shigaba daga kofar dakin na mika mata kular hannuna nace zan fara shiga wajen su Adda Fati sai ba ta musa ba ta karba ta bude kofa ta shige ciki ni kuma sai na shiga Bedroom din da ke kallonsa.

Ammh fuskata cike da karin mamaki ni ba na kayan da ke jikina naga wasu yara Biyu mata sun fito daga Bedroom din Amarya da irin material din da na saka Jiya sakin baki kawai na yi ina kallonsu, sai ace wannan shima kawai had'uwa ce? Irin Atamfar d'aya fa harda Material din ba bu wani bambamci.
Sai wata zuciyar tace Hasiya Abun nasara ai ya na da iri da yawa da wannan Tunanin na shiga dakin da su Adda Fati ke ta salla su da sauran mutanen da suka zo daga gidan Baba Jibril.
Ina shiga Adda Fati ta fara tareni Adda Rukayya na sallah, Cikin mamakin ganina tace"ke da wa ki ka zo?
Cikin basarwa nace"Ni da Fatihatu ta matsamin sai da na Biyota."
Adda Fati tace"Ta kyauta damn yanzu nake tunanin mu koma gida, jakarki na Hannuna ana ta kiran wayarki ina Tunanin mijin ki ne."
Ta fad'a ta na mikamin Jakar na amsa ina kokarin Bude Jakar naji Diyar Goggo Kona ta na kallona tace"Hasiya Atamfarki iri d'aya da ta dangin Amarya da suka yi anko."
Sai na kalleta batare da na yi mgana ba, Adda Fati ce ta kara kallon kayan jikina kafin tace"Eh mun gani sai da Adda Rukayya ta yi mgana tace iri d'aya da na Hasiya."
Ni dai ban Tsaya sauraransu ba na cire wayata acikin jakata na sake mikama Adda Fati jakar na fice daga dakin daidai Lokacin da na ke duba Calls din wajen 20missed call kuma duka Daga Assadiq.
Ba a falon na tsaya ba saboda Hayaniya sai na fita zuwa Haraban gidan na samu chan gefen wajen tankin ruwa sannan na kira Assadiq sai naji line Busy da alamu ya na nema ne sai na d'an dakata.
Sai ko ga kiran shi ya sake shigowa da Sauri na d'aga kiran rabon mu da waya Tun jiya da yammah da muka iso kaduna.
Ina Dagawa yaji muryanta sai ya sauke ajiyar zuciya kafin yace"Siya ina ki ka shige ne? Kinsan kira nawa na yi miki baki daga ba?
Zan kira Adda Fati na nemi lambarta a wayana sai kuma na rasata."
Ajiyar zuciya na sauke kafin nace"Wayar na cikin jakata karama, kuma bata wajena ta na wajen Adda Fati, ita na ba ma ajiyar jakar tun safe."
Shima ajiyar rai ya sauke kafin yace"Hankalina ya tashi Sosai dazu na samu salama Tunda kina lafiya."
Daganan sai ya cigaba da fad'amin yadda ya yi kewata na yinin ranar gabadaya ni kuma kamar an yi min wani abu na kasa yi masa Fara'a haka Kurum na ke jin raina ba Dadi.

Muna cikin wayar ne wata mata tazo gefena itama da irin Atamfar jikina ta na mgana a waya itama.
Sai dai ni na rigata gama Wayar Tunda dagachan bangaran Assadiq na ji kamar ana mgana sai ya yi saurin ce min zai kara kirana ya kashe.
Dagowa na yi ina kallonta bata da wani Tsawo fara ce ammh ba Sosai ba ta na kuma d'an jiki kad'an na Hutu da jin Dadi.
In zama girmeni da kad'an ne ko kuma mu zo Tsaran juna ni da ita.
Ashe ta gama wayar itama sai taga ina kallonta sai ta yi min mirmishi nima sai naji kunya na maida mata martanin mirmishi.
Ni sai nake ganin su, da wad'anda na gani a falon nan da ita din suna kama da wani Fuska da na sani har matar nan da Tsohuwar nan a raina ina jin kamar ni dai yanayin fuskarsu kamar nasan wani ko wata da yanayi mai kama da na su.
Har ta wuce sai ta kara dawowa ta na kallona kafin tace"Allah sarki ga irin ankon mu."
Nima sai na yi mirmishi kafin nace"Eh nima ina gani nace komai iri d'aya."
Dariya ta yi kafin tace"To ai kamfani bamu kad'ai ya bugamawa ba. Sunana Saliha ke fa?
Ta fad'a ta na bani hannu alamun mu gaisa nima sai na mikamata nawa hannun muka sarke.
Cikin maida mata martanin mirmishinta nace"Ni kuma Hasiya."
Sai ta Bude baki kafin tace"Hasiya? Ko dai Asiya?
Cikin yar dariya nace"Hasiya dai domin shine sunan yanka na."
Sai ta Rausayar da kanta kafin tace"ko? Abunda yasa kika ji nace haka nasan sunan Hasiya ai Asiya ne"

Mirmishi na yi mata ban ce komai ba ita kuma sai ta kara kallona kafin tace"Ni yayar Salima ce Amaryan da muka kawo, Ina aure a Ibadan ya'yana biyu, Sha'anin nan ne ya kawoni da zarar an gama zan koma Ibadan."
Nima sai na samu kaina da fad'in"Ni ma ina da aure ammh ban haihu ba, kuma ni a matsayin diyar yayan mahaifin Ango ne daga Zariya muka zo."
Cikin Fara'a Saliha tace"Ma sha Allah naji dadin had'uwa da ke Hasiya kina da Fara'a"
Nima cikin dariya nace"Kema haka sannan ban kai ki fara'a ba."
Gaskiya na fad'a ta na da Fara'a ni kuma haka Kurum taji ta Burgeni.
Sai ga shi mun samu wani Dutse da ke wajen mun zauna muna ta Hira ni da ita.
Har ta na fad'amin ta gama Degree dinta ammh  bata aiki sai dai kasuwanci ta ke yi, nima na sanar da ina yanzu na fara karatun nawa ina shekarar ta Biyu ne in muka koma Hutun karshen Shekara.
Ban tambayeta ba da kanta ta fad'amin akwai nisa Daga Ibadan zuwa Gusai in dai ba Jirgi ta Biyo ba sai ta kwana a hanya.
Ni kuma sai nace mata ai yanzu in ta tafi sai ta jima bata zo ba ko?
Cikin yar dariya tace"Wane ni? Ai zuwa ya kamani in dai da rai da lafiya nan da wattani uku akwai Bikin kanin mu Sadiq, da kanwarmu Sultana da ya ke diyar kanwar Abba ne kuma nan ta girma cikin gidan mu."
Sai na jinjina kai kafin nace Allah ya  Sanya alheri.
Ina so ta na tambayeta Tsohuwar nan da Matar da na gani yan'uwan su ne?ammh sai na kasa yi mata mgana.
Sai dai a raina na yi Tunanin Tabbas tare su ke yan'uwan Amarya ne.
Mun jima muna ta Hira har aka kira Isha'i sai tace ko zan yi sallah ne?
Kai Tsaye nace mata ba na sallah itama ta na Dariya tace mun yi anko.
Sai kawai mu ka cigaba da Hiran mu, sai aka kira wayarta ta dauka ta na magana naji dai ta na ambaton sunan Mama, da Umma sai kuma naji sunan Innani a bakinta.
Sai da ta gama wayar sannan ta kalleni ta na fad'in"Mamanmu ce, ta na tambayata ya innani, kakarmu ce fa irin rigimamman tsoffin nan ne wai sai ta zo Abba ya yi ya yi da ita tace sai ta zo."
Sai na yi mirmishi nace"Na ganta ba wata tsohuwa mai gilashi ba sannan itama da irin Atamfar jikin mu ko?
Saliha tace"Itace a ina ki ka ganta?
Sai kawai na yi dariya na fara bata Labarin had'uwar mu, sai da ta yi Dariya kafin tace"Umma ce ta zo ta Dauketa domin tunda muka zo muka bar mata wahala da ita, Sadiq da shi kada'i ne ya isa ya hanata zuwa wannan karon da kansa ya sakata a mota, to waye zai dauki Innani daga karshe ta rika tsine masa kwata kwata bata san abun arziki ba."
In ta ambaci sunan Sadiq sai naji gabana ya fad'i ko don sunan Mijina ne oho?
Saliha sai bani Labarin Kakarsu Innani ta ke yi, ni kuma ina ta shan Dariya sai naji ina sha'awar zama da ita, saboda ni bansan dad'in duka zama da kakkani ba.
Ta na cikin bani Labarin ne wasu yanmata Biyu suka fito suma Haraban gidan.

Ina ji Saliha ta kira sunaayensu Siyama da Sultana ta kira su da Hannunta.
Sai ga shi sun kariso gabanmu ganina da Saliha kila shi yasa suka gaishemu dayar wacce bata da Tsawon ta fi Fara'a Doguwar kuma sam ba ta yi min Fara'a ba.
Kai tsaye ta kallesu kafin tace"Sai ina?
Siyama tace"Shago zamu fita nema  Amarya ta aike mu mu siya mata Coke mai sanyi."
Saliha tace"Shine sai kun fita? Ta kira shi Mubarak din fa?
Siyama tace"Ta kira sa wayarsa baya shiga."
Saliha bata damu ba ta kalleni ta na fadin"Kinga kanwar tamu da zata auri kanin namu nan"
Ta fad'a ta na nuna mara Fara'an nan, Sai Siyama da tace kanwarta ne itace auta a gidan su.
Mirmishi na yi musu Siyama ta kara gaisheni wacce aka kira da Sultana ce kwata kwata naji bata kwantamin a rai ba kamar yadda itama gani Daya ta yi min taji ban burgeta ba saboda Farin fatata har shiga ido ya ke yi.
Sai ma ta kauda kai kawai ta na wasa da gefen mayafinta.

Ina jin Saliha na gaya musu ni kanwar Mubarak ce cousin muke, Siyama ce har suka bar wajen ta na Fara'a Sultana kuma ko kad'an banga Fara'a a Fuskarta ba.
ita kanta Salihar sai ta ce min haka take wani Lokacin ta yi ta kunci kamar an yi mata wani abu.
Sauro suka Damemu da ya sa muka tashi muka koma cikin gida.
Ammh kafin mu Rabu sai da muka karb'i lambar juna Tunda na gayamata ba anan zamu kwana ba. kuma gobe da Safe zamu koma zariya.
Dakin Amarya ta wuce ni kuma sai na wuce dakin da su Adda ke ciki na iske sun shirya ni suke jira.
Da ya ke ba nisa a kafa muka taka zuwa chan gidan, na gaji so kawai na ke na kwanta daman Dakin Zahra'u na ke kwana Gyara jikina kawai na yi na kwanta, su Adda Fati suna dakin da aka sauki sauran yan'uwansu na Zariya.
Na yi mamaki har gari ya waye ban kara ganin kiran Assadiq ni kuma ban kirasa ba, da Safen bamu koma gidan Amarya ba muka yi shirin tafiya Adda Fati na wani mganan mu jira a tafi gabadaya nace to ni dai zan yi gaba sai sun zo.

Jin haka yasa tace to mu tafi mun yi sallama da Hajiya Murjanatu tace kafin mu tafi mu shiga mu gaishe da Babanmu tunda hayaniyar Daurin aure bai sa ya san da zuwan mu ba.
Ni dai har ga Allah ban yi niyar zuwa ba ammh bani da mafita.
Abun mamaki tare da ita mukaje bai ganemu ba sai da ta yi masa bayani sannan ya ganemu ya dago ya na kallonmu kai Tsaye yace"To to cikin ku wacece mai kashin Tsiyan nan ne?
Sai Adda Fati da Adda Rukayya suka kasa magana.
Hajiya Murjanatu tace"Haba Abban Zahara'u wannan wani irin mgana ce?
Kai Tsaye yace"Maganar gaskiya ne Murjanatu akwai mai kashin Tsiya acikin su ko ba da ita kuka zo ba ne?
Kaina na kasa na kasa mgana ammh naji wani abu mai daci ya Tokaremun zuciya.
Ganin su Adda Fati sun kasa mgana yasa na dago ina kallonsa nace"Ni ba ni da kashin tsiya, ni Mutum ce kamar ka  kuma Baiwar Allah da ya Halliceni tare da Ni'imominsa."
Sai shima ya Tsaya ya na kallona kafin ma ya samu zarafin mgana naja jakata na fice daga falon ina kokarin maida kwallata.
Ko ajikinsa sai ma ya zakud'a kafad'a kafin yace"ance ta yi aure kwanaki in ji dai shima mijin bata nakasa shi ba ko?
Adda Rukkaya tace"Suna zaune lafiya."
Sai ya yi mirmishi kafin yace"Dakyau, Ina ita mahaifiyar taku? ko ta na chan garin na su ne da akace ta koma?
Adda Fati tace"Eh ta na chan tace a gaisheku da Fatan Allah ya ba da zaman lafiya"
Cikin jinjina kai yace"Ameen ku gaida Gida"
Da haka ya Dauki wayarsa da ake ta kira tun dazu.
Su Adda Fati suka fito jiki a mace Hajiya Murjanatu ta rasa ina zata saka kunyarmu.
Su Adda Fati ne suka Tsaya tabasu abun Rabo na jaka da kofi sai kayan Fulawani ni a bakin Titi muka had'u da su, kuma har muka isa tasha muka Hau mota ba mu yi ma juna magana ba.

Gidan Adda Fati muka sauka ni da ya ke ba na sallah ban Tsaya ko cin abinci ba na had'a kaya na wuce gida nace naci achan, ba su hanani ba ganin yanayina sai da na koma gida naci kuka na har na godema Allah.
Sai da yammah Saliha ta kirani tace ga su sun zo gidan ba ta ganni ba.
Murya a chunkuse nace mata mun Dawo Zariya tun dazu.
Jin muryata wani iri yasa tace lafiya? Ni kuma sai na ce mata ina Mura ne fatan samun sauki ta yi min tace suma sai gobe za su koma Gusau sauran ne da za su zo daga gusau mota ta lalace musu a hanya sai da yammah suka iso.
Fatan sauka lafiya na yi musu sannan muka yi sallama.
Na zauna na yi ta Tunanin inda mutanen da na had'u da su a kaduna suka min kama da wanda na sani ammh na kasa ganewa.

(Da ya ke Yan gidan su Assadiq ba su da mugun kama da juna, Gwara ma yan Dakin Mama ita suke Debo suna yanayi da juna akan dakin Umma Sadiq ne ma ya ke kama da Surayya kamar kwabo da kwabo).

Sai a daren muka yi mgana da Assadiq shima dai ji na wani iri sai da ya yi mgana sai nace masa mura ne. Sai yace kila iskar Mota ce tunda na gayamssa tun dazu muka dawo.
Matsamin ya yi na siya magani na sha na kwanta na amsa masa da toh.
Washegari dakyar na iya rarrafa jikina na yi share share tunda dakin ya yi kura jikina nake jin ya na min wani iri sannan Jinin da na ke yi a kallah kwana Biyar sai ga shi har Sati bai Dauke ba.
Sai na fara Tunanin kamar ba lafiya ko shi ya ke sakamin kasala ban sani ba ko abinci na rage ci da ga Tea da Safe sai Dare na Dafa Indomie.
Yau din ma Tea na sha da Safe zaman kadaici ya isheni mun yi waya da Safiya Ahmad da Safe tace mun kusa komawa makaranta.

To daman Assadiq ya bar min karamar Computer dinsa Saboda makaranta shi kuma sai ya siya Sabuwa kuma da ya ke muna yi a makaranta sannan shima ya Koyamin sai ya kasance na iya Sarrafata yanzu.
Duk da ya maida komai na shi cikin Sabuwar da ya siya bayan ya goge komai aciki fina finai Kawai ya barmun sai karatun Qur'ani.
Sai ni kuma na saka Safiya da ta zo ta Turamin Abun karatun mu na Computer aciki.

Tunda aka yi Hutu ban Daukota ba, kallo bai wani Dameni ba sai in Assadiq na nan ne mu yi tare, in kuma baya nan sai dai na gaji da danna waya ko na yi barci karatun Novel din ma da na fara yanzu na Daina bani da juriyan karatun ne kwata kwata.
Na Dauko na kunna kenan sai hannuna ya kai kan wani Draft da aka saka SSSHINKAFI a jiki ban taba Lura da wajen ba.
Ko sanda Take na Assadiq ba ko'ina ya ke shiga a gabana ba, wasu app d'in ma duk sai da ya san ya musu pin in ba shi ba, ba wanda zai iya shiga ciki.
Kamar wasa sai na Shiga sai naga Wani Hoto ne guda daya a wajen akwai alam ya makalene ba'a goge shi duka ba.
Kamar bazan shiga Hoton ba sai na Danna sai ga Hoton ya bayyana.
Hoton da sai da ya sa na tashi da Sauri Cikin kif kifta idanuwana na mamaki da Al'ajabi.
A cikin Hoton naga mata Biyun da na gani a kaduna, sannan har da Saliha aciki da yaran matan da ta nuna min Siyama da Sultana.
Sai wasu kuma da sun kai su goma sha a Hoton sun saka kaya iri daya na wani bakin leshi da Fari, sun saka Assadiq a tsakiya shima cikin Fararan kaya harda babban Riga.
Sai dai fuakarsa ta yi karama a Lokacin kamar Hoton ya jima ko wani sha'ani ko kuma sallah ne aka yi wannan Hoton.

Na gefe da gefensa sun Dafashi gabadayansu suna dariya ga Fararen Hakoransu nan a bayyane da Mirmishi da Fara'a sai gashi na samu kaina da Kara zooming din Hoton domin na kara Tabbatar ma da kaina abunda na gani shin gaskiya ne ko ni ce ban gani Daidai ba?
Sai ga shi na kara tabbatar ma da kaina abunda na gani zahiri ne acikin wannan Hoton.
Sai da na kara kura ido sai na samu amsar kokwanto na tunanin da waye sukamin kama?
Ina ganin Fuskarsu yanayi da na wanda na sani to ba kowa ba ne face ASSADIQ.!
Na dimuace sannan na shiga wani yanayi da Tunanin su waye wad'anan a wajen Assadiq? Wani lungu daga zuciyata ta bani amsawa da cewa"Ba sa wuce Yan'uwansa."
Sai kuma na ce a fili to ai yace ba shi da kowa sai kakarsa to wad'anan fa a ina ya same su?  Kamar ana min Wahayi naji bakina ya furta"Kenan Assadiq ya yi miki karya ke da yan'uwan ki."

Tabbas hakane domin ko wanda baisan kama ta jini ba yaga Assadiq da wad'anan matan yasan suna da alaqaan jini mai karfi a tsskanin su.
Na yi ta kallon Hoton nan ina sake Zooming ina kokarin gasgasta zargina zuciyata na Tunanin Assadiq bazai min karya ba? Wata zuciyar na gayamin ya yi min karya tunda har yau bai taba kaini ga wani nasa ba hatta ko kakar tasa da yace ita kad'ai ta rage masa.
Lokacin da nake zaune ina wannan Tunanin, ashe ban sani ba na yi sharkaf da jini, sai da naji abu na bin kafata sannan na farga ko da na mike sai da naji tsoron ganin jini ya bata siket din jikina yar ya bata kujeran da na ke zaune sannan ya bata har kasan Tayels wanda ya gangaro ta kafafuna.
Wannan tashin hankalin ya mantar dani Hoton da na gani na shiga cikin tashin hankali na shiga Tiolet na gyara jikina sannan na kwabe kayan Jikina na wanke su tas sannan na fita waje na shanya.
Muka had'u da Maman suhailat itama ta na shanya ta yi wanki sai muka gaisa sama sama domin ba na cikin yanayin nishad'i, na koma daki da Sauri na goge kujera in da na bata da kuma Tayels din na wurgar da Tsumman da na goge da shi.
Abun kamar wasa sai ga karaman mgana ta zama babba kwana nayi ina Zubar da jini, pad ya daina amsata na koma yaga zanina ina kunzugu da shi ammh duk a banza kafin safe sai da na cika baho da kayan da na bata har da zannuwan gado har katifan ma sai da ta baci.
Hankalina ya tashi saboda
Showing 87001 words to 90000 words out of 98628 words