jikinta na Shadda ta na fad'in"Bari na kara kiran su Umma."
Daga haka ta fita daga Falon Innani ta koma chan gefe ta na kiran Wayar Salima ammh sai aka gayamata ta na amfani da wayar.
Karamin Tsaki ta ja a ranta ta san Da angon Salima ke faman wayarta na kwazzaba, sai ta maida Akalan kiranta wajen kiran Sajida.
Kira daya ana Biyu ta Dauka cikin magana a hankali Surayya tace"Sajida ya naji shuru ne? Zasu fa tafi"
Da Sauri Sajida dagachan Bangaren tace"Laa gamu nan mun gama Saddiqa ce kinsan zata Tukami ta ci kayan Fulawa ta barke da zawo yanzu haka ta na Tiolet."
Surayya tace"Subhanallah ku kariso sai tasha magani. Ku yi sauri don Allah ko kuma ku ba ma Su Siyama kudin adaidaita su hayo da kayan su kawo mana don Allah Sajida."
Sai ta amsa mata da to shikenan sannan suka katse wayar.
Tana juyowa suka had'e da Sa'ima da Sauri tace"Sun ce fa kada su yi yamma ga hanya ba kyau."
Surayya tace"Wai Saddiq ce ke gudawa ammh nace su ba ma su siyama sakon su hayo adaidaita."
Sa'ima tace"Asshaa. Allah ya sauwake."
Tare suka koma cikin Falon Innanin, suka kara bama bakin baki da su d'an kara jira kad'an don Allah.
Innani ta tabe baki kafin tace"Wai kuna ta su jira su jira to su jira Uban me Tunda sun kawo kaya an karb'a kuma tsakani ga Allah sun ci sun sha ai sai kuma ku bar su yi haraman tafiya in ba so kuke su kwana anan ba."
Umma ce ta yi saurin cewa"Ai yanzu zasu tafi Innani."
Harara Umma ta samu kafin a tab'e mata baki, Allah ya takaita abun bata kara mgana ba sai dai ta fara Rage fara'a s ta na ta yamutse Yamutsen fuska kamar taga kashi.
Kafin su Siyama su kariso Surraya ta kira yafi sau biyar sai chan suka kariso Ita da Sultana Dauke da Botikai duk an yi rapping din su da Farin Salatif.
Yan mata Biyu ne suna kuma Sanye da kaya iri d'aya, Doguwar itace Sultana ta na sanye da Atamfa mai Ruwan green shi yasa mayafin su ma kalarsa kenan ita kuma Siyama bata da Tsawo ammh kuma ta fi Sultana jiki.
Da sallama suka shiga Falon Innani sai kallo ya koma kansu, har kasa suka gaida baki, su kuma suka amsa baki har kunne su a tunanin su d'aya daga cikin ce surukar ta su, Surayya da Sa'ima suka karb'i botikan da suka zo da shi suka Tura gaban bakin suna fadin na su ne.
Ba damar suce bazasu tafi da shi ba Tunda sun ce domin su aka yi sai suka Fara Godiya.
Sultana ce ta fara mikewa zata fita Saboda kallon da ake ta yi mata sai ta Tsargu, ita kuma Siyama har hankalinta ya tafi kan ganin kayan da akwatin da suka fara Daukan idanuwanta.
Sultana na mikewa kanwar hajiya Murjanatu ta kalli Umma cikin Dariya ta na fad'in"Ma sha Allah nace Hajiya wance ce surukar tamu ko?
Ta fad"a Lokaci d'aya ta na nuna Sultana da ke tsaye suna mgana da Surayyah.
Kamar Innani daman ta sani kasa kunni daman ta na gefen su cikin zabura tace"Wace? Wai sulsana?
Ta wani kyabe baki kafin yace"Ahir ba ita ce bace surukar taku wannan da kike gani jikata ce itama bikinta saura wattani kad'an ita zata auri babban Jikana magajin wannan gidan, shima domin kinsan magajin gida da kafiya ne yaki bari a had'a sha'anin ai da tare za'ayi, ita surukar taku da kike mgana zaku ganta wata figaggiya haka da iyayi da feleke wata doguwa haka dai to itace salimar ai bata shigo ba ne ko , ke Siyama ina kuka baro yar'uwan taku ce?
Ta fad'a ta na Daga Murya, Umma dai sai ta bige da mirmishi.
Matar ba ta damu ba ta yi ta fatan alheri.
Umma ta amsa da Ameen ta na fadin"Bayan an yi na Salima da wattani biyu za'ayi na su. Sadiq din yaro na ne ita kuma Sultana yar kanwar megidan ne tun ta na karama ta rasa mahaifiyarta sai na karb'ota na riketa a wajena."
Cikin jin dadi matar tace"Dakyau Tuwo na Maina. Allah ya nuna mana Allah ya sanya alheri."
Duk yadda suka so su ga Salima ba su samu ganinta ba saboda sun ce yammah suke gudu ga nisa.
Ita kuma tana gidan Surayya suna tare da su Sajida sai bayan tafiyar su suka Dawo gidan Saddiqa duk ta zurma Saboda gudawa sai da ta sha mgani.
Nan fa suka baje ana ta kara ganin kaya ana yabawa da kokarin Mubarak da cewa ga shi ya gama gininsa sannan kuma ga kayan aure na gani na Fad'a, Salima na gefe ta na ta latsa wayarta Siyama na ta mata kwakwazon tazo taga kayan aurenta.
Cikin Yamutsa fuska tace"Ke je ki yi ta gani, ni na san komai da ke ciki tun tuni."
Sai falon na Innani ya Dau Ihu da Shewa sai taji kunya da ta ga sun had'a ido da Umma sai ta tashi da gudu ta fice Mama ta bi ta da cewa"Salima kenan an gama ni karatu zan yi."
Dariya suka kara sakamata Sa'ima ko sai faman Turama su shahida ta ke cikin Family group din su na SS SHINKAFI'S.
Inanni na gefe ta gaji da iface ifacen da suke mata a falo ta fara masifa ta na fadin"Wai meye haka? Kun zo kun cikamin Ihu a falona ku kwashi kayan ku don Allah ku ficemin a daki zan kwanta ne na Huta."
Umma ce ta fara bata hakuri ta kuma Umarci su Surayya da suka kwashe akwatinan zuwa bangaren Mama.
Innani na jin haka sai ta sauya mgana tace a kai cikin Dakinta sai Sulaimanu ya Dawo ya gani.
Gudun fitinarta yasa akayi mata abunda ta ke so harta y'an ya'yansu Innani sai da ta tarkasu tace zata kwanta ne ba d'an jikan da zai Takura mata ita da gidan Danta.
Sai taron ya koma Falon Umma har da Mama da Sauran yan'uwanta ana ta Fira da shewa.
Alrady daman abinci da yawa aka yi  shiyasa sai ya zama ba su da yunwa.
Shiryen shiryen bikin kusan duk an kamallah hatta kayan dakin Salima an gama siyan komai ba ma ita ba Har Sultana abu kad'an ne ya rage yanzu haka.
Daman hausawa sun ce duk abunda aka sanyama Lokaci sai yazo, ga shi har auran Salima da Mubarak yazo, kuma cikin ikon Allah ya gama gininsa nan kusa da gidan iyayensa.
Sannan kuma ya ce Salima zata cigaba da karatunta tunda Burinta ne.
Kuma Saboda auransa ta b'ata Shekara daya gida a zaune bayan sun gama jarabawar SSCE.
A yayinda yanzu su Sultana na First semester ne na SS3, ita da Siyama da yanzu suka kara zama manya yan mata wad'anda keranci Budurci ya gama kere su gabadaya.
Da bikin Salima ya taso Umma da sauran yayyen Sadiq sun so a had'a auran nan Lokaci daya ammh yace daman Shi Tun farko bai ce za'ayi bikinsa Rana daya da Salima ba.
Tunda shi Magajin gida ne sai aka yi masa abunda ya ke so.
Da kuma Dalilin da yanzu ya na kula da Sultanan sosai yasa ba wanda ya taba wani Tunani.
Suna waya sosai in dai zai zo daga Zariya yana siyomata tsaraba na kayan kwalliyar mata kuma yace in dai tana bukatar wani abu ta gayamasa zai yi mata.
Kashe mata kudi ya ke tuni Abba da Umma sun daina mata wasu walwalahu Tuni Sadiq ya cike wannan bangaran.
Shi kuma abunda ba su sani ba ya yi mata adalci ne, kuma ya na yin hakane saboda kada ya bada kofar da za'a fara Zargin boyayyiyar Rayuwarsa.
Sauran yan'uwansa kuma sun masa uzuri da cewa ya fara aiki a Abuja a bari ta cewarsa ya samu natsuwa sannan ya Fahimci in da ya ke aiki kafin a yi auran na su.

*********

*Abuja.*
_EL-Rufa'i & Patners, 24 Aminu road Kano cresent Abuja Nageria._
Monday.

Zaune ya ke acikin Office sabon office d'insa tunda yau litini aiki garesa kaca kaca, hankalinsa ya kasu kashi biyu ne daya na kan na'urar da ke gabansa d'aya kuma na kan wata Takardan dake gabansa.
Sanye ya ke da Suit baki da Fari ya sasauta tektie dinsa saboda ya samu Saukin ayyuka.
Ya na aikin ya na sakin mirmishi shi kad'ai da ya tuna wayarsu da Siya yau da Safe. Shagwaba ta ke masa ko yace kukan banza saboda ya sakamata rai zai zo mata weekend sai bai samu zuwa ba.
Saboda akwai wasu ayyukan da ya tsaya yi, yasan kuma in yaje zariya bazai taba iya aikin nan ba in dai ya na ganin Hasiya.
Kuma a yadda bai jima da fara aiki ba, bazai yi wasa ba ballatana aga kamar ya fara wasa da aikinsa.
Kamar zariya gidan haya ya nema anan kusa da inda kamfanin su ya ke zaune.
Tunda aikin ya zo masa ne bagatatan, ya jima da Tura CV Dinsa bai kuma taba saka ransa ba shi mutum ne mai amfani da duk abunda ke Hannunsa.
Ya yi mamaki sanda yaga Sakon Email dinsu suna nemansa, kuma har yazo Abuja interviuw bai gama sakankancewa da zai samu aikin nan ba sai ga shi kafin ya Dawo ma sun bashi accpeted letter.
Kamar kuma Sun san ya siya mota da kud'in da ya tara zai siya, da ya gayama Abba sai ya cika masa ya siya toyota kirar 406 da ita ya zo Abuja nan sannan achan Zariya da ita ya fara zirga zirgan zuwa wajen aiki da Shiga makaranta duk da yanzu Project ya ke yi ya ma kusa gamawa.
A shekara daya da Rabin nan ya yi ta kokarin boye sirrin auransa da Hasiya, ya kuma tare duk wani hanya da wani zai Fahimci wani abu ciki harda yan'uwansa da Tahir shi kan shi.
Yana cikin wannan Tunanin yana aiki Wayar Big sis ta katse shi.
Dole ya ijiye komai ya Dauki wayarta suka gaisa.
Mganar kayan auran Sultana ta yi masa Abba ya ba da miliyan Biyu a had'a mata kayan aure.
Bai yi mamaki ba sanim Daman auren Sultana na gata ne a wajensa.
Auran Hasiya ne ya yi shi da Guminsa.
Kamar yace ta siya komai guda Biyu sai kuma ya fasa sanin abunda zai jawo sanadin subutar bakinsa.
Cewa kawai ya yi su yi mgana da Sultana sai Surayya tace shima Abba yace a yi masa a kwatinsa.
Dariya kawai ya yi yana kara jin Kaunar Abba a ransa.
Shi yasa bai yarda ya kwanta Saboda mahaifinshi na da kudi ba.
Abunda ya sani shine Abba ya tara musu kudi shima zai tarama ya'yansa Saboda yau in Abba ya fadi ya Mutu ba shi kadai zai gaji wannan dukiyar ba, ya na da Sauran yan'uwan da suma suna da Hakki a kan Abba.
Dakyar ya aminta da karb'an gidan da Abba ya ba shi hakal malak a Million Quaters dake garin Gusai.
Anan za'a saka Sultana kafin ya samu inda zai ijiyeta anan garin Abujan
Ammh har acikin ransa a zariya ya ke da Niyar barin Hasiya saboda wasu Dalilansa.
Itama ya na so ya had'a mata lefe duk da ya siya mata wasu kayan, ammh zai bari sai bayan auransa da Sultana tukunmah sai ya had'a mata da Jarin da zata fara sana'a da shi.
Sannan rayuwar da ya ke yi ta Sirri duk ta fara isansa sai dai ba shi da mafita ne.
Hasiya ta zama wani bangare na Rayuwarsa da har Abada bazai iya rabuwa da ita ba.
Shiyasa duk mafitan da ya hango sai yaga gwara ya cigaba da yin Rayuwa guda Biyu a lokaci daya domin tsira da abunda ya ke so da Muradi.
Tunda yanzu ya Fahimci ba wai mganar Tausayi ba ya na son Hasiya.
Yana son Siya irin kauna mai zafin da zai iya aikata komai domin yaga ta na Kusa da shi har gaban Abada.
Dalilinta ya samu natsuwa ta magidanta maza ma su aure, ko gida yaje haka su surayya zasu rika mganar ya kara kiba ya yi haske kamar ba shi ba.
Shi kanshi yasan natsuwar aure na Dabam ne.
Kuma Hasiya ce sanadiyar zamowarsa cikin wanman natsuwar da a koda yaushe bata gajiya da shi in yazo da bukatunsa zata killacesa har sai yaji ta ishesa.
Ba zai ce baya son Sultana ba, ammh Siya ta mamaye kaso mafi rinjaye acikin zuciyarsa.
Ya tuna kwanaki kad'an ya rage asirinsa ya Tonu kafin samun aikinsa na garin Abujan nan ne.
Suka fita cin abincin daren da suka saba da Siya duk karshen mako.
A wani  restaurant  dake zariya wani abokin karatunsa anan Abu ya gansu shi har ga Allah bai gansa ba.
To da yake gayen suna mgana da Tahir ta facebook kuma yana da lambarsa nan da nan ya kirasa ya na Tambayarsa Sadiq ya yi aure ne?
Tahir yace"A'a."
Sai yace ai ya gansa da wata mace anan zariya kuma a yanayin da ya gansu kamar dai in ba mata da miji ba to ba'a fad'in d'ayan.

Tahir ya yi mamaki sosai nan da nan ya kira Sadiq ya na tambayansa.
Shi kuma sai ya tuna Fitansu, ammh sai ya nuna ma Tahir ba shi aka gani ba Domin shi bai ma fita ko'ina ba.
Tahir kamar yaso ya Fahimci wani abu Tunda har alokacin Sadiq bai bari ya Fahimci inda ya ke zaune a zariya ba in yace zai zo sai yace ya na Gusau
To da yake Yanzu Tahir ya yi karfi a siyasa Dan majalisan garinsu ya bashi Shugaban matasan garin Daura na kafafen Sada Zumunta.
Sannan kuma ya Dauki nauyin Cigaban karatunsa a jami'ar  Alkalam da ke katsina. Kuma ya na koyarwa a wata makaranta Sakandirin gwammatin garin.
Gabadaya dai baya samun zama Shiyasa bayan komawarsu gida bai fi sau biyu suka had'u ba sai dai ta waya suna mgana sosai tunda yawancin Tsarin Bikin Sultana Tahir ne Jagora.
Ammh duk da haka sai da Tahir ya Tsaresa da tambayan ko dai bai rabu da Hasiya ba ne?

A lokacin sai da gabansa ya fad'i cikin Basarwa yace"Wata Hasiya? Ni har na manta da ita ma, inaga kamar ta koma wajen mahaifiyarta ma."
Tahir ya ce"Sadiq ka kula. ka sani in har kana wani abun ne ka Boyemin wlh Ramar da ta kwabe maka ba Ruwana Sadiq."
Maganar tahir ta jima na mai yawo acikin kansa ya sani watan watarana bai isa ya Boye wannan abun ba.
Watarana kowa zai sani.
Sai dai ranar ce ya ke jin Tsoron zuwansa, tunda dai abu d'aya ya sani Ruwa da iska ba su isa su Raba  shi da Hasiya ba.
Itama Matarsace da Aure ya ba shi ita.
Ga auran salima ya na Tunanin yadda zai yi da Siya, wannan karon karyan Wajen aiki zai yi mata in yana so su Rabu lafiya saboda yaga ta fara Fahimtar ya na Boye mata wani abu.
Ajiyar zuciya kawai ya ke saukewa a Jejjere kamar na wanda ya tashi jinya.
Sai kuma ya koma kawai ya jingina da Kujerar da ya ke kai.
Fuskar Siya ya ke gani ta na gilmasa, kirjinsa ya ke shafawa a fili ya Furta.
"I MISS U SIYAAASSADIQ..."








*Janafty*
*TMWB2K018*

*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*

https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk

Ku zo ku yi sayayya tare da Yar Gidan Imam cikin aminci da kwanciyar hankali komai akwai harda kayan gyaran jiki hamshakan mata na supliments kala kala wanda ba su da illa, akwai kuma gagarumin haɗin mu na Arabian sabaya powder wanda babu kamarsa wannan ba irin sabayar da ki ka saba gani bace, kayan kicin dogayen riguna kuwa ba'a magana ke dai ki yi sauri ki shigo domin kwasar roman wadannan kayan.

Sai da ya kwashe kimanin Sati Shidda a garin Abuja sannan daga Abujan Ranar al'hamis  ya fara sauka a Gusau, tunda ya fi masa sauki yaje Zariya daga gusau sannan Daga Zariya ya koma Abuja.
Yaje Gusau lokacin Saura Sati Biyu Bikin Salima da Mubarak ya iske gida cike da yan'uwansa mata na kusa Tunda Bikin ya karato nan suke yini.
Daman tunda ya dauki albashinsa na Farko ya yi wani Tunani a ransa.
A wani kanti ya tsaya ya siya ma Abba Agogo mai Tsada da Hula Zanna Bukar sai Bakin Takalmi sahu ciki masu kyau da yarari sai Turaren maza mai kamshi.
Sannan anan yaga wasu lesuka masu kyau guda biyu sai ya siyama Umma D'aya Mama guda d'aya, Innani kuma sai ya siya mata Atamfa mai kyau mai Taushi.
Ya so ya siyama Siya wani abu ammh kuma sai da ya yi wani Tunani sai ya fasa, wani abu dake damunsa shine duk abunda zai gani na kwalliyar mata baya hasaso kowa aciki sai Siya, Sultana bata cika zuwa ransa ba.
In ya yi tunanin kada in ya auri Sultana ya kasa adalci a Tsakaninsu sai wata zuciyar ta fad'a masa cewa Saboda Ita Sultana ta na da gata ne Hasiya kuma ba ta da kowa sai shi.
Da wannan Tunanin na zuciyarsa ya kauda Tunanin bazai iya yi ma Sultana adalci ba.
Duk da ya taso cikin jin dadi sannan bai tab'a neman wani abu ya rasa ba, duk da mahaifinsa na da kudin da yafi karfin komai a gidansa shima a matsayinsa na Namiji tilo kwara daya da iyayensa suka haifa ya na da Buri da Niyar kyautata musu da d'an abunda ya ke samu.
Shiyasa tun ya na aiki da wannan kamfanin na zariya in dai zai je gusau baya zuwa Hannu Rabbana duk abunda ya gani a hanya sai ya siya ya kai gida, Abba ya sha fad'an cewa sunan Magajin gida da Innani ta saka masa ba iya suna ba ne, suna ne da ya ke binsa har jinin jikinsa.
Ko Yan'uwan su na Shinkafi bai manta da su ba in ya samu ya kan Turama Auwalu kudi ta bankinsa yace ya ba ma Baba Sammani ya raba shi da su Goggo Husai.
Ko wannan karon ma 50k ya Tura musu yace su raba a tsakaninsu, haka suka kira sa suna ta yi masa Godiya da Fatan Allah yasa ya gama lafiya sai dai su kira Abba su ce Sadiq ya yi musu kaza kaza da su ba su sani ba.
Shiyasa har abadan Abba baya Nadamar Fifitar kaunar Abubakar acikin ransa domin D'a ne mafi soyuwa acikin duka ya'yan da ya Haifa.
Sanda ya ba ma Abba abunda ya siya masa sai da idanuwansa suka ciko da kwallah cikin Tsananin Farinciki a muryansa yace"Allah ya yi maka albarka Abubakar, Allah ya albarkaci Samun ka Allah ya Tsare ka a duk inda ka ke Allah yasa a fi haka."
Sadiq ya amsa cikin mirmishi Abba ya kara kallon kayan sannan ya jinjina kai ya na yar dariya.
Shi alheri ya na da dadi, sannan kuma koda
Showing 78001 words to 81000 words out of 98628 words