wanda yafi dangote kudi ne in ka yi masa alheri ya na so kuma zai ji dad'i.
Umma da Mama suma suka yi ta saka albarka Innani ko kuka ta fashe da shi , albarka ko ya sha shi ya fi cikin kwando, Su Surayya ma suka ce sai ya ba su na su shi kuma yace suna da mazajensu.
Sajida ce ta yi tsagal tace"Ko da mu ke da mazaje ai kai kanin mu ne zamu ji dad'i in kanin mu ya yi ma wani abun."
Harara ya sakar mata kafin yace"Da ya ke son kudi ne ai muryanki sai ta fi ta kowa zak'i."
Itama Hararan ta rama shi kuma sai ya saka mata Dariya ganin yadda ta kara zama wata cus da cikin jikinta ya girma.
Maganar Si yan ma Sultana Anko Surayya ta fara yi masa, tace har ta waya ma ta tura masa guda biyu ne material na ranar jumma'a yinin Biki kenan sai Atamfa na ranar Daurin aure.
Nan take yace yana so duka guda Biyu biyu, Cikin mamaki ta kallesa kafin ta yi mgana ya yi saurin cewa" na sultana d'aya dayan kuma zan siyama wannan abokiyar aikin tawa ta zariya sosai zama na da ita ta yi min kirki."
Surayya ta yi mirmishi kafin tace"ASIYA..."
Cikin mirmishi yace"Ita fa Big sis, ai har yanzu muna zumunci ko da na koma Abuja yanzu."
Cikin gyad'a kai tace"Gaskiya ya kamata ka siya mata ta na da kirki sosai Da fatan zaka gayyaceta ta zo mana Biki"
Da Sauri yace"Anya? Da wuya ta samu zuwa zan dai siyamata ankon in sha Allahu."
Surayya bata damu ba, Tunda duk abunda Hasiya ke ba shi in yace mata zai je garinsu gida ya ke kawowa da sunan abokiyar aikinsa ce ke ba shi ya kawo ya riga ya nuna suna zumunci da ita sosai ita da Mijinta shiyasa kusan duk yayyensa sun san sunan Asiya a baki abunda yasa basu damu ba Sanin ta ba cewa ta na da aure.
Innani ko ta sha saka ma Hasiya albarka domin har Tuwon madara ta sha yi ta aiko mata da shi, daman kuma Innani akwai son Abun Duniya.
Shi ko Sadiq duk ya zurma su ne a Buhu ya Dinke Hasiya ya ke nufi ammh sai ya sauya ma Labarin Suna da Muhalli yadda kafin su Fahimci inda labarin ya dosa za'a Dauki Lokaci.

Bayan ya siya musu nan take ya Turama Surayya kudin Tunda ita ta Daukon ankon, Sannan kuma Sakeena na Saida mayafai da Jaka ta matsa sai ya siyama Sultana, bashi da yarda zai yi yace a kirata ta zaba ita kuma Hasiya a ransa yace in yaje zai bata kudin ta siya hannun Maman Suhailat.
Ba su barsa haka ba sai da ya Turama kowaccen su 2k da sunan za su saka kati har Salima, shi kuma yace tunda hakane harda Umma da Mama da Abba suma sai ya Tura musu Falon Umma ya cika da Ihu suna ta fad'in"Allah ya yi albarka karamin kanin mu."
Umma na ta saka albarka Mama haka har ta na fadin"In sauran suka zo suka ji Labari zaka yi biyan ba shi."
Kai Tsaye yace"Suma zan Tura musu Mama."
Abba ko fad'a ya fara masa da cewa yaushe ya fara aikin da zai zo ya na wannan Hidimar? Cikin yar dariya yace"Abba bakomai ku yi ta saka mana albarka shikenan kawai mu ke bukata."
Abba ya Dafa kansa ya na ta saka masa albarka.
Ya baro Gusau Ranar Lahadi da Safe ne yace zai biya ta zariya yaga Superversor dinsa.
Ya baro su Surayya za su je kaduna Jeren kayan Salima duk da yasan an gama siyamata komai ammh sai da ya kirata shashensa shi da ita ya tambayeta in akwai wani abunda ta ke so ta fad'a masa zai siya mata.
A lokacin sai ta kallesa kafin tace"Yaya Sadiq Abba duk ya gama siyamin komai fa."
Cikin yanayin mganarsa yace"Nasani wannan na Abba Dabam ni a matsayina na yayanki me kike so na Siya miki? Ke kanwatace kuma aure zaki yi na fara aiki ina so nima na yi miki wani abu Salima."
Idanuwanta suka kawo kwallah ko acikin maza an sai antona za'a samu irin Yaya Sadiq, ko acikin yayyen sai an tona Dari kafin a samu kamarsa.
Bata Bukatar komai, ammh Saboda yadda ya Damu yasa tace ya siya mata Frem d'in Ayatul kurusiyu.
Cikin yanayin maganarsa yace"Kin tabbata?
Sai ta gyad'a masa da haka ya sallameta to kafin ya tafi ya kira Surayya suka yi mgana ya Tura mata kudi yace ta siya ma Salima Frem mai kyau da Tsada.

Ko iyayen ba wanda ya sani sai da Surayya ta siyo ta zo da shi.
Kowa yasan waye Sadiq ammh kuma ya na kara girma Hallayarsa na Dattako suna kara bayyana.
Ko da ace su Abba sun gama mata komai shi a matsayinsa na yayanta shima akallah ya yi mata wani abu.

*******

Tun ranar asabar na yi ta saka idon ganin Assadiq ban gansa ba tunda shi ya fad'amin ya na tafe wannan Weekend din.
Ranar jumma'a naje anguwan su Ramatu ta yi kitso da kunshi ammh har Ranar asabar ta kare bai zo ba da na kirasa zan fara masa kukan shagwaba sai yace ya na wani abu zai kara kirana.
Bai kirani ba sai da Daddare ni kuma Lokacin na yi barci sai da Safe nagani.
Daman ina jin haushinsa yasa ban bi bayan kiran ba.
Komawata na yi na yi kwanciyata ina ta Tura baki, gabadaya ba na jin dadin zama ni kad'ai jikina da Zuciyata ya saba da Assadiq sabon da yanzu ya ke Cutar da ni.
Chan cikin Barci naji ana ta kiran wayata na tashi da Sauri na d'auki wayar, Sai naga Assadiq ne da kamar bazan dauka ba sai kuma na Daga ina cin mgani.
Cikin Tattausan Lafazinsa yace"Ina kofar dakin ki Madam"
Zaro ido na yi kafin yace"Gaske ko wasa?
Ya na yar dariya yace"Ki fito mana ki gani."
Ai da gudu na Diro daga kan gado na watsar da wayar hannuna saman gado.
Dagani sai Rigar barci na fita naje na Bude kofa sai ko na yi farin gani da Assadiq.
Da gudu na tafi na Rumgumesa ina Murnan ganinsa shima rumgumeni ya yi a jikinsa ya na yar dariya yace"To kada ki ka damu mana Siya."
Sai da ya fad'i haka na sake shi bakina har kunne ina yi masa sannu da zuwa.
Jakar kayansa na karb'a sai ledan Hannunsa shi kuma sai yace bari ya shigo da Motarsa ciki.
Daki na koma bayan na ijiye masa kayan acikin daki na sako Hijabi na fito.
Ni na tayasa Bude get ya shigo da Mota na koma na Rufe shi kuma ya gyara parking ya kashe Motar ya fito muna Rike da Hannun juna har tsakiyar Falon mu.
Rumgumeni ya karayi cikin wani irin Jan Numfashi yace"Na yi kewarki Siya."
Nima ina kara nutsewa cikin jikinsa nace"Ni ma na yi kewarka.".
Dagoni ya yi kafin yace"Kamar sau nawa.?
Ina fari da ido nace"Zaka iya kirga nawa ne acikin Buhun gero?
Ido ya zaro ya na dariya nima ina Tayasa nace"To kamar haka na yi kewarka."
Ba tare da Tunanin komai ba kawai ya had'a bakin mu waje daya ni kuma sai na tallafeshi na fara ba shi had'in kai.
Tun muna Tsaye har muka zube saman kujera.
yanayinsa da na gani yasa na san abunda ya ke so.
Cikin shakewar murya na kira sunan Shi"Assadiq..!"
CIkin magagin abun yace"Uhm Uhm!"
Da Sauri nace"ban fa yi wanka ba."
Na fad'a cikin yar shagwaba.
Bai Saurareni ba sai chan da na kara magana yaja Numfashi kafin ya mike Tsaye dani a jikinsa ya na fadin"ya ma fi dad'i Siya."
Bai Direni ko'ina ba sai saman gado nan muka sha Sha'anin mu sai bayan mun natsa ne sannan muka yi wanka mu ka Tsarkake Jikin mu.
Tare da shi muka shiga kitchen na yi mana abun karyawa.
Dankali da kwai na soya sai kuma Tea da muka sha.
Bayan mun gama shi ya tayani muka gyara dakin muka goge, wanke wanke kuma ni na yi ammh shi ya rika Dauremin ya na kai su muhallinsu.
Muna gamawa kuma muka Dawo Falo saman kujera muna manne da juna muna Hiran mu ta ma'aurata.
Tare mu yini muna shan Soyayyarmu, Sai sallar mangariba ne ya fita Sai da aka yi isha'i ya dawo Lokacin naci gayu na, na kuma saka masa Rigiman sai ya zo mun fita mun ci abinci a waje.
Ba shi da yarda zai yi illah shima ya Shirya muka fita mukaje shan Ice cream sannan muka siyo kaza da Madaran Hollandian sai katan din Ruwan gora da na malt da ya siyamin sai da muka dawo ne ya bani Kaya Atamfa da Material yace na Kai Dinki.
Sannan yace daga baya zai Turamin kudin d'inkin ta acct dina tare da kud'in mayafi da Jaka.
15k ya bani dubu biyar yace na Rike  Dubu Goma kuma yace na Turama Amma da ya ke ya kaini na Bud'e bankin Gt bank.
Sai gani ina kuka ina masa Godiya jawoni Jikinsa ya yi ya Rungumeni ya na lallashina fadi ya ke" in ban yi miki ba wa kike da shi da zai yi miki?
Kuma gaskiya ya fad'a bayan Allah da su Adda bani da kowa sai Assadiq.
A daran nan mun sha Soyayya kamar za'a rabu da juna har Abada, ban fara siyan maganin Mata ba ammh ina shan Madara da su Fruit.
Washegari da Safe ya wuce da Sassafe, ammh sai da ya shiga cikin makaranta yaga Superversor dinsa sannan ya Dauki Hanyar Abuja.
Kud'in da yace na turama Amma Hamma Isuhu na turamawa nace ya bama Amma sakon Assadiq ne.
Ta kirani a waya ta na ta saka albarka tace shima zata kirasa tunda ta na da Lambarsa ya na kiranta Lokaci bayan Lokaci su gaisa.
Dinkina Telan Ramatu na kaima wa yanzu Tun bayan aurena ita na kaimawa ita kuma tace zata kai masa.
Sai Santin kayan ta ke yi har ta Furtamin tace Assadiq ya iya zab'an kaya masu kyau da yarari.
Da yake akwai kud'i a hannuna da su na yi amfani na Biya kudin Dinki, ina da komai na kayan abinci da abun amfani Assadiq bai taba barina na neni wani abu ba.
Kuma ya na barin min kud'i in zai tafi ban da kitso ko kunshi sai in ina makaranta na Trasport ba na komai da su.
Da yake telan bai da wasa, kwana uku Tsakani ya gama min dinki Ramatu ta kirani tace ya gama nace ta kwatanta masa gidana ya kawomin.
To Ranar da ya kawo min Adda Fati tazo min yini ita da Habiba da yara sai suka ga kayan
Itama ta rika Santi ta na fadin"Kai sun yi kyau Hasiya daga gani suna da Tsada."
Na yi mirmishi ban ce komai ba Habiba ma sai yabawa ta ke yi ta Dauki Material din da aka yi min Doguwar riga mai kyau tace ta na so na Bata Adda Fati ta kwace a Hannunta ta na fadin"Baki da Hankali ne? Mijinta fa ya siya mata kinga ai ya na so ya ganta da shi ne."
Tura baki Habibaa ta yi ni kuma sai nace ta Sha kuruminta zan siya mata in sha Allahu.

Sai da Habiba ta Shiga kitchen ita da Hanif suna min wanke wanke sannan Adda Fati ke gayamin akwai biki a kaduna nan da sati daya da wani abu.
Cikin mamaki yace"Bikin wa kuma?
Kai Tsaye tace"Bikin Babban yaron Baba Jibril na kaduna mana."
Sai da na yi dogon nazari sannan na iya Tuna wai ashe Kanin Babanmu ne Baba Jibril da ni na ma manta da shi kwata kwata a rayuwata.
Cikin Tabe baki nace"Tab daman wai ya na nan? Ni fa inaga tun Rasuwar Baba ban kara ganinsa ba."
Adda Fati tace"Kinsan ai ma'aikaci ne a garin kaduna chan ya ke shi da iyalansa"
Cikin Halin ko in kula nace"to ke waya fad'a miki.?
Adda Fati tace"Amma ta kirani ta fad'amin kuma tace lalle na yi muku mgana mu tafi tare da ku."
Cikin jinjina kai nace"Kaji Amma da wata mgana to ita ina ta sani? Nasan dai ba zumunci suke yi da ita ba."
Adda Fati tace"Tace da ta kira Baaba ta lagos ne ta ke fad'amata ta na nan zuwa bikin kin ji inda taji zencen."
Hasiya ta yi shuru kafin tace"ita yanzu Amma daman dalilin da yasa tace duk ki saka mana lambobin su kenan? To Allah ya kyauta ni kan sai na Tambayi Assadiq in ya barni Shikenan in bar barni ba bazan matsa masa ba."
Adda Fati ta ce"A'a ki dai nuna masa Muhimmancin zuwa kin ji ko?
Gyada kai na yi ammh har a raina ba wai naji ina son zuwan ba ne.
Amma ce ke bani mamaki wanda ya had'a ya raba tunda kuma su ka banzarta damu har da ita ma kanta ammh ta na yin waya duk tace Adda Fati ta saka mata lambobin su.
Da na yi magana nace Allah fa ya Raba wannan zumuncin Tsakaninta da su Baba tanko.
Bud'e bakin Amma sai tace"Allah ya riga ya had'a Hasiya Tunda ya bani ku."
Daganan sai ta kashe bakin  kowa ciki har da ni kaina.

A gidana Adda Fati ta Kira Adda Rukayya ta fad'amata itama bata wani Damu ba tace zata ma Baban Amna mgana in ya amince shikenan
Ita Adda Fati nufinta sai ta tasamu mun tafi tare har ta na cewa Amma tace in muna da kudi mu Had'a wani abun mu je da shi.
Cikin bacin rai nace"Nan fa d'aya ga zuwa ga na biki? Mu uwar me Baba Jibril d'in ya taba yi mana?
Adda Fati da taga bazan gane ba sai ta Kira Amma ta fad'a mata ta kuma ce a bani waya ta dinga yi min nasiha da Fad'an cewa bamu isa mu sauya ma Tuwo suna ba.
Dangin mu ne, ba mu da kamar su saboda haka mu shirya mu tafi a yi sha'anin damu kuma mu had'a wani abun mu kai mu dai mun sauke namu Hakkin da ke kan mu.
Gum na yi ma Amma da taji hakane tace"Kin ji ko Hasiya?
Bani da mafita illah na amsa ma Amma ammh har acikin raina ban yi ra'ayin zuwa ba.
Shiyasa ko a waya ban fara gayama Assadiq ba mantawa ma nayi da zencen kwata kwata.
Sai cikin karshen Satin Assadiq ya zo Tun Ranar jumma'a ni fa in ya na gari mantawa na ke da kaina ma ba wani ba.
Sai ga Adda Fati ta kirani ta kara Tunanin Bikin wannan Satin ne dalilin da yasa kenan na gayamasaa.
Shuru ya yi kafin ya kalleni ya na Fadin"Dama kuna da yan'uwa a garin kaduna ne?
Sai naji kunya da Sauri nace"Eh mana Shi ke bin Babanmu da ya ke ma'aikacin gwammati ne chan ya ke zaune da iyalansa."
Bai damu ba yace"Yaushe zaki tafi? Kuma ke da waye zaku tafin?
Kai Tsaye nace"ni da su Adda Amma tace mu tafi, Adda Fati tace mu tafi Ranar jumma'a sai mu dawo Lahadi da Safe."
Jinjina kai ya yi ya na Tunanin abun ya yi daidai kenan da bikin Salima.
Daman yazo wannan satin ne sati na sama zai ce aiki ya yi masa yawa ba zai Samu zuwa ba.
Saboda Gusau zai yi wannan Weekend din, sai kuma ga wannan mganar tawa sai kawai yaga komai yazo masa da sauki.
Daman nasan bazai hanani ba Duk da shine karon farko da na yi tafiya Tun bayan auran mu bayan wajen Amma da naje sai wannan karon.
Shi dai kawai yace na kula da kaina ne sannan yace wannan Satin mai shiga Daman bazai samu dawowa ba shikenan a raina nace ta kwana Gidan Sauki.
Ranar Lahadi da rana ya tafi, muka rabu kamar kada mu rabu bayan ya bani kudi a Hannuna, na mota da na  Zirga zirga sannan ya cika alkwari ya bani kudin dinki da na mayafin
Wajen maman Suhailat na siya takalmi da mayafin a raina nace kayan da Assadiq ya siyamin da su zan yi amfani a sha'anin kaduna.
Adda Rukayya ta kawo Dubu Biyar nima na ba da Biyar Adda Fati ta saka Biyar sha biyar kenan tace mun je zata bama mai bikin.
Ni na Dauka mu kad'ai zamu tafi ashe Adda ta kira gidan Baba Sammani da Baba Tanko wai in zasu wuce mu tafi tare aiko suna ji dani aciki duk suka zame a cewarsu wlh bazasu hau Mota daya dani ba mota ta kife da su duk su mutu ba.
Ni bansan ma sun yi haka ba sai Ranar jumma'an da na zo gidan Adda tare da kaya zamu tafi Adda Rukayya ke fad'amin dariya kawai na yi kafin nace"Ashe ba su yarda da Allah ba  karyan Musulunci ma suke yi ashe."
Kamar zan ce ma Adda Fati ta daina kokarin chusa kanta a cikin Dangin nan da basa son mu saboda bakin Fentina sai kuma kawai na kyaleta Tunda Assadiq ya koyamin takawa da yakana.
Mu uku kad'ai muka tafi Adda Fati daga ita sai Hanif hakama Adda Rukayya sai Goyonta Yara an bar ma Habiba su ni kuma dagani sai jakata akwati daman a ta Adda Rukayya muka saka kayammu waje daya.
Material din na saka sai na yi amfani da mayafi coffe mai kyau da shi.
Sai na zama kamar wata Baturiya ballatana da na kara fari da kyau.
Na saka d'an kunnayena na da siya wajen Yayar kawata Safiya Ahmad da ya ke ta na harkan Saide saide itama ta Online.
Su kansu yan'uwana sun kalleni sun kara kallona har sun gaji sun Furtamin na yi kyau mirmishi kawai na yi a raina ina kara godema Allah sannan ina kara godema Assadiq domin a sanadinsa na zama Mutum kamar kowa.
Tun muna gidan Adda Assadiq ke kirana yaji ko mun tafi nace masa bamu tafi ba sai ya fara min fad'a da cewa kada mu yi dare a hanya.
Ni kuma sai nace masa ai yanzu Hanyar kaduna Lafiya lau an gama gyara ba wani cikowa ko wani matsala.
Hankalinsa bai kwanta ba sai da ya Kirani nace gamu a tasha har mun shiga Mota zamu tafi, sannan hankalinsa ya kwanta ya yi mana Fatan sauka lafiya.
Shi ko a daidai Lokacin da ya ke kirana saukansa a Gusai kenan ba jimawa Daga Abuja.
Gida ya cika da mutane bakin Shinkafi kwansu da kwarkwata sai Bakin Gammi Ahalin Umma ga Bakin cikin garin Gusai Ahalin Mama.
Ga Ya'yan cikin gida yan nesa da na su ya'yan irin su Yaya subai'atu da su Shahida, Wasu har da guzarin kawayen su da Dangin mazajensu da abokan arzuka.
Kowani Shashi ya cika da Mutane Tunda Ranar suke taron Biki gobe asabar ana Daura aure za'a tafi da Amarya.
Shashensa ma an sauki Mutane sai kawai ya tafi bangaran Abba ya
Showing 81001 words to 84000 words out of 98628 words