ta na Tagging da Amaryan Magajin gida, gwara ita yar gatace kowa na santa ni fa bani da kowa a baya sai Allah. Assadiq bani ya ke so ba jikina ya ke so Sultanace abar son sa kuma itace uwar ya'yansa. Ko kuma nace ita ya zab'a ta zama uwar ya'yansa bani ba.
Na yi ta masa godiya ina sharan hawaye, shi kuma sai ya Rumgumeni ya na fadin"Shii ki daina kuka Siya in da ina da shi kasuwar duniya zan kai ki ki dauki duk abunda kike so domin na nuna miki kin chanchanta a wajena kuma matsayin ki ya zarce yadda ki ke Tunani ko hasashe."
Kallonsa na ke idanuwana na tara kwallah kafin nace"Ka tabbata ka na so na Assadiq?
Gyadamin kai ya yi kafin yace"Kina da Shakku me a kan son da na ke yi miki SiyaAssadiq?
Sai na kasa mgana sai kuka, kawai sai na Rumgumesa ina fadin"Ban damu ka so ni ba Assadiq, ammh ina rokon ka ka ji tausayina watarana ka Tsaya a baya na, ka zame min bango abunda zan jingina in ji sanyi a raina."
Cikin wata irin murya yace"in sha Allahu bazan taba barin ki ba, ki saka a ranki ko da kowa zai gujeki ni Assadiq ina tare da ke har Abadan."
Ko da karya ya ke fad'amin sai naji zuciyata na yaudarana da cewa Assadiq na sona ba shi da zabi ne.
Ni da kaina na had'e bakin mu waje d'aya ina Sumbatarsa.
Sannan ni da kaina na gayyacesa kan gadon mu muka gudanar da sunna, sannan ni da kaina na ja ragamar duk abubuwan da suka faru.
Ya yi ta sakamin albarka kamar zai lasheni, kafim ya tafi sai da ya siyamin kayan abinci sannan ya yi min Cefane.
Mganar kaya kuma na shawarcesa da cewa ko na siya wajen Maman Suhailat ne? sai yace kudina ne na yi duk abunda ya kamata.
Jin haka yasa bayan tafiyarsa na Kira Adda Fati na gayamata ita da Ramatu har Amma sai da na kira.
Ita Adda Rukayya tace ne akwai kawarta mai saida kaya zata yi mata mgana, ammh sai Amma tace tunda makociyata na saidawa ba'a haka na yi mata cinikin yafi na kai wajen Tunda an zaune lafiya.
Nima sai na aminta da Shawaran Amma shima da na kirasa na gayamasa abunda Amma tace sai ya yi mirmishi yace"Madallah da Amma Madallah da Uwar da ta haifi Hasiya matar Abubakar Sadiq."
Sai ya bani dariya a kalamansa na san shima ya aminta da na siya Hannun Maman Suhailat.
Haka ko a kayi wajenta na siya, da ya ke ta na kaya ta fito min da su na zaba da takalma, mayafai hijabai, da Tamfiofi da lesuna sannan sauran kudin kuma na Rage muka shiga kasuwa da Ramatu na siya akwatina Guda Biyu sai Inears, sai Dankunneye jaka Biyu na siya wajen maman sulahait nafi siyan kaya tunda sune na ke da karancin su a hakan ma na godema Allah, tunda Assadiq ya siya min wasu a baya.
Wannan zirga zirgan yasa na manta da Kudurina na zauna na yi Tunanin ya na da kyau na aikata abunda zuciyata ke Umurtana kuwa?.
Sai naga kamar in nayi hakan ban kyauta ba, gwara na Tsaya a iya matsayina kada naje garin neman gira na rasa idanuwana.
Saboda haka yasa na daina Duba Status din Saliha Tunda har kirana ta yi tace min ta zo garin, ta na kara min Tuni tunda nace mata zan zo mata Biki.
Ranar Al'hamis ma ta kara kirana sai kawai nace mata ba na jin dadin jikina zai yi wahala nazo, duk sai bata ji dadi ba ta ce har ta fad'ama sauran Sister's dinta zan zo mata biki.
Kenan har ta ba su labari?
Abunda ban sani ba tuni har sun san ta na zumunci da yar'uwan mijin Salima.
Har ita Saliman ta gayamata ta yi ta mata kwatancena sai tace bata gane ni ba.
Har Safiyar Jumma'a ban bari zuciyata ta Rinjaye ne ba, sai da rana da na yi kiran Assadiq bai Dauka ba, Tuni kishi ya Rufemin ido zuciyata ta bani ya na chan tare da Amaryar so wacce ya ke so.
Kawai sai na kwanta ina ta kuka ni kadai bani da mai lallashina sannan na Bude wayata naga Hotunansu Saliha sun ci gayu daga inaga Abu suka yi ga shi nan duk sun saka kaya iri daya.
Amaryan ta sha kyau har tagaji da kyau kamar ita ta yi kanta.
A raina nace Dole Assadiq ya so Yarinyar nan saboda kyakyawace ajin Farko gata yar yarinya karama.
*****
Ranar Daurin aure.
A garin shinkafi aka Daura auran Abubakar Sadiq da Sultana, Abba ya ba da auran Sultana Mallam Shitu kuma ya karb'an ma Sadiq.
Daurin auren da ya samu mahallata ma su yawan gaskiya Tahir duk sai da ya gayyato abokan karatunsu na Zariya har da su Jb da Mb da suka zauna Daki daya Cikin makaranta.
Wasu ma Sadiq ya manta da su Ammh Tahir bai manta da su ba.
Abokan kasuwancin Abba duk sun hallata mazajen su Surayya Harda Alhaji Jibril da ya zama na Hannun Daman Abba shi da Mijin Salima Mubarak.
Sannan yan'uwan Mallan Shitu da abokan arzuka duk sun hallata har da wasu daga cikin cllasmate din su Sultana da Siyama.
Hatta da Dangin Umma da Mama sun Hallaci wannan Daurin auran.
Bayan an gama daurin auran daman daga Gusai sun taho da abinci wad'anda za su koma Gusai suka Tsaya suka yi sallah suka ci abinci a nan gidan mallam Shitu.
Wadanda zasu koma daga nan aka Raba musu Takaway mai tsire da Lemuka.
Sadiq ba shi da wasu abokai Daga Tahir sai Jb sai Mb sauran duk sun tafi, Jb ma daganan ya wuce kano Mb ne kawai sai Tahir, Tahir ma yayyensa duk sun zo ammh daga shinkafi suka wuce Daura Hajja da matan su kasim suna Gusai ana cin Biki da su.
Saboda matsalan hanya Karfe uku suka baro shinkafi zuwa Gusai
Abba da Mutanensa sun riga su yin gaba su Surayya suna ta kiran Assadiq yazo ga mai Hoto ya zo shi fa ake jira.
Ango na ta fama da Babban Rigar Shadda mai ruwan kasa, takalmimsa baki da hularsa dara kalan aikin jikinsa agogon hannunsa ma baki ne,
Cikin kayan da Abba ya Dinkamasa ne Tahir ma Babba rigane a jikinsa kamar shine angon.
Duk da a saman Fuskarsa ya na Fara'a ammh daga kasan ransa damuwa ne damkam aciki sai ya ke ji kamar ya ci Amanar Siya me yasa bai fad'a mata gaskiya ba Tun farko?
Shi dai ya ke kawai ya ke yi, ammh kuma ya rasa sukunsa kaddara ta riga fata daman chan Allah ya Rubuta masa Hasiya da Sultana su ne matansa anan duniya.
Ba shi da wani Tsumi ballatana Dabara hakan wani kadararren Lamari ne daga cikin littafin kaddaransu Wato Launil Mahafuz.
Sun iso Gusai biyar da wani abu na yamma, daman a Hotel ya sauke su Tahir tunda suna garin tun jiya, ya so su koma ta chan ammh kuma Tahir yace su Surayya sun matsa.
Sai suka wuce gidan suna zuwa gidan cike da Mutane duk suna Haraban gidan ana ta Daukan Hotuna.
Amarya ta saka wani irin leshi mai kyau da yarari kalan Deep Blue, an yi mata kwalliya sannan ta yane kanta da Neat mai sharara takalmin kafarta ya na da tsini Rigar jikinta Fitted gown ne ta kamata sosai daga kasa ta na sharan kasa.
Wuyanta da Hannayenta Gold ne, ta sha jan lalle da ya kara fito da kayanta, su kuma su Surayya suma leshin a jikinsu, ammh na su fari ne da gold ajiki,suma sun yi kyau kuma sun sha kwalliya har ta su Umma ma Less din ne sai da su kalan nasu Dabam.
Innani ma less din ta saka ta ci Uban Dauri kamar wata Bayarbiya.
Suna shigowa tunda suka hangosa suka Dauki Ihu suna fadin"Ango ya sha kamshi."
Suka jasa zuwa inda Sultana ta ke daman suna ta faman daukan Hotuna ne, Umma ta koma ciki wajen mutane Mama ce a ke Dauka da ita, itama kiranta aka yi, Sai Innani ce da duk Hoton da za'a yi sai ta shiga mai Hoto na Dauka wasu na Dauka ta waya.
Daga gani wannan sha'anin babban sha'ani ne da ke ji da shi acikin gidan.
Tun da naji ana ihun kiran Ango ya sha kamshi na sauko daga kan Barandar Mama da ni ke Tsaye Tun dazu bayan Saliha ta matsamin na fito za'a yi Hoto.
Lokacin da gidan suka samu Labarin an Daura aure sai suka cika gidan da Gud'an Farinciki ni kuma alokacin sai naji kamar kafafuwana sun kasa Daukata saboda yanayin da na ke ciki, sai naji kamar zan fara Nadaman zuwa na tun yanzu.
Na fito ne na kara tabbatar ma da kaina Shin Assadiq ne nawa ko wane ne wanda ban sani ba!?
Sai dai Lokacin da na Fara takawa inda suka cika ana Ta hotuna.
Ina sanye cikin Sabon leshina dinki Riga da zani mai Ruwan madara ne sai mayafina Gold dake saman kafadata.
Saliha taso a yi min kwalliya nace mata bana bukata ammh su dukkansu sun yi kwalliyarsu.
Sai da naji kamar an fizge zuciyata daga zuciyata a lokacin da na yi Tozali da Assadiq gefen Sultana ya rike mata kugunta ana ta Daukan su Hoto.
Kura musu ido na yi, ina kara neman Tabbaci kada ya zamto idanuwana ne suka faramin gizo ko ba na gani Daidai ne.
Sai dai har wajen mintina goma abu d'aya na ke gani sai na kara samun Tabbacin tabbas ASSADIQ ne MIJINA Kuma sannan MIJIN SULTANA.!
Idanuwana sun fara tara Ruwa jiri na ke gani, kaina naji ya fara saramin sai naji duniyar ta fara juyamin.
Kawai sai na juya na fara tafiya kaina na kasa sai naji naci karo da mutum da Sauri na Dago cikin sanyin murya ina fadin"Sannu ban kula ba n.."
Sai maganata ta makale lokacin da na ci karo da Tahir.
Tabbas nasan shi Tahir ne abokin Assadiq da na fara sanin su tare duk da yanzu ya ijiye gemu na ganesa.
Waya ya ke yi kuma kamar ya na cikin gaggawa ne da yasa bai Tsaya ba kawai yace min"Bakomai."
Ya wuce sai na bi shi da kallo cikin mamaki.
Kila bai gane ni ba kamar yadda na ganesa, Gidan naji kamar ya fara juyamin sai na kama hanya zan fita ina sharan hawaye.
Sai sai ji na yi Saliha ta rikoni ta na Fadin"ina zaki? Taho mu yi Hoto tare."
Sai da nayi Dubaran goge kwallata ina yi mata ya ke, ina shirin nace mata bazan shiga Hoton ba sai da ta jani, sai dai muna zuwa wajen itama Yan'uwanta suka jata za su yi family Picture gabadayansu mata Amarya da Anko na Tsakiya.
Kamar an Dasani sai gani Tsaye ina kallon Assadiq ba na ko kiftawa kamar kuma ance ya kalli barayin da na ke sai muka had'a ido da shi.
Bansan ko wani irin Hali ya shiga ba ammh ya samu Daukewar Numfashi da Tsayawar gudun jini na wani Lokaci.
Ni kuma da na Tabbatar da ya gani sai na sakar masa mirmishi, mirmishin da ya fito da zubar kwalla daga Idanuwana.
Ba wanda ya Lura da inda Sadiq ya Kurama Ido sai Tahir.
Cikin mamaki ya kallo in da ya ke kallo sai kawai ya gani.
Da farko bai gane ni ba, Hasken Fatata ya fara Tona ni a wajensa.
Cikin mamaki ya kara ware idanuwansa kafin yace"HASIYA.?
A fili cikin mamakin ganina.
Ya juya ya na kallon Sadiq sannan ya juya shima ya na kallona.
Da Sauri Tahir ya karisa wajen Assadiq ya jawo hannunsa ya na fadin"Ku ban aron ango na minti biyar."
Su Sajida suka fara masa caa ya na yake yace mgana za su yi yanzu zai Dawo.
Kamar rakumi da akala haka Tahir yaja Sadiq gefe da yaji kamar Duniya ta Tsaya masa cak.
Cikin Fitan hayyaci Tahir yace"Sadiq ka ga abunda nake gani kuwa?
Sadiq na kallona yace"Me ka gani Tahir?
Tahir yace"Hasiya mana zabiyar matar da ka saka ita nagani mana, ga ta chan ko ba ita ba ce?
Ya fad'a ya na nuna masa ni da ni ke tsaye ina kallonsu.
Cikin sanyin jiki da na zuciya Sadiq yace"In dai kai ma kana ganin ta to da gaske itace. SIYA ce."
Tahir ya Dafe kansa kafin yace"Innalillahi akwai matsala, akwai matsalan"
Kaawai sai ya Juya da Sauri Sadiq ya Rike masa Hannu Lokaci daya ya na fadin"Ina zaka? Me zaka yi?
Ya fad'a cikin Rawan murya.
Da Sauri Tahir yace"Zan je na sallameta ne zan gayamata ta tafi don Allah nan ba Muhallin zuwanta ba ne"
Da Sauri Sadiq ya kara Rike masa Hannu Cikin Muryansa da Firgici ya fara Disasar da ita yace" Muhallin zuwanta ne Tahir Tunda Gidan Iyayen MIJINTA NE."
Tahir ya kallesa da Sauri Cikin Bude ido da baki, jinjina masa kai Sadiq ya yi ya na jin mutuwar jiki da na zuciya yace
"HAR YANZU HASIYA MATATA CE TAHIR."
Bakin Tahir sai ya fara barin Makauniya ya yi sama ya yi kasa lebensa na sama da kasa har Numfashinsa yaji ya Sarke ya na bin Sadiq da kallon ko ya fara Hauka ne.
Sakin Hannun Sadiq ya yi sanda yaga na Juya ina sharan kwallah da zafinsa ya biyo ni har Babbar Rigarsa na Hard'esa.
Baki a hamgame ya na Rufewa ya na Budewa haka Tahir yabi Sadiq da kallo ya kasa Motsi.
Sahida ce ta hangosa suna chan suna Hotuna a zatonta ya gaji ne zai gudu da Gudu taje ta Rikosa ta na fadin"Big sis zai gudu fa."
Kafin ka me? suka Yayyamesa suna masa Ihun yau Ranarsa ce sai ya gaji da Hoto.
Ya na leken Hasiya sai yaga kuma ya nemeta ya rasa so ya ke ya yi mgana ya kasa haka suka jasa suka maida shi kusa da Sultana.
Dage ya ke yi da kansa Ya na son hango ta ina Siya ta bi? Ya na da Tabbacin ita ya gani ba Aljannah ba.
Surayya ce ta zo kusa da shi ta na gyara masa kai tace"kai daina mana Salon Daukan Hoton yan zariya."
Dariya suka saka masa gabadaya shi ko gabadaya Hankalinsa baya jikinsa.
Yaga wajen Siya da Tarin Tambayoyinsa.
Ta ya ya aka yi ta san nan gidan? Waye ya kawota? Me ta sani a game da shi?
Tahir kuma ya na nan Tsaye a wajen da Sadiq ya barsa kamar an dasa shi
Kwakwalwarsa na faman maimaita masa kalaman Sadiq.
"HASIYA MATATA CE HAR YANZU."
KO dai Sadiq ya zare ne? Baya cikin Hayyacinsa ne zai kira matar da ya saka da matarsa?
Sai wata zuciya tace to in bai saketa ba fa?
Sai da yaji wani irin Gif a saman kansa in dai ko Hakane Sadiq ya cika Babban Mahaukaci.
Ni ko ina nan acikin Haraban gidan banfita ba, bayan wata mota na samu na Labe ina Danne bakina.
Kada a jiyo kuka na , kasa na Durkushe kafin na saki bakina na fashe da wani irin kuka, kukan rashin madafa da ganin abunda baka taba zato ko tsammani ba.
Duk da tarin Hujjoji sun Tabbatar min da gaskiyan waye Assadiq ganin da na yi da Idanuwana ya fi komai Tarwatsa Rayuwata.
Nan ne gidan su Assadiq.
Matar da na gani a kaduna itace Mahaifiyarsa.
Mutumin data gani yau da Safe Abba shine mahaifinsa gidan nan kuma cike ya ke da Ahalinsa da yar'uwansa.
Ni miye matsayina?
Assadiq da abokinsa sun gani gwara Bakina alaikun na sulale na bar gidan nan tun kafin abunda ke Boye ya bayyana wanda bayyanarsa bazai yi ma kowa dadi ba, kuma rashin jin Dadin sai ya fi muni a kaina.
Da Sauri na mike ina waige waige da Mayafi naa na saka na Rufe fuskata na bi cikin jama'a na isa bangaran Mama In da Saliha ta saukeni a Daran jiya da na iso.
Dakin da muka kwana jiya na shiga duk suna haraban gidan ba kowa a bangaran Mama har na Dauko karamin akwatina na fito
Kaina cikin mayafina ina rike da karamar jakana ina kuka da Hawaye shabe shabe na fice Daga gidan su Assadiq.
Ashe Tahir ya ga fita ta, suna tare da Mb da yazo ya same shi cikin wannan Halin Dimuwan.
Ce masa ya yi ya na zuwa da Sauri yabi bayana domin so ya ke kara jin Tabbacin abunda Sadiq ya gayamasa Daga bakina.
*K'arshen littafi na biyu, Zamu cigaba da littafi na biyu bayan mun je Hutun kwana Biyu*
Nagode madallah da Masoyan Janafty.
*Janafty*
Showing 96001 words to 98628 words out of 98628 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33