.
Ɗan jan sheshsheƙa tayi, cikin muryarta da bata fita sosai tace.
"Na aikata laifi mafi girma, wanda yasa saboda haka Babana da kuma duka ƴan uwana suke fushi dani, sanadiyar haka har Adda Maryam ta rasu, bamu sake ganawa ba, nabar kowa da komai saboda idanuna sun rufe da son wanda ni kaina yanzu na yarda bazan sake ganinshiba, sai-dai kuma nasan awannan lokacin da ban samu goyon bayanki ba Mama, tabbas da bazan tafi nabar kowa ba, nayi kuskure me girma arayuwata, wanda kuma bana fatan sake maimaita irinsa agaba ɗaya rayuwata, fushin Baba Malam da Hamma Saif fushin Allah ne, bakuma zanso su sake fushi dani ba, ayanzu al'barka kawai nake nema, saboda na ɗauki al'ƙawarin zan zauna agidan aurena da daɗi ko ba daɗi, saboda haka ina buƙatar kyakkyawan fata daga gareki, domin har gaban abada ke uwace agareni, wanda kuma bazan taɓa sanjaki ba." taƙare maganar tana me kama hannun Mama, tuni hawaye kuwa wani nakoran wani akan fuskarta.
Idanun Maman ne suka ciko da hawaye, tabbas tayi nadaman abun da ta aikata na bin zugar kafurar yauarta, tunda ga lokacin da labarin rasuwar Adda Maryam ya riski kunnuwanta, tayi nadama ƙwarai sannan jikinta yayi sanyi sosai, duban Zaleehan tayi sosai, ganin yanda Zaleehan ta rame, ta zama wata abun tausayi, lokaci guda ta fita hayyacinta, yasa taji kuka nason zuwar mata, cikin sauri ta miƙe tsaye ta nufi ɗakinta, dan tsayawarta zai iya baiyanar da raunin zuciyarta tana gab da shiga ne tace.
"ALLAH ya baku zaman lfy Zaleeha."

Ganin haka yasa Zaleeha kwantar da kanta ajikin kujeran da Maman tatashi, ta saki wani marayan kuka,

Aunty Aisha ne ta share hawayen da suka cika idanunta, asanyaye tace. Ta kalli Zaleeha cikin sanyi tace.
"Jiya Solomon da matarsa sunzo sunyi gaisuwa, sunce suna son ganinki akwai abu mai mahimmancin da sukeso sanar dake, to lokacin bamu san inda kikeba sun kira layinki kuma baya shiga, amman sunce zasu zo nan bada daɗewa ba."
Wani irin sanyine ya ziyarci Zaleeha Allah yasa musulta zasuyi, Allah yasa musultan sune yayi sanadin zuwanta garin Numan".
cikin nitsuwa Aunty Shatu tace.
"Saifuddeen kamata kuje, Allah Ubangiji yayiwa rayuwar aurenku al'barka, ya baku zuri'a me al'barka."
Kansa yaɗan jinjina, sannan ahankali ya murza wheelchair ɗinsa ya ƙaraso har gaban Zaleehan, hannunsa yasanya yaɗan ɗago kafaɗunta, tare da miƙar da ita tsaye, hannunta ya kama, cikin nutsuwa ya jata suka nufi hanyar barin falon,
Aunty Ruda kuwa baki ta sake tana kallonsu, har suka fice daga cikin falon.
Haka suka fito compound ɗin gidan yana riƙe da hannunta, yayinda Zakariyya kuwa ke biye dasu abaya sai kallonsu yake, sai ayau yasake ganin dacewar Hamma Saifuddeen ɗin da Zaleeha, kallo ɗaya zakayi musu kaga kaman dansu biyun akayi kowannensu.
Sule driver na hangosu cikin hanzari ya buɗe musu murfin motar, zuwa lokacin kuwa tuni har ma Dirankadi yabar gidan, dan dama akwai inda zaije, sakin hannunta yayi, tare da juyowa ya sake bawa Zakariyya hannu sukayi musabaha, cikin ɗan jin daɗi Zakariyya yace. "Asauƙa lafiya Hamma, Allah Ya saka da al'khairi."
Kai kawai ya jinjina masa, sannan ya shige cikin motar bayan itama ta shiga.
Cikin nutsuwa Sule driver ya ja motar suka bar cikin gidan, Zakariyya kuwa saida yaga fitarsu kafun yake komawa cikin gida.

Tunda suka baro gidan take sakin sheshsheƙan kuka, haka ta ɓoye kanta acikin cinyoyinta tana sakin wani numfashi me zafi, duk abun da takeyi yana lure da ita, amma sai ya kawar da kansa gefe yayi kamar bai ganta ba,
saida tafiyar tasu ta ɗanyi nisa, kafun ta ɗago kanta, ahankali ta sauƙe idanunta akansa, wasu hawaye masu zafine suka sauƙo daga cikin idanunta, ji tayi gaba ɗaya zuciyarta tayi rauni sosai, wani irin ƙima da kuma girmansa ne suka cika idanunta, tabbas ayau ya taimaketa, yayi mata abun da mutane da yawa suka kasa yi mata shi, yau ya zame mata inuwa kuma majingina, ya kareta daga rana, sannan yayi ƙoƙarin haskaka rayuwarta, ya ɗaukota daga duhu ya kawota cikin haske, dame zata saka masa? wani irin kuka ne ya zo mata, hakan yasa ta faɗa jikinsa tare da rungumesa ƙam-ƙam tamkar zata haɗesu wuri ɗaya.
asakamakon hakan kuwa wani irin shock yaji ajikinsa, karon farko kenan da ta fara shiga cikin jikinsa dan kanta, hannayenta ta sanya ta zagayeshi, tare da ɗaura kanta akan faffaɗan ƙirjinsa, ta saki wani irin kuka mai taɓa zuciya, cikin kukan nata ne ta cusa fuskarta acikin ƙirjinsa, wanda hakan yasa aninayen dake gaban rigarsa ɗan ɓallewa, take kuwa fatan ƙirjinsa ta bayya, hakanne kuma yasa ahankali hancinta da laɓɓan bakinta ke gogan skin chest ɗinshi, wani irin kuka takeyi me taɓa zuciya, still kukan take tana ɗan jujjuya kanta acikin ƙirjinsa, hakan da takeyi ne yasa gaɓa ɗaya jikinsa yayi weak, wani irin abu ne yakeji na yawo ajikinsa, wanda zai iya rantsewa, cewa tunda yake aduniya bai taɓa jin irin hakan ba, wani fitinannen feeling yakeji, gefe guda kuma ga wani pleasure wanda ko sex suke da Ameena bai taɓa jin irin wannan pleasure da kuma feeling ɗin ba, babu abun dake neman zautar da tunaninsa kaman yanda tausassun laɓɓan bakinta ke gogan fatar ƙirjinsa,
A hankali ta ɗago kanta ta zuba mishi,ido shima idon ya zuma mata, goshinta na manne da haɓarss cikin Muryar me sarƙewa haɗi da sheshsheƙan kuka tace. "Nagode! Nagode!! Nagode!!! sosai Hamma Saif, tabbas ka taimakeni arayuwa, sanadinka gashi Baba Malam ya yafemin, nagode maka ƙwarai matuƙa, Allah Ubangiji ya biya maka buƙatunka na duniya da lahira, Allah yafaranta maka kamar yanda ka faranta min, Allahu rabbi ya gafarta maka zunubanka, kamar yadda kayi sanadin yafe min da Baba Malam yayi, tabbas kamin abun da kowa ya kasa min, nagode sosai Hamma S..a..i..f."
Kukane ya ci ƙarfinta, sai kawai ta sake rungumesa sosai. Ahankali yaɗan lumshe kyawawan idanunsa wanda suka soma runewa zuwa kalan ja, hannunsa yasa ya tallafo haɓarta, tare da ɗan ɗago fuskarta, hakan shi ya bawa fuskokinsu daman kusanci da juna, idanunsa wanda suke ɗan lumshewa kaɗan kaɗan ya zuba mata, ahankali ya matso da fuskarsa gareta har hancinsu na gogan na juna, goshinsa ya ɗaura kan nata hancishi na bisa tsinin hancinta haɗuwar numfashinsu waje ɗaya, shiya sanya suka lumshe idanunsu atare, ahankali laɓɓanta suka ɗan buɗe, saboda sheshsheƙan kukan da takeyi.
ɗan buɗe idanunsa yayi, kana ya ƙurawa kyawawan laɓɓanta, shanyayyun idanunsa, wani irin abune ke yawo acikin jikinsa, haka yakejin kamar ya kamo kyawawan laɓɓanta yayi kissing ɗinta,
Idonshi ya maida ya lumshe tare da ɗan zaro harshenshi ya ɗan lashi tattausan lips ɗinta,
da sauri ta buɗe ida nunta, ganin haka sai kuma ys janye fuskarsa baya yana sakin wata irin ajiyar zuciya yayi kamar bashi ya lashi laɓaɓɓan nataba, ahankali itama ta ɗan janye jikinta baya, nan kan kafaɗansa ta ɗaura kanta, ahankali take sakin ajiyar zuciya, har yanzu kuwa idanunta basu daina zubar da ƙwalla ba, saidai acikin zuciyarta farinciki ne me tarin yawa, ji take kaman anyaye mata duk wata damuwarta ta duniya, yafiyar Baba Malam da na Hamma Saif yasanya tanajin kanta, awata sabuwar duniya ta daban.
Hannunta ta saƙala acikin nasa,
Showing 123001 words to 126000 words out of 237945 words