Ina Tunanin jinana ya kusa karewa, ni ba Ciki gareni ballatana nace ko bari zan yi tuni har karfina ya kare ma fara ganin jiri jiri dakyar na iya wanke kayan da na bata na fita na shanya, daga baya da naga zanin ya daina Tarenin jinin duk inda na zauna sai na bata ina tafe ina yoyo da sauri na Daga waya na Kira Adda Fati a Lokacin ban yi Tunanin kiran Assadiq ba Sanin da na yi baya kusa kafin ya kawomin agaji na mutu.
Cikin tashin hankali nace mata tazo gida yanzu, jin yanayina yasa tasan ba lafiya, ko da ta zo ta iskeni zaune ina kuka ga jini na ta bin kafafuna.
Cikin tashin hankali ta rikeni ta na Fadin"Innalillahi Hasiya? Me ya sake ki? Ko bari kikayi?
Cikin kuka nace"Bansani ba, daga al'ada ne jini ya tsinke min adda Tainakemi ki kaini asibiti kafin na mutu jini na ya kare."
Adda Fati ta rakani Bayi na gyara jikina ta ninka wani Dankwali na yi Kunzugu da shi sannan na sauya kayan Jikina, ita ta Rufe dakin muka ta fi asibiti abun da ya kara ba ma Adda Fati tsoro tun muna adaidaita jini ya fara bin kafata kuma duk ya bata kayan jikina da Hijabina
Asibitin musulmi ta kaini mun jima kafin mu ga likita don ma wai jama'a sun Tausaya ganin ina ta zubar da jini ga shi nan inda na zauna har ya na gangara.
Ni dai nasan Adda Fati ta rikeni zuwa ofishin Likita, daganan bazan iya tuna komai ba, sai da na farka da misalin hudu na yammaci na gani kan gadon asibiti a wani daki ni kad'ai sai Adda Fati a Tsaye a kaina sai kuma Ramatu na zaune gefena ta na rike da Hannuna.
Cikin Nauyin jiki da na ido na farka ina bin su da kallo suma kallona su ke yi ganin na Bude ido yasa Ramatu tace da Sauri"Adda Ina ga ta farka."
Jin haka yasa ta kariso gabana ta na fadin"Hasiya."
Amsawa na yi cikin dakushewar murya ina kokarin tashi ta kamani na tashi lokaci d'aya ta na fadin"Ki bi a sannu kada ki fama Hannun ki."
Sai na bi hannun da kallo cikin mamakin ganin bandage a hannuna, sannan kuma na duba kafata ban ga jini na bi na ba, ammh daga kasa naji kamar an sayamin Audugan mata.
Cikin neman karin bayani na kallesu kafin na yi mgana Adda Fati ta Bude kofa ta Fice ta na fadin"Bari na Fad'a ma Likita ta farka."
Ramatu na rika tambayan me ya sameni? Ko jinina ne ya kare? Sannan miye ya sameni a hannu.?
Ramatu bata amsamin Tambayata ko Daya ba sai ma wani kallo da naga ta na yi min kafin kawai tace"Uhm Hasiya kenan."
Daga haka ta tsuke bakinta sai abun ya bani mamaki, Adda Fati ta dawo tare da likita ya duba ni sannan ya yi min Tambayoyin ya na ke ji nace ba komai ina jin jiri nace a'a? Ina jin zubar jinin yanzu? Nace ba na ji.
Sai ya kalli Adda Kafin yace"Kada ku damu zubar jinin ya tsaya, daman kuma shi Inplant da zarar an ciresa ya na tafiya tare da matsalansa ne, Saboda ta samu karfin jikinta sai ku kwana anan da Safe sai ku tafi gida."
Bayan fitan liktan ina so na yi tambaya ammh Daga Adda Fati har Ramatu ba su bani Fuska ba.
Haka suka yi Fuska kamar ba su sanni ba, kudi kawai Adda Fati tace ko akwai a Hannuna nace suna banki.
Sai na gayamata in da na ke ijiye Atm dina Ramatu tace zataje gida ta dauko sannan tazo min da wasu kayan.
Sai lokacin na lura da na jikina ba nawa ba me na Ramatu ne wad'anchan kenan sun lalace komawa na yi na kwanta ina Tunanin abunda ya sameni da bansani ba.
Adda sam taki sakarmin Fuska, Ramatu ta je gidana sai ta wanke kayan da na bata sannan ta Dauko min zani da riga, sai pant guda Biyu sai ta dabo Ruwan zafi a fulas ita ta gayama Maman Suhailat ina asibiti ba ni da lafiya ammh gobe zan dawo gida.
A hanya ta tsaya ta cire kudi ta siyo kayan marmari da Buredi, sanda ta dawo ina barci sai daga baya na Farka Adda Fati ta rakani bayi na yi fitsari sai naga jinin ya tsaya sai dai dis dis ya ke diga a saman Audugan.
Tea Ramatu ta hadamin na sha Daman yunwa nake ji, sai kuma Kayan marmarin da na sha, yadda suka min gim nima sai ban kara mgana ba ina so nace ina wayata ammh na kasa tambayar su.
Adda Fati ce ta kwana dani Ramatu ta koma gida Tundaga Noor.
Da Safe ma sai dai ta same mu a gida Tunda da wuri aka sallame mu.
Sai ga shi da kafata na shiga Daki na tare da Adda Fati, Maman Suhailt da Ummi sun shigo sun gaisheni.
Adda Fati ta had'amin Ruwan wanka na shiga na yi sai dai tace na kula kada na Fama Hannuna.
Bayan na fito na sauya kayan jikina , na saka pant da pad duk jinin kad'an Ya ke zuba ita kuma har ta had'amin Tea ta soyamin kwai.
Kadan naci kwan Tunda bakina baya min dadi, sai ta bani mganguna guda biyu na sha wanda inaga aka Rubuta daga asibiti ne.
Adda Fati ta share dakin ta goge ni kuma ina zaune saman kujera ina Tunanin karo na Biyu kenan a sakamin Bangade a hannuna kuma duka ba acikin yanayin Hankalina ba to me ke faruwa ne?
Wajejen sha Biyu sai ga Ramatu, ta zo suka had'u da Adda fati suka zauna waje daya suna ta magana kasa kasa bana jin me suke fad'a.
Wayata ce a hannuna ina duba kiran da na rasa Assadiq sau biyu ya kira jiya da Daddare, sai bai kara kirana ba Kila ya na Tunanin na yi barci ne.
Gabadaya sai na Tsargu, na fahimci kamar da ni suke.
Sai na tashi Zaune dakyau ina kallonsu cikin mamaki kafin nace"Adda, ramatu wai don Allah me ya ke faruwa ne ? Tun a asibiti na ke tambayar ku shuru baku ce min komai ba ?
Adda Fati ta Kalleni kafin ta harareni tace"Gani mu ka yi tambayar taki ba ta da amsa, Tunda kinsan abunda kika aikata."
Cikin mamaki nace"Bangane ba? me na aikata?
Ramatu ta ce ka tsaye"Ki na so ki gayamana baki san abunda kika saka a jikin ba ne da ya sakar miki jini ba?
Cikin wani karin mamaki nace"Wani abu kenan? Don Allah ku fad'amin bansani ba."
Adda Fati cikin bacin rai tace"Hasiya da wayau ki da komai me ya kai ki? Baki taba Haihuwa ba me ya ja miki saka Tsarin iyali? Abun takaicin ma in za ki saka Tunda baki son Haihuwar yanzu sai ki saka na shekara d'aya ko Biyu ammh Saboda Rashin Lissafi har na Shekara biyar kikaje aka saka miki to Allah ne ya cece ki, sai da aka yi miki karamin Tiyata a hannun nan naki aka Cire abunda kika kai kan ki aka saka miki"
Har alokacin Cikin Duhu nake cikin Sigar tambaya nace"naje aka sakamin mene? Kuma a yaushe?
Adda Fati tace"Bana son Renin wayau Hasiya, inplant din da kika saka na Tsarin iyali na shekaru Biyar."
Na bud'e baki ya fi sau biyar ina Rufewa Lokaci d'aya ina kallon Adda Fati cikin mamakin kalamanta.
Cikin fitar hayyaci da Sigar tambaya na maimaita"Inplanta kuma? Menene shi?
Ban gama Rufe baki ba Ramatu ta ballamin harara kafin tace"kin fi mu sanin koma menene shi tunda kika iya aminta kika kuma saka shi a jikin ki Hasiya, kin bani mamaki ban zaci haka daga gareki ba."
A zahirance ne na ke kallon Ramatu, ammh a badini ba ita na ke kallo ba na lula wani Tunani na dabam
Ina jin acikin fad'an Adda Fati sai na gano ma'anar abunda aka gani ajikina.
Inplanta wani abu ne na tsarin iyali, to yaushe na saka bansani ba?
Kwakwalwata ta shiga Tunanin a watarana, sannan da wani Lokacin har haka ta faru bansani ba?
Kamar an nuno min ranar sai na fara ganin sanda mukaje asibiti da Assadiq da duka abubuwan da suka faru da Farkawan da na yi na samu kaina a irin yanayin da na samu a yau.
Kwakwata ta fara had'amin abubuwa a cikin kaina sanda na fara a wanchan ranar naga hannuna da Bandage ce min aka yi wai na fadi na cake da allura yau kuma ana gayamin a wajen na saka abun Tsarin iyali.?
To waye ya sakamin?
Wata zuciyar tace"ASSADIQ mana.."
Sunansa kawai da na Tuna sai da naji jikina ya fara rawa. tabbas Biri ya yi kama da Mutun na Tuna duk abunda suka Tattauna da likita a ranar ba'a gabana ba ne.
Ce min kawai ya yi za'a Dibi jinina kuma da hayyacina aka Dibi jinina in lissafina ya yi daidai tabbas lokacin da Nures din tamin allura ta barci ce kuma a lokacin da na samu barcin ne da Umarnin Assadiq a sakamin abun Tsarin iyali a jikina batare da na sani ba.
Tabbas haka ne abun ya faru wannan shine hakikanin gaskiyan mgana.
Kaina na Dafe kafin na saki salati a fili cikin fitan hayyaci nace"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un.
Adda Fati ta tabe baki kafin tace"Ke kika sani Hasiya ammh wannan abunda kika aikata abun kunya ne na gode ma Allah da mijin ki bai sani ba da bansan da wani ido zaki kallesa ba"
Ramatu ta karbe da fadin"To mene ma dalilinta na rashin son Haihuwa tunda ita ba haihuwar ta taba yi ba?
Kamar Ramatu ni ta ke tambaya acikin zuciyata nace"Saboda Assadiq baya sona. Sannan baya son ya had'a Zuru'a da ni."
Sai na fara Tunanin abubuwa da Dama, na game da Assadiq rashin wayarsa a gaba na, da sauran alamomin rashin gaskiyarsa in na auna da Hoton da na gani sai na samu wata gaskiya
Assadiq baya sona ya aure ni ne saboda Biyan Bukatarsa, kuma karya ya ke yi ya na da Ahali kilama har da iyaye.
In hasaahena ya tabbata ba bu wani ta bangaran Ahalin Assadiq da yasan dani a matsayin matarsa.
Rayuwarsa guda Biyu ce ta boyayyiya da ta Zahiri.
Ta Boyen itace tawaa, Ta zahiri kuma itace na hoton da na gani.
Sai kuma na Tuna Saliha ta gayamin kaninsu zai aure yi mai suna Sadiq.
Wani Sadiq din ta ke nufi? Assadiq ko kuma wani Dabam?
Bani da mafita illah na dora zargin komai a kaina.
Saboda kada su Adda su fahimci Rayuwata ta kara gangara cikin Tsaka mai wuya.
Sai kawai na fashe da kuka ina fadin"Ku yi hakuri, ni tsoro na daman kada na zo na Haihu ya'ya na su Fuskanci Rayuwar Tozarci da wukakanci da ni na Fuskata wlh shi na ke tsoro."
Sai kuma kalamaina ya saka jikinsu ya yi sanyi barin ma yarda na ke kuka. Sai suka sauko da ga jin Haushina suka zauna suna ta bani baki da nasiha har na yi shuru na nuna musu komai ya wuce.
Sai yammah suka tafi bayan Ramatu tamin girki daman na kosa su tafi, Suna tafiya na tashi naje na Dauko Computer na kara Bude wannan Hoton ina Kallo.
Ban yi wata wata ba na Dauki wayata na Kira lambar Saliha sai a lokacin na fahimci dalilin da yasa Allah ya had'amu saboda nasan gaskiyan da ya kamata na sani kan Assadiq.
Bayan ta dauka mun gaisa na ke tambayanta ta koma Ibadan?
Sai tace ta koma jiya, kai Tsaye nace sai biki kenan? Tace sai bikin in sha Allahu.
Ina daidaita yanayina nace"Ya sunan Angon ma?
Cikin Fara'a tace"Abubukar muna kiransa Sadiq ko magajin gida."
Sai na jinjina kai kafin nace"Kila na zo bikin in sha Allahu in dai kika gayyaceni."
Cikin murna tace"Me zai hana? In sha Allahi zan sanar da ke in Lokaci ya yi, Gusai ba nisa daga zariya."
Sai na yi mata yake kafin nace"In sha Allahu."
Daga haka muka yi sallama ina Dauke hawayen idanuwana.
Na tuna da kayan da na gani tare da su irin kayana ne kuma Assadiq ne yazo min da shi ammh sai yace a Abuja ya siya.
In na kara hasaso wani tabbacin Kanwar Assadiq ce ta auri Mubarak yaron Baba Jibril kuma matan da na gani a kaduna tabbas na had'u da Ahalin Asssadiq ban sani ba.
Kuma wannan Tsohuwar itace kakarsa wacce ya yi min karya da sunanta.
In ko hakane ya yi kuskuren yi min karya, tabbas zan gano sauran gaskiyan abunda ya Boyemim
Wannan alkawarina ne.
*Janafty*
*TMWBK2020*
*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*
https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk
Ku zo ku yi sayayya tare da Yar Gidan Imam cikin aminci da kwanciyar hankali komai akwai harda kayan gyaran jiki hamshakan mata na supliments kala kala wanda ba su da illa, akwai kuma gagarumin haɗin mu na Arabian sabaya powder wanda babu kamarsa wannan ba irin sabayar da ki ka saba gani bace, kayan kicin dogayen riguna kuwa ba'a magana ke dai ki yi sauri ki shigo domin kwasar roman wadannan kayan.
Nayi kokarin yaki da abunda ke cikin zucuyata game da Assadiq, saboda ba na so ya fahimci na fara sanin wani abu game dashi wanda ya boyemin bai so na sani ba.
Ya yi ta kirana a waya ban dauka ba adaran sai da safe na dauka muka yi mgana, ko a muryanta bai Fahimci wani abu ba, ballatana a saman Fuskata duk da baya ganina.
Kafin ma ya yi korafin rashin Samu naa a waya na yi masa karyan da cewa wayar ce ban ganta ba tun shekaranjiya ashe ta fad'a kasan gado sai da Habiba ta zo ta kama min muka Daga katifan sannan muka gani.
Sai ya sauke ajiyar zuciya na samun salama Tunda ya tabbatar ina lafiya kuma wani abu mara dadi bai sameni ba.
Tunda lokacin muka cigaba da wayarmu lafiya lau ni da shi kamar baya, bai dawo a satin ba sai na sama ya dawo min Weekend, na yi kokarin kada ko a saman Fuskata ya Fahimci na san ya sakamin Inplant duk hanyar da zai gane wani abu ban bari ya gane din ba.
So na ke na ba shi mamaki kwatakwacin irin mamakin da shima ya bani, Ban damu saboda bai Fad'ama Ahalinsa game dani ba, ammh ni meyasa ya yi min karya ni da Yan'uwana game da shi?
Kuma meyasa ya ke zaune dani Domin Biyan bukatunsa na Rayuwa ba domin ya na sona ba.
In na tuna haka sai naji na Raunana har na fara kuka ban sani ba, ina Tunanin Rayuwata ta fita cikin Tsaka mai wuya ashe ashe bansani ba Zata kara shiga cikin wani Tsaka mai wuyar ne wanda ban taba shiga irinsa a baya ba.
Duk abunda na saba na tarbarsa sai da na yi masa, kitso ne ban yi ba sai dai na gyara kaina na yi kunshi, a makotan mu akwai mai kunshi Shiyasa bani da matsala, sannan na yi masa girken girken tarba kuma naci kwalliyata kamar yadda na saba.
Sai dai duk yadda na so na saki Jiki da shi na kasa kamar baya, da nake jin Matukar kosawa kasancewa da shi a lokacin naji komai ya fita kaina.
Shi kanshi ya Fahimci wannan karon ban yi zumudin zuwan shi ba sannan ban yi masa rawan jikin da na saba yi masa a shimfid'a ba, ban kuma nuna na yi kewar kasancewa da shi ba kamar yadda ya rika gayamin lokacin daga ni har shi muka samu natsuwa.
Da ya neme ni ban hanashi kaina ba, Saboda in na hanashi zai zargi wani abu Tunda ban taba yi masa gaddama ba ni mai tallafinshi ne in dai ya zo da Bukatarsa.
Shiyasa na ba shi had'in kai ammh ba Dari bisa dari ba, abunda bai sani ba yana kasancewa da ni ina Sharan hawaye tunda nasan daman ya ijiyeni ne saboda na zama abar Deb'e masa kewa sannan ina Tunanin wata kila nan da Lokaci kad'an zama na da Assadiq zai zama shud'adden Tarihi kamar yadda na Abubakar da Salisu ya kasance a Rayuwata.
Sai da muka Tsarkake jikin mu sannan muka sake komawa muka kwanta duk yadda na so na makale masa a jiki kamar yadda saba a baya na kasa sai na koma gefen gado na lafe ina maida Numfashi.
Sai jinsa na yi ta bayana ya kwantar da kansa a saman wuyana ya na leken Fuskata sai na yi Saurin Runtse ido alamun na fara barci.
Yar dariya ya yi ya na Jan Hancina kafin yace"Siya fushi ki ke dani Saboda ban zo miki wanchan satin ba ko?
Ban ce masa komai ba ya cigaba da Fadin"Ki yi min afuwa Siya ta, kinsan yanayin aikin namu, sannan ga nisa in nace duk sati na rika dawowa akwai gajiya acikin Lamarin, ammh ina nan ina kokarina Dauke ki zan yi na maida ke kusa da ni in sha Allahu."
Ina jinsa a raina nace ji karya ba Sai dai kila Sultana ka ke nufi.
A fili ko dan motsawa na yi kafin nace"Ni ba fushi na ke yi ba, Barci kawai na ke so."
Jin haka yasa ya juyo dani muna Fuskantar juna kafin yace"Kin tabbata.?
Sai na gyad'a masa kai cikin sanyin murya nace"Na tabbata."
Saboda ina so ya kyaleni, ban san kuma wata Doguwar mgana sai ji na yi ya rumgumoni a jikinsa ya na fadin"Nan ne wajen barcin ki kin sani ko?
Sai na gyad'a masa kai, kaina ya kwantar saman Kirjinsa lokaci d'aya yana shafa sumar kaina zuwa bayana.
Runtse idanuwana nayi kamar mai barci ammh ba barci na ke yi ba.
Kamar yadda shima ba barcin ya ke yi ba ya lula cikin Tunanin mafita.
Da gaske ya ke yi ya fara Tunanin neman Muhallin zama a Abuja.
Kuma in dai ya samu to da Siya zai tafi domin ya na Azbatuwa saboda rashinta.
Sultana kuma ta zauna a Gusai ya rika zuwa ya na ganinta.
Barci ne ya kwasheni ban sani ba, shi kuma sai da Dare ya Tsala ya samu barci.
Da Safe sai da na bari mun tashi mun karya, mun yi wanka ni kuma na gama Share share da goge goge, ya na zaune saman kujera ya na aiki a laptop dinsa na dauko nawa na zo kusa da shi na zauna.
Bai damu ba ya Dauka wani abu zan nuna masa na bangaran karatuna.
Hankalinsa na kan abunda ya ke yi yace"Kun kusa komama makaranta ko?
Kai Tsaye yace"Eh Monday ta sama."
Na fad'a ina Nuno masa Hoton nan sai da na kallesa sannan nace"Assadiq su waye wad'anan da nagan ku kun yi hoto tare?
Da Sauri ya Dago ya na kallon Abunda na ke
Showing 90001 words to 93000 words out of 98628 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31 Chapter 32Chapter 33