Tura masa, Sandarewa ya yi a zaune kamar ruwa ya cinyesa.
Duk da Safiya ne sai da naga ya fara zufa sannan rashin gaskiya da Razana ya bayyana Kuru kuru a saman Fuskarsa
Sai na yi mirmishi kafin nace"Abokan karatun ne ko?
Da Sauri yace"Eh Eh, tare muka yi karatu da su a zariya."
Cikin kallonsa nace"Ayya sai kuma naga kamar a gida kuka Dauki wannan Hoton? Hala gidan daya daga cikin su ne?
Da Dauri yace"Eh.! Eh."
Sai ya kasa mgana da Sauri ya karb'i Computer a hannuna a gaba ya latsa Delete ya goge shi.
Cikin mamaki na kallesa kafin nace"Me yasa ka goge min?
Kai Tsaye yace"Ba shi da Muhimmanci ne."
So na ke ya kalleni ammh ya kasa duk ya Daridice alamun rashin gaskiya Muraratun
Kamar zan yi mgana sai kuma na fasa, ina ganinsa ya na ta kara Dube Dube a cikin Computer Tunaninsa ko kila akwai wani abun da in nagani zai Tsarwarsa komai.
Ban nuna masa na Damu ba, ko na nuna na Fahimci ba shi da gaskiya.
Yadda ya kasa samun natsuwa yasa na kara Tabbatar da Zargina.
Tashi na yi na bar masa falon ganin yadda gabadaya ya rikice ya kasa aikin gabansa sannan ya kasa iya kallon Barayin da na ke saboda kunya da nauyi.

Assadiq bai taba kawo ma ransa da cewa Hasiya ta had'u da yan'uwansa a kaduna ba, Shiyasa sai ya yi Tunanin tunda ya goge Hoton ba lalle ta Zurfafa Tunani a kansa ba, ballatana har ta gano wani abun ba.
Ya so ya kama kanshi Sanda yaga Hoton ne tambayar da na yi masa ita ta bashi Tabbacin ban Fahimci komai da ya Danganci Hoton ba.
Abunda bai sani ba na Dinkesa ne a baibai kamar yadda shima ya jima ya na Dinke ni.
Har ya gama Weekend dinsa ya tafi Ranar Lahadi da yammah ban kara nuna masa wani abu ba, abunda ya kara bani mamaki ko kafin Tafiyarsa sai da ya nemeni kuma na bashi Had'in kai sai bayan tafiyarshi na zauna Ina Tunanin haka Assadiq zai ta moran jikina a banza ni ya so ka shemin Rayuwa ya hanani haihuwa.
Shi kuma zai yi auransa da Matar da ya ke so kuma Danginsa ke so ta haifa masa kyakyawan Zuru'an da ya dad'e ya na fata.
Ni kuma ko Oho rayuwata bata da wani amfani ban chanchanci samun wani abun Farinciki a Rayuwa ta ba Tunda Kaddarata ta zo a haka, sannan ina Dauke da Bakin Fentin da zai iya shafar Rayuwata kila har bayan Mutuwata.
Na yi kuka kamar raina zai fita kukan da ya zame min sana'a a kwanakin nan ga shi ba ni da bakin mganar da zan iya taran wani na yi masa mgana, Wannan al'amarin abunda ya shafi Rayuwata ne ban zan so na zame ma yan'uwana Damuwa a koda yaushe ba.

Na yi Tunanin Ramatu sai kuma na Fasa Tuna itama na yi mata karyan, naje garin su Assadiq naga Ahalinsa ni ma kuma sun gani, yanzu ban isa naje musu da wata mgana ba.
Amma ce na yi Tunanin kira sai da kuma na Kirata na kasa gayamata abunda ke damuna.
Sai kawai na Bige da ce mata"Amma in bawa ya shiga matsanancin Damuwa  sannan ya rasa mafita wani irin mataki ya kamata ya Dauka?
Sai Amma tace"Matakin da zai Dauka shine na Dogara ga Allah, ya maida Lamarinsa ga Ubangijin Sammai da Kassai, ya kaskantar da kansa a gabansa ya Rokesa mafita Allah shi Kowa ne in nace kowa ina Nufin kowa da komai shi ke samar da mafita da warwara al'amuran mu cikin gaggawa in ya so hakan Hasiya, ko kuma ya jinkirta al'amarin har zuwa Lokacin da zai Ribanya maka kyakyawan Tanadin da ya yi ma bawa."
Da kalaman Amma na yi amfani na maida lamarina a wajen Ubangiji, na Dage da Ibada ba rana ba Dare na yi kuka na roki Allah in har aurena da Assadiq akwai alheri aciki Allah ya Daidaita al'amarin da kansa, in kuma babu Alheri Allah ya sa ya sahalemin cikin kwanciyar Hankali ba sai Rayuka sun baci ba.
A haka muka zo muka koma makaranta, sai hakan ya rage min Damuwa na dage da karatuna gefe daya kuma muna tare da Safiya Ahmad.

Assadiq bai zo ba sai bayan Sati uku, a kuma zuwan ne ya biya min kudin makaranta sannan ya bani kudin Handout da sauran Bukatu da zai tafi ya Turamin 50k yace na ijiye a acct dina, bayan 10k din da ya bani a Hannu yace min na zirga zirga ne.
Duk da ina addu'a ammh muna taba juna a waya ni da Saliha so na ke kada Lokacin Bikin ya bace min a lokacin ne na ke so na kara tabbatar da abunda na ke Zargi a kan Assadiq.
Abu kamar wasa sai ga shi mun kulla Zumunci da Saliha ita ke fad'amin ma yar'uwanta Sajida ta haihu a Gusai ammh bazata samu zuwa ba, sai biki Saboda ya yi nisa da ya ke mun yi Saving din Lambar juna muna ganin Statue din junan mu.

Anan naga ta Dora Hotunan Taron suna na yan'uwanta da aka yi a Gusai.
Wani Hoto da yaja Hankalina Shine wanda Maijegon tare da wata ta rike Jajarin a Hannunta Fuskarta da yanayin mirmishinta kamar Assadiq.
Sai da na yi Tagging na Tambayeta"wannan ma yar'uwarki ce Saliha?
Sai tace"Yes Big sis kenan itace Babba a gidanmu Sunanta Surayya itama anan Gusau ta ke aure"
Wannan Hoton har Daukansa na yi na rika Zooming ina ganin abun mamaki.
Ina da Hotunan a Assadiq a wayata wasu tare mukan Dauka wasu kuma shi ya Turamin na rika Dubasu ina mamakin ga kammani nan Zahiran da suka kara bani Tabbacin abunda na ke Zargi.

Sannan kuma in ban manta ba a lokutan baya ya sha fad'amin sun tafi aiki da Megidansa Gusai kenan Gusai ne anihin mahaifarsa.
Saboda kara samun Tabbaci yasa na Tambayan Saliha da cewa su yan wani gari ne?
Ma'ana assalin su, kai Tsaye ta ce min su Asalin Mahaifinsu mutumin Shinkafi ne.
Kawai a raina sai nace shikenan Hujjoji masu karfi sun kara tabbatarmin da wad'anan matan da ma had'u da su a kaduna sune Ahalin Assadiq da ban sani ba.
Sai na Kudira a raina mamakin da zan ma Assadiq bai taba zaton zan iya basa wannan mamakin ba.
Na kudiri wani niyya acikin Raina Niyar daga ni sai Ubangijina suka sani.
Zan shayar da Assadiq mamakin da ya shayar da ni, kila ma nawa mamakin yafi gigitasa fiye da nawa.

*******

Kwanci tashi ba wuya a wajen Allah, ga shi har sha'anin bikin Assadiq da Sultana ya kawo saura Sati uku, dukkan Shiryen shiryen sun gama kamallah a nan garin Gusai.

Tuni har an yima sultana Jerenta da kayan alfarman da Abba ya siya mata, a kuma jera mata su a cikin kayattacen gidan da Abba ya mallaka ma Assadiq Hakal makal.
Sannan Surayya ta gama had'a akwatina Guda takwas shake da kayan alfarma, sai wanda ya gani kaya na gani na fad'a na ya'yan gata.
Ta bangaram matan sun fi shirye shiryen Bangaren Ango Sadiq kuma sai in ma Tahir ya kirasa ne ya ke Tunawa da zencen auran.
Shi dai ya na gefe sai abunda aka kirasa akace masa ya ke amsawa.
Shi dai bai zira jikinsa ba, sannan bai yi baya ba.
Tunda auran gata Abba zai yi masa, sai ya kudira a ransa zai ba ma Sultana kudin gyaran jiki da kwalliya sannan shi yanzu Fafutukarsa na Kudin da zai bama Siya ta siya kaya ne bisa adalci Tunda ita bai yi mata Lefe ba.
Kudin da ya ke Turamata ta acct dinta sun kai yanzu Kimanin dubu Dari biyu da wani abu ya na so su kai uku ne yace ta Dauka ta siya abubuwan da ta ke so.

Sannan ko mganar kayan angwanci Big sis tace Abba ya ba da kudi an had'a masa akwati guda, sannan Tahir ya yi masa wasu, ko katin Biki na waya da na Hannu Tahir ne zai yi komai
Yana Abuja Tahir ya kirasa kan mganar inda za'a Daura aure saboda Buga kati, shi kuma ba shi da Say akan haka duk da suna mgana da Abba da Umma sosai Sisters dinsa ma suna yawan Kiransa, ita kanta Sultana ya na Kiranta ammh kuma sai ya tuna da Siya sai goma ya Kirata kafin ya Tuna da Sultana ya kirata.
Ce ma Tahir ya yi ya bari in ya yi mgana da Abba zai kirasa ya fad'a masa.
Sai dai ya yi ta kiran Abba bai Sameshi ba  har zuwa Dare sai ya Kira Umma ya yi mata zencen.
Ita kuma ta warware masa Halin da ake ciki saboda kara Abba yace a shinkafi gidan Mallam Shitu Mahaifin Sultana za'a Daura aure.
Ammh Innani ta Daka Tsalle tace Uban kuturu ya yi kad'an in kuma Sulaimanu ya Dage to ita dai ba da yawunta ba, ga shi Abba ya kira ya Furta Kowa ya sani ya rasa yadda zai yi da Innani.

Sadiq na jin haka ransa ya baci da innani a satin Zariya ya so tafiya saboda ya cikama Siya kudin nan, ammh sai ya sauya Tsari washegari jumma'a Gusai ya tafi, yasan wacece Innani kan wannan mgamar sai ta yi Sanadiyar da Rayukan wasu bayin Allah za su baci.
Ya kuma je ya isketa a na daru da ita ammh tace ba'a isa ba sai faman Zagin Mallam Shitu ta ke yi ta na kawo wasu labarai marasa Tushe ballatana makama, baiwar Allah Sultana sai kuka ta ke yi abun da zafi a rika zagin mahaifinka a kunnen ka.

Su Umma sun gaji da mgana Daga karshe Innani ta had'a da su ta Zage daman kwanaki sai da ta yi kan kayan Dakin Sultana, wai shima sai an yi masa mgana ya kawo wani abu Tunda Ubanta ne shi, kuma an yi masa kokari an riketa na Shekaru sha ba tare da sisinsa ba.
Kuma sanda Mallam Shitu ya zo a gabansa Innani ta rika mganganun har ta na yi masa gori, abun ba dadin ji, kuma Tsakani ga Allah ya kawo kudad'e ya bama Abba sai yaki karb'a yace ko Hauwa na da rai Sultana yarsa ce har gaban Abada, ammh Innani ta rika bala'i ta na masifa.
An samu wanchan mganar ta wuce ga wannan kuma ta tsiro da shi.
Sadiq Abba ya fara samu ya yi ma mganar bude bakin Abba sai yace"Magajij gida Innani uwa ce a wajena kuma akwai Rikicin Tsufa a tare da ita, gwara ku tayani lallabata mu Rabu lafiya."
Sadiq na jin haka yasan Abba ya tsaya a matsayar Innani Tunda har ya na mganar zai samu Baba Sammani ya gayamasa yasan yadda zai yagama Mallam Shitu Saboda yana jin kunyarsa.

Sadiq na jin haka yasan sai ya samu Innani ya fito mata ta bayan gida.
Sai da ya bari dare ya yi ba kowa a shashen nata sai ita kad'ai yadda zai ji dadin yi mata abunda ya shirya.
Kamar ko ya sani batare da ya tambayetaa ba ta fara rattaba masa Labarin abunda ya faru har ta na fad'in"Yo ni za'a kawo ma iskanci? Yarinya tun ta na jarriyarta Sulaimanu ya yi wahala da ita sai yau Rana Tsaka a wani ce gidansa za'a je daura aure in ya isa shegiya na ke, ai na ce in dai chan za'a je ni Dije ba da yawuna ba."
Kallonta kawai ya ke yi cikin tattaro mganar bakinsa, Cikin kaushim murya yace"Daman gidan Ubanta nan ne a hakku a daura mata aure."

Innani ta yi galala ta na kallonsa kafin tace"me ka ke nufi Magajin gida?
Kai Tsaye yace"Abunda na ke nufi a shinkafi za'a daura auran nan a kuma gidan mahaifin Sultana."
Innani ta ballamai Harara kafin tace"Au to daman turo ka suka yi ko?
To wlh wannan karon ba wanda ya isa nan gidan Sulaimanu nan za'a Daura wannan auran naga Uban da ya isa ya ce Ba haka ba."
Sadiq yace"Ba isa ba ne Innani, Sai dai ki sani matukar kika dage sai anan za'a Daura auran nan ni kuma wlh Tallahi kin ji na rantse miki da Allah zan fasa auran Sultana kuma da gaske na ke yi."
Sai Innani ta yi shuru ta kasa mgana, shi kuma ya kura mata ido ya na kallonta ganin ta yi shuru yasa ya cigaba da fadin"Ke shikenan bakya yafiya? Ki rika afuwa Innani Domin ke kam baki san Tarin laifukan ki wajen Allah ba, da Allah baya yafiya ma da Tuni An dade da shafemu a wannan Duniyar, ya kamata ki Sassuta ma kanki wannan kiyayyar in ba haka ba zaki Mutu ana murna da Mutuwarki."
Sai kawai Innani ta Fashe da kuka ta na Fadin"Ai shikenan na bar mganar ka gayama Sulaimanu na hakura aje a daura auran a shinkafi wlh na bar mganar har Abada."

Jinjina kai Sadiq ya yi kafin ya ce"Dakyau naji dadin haka , Ni ina so in kin mutu Ranar Lahira ki Rabauta kakata, na baki wani kissar da zai taimaka miki wajen cire jin haushin wani a ranki?
Bai bata Damar mgana ba ya Cigaba da fadin"A zamanin Annabi muhammad Sallahu alaihi wasallama, watarana ya na zaune acikin masallaci Tare da Sahabbai kawai sai Annabi yace ga dan Aljannah nan zai shigo, Sai Sahabbai suka yi shuru tare da kurama kofar masallaci ido su ga waye zai shigo.
Sai ga wani bawan Allah ya shigo cikin masallaci kuma bayan Shi ba wanda ya kara shigowa, sai abun ya ba ma Sahabbai mamaki da jin abunda Annabi yace, na cewa shi d'in d'an Aljanmah ne, sai cikin Sahabban Annabi wani ya bishi gida yace ya ba shi masauki na kwanaki sai ya bashi da niyar ya rika ganin wani irin Ibada ya ke yi da Tun a Duniya Annabi yace shi dan Aljanna ce, sai yaga duk tsawon kwanakin da suka yi tare ko sallar Dare ba ya gani yana yi ban da kamsil salatu a ranar na uku ne wannan Sahabin ya sameshi ya gayamasa abunda Annabi ya gayama su game da shi, Dalilin da yasa ya zo wajensa saboda yaga wani irin Ibada ya ke da har tun a duniya Allah ya bashi Aljannah.
Sai wannan bawan Allah ya yi Kabbara sau uku kafin yace" bai san har yakai haka ba, abu d'aya kawai ya sani Tunda ya ke bai taba kwana da wani a ransa ba duk abunda aka yi masa nan ta ke yake yafewa kwana yake zuciyarsa wasai ba kowa acikinta"
Dan dakatawa Sadiq ya yi ya na kallon Innani da ta natsu ta na ji harda jan Doguwar kabbara."Allahu Akbar" lokaci daya ta na faman sharan kwallah.

Sai Assadiq ya sauke ajiyar rai kafin yace"To kisance mai yawan yafiya Innani domin masu yawan afuwa Samakonsu na wajen Allah"
Da Sauri Innani tace"Allahu Akbar Wlh na yafe ma kowa Allah Sarki. na yafe ma kowa ni yanzu shima Shitun na yafe masa duniya da Lahira Magajin gida ni yanzu zuciyata wasai."
Sadiq yace"To ina fatan bazaki kara tada wata mgana ba.?
Da Sauri tace"In sha Allahu Magajin gida kai dai Allah ya yi maka albarka kawai."
Ya amsa da Ameen, Shikenan magana ta Mutu, sai dai su Abba sukaji sabon zencen Innani da kanta tace ko Bikin ma in chan za'a yi sai su kwasa su je gabadaya chan Abba yace nan dai za'ayi Sha'anin Daurin auran ne dai za'ayi achan.

Duk da bai fito ya fad'a ba kowa yasan aikin Magajij gida shine kawai Maganganunsa ke sa ka Innani Ladabi da Nadaman Dole, kafin kwana Biyu ta koma gidan jiya.
Ranar lahadi ya koma Abuja Da Safe ya tafi da cewa sai a satin biki zai dawo, sai da ya koma sannan ya Kira Tahir ya gayamasa ga inda za'a Daura auran Shima Tahir yace hakan ya yi daidai bisa adalci.
Duk Abba yaki karban komai sai da Mallam shitu ya aiko masa da Buhuhunan shinkafa da gero da masara yace ya karb'a ba Saboda sultana ya ba shi ba domin Allah ya ba shi sannan ya karb'a bayan Sadiq ya saka baki.

Ya so kwarai kudin da zai bama Siya su kai 300k ammh abu ya ci tura Tunda Big sis ta ishesa da kiran ya turo da kudin gyaran jikin Amarya da kudin kwalliya daman bata san yana da Niyar bada wa ba.
Dubu 100k ya Turama Surayya, ita kuma ta cire 30k ta turama Surayya Dee marubuciya mai Saida saiwowin Gudiyo, da ya ke ita Surayyan ta santa tana tsiyan Littafanta har suka Saba sosai ta yi mata ragi sosai ta had'a mata ma su kyau da inganci duk da daman kayanta suna da kyau sosai.
Daga Kano aka saka a mota sai Gusai Surayya ta karba sakon cikin murna nan da nan tabi Tsarin mgangunan suka Fara dura ma Sultana a cewar su sai sun gigita Kanin nasu yaji ya Ciji yatsan tsaikon da ya tsaya Tuntuni bai yi aure ba.
+234 803 277 3332
Sun yi anko, wannan karon Less da Atamfa, da suka damesa da kiran ya Turo kudin ankon Sultana yace ba shi da kudi su a matsayinsu na yayyenta mata su siya mata mana.
Shi kuma Duk Tattalinsa na Siya ne itama ya na so ta siya kaya masu yawa na alfarma a kallah ko da ba su kai na Sultana ba itama dai ta shaida Tunda bai yi mata lefe ba.
A tsarin da ya tsara daman aa satin da Bikinsa ya rage sati daya da Sultana zai je zariya, satin Biki kuma ya je Gusai daman kuma ya Rubuta takardan hutun Sati daya na auransa in ya yi sati Biyu a gusau sai ya koma Abuja ya yi daya sannan yaje Zariya yaga Siya duk da yasan zai mata laifi ammh ba shi da mafita ne.

*******

Shi baisan duk na san bikinsa da Sultana ya matso ba tunda muna mgana da Saliha tace min ta na nan tafe cikin Sati mai shiga in sha Allahu.
Sanda yazo ya na fad'amin zai jima a Gusai  kafin yazo ban nuna masa na Damu ba.
Sai dai na yi matukar mamakin da yace min kudin da ke acct dina 256k na Dauka na siya kayan sawa ya so ya yi min lefe na alfarma ammh kuma bashi da kudi ammh ko yanzu bai cire rai ba a gaba in ya samu zai siyamin duk abunda na ke so.

Sai na fara hawaye shi ko ya Dauka na Kukan Farimciki ne nan kuwa a cikin zuciyata na wani irin kishi ne da Tunanin kudin fad'ar kishiya ya kawomin.
Ina ganin Hoton Sultana a kwanakin nan Tunda Saliha na yawan sakata
Showing 93001 words to 96000 words out of 98628 words