sun shige Shashen Mama ba su lura da shi ba.
Ammh Sultana ta ganshi shiyasa ta tsaya kyam ta na kare masa kallo Zuciyarta na Harbawa.
Sai yanzu da ta kara wayau sannan ta had'u Da Sabbin kawaye a makaranta ta kara sanin muhimmancin Sadiq a Rayuwarta.
Ba ta san ta Tsaya ta na kare masa kallo ba, ta shagala da alfaharin yanzu wannan Had'adden gayen na ta ne ita kad'ai tuni wani alfahari ya cika kirjinta tare da wani kaunar Sadiq da tun daman ta na cikin zuciyarta Boyewa ta yi,
lokaci d'aya kuma kishi ya zo ya lullubeta na yadda zai fita har wasu matan su kalle mata abunta.
Sultana bata gama Fahimtar kanta ba ammh ta riga ta tabbatar da abu d'aya.
Ta na cikin Sahun mata ma su mugun kishi kishi ma na Hauka, ba ta kaunar taga wani ya rab'i da abunda ta ke so bata so ta kare rayuwarta a haka kamar yadda mahaifiyarta ta rasu ta bar duniya ta bar Baba da wasu matan kuma ya na cigaba da Rayuwarsa.
Ba ta son ta yi aure ta rika rab'a mijinta da wata kamar Umma da Mama, ba ta son ta yi auri taga wata matar na haihuwa da mijinta da ta ke so bayan ita, ba ta son ganin ya'yanta sun taso kamar su Salima da su Anty Surayya ta fi son komai in ya kasance nata ne to ya zama natan har gaban Abada nata ita kadai da bazata taba sharing d'insa da kowa ba.
Ta na cikin wannan Tunanin bata sani ba har ya gama saka Links dinsa ya Dago da kansa da su Umma ya fara cin karo suna masa mirmishi.
Shima cikin sauri ya maida musu da martanin mirmishin nasu sai dai ya yi Saurin kauda kansa gefe saboda ya na jin nauyin Umma da Abba a kan abunda ya aikata ba da sanin su ba.
Inda ya kai kallon nasa ne ya hango Sultana Tsaye kofar bangaran Umma cikin kayan makaranta goye da jaka a bayanta.
Abunda ya ba shi mamaki abu d'ayane zuwa Biyu, na farko ta yi kiba kamar ba wannan siririyar yarinyar Sultana ba na biyu kuma kuresa da idon da ta yi yasan tare suka ta shi a karkashin Rufi d'aya ammh bai taba sanin Sultana da kallo haka ba. yarinya ce mai kunya da shuru shuru.
Ya yi mamakin yadda ya ke kallonta ido cikin ido itama kuma ta na kallonsa bata Dauke idanuwanta ba.
Bai dauke kansa ba sai da yaji Umma na kiram sunansa sannan ya Sauke Numfashi ya karisa ga Umma ya Rankwafa ya gaisheta.
Ita ma kamar Abba Rumgumesa ta yi ta na fadin"Auta na ya kara girma."
Ya na mirmishi yace"Umma ta kina lafiya?
Ya fad'a ya na shafa fuskarta acikin ransa kuma fad'i ya ke Umma ki yafemin na yi miki Laifi.
Cikin jin dadi Umma Ta rike hannunsa ta na fadin"Lafiyata kalau sai dai ina kewar Auta na."
Kai ya kad'a kafin yace"Umma zan yi dogon Hutu wannan karon Autan ki zai dade tare da Ummansa."
Umma ta washe baki ta na kallon Abba kafin tace"Da gaske Auta?
Kai ya gyad'a mata sai kawai ta Rumgumesa ta na fad'in"Allah ya yi maka albarka Abubukar Sadiq"
Ya amsa mata da Ameen Ameen shi da Abba.
Sai a lokacin yaga Mama sakin Umma ya yi ya karisa gabanta ya Rankwafa ya na gaisheta ta saka hannu ta Dagosa ta na amsa cikin Sakewa.
Jinjina kai ya yi Lokaci d'aya ya na fadin"Mama duk kuna lafiya ko?
Mama tace"Lafiya kalau mu ke Sadiq ya zariyan?
Ya amsa mata da Alhamdulillah, Abba ya duba agogon Silban da ke hannunsa ya na fadin"Zamu makara fa Magaji."
Da Sauri yace"Mu je Abba."
Key din motar ya mika masa ta kamfanin Toyota.
Sadiq ya shiga gaba Abba na binsa a baya su Umma suka rakasu da Allah ya tsare.
Ba su bar wajen ba sai da suka ga Fitan su daga gidan sannan kowacce ta nufi bangaranta.
Umma bangaren Innani ta leka Allah Sarki ta iske ta barci ya kwasheta a kasa daga zaune sai ba ta tasheta ba ta koma bangarenta da Niyar in da idar da Sallah sai ta koma ta tasheta.
Ko kafin su Abba su dawo masallaci Umma ke da girki Ranar ita da Sultana da Hajiya yar aikinta sun gama had'a komai na abincin rana.
An kai na shashen Mama, Abba kuma da na Sadiq Umma tace akai bangaran Abba tunda tasan in suka dawo zasu zauna tare su tattauna.
Na Innani ne Umma ta Umarci Sultana da dauka ta kai mata sannan ta tasheta ta yi sallah.
Sultana ba ta yi niyar zuwa ba saboda tun jiya su ke fad'a da Innani daga jiya da Safe kafin su tafi makaranta ta shiga gaisheta sai tace ta kunna mata Tv tashar Larabawan nan.
Ba musu ta zo zata kunna sai Tv ya ki yi ashe kan soket din ya lalace.
Innani taji shuru ba'a kunna ba ta kara mgana Sultana tace ya lalace.
Ai Innani bata jira taji me ya lalace ba ta fara salati ta na salallami da cewa Sulaimanu ya siya mata Tibi ammh Sultana ta lalata mata Saboda mugunta da keta.
Ita kuma Sultana taji Haushi tace ba ita bace sannan ta daina ce mata muguwa.
Ai ko Innani ta harzuka ta lalubo sandarta ta daidai Saitin Sultana ta Rafka mata sai a saman kafarta sai da wajen ya kumbura sannan bai isheta ba ta bita da Zagin cewa Albasa ba ta yi Halin Ruwa ba, ba Halin Kuluwa ta Dauko ba bakin Hali da mugunta na Ubanta shitu ta gado.
Sultana na kuka ta bar bangaren Innani ta kuma yi alkwarin sai ta nemota bazata kara komawa ba jiya kam duk wanda ya shiga sai ta gayamasa Sultana ta lalata mata Tibinta Saboda muguntar da ta gada wajen Ubanta Shitu.
Saboda Umma ce shiyasa ta kasa mata gaddama.
Ganin ta na Tura baki yasa Umma ta yi dariya ta na fad'in"Ke da Kakarki taki kuma yau Sultana? Ba mai ji kan ku fa ke da Innani."
Sultana ta kwabe fuska kafin tace"Muguwa fa ta ke kirana yanzu."
Umma tace"Ki je ki kaimata zaku shirya ne."
Ba ta da Halin yin musu sai ta yafa mayafin Maryam's Egyptain Abayan da ke jikinta mai kalan sararin Samaniya
https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V
+201123302418
Sannan t Dauki Farantin abincin Innani zuwa Banagaranta.
Ta na shiga ta iske ta bata Falon ga dai Sandarta da gilashinta nan.
Dankwafar da abincin ta yi a kasan Cafet din sannan ta saka kafa ta shure sandar Innani kamar itace da kanta ta Daketa.
Innani da ke cikin Dakinta bayan ta idar da sallah taji motsi daga ciki ta wage Murya ta na fadin"Waye nan?
Shuru ba'a yi mgana sai kawai Innani ta yi tsaki ta na fadin"Ko ma wani shegen ne kada ya yi magana. A fitar min daga daki tunda ba d'an wani ya gina min ba Ehe."
Sultana na jin haka bata kara ko Second ba ta fice daga bangaren innani da gudunta.
Innani ta ji gudun sai dai bata san ko waye ba kyafci ta yi kafin tace"Yanzu haka cikin ya'yan Suwaiba ne. Ina ga ja'irar nan ne Salima Mara kunya."
Bata san cewa Yar gaban goshinta ba ce Sultana da suka yi fad'a.
Sultana na komawa tace ma Umma ta kai mata Umma ta kalleta ta na Fad'in"Kin ta sheta ta yi sallar?
Sultana tace"eh"
Saboda in tace a'a Fad'a Umma zata yi mata..
Daman tare suke cin abinci da Umma suna zaune a tsakiyar falo Sajida ta kira wayar Umma ta Dauka suna mgana anan taji Umma na cewa Yaya Sadiq ya ce zai jima a wannan Hutun kafin ya koma haka kurum taji sanyi acikin ranta ko bakomai zata rika ganinsa Sosai ta na jin dadi.
Abba da Sadiq suna dawowa masallaci suka yada zamansu a shashen Abba tare suka ci abinci suna ta Hira duk da yawanci Hirar ta Abba ne kuma hirar kasuwancinsa ne.
Shi kuma Sadiq ya na ba shi amsa ya iya abunda ya sani duk da bai karanta kasuwanci ba ammh mu'amala da Abba da sanin wasu al'muransa yasa yasan wani abu da yawa akan kasuwanci.
Sadiq ya gaggayama Abba wad'anda suka kirasa daga Shinkafi.
Ciki harda Goggo Husai na mganar Yarta ta samu gurbin karatu a jami'ar Buk kano zata karanta low ta na Bukatar taimako.
Abba ya kalli Sadiq kafin yace"Ita dai Husai bata jin mgana na fa gayamata ta yi ma yarinyar nan aure tunda y'a macece karatunta ba Dole ba ne."
Sadiq ya kalli Abba kafin yace"Abba karatun y'a mace a wannan zamanin Dole ne, kamar yadda Namiji ya zama Dole ya yi ilimi domin ya Tsaya da kafafunsa haka itama mace zata yi wannan Ilimin domin ta tsaya itama da Kafafunta."
Abba yace"Ita fa mace mutumcinta shine gidan auranta."
Sadiq ya murmusa kafin yace"Ban ki mganarka ba Abba. Kowa yasan aure shine cikar kamala da Mutumcin y'a mace. Ammh kuma ka sani wannan kimar ba ta cika ta zama Daidai sai mace ta samu cikakken ilimin addini da na zamani saboda ita ce uwa kuma mata sannan yaya ce in ba ta da ilimi bazata gyara zamantakewarta ba Abba."
Sai Abba ya yi shuru alamun ya na gamsuwa da mganar Sadiq.
Ganin haka yasa Sadiq ya cigaba da Fad'in"Abba duk wanda ya ilimantar da Mace guda d'aya kamar ya ilamantar da duka Duniya ne gabadaya. Ka da ka kara fad'in wannan kalmar saboda kada ka fad'a gaban wani da ya ke ganin girman ka Abba, kada ka auna kai ya'yanka sun samu mazaje da wuri ammh ai sun cigaba da karatunsu a gidajen mazajen su yaki da karatun ya'ya mata a wannan zamanin Jahilci ne Abba."
Da Sauri Abba yace"Hakane na bari. Za'a taimaka in sha Allahu sai kuma me?
Nan ya shiga zayyana masa duk wayar da suka yi masa ya na makaranta kananun da zai iya musu mgani ya yi musu wad'anda suka fi karfinsu daman yace zai fad'a ma Abba.
Nan take kuma Abba ya bashi Umarni a taimaka musu Sadiq da kansa ya rika kiransu yace su turo acct lambar da za'a sanya musu kudi.
Zamansu bai tashi ba sai da aka Biya ma kowa Bukatunsa Alhaji ya sha addu'a Sadiq sai masa Fatan gamawa da Duniya lafiya suke yi.
Sannan Sadiq ya rika yi ma Abba nasiha kan riko da zumunci
Abba ya sunkuyar da kai domin yasan ba shi da wannan.
Sadiq ya kallesa kafin yace"Abba yaushe rabonka da kaje shinkafi ka gaida yan'uwanka?
Abba ya yi jim kafin yace"Ina jin tun zuwan da muka yi tare. Kasan ba na samun zama ne Magaji"
Sadiq yace"Abba naji baka zama ammh waya fa? Itama ai ana zumuncin da ita ka ware Lokaci duk sati ka rika kiransu kuna gaisawa nasan a baya suna kiranka gajiya suka yi suka kyaleka. Abba ka sani Allah ne ya Umarcemu da mu Sada zumunci sannan yace mu yi zumunci da wanda bai yi damu ba, Sannan yace ya tanadi Aljannnah ga ma'abota sada zumunci wanda kuma ya raba zumunci ya barranta da Abunda Allah ya yi mana Umarni."
Abba ya jinjina kai kafin yace"Hakane."
Sadiq ya cigaba da fadin"Abba ka na da Halin da zaka taimaka musu da abunda Allah ya baka don Allah ka Sada zumumci da yan'uwanka sannan ka ja su ajikin ka bayan su baka da kowa yau ko mutuwa ka yi ba mu da wajen da zamu je mu sai wajen su."
Abba ya fara matsan ido ya na Fadin'"In sha Allahu zan gyara, Daman Innani ce....!"
Sadiq yace"Abba Innani akwai Rikicin Tsufa tare da ita. ka daina biye mata kai dai kayi abunda Allah yace ai ba komai in zaka yi ma yan'uwanka sai ta sani ba."
Abba ya kad'a kai ya na fadin"Allah ya yi maka albarka Madallah da Nagartattacen d'a kamar ka."
Sadiq bai bar shashen ba sai da Abba ya tabbatar masa da zai gyara zumunci da yan'uwansa in sha Allahu.
Sadiq shashensa ya koma ya kwanta Saboda ya Huta.
Sai ga kiran wayar Tahir ya na Dauka yaji sa ya na zaginsa tare da Fadin"Baka iya kira kaji ya Mutum ya isa ko?
Sadiq na lumshe ido yace"Ka isa lafiya? Ya su Hajja?
Tahir ya yi tsaki ya kashe wayarsa.
Sadiq ya wancakalar da wayar gefe ya na mirmishi.
Karaf sai ta fad'o masa a rai kuma ya yi alkwarin zai rika kiranta.
Da Sauri ya ta shi zaune ya Dauko wayar ya nemo lambarta ya kira.
Sai dai har ta katse bata Dauka ba sai ya kara kira nan bata dauka ba.
Sai wata zuciyar tace"Ko dai ta na kitchen ne? Ko kuma ta na waje ba."
Da haka ya koma ya kwanta ammh wayar na Hannunsa ya Kurama lambarta da ya yi Saving da SIYA ido.
Ita ke mai gizo a fuskarsa tunata da ya yi kawai sai da yaji jikinsa ya Dauki Dumi.
Hannunsa ya jimke ya lume kansa jikin Filo ya na jin kamar alokacin ya rika hannunta cikin nasa hannun Dumin hannunta na ratsashi har kwakwalwarsa.
A haka barci ya kwashe shi sai Hudu Saura ya tashi ya sake yin wanka ya Saaka Saukakkun kaya.
Abba ranar ya na gida bai fita ba, tare suka fita masallaci achan ma wani bawan Allah na neman taimako matarsa zata haihu a asibiti kuma za'ayi mata aiki.
Sadiq yace ma Abba suma zasu taimaka kudin dake Aljihun Abba duka Dubun goma Abba ya ba da sai ga shi lokaci kad'an an had'a masa ya kai Dubu arba'in tunda akwai masu kudi irin su Abba sosai.
Sai dai wasu ba zuciyan yi ne in kuma an yi dace da ya'ya irin su Sadiq a gefe sai su zama ya'ya nagari masu kai Mahaifansu ga Tudun tsira.
Suna Dawowa Abba yace bayansa ke ciwo bari ya kira Umma ta Shafa masa mam zafi.
Sadiq na jin Haka yace bari shi ya shiga bangaren Innani su gaisa.
Da yaso ma yace su je ya shafa ma Abba ammh jin ya ambaci Hajiya Umma ya sa ya gane wannan karon ba'a bukatarsa Lokacin Umma ne.
Kai Tsaye Shashen Innani ya shiga ba kowa shuru Falon nata.
Sai dai ga Farantin abinci nan da ta gama ci ga gilashinta a wajen.
Innani da ta shiga makewayi ta yi alwala tazo ta yi sallah bayan ta idar ta fara Laluban gilashinta bata gansa sai Sandarta.
Sai ta fara bin bango ta na ta masifa fad'i ta ke yi"Kai Allah ya rabamu da abun nasara masu jajayen kunnuwa ba su da tabbas yanzu yanzu ace gilashi na ido na na nema na rasa? Tabbas watarana zan iya fad'i ma na nakasa kaina in dai da wannan gilashin na Dogara."
Sadiq na falon ya na jinta sai da ya Murmusa.
Da Dafa bango ta fito falon ta na Fadin"Bawa ace ya na tafiya ya na Lalube kai jam'a? Ga dai mutane a gidan ammh duk ba ma su mutumci ba ne sun barni ni kadai a katon wajen wato Dije ci kanki kenan."
Kyafci ta yi cikin takaici Sadiq ya yi yar Dariya har Innani taji Sautinta.
A zatonta cikin su Siyama ne a Fusace tace"Ko wace ja'ira ce uwarki dai ki ka yi ma dariya ba ni ba."
Wajen gilashinta ya isa ya Dauko mata yazo har gabanta ya saka mata Lokaci d'aya ya na fadin"Kakata."
Innani na jin Muryansa ta ware idanuwanta ta cikin gilashin ta na fadin"Muryan wa na ke ji kamar ta magajin gida?
Sadiq ya kara taro Fuskarsa gabanta ya na fadin"Ko har yanzu baki ganin ne?
Da Sauri ta saki Sandar hannunta ta Rikosa ta na sakin kabbara.
Sai kuma ta fashe da kuka yasan Halinta yasa ya jata kan kujera ya zaunar da ita, sannan ya koma ya Dauko mata sandanta yazo ya zauna kusa da ita ya saka mata Sandar a Hannunta, lokaci d'aya ya na fadin"Innani gayamin waye ya tabamin ke a gidan nan yau mu raba gari da shi?
Innani na faman goge hanci da Haban zaninta tace"Kana dai gani a wulakance nake acikin gidan nan ba mai dubani kamar mayya Sulaimanu ne in yazo da Safe kuma sai Dare kasan sa da Sabgogi., salamatu ce kuma yanzu itama ta Lalace suwaiba ta zugata, Siyama da Salima daman marasa kunya ne ba su da wani amfani Sulsana ce ke kula dani itama inaga uwarta ta zugata jiya da yau ko Kafarta ban gani ba."
Sadiq na jinjina kai yace"Gaskiya ko in hakane ba su kyauta miki ba.
To yanzu ya kike so ayi?
Innani na jan Hanci kamar gaske tace"Yauwa Dan albarka daman nasan inda ka na nan hakan bazata Faru ba. Ni dai na gaji da zaman nan kawai ka tafi dani chan ina ne ma in da ka ke karatu?
Sadiq ya yi Tagumi kafin yace"Wai Zariya Innani?
Innani tace"Koma ina ne ka tafi dani su ci kansu in ina da amfani a gidan ai za su sani daga baya."
Sadiq yace"To innani ta ya za'ayi na tafi dake zariya? Dama na yi aure ne sai na tafi dake gidana ki zauna in su ba sa sonki ni ina kaunarki."
Innani na jin haka sai ta yi shuru shi kuma fadin haka yasa sai Hasiya ta fad'o masa a rai
Innani ce ta katseshi da cewa'"Kuma fa hakane? Ko na jira in an yi auranka da Sulsana sai na koma gidan ku da zama?
Kai Tsaye yace"Yauwa hakan ma zai fi."
Innani ta washe baki kafin tace"Haka za'ayi ammh ka yi shuunka kada Sulaimanu yaji sai kaga yaji Haushi kasan mutum sai Allah."
Sadiq yace"Sosai Innani ai ba wanda zai ji sirri ne tsakanin mu "
Nan fa Innani ta gyara zama ta shiga basa labarin duk abubuwan da suka faru da bayanan harda Labarin Alhaji Jibril da zuwansu da maganar da ya zo da shi.
Cikin mamaki yace"Ni kuma? Ina zan kai mata uku Innani?
Sai da yaji Innani tace"Mata uku kuma?
Sannan ya dawo hayyacinsa da Sauri yace"Ina Nufin Sultana ta isheni Innani."
Innani tace"Kwarai ai na yi musu Fata Fata daga uban naka har abokin sa na kuma ce ko bayan raina ban amince ka yi ma Sultana kishiya ba. Kaganni nan ko ni da na ke jan wuya na sha wahala kishiya ballatana Sulsana da ta ke jinta kamar wata gaula kai sai da sukaji nace ko kai ne ka yi mata kishiyan da kanka ba ni baka sannan nace Allah ya tsine ma wand daura aur..!!
"Innani.."
Da sauri Sadiq ya katseta da kiran sunanta ya na kuma kallomta cikin mamaki.
Dariya ta saka kafin tace"Ahto suma haka suka Tsorata da kalamaina ai sai kaji mgana ta mutu na dai ce ga mara kunyar nan Salima in suna so sai ayi had'in zumumcin da d'ansa da ya zo da shi wani Dan Saurayi haka a fuska dai kamar na Allah ba'a son abunda
Showing 42001 words to 45000 words out of 98628 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15 Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33