ganewa ba Tahir, Saboda har yanzu baka girma ba."
Tahir sai ya tsaya kawai ya na kallon Sadiq cikin mamaki tun ballatana da sai a lokacin yaga Sadiq din duk ya Sauya idanuwansa sun ji ja, sannan Jijiyoyin kansa sun mike Rad'au.
Har yammah bai wani sake ba yadai kwanta kawai ya yi shuru ya na Juye juye.
Tahir ya gaji da tambayansa meke damunsa ganin ya yi banza da shi yasa yace"Wai ka na damuwa saboda ka saki zabiyar yarinyar nan ne Sadiq?
Sadiq ya taso ya na fadin"Ba sunanta Zabiya ba Her Name is Hasiya. Hasiya Tahir."
Tahir sai ya Bude ido kafin ya yi mgana Sadiq ya mike ya na fadin"Tahir ka kyaleni don Allah.'
Yana gama fad'in haka ya shuri takalminsa ya bar Tahir da sakin baki kafin cham kuma ya daga kafad'a alamun dai bai damu ba.
Sai Dare Sadiq ya Dawo kawai gari ya shiga shine har kofar gidan su Hasiya da suka zauna kuma baisan meyas kaisa ba abu daya ya sani Hasiya na cikin zuciyarsa kuma Tunaninta da Tausayinta na neman ya hanasa Sukuni.
Koda ya Dawo ba su shiga Harkan juna shida Tahir ba kowa sabgar gabansa ya yi, Sadiq kwana ya yi bai yi barci ba daga karshe ya tashi ya yi addu'an neman zabin Allah da asuba da ya tashi sai ya samu kanshi cikin Halin Janaba saboda ya yi mafarkin ya kusanci da Hasiya sai da ya yi wanka.
Sannan wannan nauyin kirjin da rashin sukunin duk ba bu shi sai dai Tunanin Hasiya na manne acikin Zuciyarsa.
Shiryawa suka yi cikin Complete kayan Hidiman kasa suka tafi Zonal office ba bata lokaci bayan karban Shaidar kamallawansu suka Tsaya yin Hotuna da abokansu masu Hidimar kasa.
Sadiq ya fara baro Tahir a wajen Domin Tahir baisan hotuna kala nawa zai Dauka ba.
Tahir yazo ya iske duk ya had'a musu kayan su yana ma shirin kyautar da wasu kayan girkinsu zuwa ga yanmakaranta da suke tare da su.
Daman masu gidan tuni sun gayamusu zasu tafi duk da daman kudin su ya kusa karewa.
Tahir yace yana son gas da katifan su sai Karamin Fridge.
Sadiq ya kallesa Fuska ba Annuri kafin yace"Zaka iya jigilan Daukan su?
Tahir yace"Me zai hana?
Sai kawai Sadiq ya bar masa botikai ne da wasu kayan filets da kololi Sadiq ya kyautar da shi yan makaranta suna ta Godiya.
Ga kayan abinci ma duk ya had'a ya basu ba su had'a komai ba face kayan sawan su.
Sadiq duk ya rage wasu kayan sawansu saboda baya som Daukan kaya, Tahir ne mai akwatina uku Sadiq kuma Biyu sai jakar baya sannan akwai karama ta Hannu da ya sanya takalmansu wasu ma duk ya ba ma Tahir saboda ya tsani Tafiya da kaya.
Sun yi sallama da yan makarantan su suka rakasu ma har bakin Titi suka samu adaidaita zuwa tasha suna Daga musu hannu Domin an yi zaman Amana
A tashar yan karfe da ke garin Zariya Tahir ya samu Motar Daura shi harda katifa, Sadiq kuma ya hau ta Gusau.
Bayan sun yi sallama da Tahir har yana cewa"Ka yi ma zariya kallon karshe domin ban Tunanin zamu kara Dawowa"
Sai da Motarsu ta cika sun hau Hanya sannan Sadiq ya furta a fili" Ta ina zan yi ma garin Zariya kallon karshe tunda ina da wani abu mai muhimmanci aciki.
Tabbas zan dawo. Zan dawo gare ki HASIYA..!"
*BOJUWA HERBAL'S BY SURAYYA DEE*!
*Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Saiwowin maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Gaban ayu*.
*Hakkin daka gangariya*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*.
*Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya*
*08032773332*
*Ana dafa GIMBIYAR KAZA da tattabarun garari*.
*Janafty*
*TMWBK2014*
*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*
https://chat.whatsapp.com/GoRzZ7ZgslV2alO5hYGAnj
Mata muntashi tsaye mu yaki infection (sanyi) Wani ciwone Mai nacin gaske Wanda idan kikayi wasa xaihanaki jindadin Aure Sannan maganin shi saikin daure da nacin shanshi Akai Akai toh kufito🤌🏽 KUSAI TSIMIN TABAJE DOMIN MUNA DAFASHINE DA INGANTATTUN SAIWOYI MASU AMFANI AJIKI DAKUMA LAFIYA, CIWON SANYI, SANYIN MARA, BASIR DASAURANSU INSHA ALLAH DUK WANI CIWO INDAE NA SANYINE ZAIZO KARSHE DA YARDAN ALLAH KIDAE KIDAURE KIDUNGA SIYAN TABAJE KIJEFI TSUNSTU GOMA DA DUTSE DAYA💃💃💃
Akwai infection Wanda yake nuna kanshi Akwai Kuma kurman infection Wanda baxaki San kinada shiba Amma yanacan yana Miki illa domin duk kyan Kayan mata baxakiga aikinsu ajikinki ba ko Kuma sumiki aiki bayanda akaso ba
Anason duk bayan wata 1 mace tasha maganin infection sbd samun lafiyar jikinta
Alamomin shi sune
Fitar farin ruwa
Kaikayin gaba/ko kuraje
Jin zafi yayin sex
Daukewar ni'ima
Daukewar sha'awa dadai sauran su
Kafin kifara Shan maganin mata yakamata ki fara Shan maganin infection
Ina Yan mata Budurwa kema Yakamata kidinga Shan maganin infection Dan kariya da lfy ki karsai kinyi Aure infection ya Riga yamiki illa Baki saniba Allah y bamu lfy y karemu Ameen 🙏
*Gusau.*
Har suka isa Gusau Tunanin Hasiya ne cunkushe acikin zuciyarsa. Tunaninsa da Hankalinsa gabadaya ya na kanta ne sai yake ji kamar gangar jikinsa ne ke cikin Mota Ruhinsa da zuciyarsa na chan wajen Hasiya ya baro.
Sai yake jin wani iri a cikin jikinsa kamar mara lafiya kamar kuma wanda wani abu mara dad'i ya faru da shi, ko kuma wanda ya kwanta Jinya na wani dogon Lokaci.
Adaidaita ya samu Daga tasha zuwa gida kamar Mallam Tajudeen ya sani ya na jin karan adaidaitam ya bud'e karamar kofa ya leko sai ya ci karo da Sadiq yana sauke kayansa da Sauri ya fito yana yi masa maraba da sauka.
Shi ya taimaka masa ya rage masa wasu kayan zuwa cikin gida suna tafe suna gaisawa cikin mutumtatawa kamar yadda suka saba.
Sadiq ya tambayi Mallam Taju yana fatan gida kowa lafiya?
Sai mallam Taju ya Rusunar da kansa yana Fad'in"Kowa lafiya Ranka ya Dad'e."
Sadiq bai ce komai ba ya cigaba da takawa zuwa bangaran Umma, sai dai me? sai ya Lura da bangaren Abba a Bude ne sannan ga takalma nan a kofar falon tabbacin dai akwai mutane aciki da Sauri ya kai kallonsa kan haraban gidan inda Motocin gidan suke nan yaci karo da Motar Abba.
Cikin mamaki ya kalli Mallam Taju ya na fadin"Abba na gida ne?
Mallam Tajuddeen ya gyad'a masa kai kafin ya samu zarafin mgana Sadiq ya rigasa da cewa"Ok kila yau jumma'a shiyasa bai kara fita ba."
Haka zuciyarsa ta basa shiyasa ya fad'a Mallam Tajudeen daman bai yi niyar fad'a masa komai ba shiyasa ya yi shuru ya na Rausayar da kai.
Chanza alaqan tafiyarsa ya yi Daga Shashen Umma zuwa bangaran Abba.
Yana sanye da kayan yan Hidiman kasa sai jakarsa ta baya da ta Hannu akwatunan kuma suna Hannun Mallam Tajudden da ke bin bayansa.
Siyama ce ta fito daga Shashen Mama dauke da Faranti shake da Ruwa da lemuka, ta na fitowa taci karo da shi ai sai ta zaro ido cikin washe baki da karfi tace"Yaya Sadiq.."
Ta fad'a lokaci daya ta na kwaso gudu har lemu na fad'owa daga cikin Farantin Hannunta.
Dakatawa ya yi ya na kallonta cikin d'an mirmishi ya ke fad'in"Siya ki yi a hankali."
Sai kuma ya ji wani Dam! Sunan da ya kirata da shi sai ya famo masa da Tunanin Hasiya.
Har Siyama ta kariso gabansa Tunaninsa na chan Zariya inda ya fito sai da yaji karad'inta a saman kansa cikin Murna ta ke fad'in"Yaya Sadiq sannu da zuwa."
Ta fad'a ta na kallonsa domin ba su taba ganinshi da kayan Bautar kasa ba sai yau sosai kayan suka zauna ajikinsa suka yi masa kyau.
Mirmishi ya sakar mata kafin yace"Siyamar Abba kina lafiya?
Cikin washe hakoranta tace"Lafiya lau Yaya Sadiq sai dai Abba ne ba shi da lafiya har Su Baba Sammani sun zo ma dubashi yau."
Cikin Tarin mamaki yace"Abba ba shi da lafiya?
Siyama tace"Eh jiya ma aka sallamosa daga asibiti Innani nata kuka tun jiya."
Bai kara tsayawa sauraranta ba ya wuce da Sarsarfa takalman kafarsa na kara taimaka masa wajen kara bayyana Takunsa na Gif! Gif!.
Siyama ta bi shi a baya da gudu ita da Mallam Tajudden da ke Dauke da akwatinsa.
Ya na Bud'e kofar Falon ya shiga tare da sallamansa cikin Kakkausan Muryansa.
Gabadaya mutanen Falon suka Dago suna kallonsa shima cikin abunda bai gaza mintina biyar ba ya gama Nazarin mutanen dake cikin Falon na Abba.
Umma da Mama ya fara cin karo da su suna zaune a kasa gefe, Abba na Tsakiyar Falon a zaunar da shi bayan an saka masa filo ya tokare bayansa sanye yake cikin jallabiya kansa ba Hula ya mike kafafunsa saman Italiyan Cafet d'in da ya yi ma Falon kwanya.
Daga gefen hannun Damansa kuma Innani ce zaune da makeken gilashinta ta yi zaune rashe rashe gabanta wani katon farin botiki ta Dafe shi kamar ranta ne aciki ya ke daga chan gefenta daga saman kujera kuma Baba Saminu ne da Yaronsa Auwalu sai Goggo Husai itama da Lullubinta daga gefe.
Chan bangaran hannun Hagun da su Umma suke kuma ya hango gabadaya Sisters dinsa mata har da masu nisan sun zo suma.
Yaya Saddiqa ce kad'ai bata ciki inaga ita bata kai ga isowa ba kenan.
Sai kuma ya hango Mallam Shitu Mahaifin Sultana da Matansa duka Biyu yana kyautata zaton tare suka zo da su Baba Sammani.
Tsaye ya yi da jakarsa a hannu duk ya na kallonsu kamar yadda suma suke kallonsa Siyama ce ta karisa tsakiyar Falon ta na sauke Farantin Hannunta tace"Yaya Sadiq ne ya Dawo.."
Mallam Tajudeen kuma akwatinan Hannunsa ya sauke anan bakin Falon sannan ya fice.
Sallamar da ba su amsa masa ba ne yasa ya coge bai karisa shigowa falon ba.
Sai da ya kara yin wata sallamar sannan suka amsa masa gabadaya cike da Mirmishi da jin dad'in ganinsa.
Yan'uwansa mata suna kallonsa cikin alfahari ne ganin yadda Kayan Hidimar kasar suka amshe shi kamar domin shi kadai akayi kayan.
Sultana na chan gefe kusa da Big Sis Anty surayya ta na leken Sadiq cikin alfahari da Muradi mai girma.
Sai Annuri Fuskarta ke saki kamar taga wani zara acikin wata.
Bai Saurari Sannu da zuwan da ke tashi a Falon ba ya fara da Sauke Jakar Hannunsa yana mai tafiya zuwa gaban Abba.
Sai da ya duka ne sannan ya Sauke Jakar bayansa lokaci daya ya saka Duka Hannunsa ya riko Abba cikin Sanyin Murya yace"Abba me ya same ka? Wai baka da lafiya da gaske?
Ya karishe fad'a ya na kara nazarin Abba kuma Tabbas ya shaida ba shi da Lafiya saboda yaga ya rame idanuwansa sun zurma.
Abba ya kallesa cikin son kwantar masa da Hankali yace"Ba bu abunda ya Sameni Magajin gida zazzabi ne kawai da zirga zirga."
Sadiq ya yi saurin cewa"Abba da rashin Samun Hutu ko? Sannan kuma baka da lafiya ba wanda ya iya Kirana ballatana nasan me ke faruwa?
Ya fad'a ya na zagaye kallonsa acikin Falon Umma da ke gefe ta kallesa bata dai yi magana ba.
Sajida ce ta yi karaf tace"Abba ya hana kowa ya fad'a maka saboda baya so a tada maka Hankali."
Kallonta ya yi cikin nazarinta sai yaga ta kara kiba sannan komai na Fuskarta ya koma babba ta yi baki sai Uban kuraje.
Sai da ya kara kallonta yaga Ciki ne da ita har ma ya tsufa tabe baki ya yi bai ce komai ba.
Juyawa ya yi yana gaida su Baba Sammani suka amsa masa cikin Sakewa Auwalu kuma ya bashi Hannu suka yi musabaha shi da Mallam Shitu.
Gefen Abba ya zauna har ya na matse Innani da ke zaune ashe barci ne ya fara D'ibanta ta na daga zaune sai gyangyad'i ta ke yi.
Jin an tureta yasa ta Farka da Sauri ta na fad'in"Wani mara mutumcin ne ke kokarin Tureni kusa da D'ana?
Ta fad'a ta na kokarin gyara zaman gilashinta domin taga wani ja'irin ne yazo zai shiga tsakaninta da Sulaimanu a wannan Halin da ya ke ciki.
Ido ta rika zarowa ta cikin gilashin nata ta na kallon Sadiq shi kuma ya juya ya na gaida su Umma da Mama.
Mama ta amsa cikin Fara'a Lokaci daya ta na fadin"Mu ka ganka da kaya haka Magajin gida? Ko zaman zariya ya kare ne?
Sai da ya gyad'a kai sannan yace"Mun gama da Hidimar kasa in sha Allahu."
Gabadaya Sisters dinsa suka Had'a baki wajen fad'in"Alhamdulillah..!
Kallonsu ya yi cikin mamaki Surrayya tace"Daman na tsani Zariyan nan bansan Dalili ba wlh.".
Sajida tace"Nima wlh kiga har wani Rawan jiki ya ke yi in zai koma zariyan kamar wani chan ne gidan su."
Hararanta ya yi kafin ya yi mata wani kallon Sama da kasa sannan ya tabe baki yace"Malama ki ji da kanki don Allah.".
Yadda ya yi mganar ne yasa sauran suka sakamata Dariya.
Shahida tace"lil bro ba ka da kirki."
Ta fad'a ta na Danne Dariyanta domin kowa yasan yadda cikin nan ya Saka Sajida wani munin bala'i.
Ai sai ta fara kumburin baki ta kalli Umma ta na fadin"Umna kinga Sadiq ko? Ki gayamsaa ni ba Sa'arsa ba ce wlh."
Umma ta harareta kafin tace"Bakin ki na ciwo ne? Ba ga ki ga shi ba ki fad'a masa sai kin aike ni?
Sai Sajida ta kasa mgana ta koma ta na wani cika baki da Sadiq.
Sadiq ko hankalinsa ma baya kansu yana kam Abba suna mgana kasa kasa .
Muryan Innani ce ta karad'e falon cikin Masifarta tace"Wai muryan wa nake ji kamar ta magajin gida?
Baba Sammani yace"Shine Innani ga shi nan a gefen ki."
Da Sauri ta riko Sadiq shi kuma ya kwace jikinsa yasan fa ta ganshi ammh wai ta na nuna bata ganesa ba.
Kawai ana zaune kalau Innani ta fashe da kuka ta na fad'in"Allahu Akbar Allah ya yi magajin gida akwai Rabon ganawa tsakaninka da Sulaimanu, gani nan tun shekaranjiya Rabona da barci makiya da magauta sun sako min Sulaimanu a gaba, Lafiyan Allah ya yi min sallama ya fita ammh sai dawo mana da shi aka yi rai a Hannun Allah fa, sannan ni ina ganinsa Sannan Jifan magauta ne ba yadda ban yi kada su kaisa asibiti ba Amma Salamatu ta fara zama Mutuniyar kawai ta Daukesa ita da Suwaiba suka kaisa asibiti chan ya kwana sai jiya suka Dawo min da shi , ni daman Tunda na Fahimci Laluransa na nemo masa magungunan Tsarin jiki na jika masa su, to duniya duk ta lalace Mutane ba Allah a ransu ballatana sun ganshi Bul bul da Shi jajir da shi sun yi Tunanin ya na da wani shahararren arziki ne ba su san Rufin asirin Allah ba ne za su kashemin d'ana da ba ni da kamarsa"
Ta karishe fad'a har majina na Zubowa Sadiq ya kauda kai kafin yace"Meyasa baki kirani kin Fad'amin ba? Da Sauri Innani tace"Ta ina zan gayamaka? Yar wayar tawa daka siyamin an dakaleta ta daina yi kwata kwata, su kuma iyayen naka sun ce wai Sulaimanu yace kada a kiraka a Tada maka Hankali, ni kuma kasan bansan garin da ka ke masta ba ai da ka ganni nazo na gayamaka ni fa Daman abunda nake tunani gwara kazo ku gana da Sulaimanu kila akwai Wasiyar da ya ke so ya bar maka Tunda kai kad'ai ne magajinsa a wannan Duniyan"
Cikin Mamaki Sadiq ya kalli Innani sai Faman jan majina take yi girgiza kai ya yi kafin yace"Waya fad'a miki Abba zai mutu yanzu? Ai sai kin rigasa Mutuwa ma in sha Allahu."
Sai Innani ta yi gum da baki.
Abba na gefe ya na yar dariya shi da su Umma kowa na Rufe bakinsa Tuna yadda Innani ta rika kuka ta na fadin gwara ita Mutuwa ta zo ta Dauketa akan ta Dauki Sulaimanu shi kad'ai gareta in ya Mutu bata san ya rayuwarta zai kare ba.
Yanzu ma kara fashewa ta yi da kuka kafin tace"haka nace dai gwara ni mutuwa tazo ta Daukeni ta bar Sulaimanu, shi kadai gareni da ya Ragemin sanyin Idanuwana, daman shi da Kulawa kad'ai na Haifa to bakincikin wasu maketatan sun kashemin ita da bakinciki Allah dai ya isar min wlh bazan yafe ba.".
Tafad'a ta na sharan Majina da Haban zaninta ta cikin gilashinta sai Faman Hararan Mahaifin Sultana ta ke yi shi da Matarsa.
Baba Sammani ne da goggo suke ta bata hakuri ta na kara auna Allah ya isa bata yafe ba cikin gayya.
Sadiq na jinta ya kasa mgana gabadaya a gajiye yake ga Hayaniyar Innani duk ya ishesa.
Jinginar da kansa ya yi jikin kujeran da ke kusa da shi ya lumshe ido ya na jin ana Dirama da Innani akan sai ta bama Abba wani magani da ta jika cikin Botiki wajen kwana Biyu kenan wai maganin magauta ne sannan da Jifa.
Umma ta Dake ta na gayama Innani illar shan wannan jike jiken da ba wanda yasan wasu itatuwa ne ma Innanin ta jika zata Dora ma Abba, shi kuma bai isa ya yi mata Musu ba haka ma su Baba Sammani suna mgana yanzu Innani sai ta iya cewa ina Ruwansu da sha'anin D'anta.
Ilai kuwa Baba Sammani ganin ana ta Daga da ita ta Dake yasa cikin Lallashi yace"Innani tunda har an fara na asibiti ki bari zuwa gaba sai ya fara shan na kin"
Ai sai Innani ta kallesa a Dage kafin yace"Kaji min wani Tsirfa da Iyayi ko shisshigi Tusa kai ba kwarjini, ina Ruwan ka da sha'anin d'a na da zaka rika Tsoma min baki ? Ba asibiti ba asibito dole zan gina Sulaimanu da maganin Tsarin jiki tunda har kuna gani magauta sun fara sako sa a gaba."
Ta fad'a ta na wani kumfar baki Duk ta gama Tofe na kusa da ita da Miyan bakinta.
Juyawa ta yi ta na neman wanda zata aika chan idanuwanta suka hango mata Sultana da Sauri ta ya fito da Hannu sai da ta zo gabanta sannan tace taje ta Dauko mata karamin kofi ta Tsiyayan ma Sulaimanu mganin nan.
Sadiq duk yana jinta baya so ya yi mgana ne Hayaniyar Innani ba ta karewa daga an hanata wannan sai ta koma kan wannan.
Sai da Sultana ta Dawo da Kofin Inanni ta cika shi da wani kalan mgani baki har ya na wani yauki yauki ta kalli Sadiq ta na fadin"Magajin gida d'ago min Sulaimanu dakyau ko bai sha ba, Dore zan masa tunda ni na kawosa duniyar nan ba wata ba."
Bude Idanuwansa ya yi da suka Sauya Launi kafin
Showing 60001 words to 63000 words out of 98628 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21 Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33