da shi Lokaci d'aya ta na fad'in"Baban batul Me yasa ka ke kauce ma mgana da ni ne ?
Ko saboda kasan baka kyauta ma yarmu ba ne?
Kai tsaye ya kalleta cikin kaushinsa yace"Dama na yi mata wani abu ne da ban kyauta ba Murjanatu?
Ta gyara zama kafin tace"Haba baban batul kai ma kasan abunda ka aikata bai kamata ba taya ya mu ke da y'a mace kuma sai ace mu ne zamu je neman aure da kanmu a hanamu sannan daga karshe a bimu da cin zarafi akan yarmu gaskiya Abunda ka yi bai dace ba"
Ta fad'a ranta bace cikin d'an mirmishi ya kalleta kamar bazai yi mgana sai kuma yace"ke kike ganin abunda na yi a zuwan bai dace ba.
Ni kuma ina ganin abunda na aikata a matakin wani babban nasaran da na ke fata nan gaba ne kad'an.".
Cikin mamaki ta kallesa kafin tace"Bangane ba?
Cikin mirmishi yace"Zaki gane ammh ba yanzu ba."
Hajiya Murjanatu ta kura masa ido daman tasan halinsa kuma sai da ta zargi haka tasan baya kwansa sai da zakara.
Cikin kufuluwa tace"Ni dai kada garin son abun duniyar ka ya kara saka ka ka yi tallar ya'ya na, ba rasa masoya suka yi ba ballatana a ci zarafin su.".
Kamar abun arziki yace mata"To."
Ita kuma jin haka sai ta cigaba da Fadin"In da ka nemi shawarata wlh bazama ta kaimu ga haka ba baban batul. Kowa ya tsaya iya matsayinsa ya tsaya iya abokin Huldar ka ta kasuwanci ammh ban yi sha'awar had'a zuru'a da su ba gaskiya."
Kai Tsaye yace"kina da Hujja ne kan haka?.
Rausayar da kai ta yi kafin tace"Ba matakin Rayuwarmu d'aya ba. Gwara kowa ya zauna a muhallin da Ubangiji ya so ya ganshi in za'a yi zumunci to a yi saboda lillahi shikenan Fakat."
Kai ya kad'a kafin yace"Naji Salamatu uwata.'"
Ya fad'a Hankalinsa kwance kamar ba mgana ya daba mata ba.
Jin haka yasa sai bakinta ya mutu ta kasa motsi ballatana mgana.
Shi kuma sai ya sauko daga kan gadon ya na fad'in"Ki ma shirya domin nan da Lokaci kad'an alaqarku zata fi karfin zumuncin da ki ke fad'a."
Ya na gama fad'in haka ya wuce tiolet ya na mirmishin nasara.
Ba zahra'u kad'ai ya Haifa ba ya na da wasu ya'yan in ita bazata iya kaisa ga Nasara ba ya tabbata Mubarak zai kaisa ga nasara watarana.
Tsohuwar nan ta gama Haska masa komai sai yanzu ma ya ke Tunanin Mubarak din nw daidai da Tsarinsa.
Baki sake Hajiya Murnajatu ta bisa da kallo har ya shige cikin makewayin.
Tasan Halin shi wajen son abun duniya da biyan bukatansa ba shi da karaya ko Sarewa.
Ta kuma san duk Saboda kudin da Alhaji Sulaiman ke da shi ne, ta na Tunanin akwai abunda Baban Batul ya ke hari.
Hannayenta ta d'aga sama ta na fad'in"Allah ga ya'yana ka karemin su daga tozarcin duniya da mutanen cikinta."
Ta na shafa addu'ar ya fito daga Tiolet din ya na mirmishi kamar yaji abunda tace ammh kuma ko a Fuska ko fatar bakinsa bai nuna mata yajin ba.
Ranar haka suka kwanta kanzil ba wanda ya kara cema D'anuwansa ita ta na ta Tunanin wannan karon kuma me Baban batul ya ke shirin kara aikatawa?
Shi kuma ya na ta tunanin mafitar da Hanyar da zata bulle da shi in har abunda ya ke Hasaahe ya tabbata.
Daga ganin yadda fuskarsa ta cika da Annuri ta cikin Duhun dakin zakusan ya gama hango nasara mai tarin yawa a nan gaba kad'an.
*******
*ZARIYA*.
Tunda Tahir ya dawo bai kara barin Gefen Sadiq ba ballatana ya samu ya je gidan Hasiya.
Wajen aiki ne kawai kowa ya ke zuwa inda ya cancancesa.
In kuma suka tashi kafin ya samu ya biya gidan Hasiya sai Tahir ya kirasa a waya yace ya dawo gida ya na jiransa ba Halin kuma ya yi masa wata karyar balle ya samu yaje ya Dubata.
Sai dai kullum da Safe in yaje wajen aiki ya na kiranta sau d'aya a rana Domin yaji Lafiyanta.
Duk da ta tabbatar masa ta na lafiya ammh a kasan ransa sai yake jin wani iri da zama da Tahir sai yake jin kamar yafi samun annushuwa in ya na zaune da Hasiya.
Har maganar Laptop dinsa ta yi masa yace mata in ya dawo zai zo ya Dauka.
Bai samu kuma yaje ba sai da aka Rufe sati sannan ya samu ranar da Sassafe kafin ya wuce wajen aiki ya biya ya dauko saboda Tahir sai masa mgana ya ke yi ganin bai saba barin komai nasa a wajen aiki ba.
Bayan laptop bai dauko komai ba, ammh kuma ko bayan ganin Na'uran Tahir bai daina bincikarsa ba kamar yana zarginsa da zama a wajen Hasiya.
Bayan takalma ya lura ba wasu kayan Sadiq har da wata jallabiyansa.
Kai Tsaye ranar da Safe suna shirin Fita wajen aiki Tahir yace"Wai ni ko ina jallabiyar nan taka na daina ganinta ne kwata kwata.?
Sadiq na duke ya na Daure igiyan takalminsa na masu hidimar kasa da gwamamati ke ba su, yau laraba suna da CDS, Hatta Tahir shima shigar kayan su na Bautar kasa ya yi.
Cikin Halin ko in kula Sadiq yace"Wata jallabiya kenan?
Tahir yace"Wacce kace ka siyo ta a Saudiya sanda ku ka je tare da Innani."
Sai a lokacin ya tuna da ita ta na cikin kayan da ya baro gidan Hasiya.
Kasa mgana ya yi shi kuma Tahir bai damu ba sanin Halinsa daman kana mgana yaji kuma ya yi kamar bai ji ba.
Sai kawai yaji yace"Ta bace."
Cikin mamaki ya juyo daga saka rigar jikinsa ya na kallon Sadiq yace"Ta bace? A ina.?
Ba zato kawai Sadiq yaji bakinsa na fad'in"Wajen wanki mana."
Tahir cikin tantama yace"Wajen wanki kuma? Yaushe ka fara kai wanki kai da kace baza ka kara ba shi wanki ba.?
Sadiq ya runtse ido na wani Lokaci bayason ya na karyan nan ba Halinsa ba ne ammh kuma ya zama Dole.
Mikewa ya yi ya na fadin"Eh na ji na gaji ne sanda baka nan shiyasa na ba shi."
Tahir ya gyada kai kafin yace"To ka yi masa mgana?
Sadiq da sauri yace"Sharesa kawai ko an yi mgana ai ba ganinta zan yi ba kasan Halinsa zai ce zai duba ammh kuma shuru zaka jisa."
Tahir yace"A'a da dai ka yi masa mgana yasan abunda ake ciki ko?
Sadiq yace"Tahir ka bar mganar nan kawai kaji."
Tahir kamar bazai yi mgana ba sai kuma ya jinjina kai kafin yace"Shikenan tunda kace haka."
Sai kuma bayan sun gama karyawa zasu tafi Tahir ya duba ma'ajiyar takalmansu yaga har alokacin ba wasu cikinsu cikin Maganarsa yace"Wai baka karb'o sauran takalman ka wajen mai Foolish din ba ne?
Sadiq yaji kamar ya kurma Ihu ya na rataya jakarsa ta baya yace"Naje an ce ya tafi garinsu.".
Tahir ya mike ya na fad'in"What!?
Sadiq ya fice daga dakin batare da ya kara ma Tahir mgana ba.
Shi ko Tahir mamakin Sadiq ne ya kamashi duk da yasan Halinsa na rashin ba ma wasu abubuwan Muhimmanci.
Ko a hanya ma Tahir korafi ya rika yi ma Sadiq na ya rika kula da kayanshi ko don yaga ya na da su da yawa shiyasa baya maida kansa?
Sadiq ya kallesa kafin yace"To Tahir."
So ya ke daganan mganar ta tsaya shiyasa yau yace su hau mashi.
Kowa kuma sai ya nufi inda za shi.
Ya na Office din su na yan Castelia Hasiya ta kirashi har gabansa ya fad'i ya zata ko wani abu ne.
Sai da yaji tace Yaron Adda Fati ne ba lafiya ta na so taje ta gaisheshi in ya bata izini.
Cikin muryansa ta sanyi da natsuwa yace mata duk inda ta ke son zuwa kada ta damu da sai ta tambayesa ya riga ya yi mata izini.
Da tl ya tambayeta ko ta na da kudi? Sai tace akwai wanda ya ke bata bata komai da shi sai ta yi amfani da shi na abun hawa
Da haka suka rabu da juna bayan sun yi sallama.
Sadiq ya yini Tunanin rayuwar da ya saka kansa aciki wato wata rayuwa ya ke yi, wacce kowa yasan ba itace ainihin Rayuwarsa ba.
Har ga Allah Saboda ya taimaki Hasiya ya aureta sannan saboda tsaida kuka da damuwa daga Idanuwan Uwa irin Amma.
Har kuma a zuciyarsa kuma ya na da Niyar sakinta in zai koma gida Saboda rayuwarsa ta zariya dabam ta ke da Rayuwarsa ta gusai.
Sai dai kuma da abun ya matso sai yake jin kamar in ya saki Hasiya bai yi mata adalci ba tunda tun farko bai kafa musu wannan sharadin ba.
Sai yake jin girman abunda ya ke so ya aikata zai iya shafe Ladan Taimakon da ya ke tunanin ya yi mata.
Duk sai ya kasa samun Mafita ya na cikin Tsaka mai wuya gaba kura baya Damisa duk iya hangensa da Tunaninsa ya kasa gano wata mafitan da zata bulle da shi bayan ya saki Hasiya ta kama gabanta shima ya koma in da Rayuwarsa ta dace.
Gashi Sauransu bai fi wata uku ba suna zuwa hutu gida suka dawo sai na tafiya gabadaya.
Ya kamata duk wani taimako da zai yi ma Hasiya ya gaggauta taimakonta cikin wannan wattanin kafin Lokaci yazo ya kure masa.
Suku suku ya yini kamar mara lafiya duk wanda ya yi masa mgana sai yace kansa ke ciwo har gida akace ya koma ammh sai yace a'a saboda yasan ko ya koma banda Tunanin da zai addabesa ba abunda kuma zai iya tsinana ma kansa.
Da ace Hasiya na nan ne sai yaje wajenta ya kwanta ya Huta ammh yasan tunda ta masa waya ya na da Tabbacin ta tafi in da tace zata je d'in.
Kamar ya sani muna gama waya da shi cikin murna da Farinciki na shirya na tafi saboda zumud'in da na ke ciki na fara fitata a karo na farko.
Gidan ba dadi Ummi na makaranta sai dai kuma akwai yan jere za'a kawo amarya a dakin da ke kusa da na Ummi zamu karu mu zama mu uku kenan.
Ban kira Add Fati nace mata zan zo wajenta ba, Amma kawai na fad'amawa da muka yi waya da Safe.
Itace ta tambayeni ko na nemi izinin mijina? Sai na ce mata baya gari.
Ita ta matsamin sai da na kirasa a waya na tambayesa cikin ikon Allah kuma ya bani izinin zuwa duk inda ya kamata.
Dubu biyu na dauka acikin kudin da ke hannuna Dubu shidda ne daman a hanya na tsaya na siyama yaran Biskit sannan na karisa koda naje ma Adda Fatin bata nan taje kai Hanif asibitin madarkaci ta yara Habibun ne kad'ai a gida sai da na zauna na jirata sannan.
Sai dai ta dawo ta ganni kamar Daga sama ko da bata fad'a ba sannan taji Dadin ganina.
Hankalina kwance sannan har kiba nayi, Hanif yaji sauki zazzabi ne da Mura na ba su Tsaraban su shi da Hanifa sai bayan azahar Habiba ta Dawo daga makaranta ta na ganina ta Hau ihu ta zo da gudu muka Rumgume juna.
Adda Fati na gefe ta na mana mirmishi.
Ranar ni na yi mana girkin rana har miyan tuwon dare ni na Daura mata, Sai kallona Adda ta ke yi ta na mirmishi ganina cikin natsuwa da walwala kuma hakan ya na nuna ina cikin kwanciyar Hankali a gidan aurena.
Mun sha hira duk da rabin Hiran na Amma ce ina ta ma Adda Shagwaban ya kamata mu shirya muje mu Duba Amma, Adda Fati tace Amma tace kowaccen mu ta zauna gidan mijinta ta yi biyayyan Aure ita lafiyanta kalau.
Ba ni da tacewa tunda nima haka Amma ta fad'amin ammh mganar gaskiya ina kewarta sosai ina kewar cinyarta in da na ke kwanciya naci kuka na har sai na koshi.
Sai da biyar ta gota ne Adda Fati ta fara min mganar na zo na shirya na tafi gida.
Ina Tura baki nace"Kai Adda kamar ki na kora na? Duba fa agogo shidda ma ba ta yi ba"
Adda Fati tace"To kafin ki shirya ki fita ai shiddan ta yi kuma kinga in yamma ta yi wahalan abun hawa."
Jin haka yasa Sai ban yi gaddama ba naje na shirya na fito ina ce mata zan tafi sai taje na jira Habiba ta Dawo taje siyomin kayan miya ne da zan tafi da shi.
Sai na zauna saman Hannun kujera ina Fadin"Ina so naje gidan Adda Rukayya ina tsoro."
Na fad'a cikin wani yanayi Adda Fati ta kalleni kafin tace"Kada ki je yanzu ki bari sai nan gaba."
Kai na jinjina mata kafin nace"Shikenan gobe sai naje gidan Ramatu na yi mata yini."
Adda Fati ta kalleni cikin mamaki kafin tace"Gobe kuma?
Na gyada mata kai ina yar dariya cikin Harara tace"Baki da Hankali ne? Ai sai ki bari a kwana biyu ko Hasiya?
Kai tsaye na fara bata labarin yadda muka yi da shi a waya yau da Safe.
Sai ta jinjina kai kafin tace"Baya gari kenan?
Da kai na amsa mata alamun Eh kai Tsaye ita kuma tace"To wani gari suke zuwa shida megidan nasa?
Na yi shuru kafin nace"Wlh bansani ba Adda."
Adda Fati itama sai ta yi shuru sai a lokacin ta fara wani tunani anya ba su yi kuskure ba? Ba su san komai fa da ya Danganci Abubakar ba kuma ba'a aure cikin Duhu.
Ni kuma iya gaskiya ta na fad'a mata tunda bai taba fadamin ga inda suke zuwa ba, muna cikin hakane sai ga Habiba ta kawo min kayan miyan sai na mike ina ma Adda Fati sallama.
Har kofar gida ta rakani har na fita sai ta saka baki ta kirani na juyo na dawo kai tsaye tace"Kun yi mgana da shi akan ya kai ki chan garin na su ki ga yan'uwansa?
Shuru na yi kafin nace"Eh yace zamu je ammh ba yanzu ba."
Adda Fati tace"Ba yanzu ba sai yaushe?
Kai tsaye na kalleta kafin nace"Bansani ba Adda."
Sai kawai ta girgiza kai kafin tace"jeki Allah ya tsare sai mun yi mgana."
Da haka na wuce Habiba ta rakani na samu mashin tunda yafi sauki muka rabu ina ce mata ina jiranta wannan Satin ranar da ba makaranta.
Maganar da Adda Fati tamin ya tsayamin arai nima kuma sai naga ya kamata zuwa yanzu nasan waye na ke Aure.
Duk da auran namu bai gama cika matakin kowani aure ba, ammh dai akallah tunda an kwarari wattani ya dace ace yan'uwansa da suka Rage masa su san da ni.
Irin yadda ta min mganar haka ma Ramatu ta min washegari da na je mata yini.
Duk da ban fito na bayyana mata baya kwana a gida ba na, in kuna ya kwana to muna mabambamtan muhalli.
Ammh itama ta nuna min zuwa yanzu ya kamata na san wanda na ke aure sannan kuma yan'uwansa suma susan dani.
Da farko bana wannan Tunanin ammh sai da Adda Fati da Ramatu suka ankarar da ni sannan na ga cancantar haka.
Na kuma kuduri niyar zan masa mgana ya kai ni garinsu naga Danginsa.
Abun sai kuma ya fara Damuna acikin raina haka ma Adda Fati ita Damuwar nata ma guda biyu ne, na rashin sanin takammman Sana'an da Abubakar ya ke yi.
Damuwar ta bayyanan mata har a saman Fuskarta har sai da Baban su Hanifa ya fahimci ta na da Damuwa sai ya tambayeta.
Cikin damuwa tace"Baban hanifa Sai yanzu na fara tunanin anya bamu yi kuskusren biye ma Amma ba?
Kai tsaye yace"Kuskuren mene?
Cikin Alhini tace"kan mganar auran Hasiya da Abubakar. Ka duba ka gani bamu san komai a kanshi ba babban abun tunanin ma bamu san sana'arsa ba ya dai ce shi mutumin Shinkafi ne sannan karatu ya kawosa nan da kuma Buga bugar sana'a."
Habibu ya yi shuru bai ce komai ba, ya na nazari kafin ya nisa yace" Yanzu me ne mafita?
Adda Fati tace" Na rasa mafita kaina duk ya kulle mun yi mgana da Hasiya ta ce itama batassn ina ya ke zuwa sana'ar tasa ba, kuma maganar ya kaita taga danginsa yace ba yanzu ba to sai yaushe? Tunda an riga an zama Daya, ai yakamata ya kaita ta ga Ahalinsa tasan wanda ta ke aure."
Habibu ya jim kafin yace" Nima da farko da naji mganar auran Hasiya sai da wannan tunanin ya fad'omin sai dai jin abun daga Amma ne yasa ban ce komai ba ammh mafi a'ala acikin aure mu bi dokikin da Annabi muhammadu salallahu alaihi wasallam ya sanar damu ya yin bada auran ya'yanmu sana'a da sanin mu'amala tare da sanin Ahali shine ginshikin aure."
Adda Fati sai ta zabga Tagumi ta kasa mgana sai a yanzu ta tabbatar ma kanta sun yi kuskure Halin da Amma ta ke ciki na Tsaka mai wuya shi ya kaita ga yanke wannan Hukuncin da zai shafi rayuawar Hasiya gabadaya.
Habibu ya dinga lallashinta da ta kwantar da Hankalinta ba abunda zai faru sai Abunda Allah ya so.
Za'a bincika har chan shinkafin domin a san ko waye shi ammh yanzu dai Hasiyan ta fara matsamai sai ya kaita garinsu tasan Yan'uwansa.
Da wannan shawaran na Baban su Hanifa ta kirani da Safe ta na gayamin na matsamai sai ya kaini chan Shinkafi na had'u da Danginsa.
Ni dai sai na bita da toh kawai bani da wani zabi sai dai ta yadda zan yi masa mganar ne na rasa yadda zan yi.
Kada yaga kamar na nuna zakewata da yawa ne.
Adda Fati sai ta yi karambanin kiran Adda ta sanar da ita tunanin da ta yi Adda kuma ta bata goyan bayan cewa ya kamata a bincikan aure ba mganar wasa ba ce kuma tun farko da Amma ta yi shawara da ita baza'a yi auran nan sai su san waye Abubakar da abunda ya Dangancesa gudun auran wanda bai dace ba.
Adda ce bayan sun gama mgana da Fati ta sanar da Amma komai da kuma yadda Adda Fati tace Hasiya zata matsa masa ya kaita chan shinkafi in ya nuna ba yanzu ba sai a tada wani yaje chan ya bincika ya gani.
Amma na jin haka ta saci idon Adda lokacin da ta shiga makewayi ta kirani a waya ta gargad'eni kada na sake na matsama Abubakar kan maganar sai ya kaini garin su domin naga yan'uwansa na bari in har shi da kanshi ya yi min maganar sai na shirya ya kaini.
Cikin mamaki nace"Amma me yasa? Ai ya na da kyau nasan komai game da shi"
Cikin kaushin Murya Amma tace"In lokacin da yakamata ki sani ya yi zaki sani Hasiya. Kada ki matsa ma kanki kan sanin abunda ba'a so ki sani ba. Zaki iya zuwa kisan abunda zai iya hana ki zaman lafiya ki jira shi Lokaci da ya so ki san komai a kansa shi
Showing 36001 words to 39000 words out of 98628 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13 Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33