sai na Dauki na Fatam na bi bayansa.
Ya fito kenan muka kusa cin karo, da Sauri muka kalli juna kafin ya yi mgana na rigasa da cewa"Sannu da zuwa." Bai amsa ba abun Hannuna ya karb'a Lokaci daya ya na fadin"Yarinyar nan na Lura baki jin mgana ko?
Sum sum na wuce zuwa Falo na samu kujera na zauna.
Shima ya kai sannan ya fito da bakin lemu ya zo ya ijiye nima ya Daukomin Fanta ya bani na karb'a.
Cikin dakin ya koma sai gashi ya Fito da karamar Na'urarsa ya koma ya zauna ya kunnata.
Ya na aikinsa lokaci bayan Lokaci ya na shan lemunsa.
Sannan sai ya kalleni ya kauda kai har dai yaga ban sha lemun ba ya min mgana sai na Dauka ammh na kasa Budewa duk ya na kallona.
Bansan ya taso ba sai ganinsa nayi a gabana kawai ya mika Dogon hannunsa ya karb'a ya bud'emin sannan ya maidamin ya na fad'in"In nace baki da karfi sai ki ga kamar ban fad'i gaskiya ba."
Baki na Bude kafin nace"Laa..!
Bai barni na karisa ba ya saka hannu ya rike hannuna ya Tura lemun a bakina sai da na kurba sannan ya saki hannuna ya koma ya zauna da wani kallo na bisa, shi kuma bai kara kallona ba ya cigaba da abunda ya ke yi.
Muna nan zaune yana aikinsa ni kuma ina faman kallonsa, Fanta kad'an na sha Saboda gas kada ya rika tasomin bayan na kwanta, Shi kuma Tas ya shanye coke dinsa sannan ina gani aka kira wayarsa kamar bazai Dauka ba sai kuma ya tashi ya na kallona ta gefen ido ni kuma sai nayi kamar ban gansa ba.
Fita ya yi waje inaga ya yi wayarsa sannan ya dawo ya cigaba da abunda ya ke yi ganin yamma na yi ne yasa na tambayesa me zamu dafa?
Ya yi shuru sai kuma chan yace kada na Dafa komai tukunnah.
Bamu muka tashi daga falon nan ba sai da aka kira mangariba ni ce ma da nagaji da zaman na d'an kishigid'a.
Sai da ya juyo ya ganni ne yace min na tashi na zauna an kusa kiran mangariba.
Shi fita ya yi masallaci ni kuma sai nayi nawa a gida, bai dawo gidan ba sai bayan isha'i da ya dawo wanka ya Sakeni ya sauya kaya zuwa wani Saukakken yadi ni kuma yace na yi wanka zamu fita ne.
Ban musa ba na shiga na yi wanka na sauya kaya zuwa wanda na dinka da Auran mu, na saka farin Hijabina shi ya Kulle Dakin muka fita.
Bai gayamin ina zamu ba sai da muka hau adaidaita muka isa sai naga An Rubuta Usmaniya Restaurant.
Karo na Farko da na Taba zuwa Restaurant a rayuwata kenan
Dare ne ammh kamar rana mutane sai harkokinsu suke yi.
Ga masu zuwa cin abinci nan birjit wasu irin mu wasu kuma su kad'ai.
Zabin abunda zan ci ya bani sai na rasa me zan ci sai nace a bani White Rice da Miya.
Shi kuma sai yaci chips da Maltina kawai ya ce ni bazan ci chips din ba? Sai na girgiza masa kai.
Bai kara mgana ba sai ya yi mgana aka kawomin Ferfesun kaza sai da aka kawo naji kunya tunda muna cikin wani babban Falo ne ga mutane suma duk a zaune sai dai kowa ya na Harkan gabansa ne shiyasa nace masa bazan ci ba.
Harara ya sakarmin kafin yace"Duka zaki cinye tunda ba asaran kudina zan yi ba."
Ba wasa a mganarsa yasa na fara ci kad'an kadan.
Lemun Holladian ya ce a kawomin tunda yaga ban cika shan masu gas din nan ba.
Karshenta dai sai da kowa ya watse ya barmu ina ta cin abinci sannu sannu.
Ga shi cikina ya cika na kasa cinye Ferfesun kazan shi kuma tuni ya gama yana gefe ya yi fuska a bunsa.
Ganin haka yasa na kira sunansa"Assadiq."
Juyowa ya yi ya na kallona bai amsa ba ganin haka yasa nace"Na koshi wlh."
Zai yi mgana saurin na kara cewa"Wlh kalli cikina".
Gani ya yi kamar ina kokarin Bud'e masa cikin yasa da Sauri ya mike yace mu tafi.
Muna tare da shi ya ciro walet dinsa ya ba su wani kati kamar dai Atm ne suka cire kudinsu.
Mun fito daga wajen kenan yana tafiya ina gefensa sai faman kalle kalle na ke yi ina kara kallon wajen chan garin kallon na ci Tuntube na kusa fad'uwa sai da ya tareni.
Cikin Tsareni da ido yace"Me ki ke kallo haka?
Cikin Sauri nace"Assadiq ina ne nan?
Sai da ya sakeni sannan ya rikemin hannu muna tafiya zuwa bakin Titi yace"Kina jin ana cewa kango?
Sai na gyad'a masa kai shi kuma ya Cigaba da fadin"Nan ne kango"
Kara bin wajen na yi da kallo ina fadin"Wajen da na kyau."
Bai yi mgana ba sai ma kokarin tsaida mana da abun hawa da ya ke yi.
Mun koma gida tara da wani abu na dare gashi na koshi da yawa shiyasa muna komawa na yi shirin kwanciya shi kuma sai da ya kara yin wanka ni har mamakinsa na ke yi baya gajiya da wanka ne?

A falo ya kwana kamar yadda muka Saba da Safe kuma shi ya fita ya siyo kwai na soya mana sanin bayason karni yasa na saka ma kwan kayan kamshi irin su citta da Tafarnuwa.
Muka sha Tea tunda ya siyo mana Buredi mai taushi.
Da rana kuma yace na yi masa Danwake da salat mai kwai shi na yi mana muka ci muka koshi Tuni na manta da su Ummi ban kara bi ta kansu ba Tunda ba na fita koda yaushe muna cikin Daki tare shima in ya Fita sai dai in za shi masallaci ko zai fita siyan wani abu.
Da daddare kuma Tsire yaje ya siyo mana da Yourghour muka sha muka kwanta da Safe kuma ya je kasuwa ya narko min Cefane wannan karon bai siyo Kifi ba sai nama sai kuma ya Siyo naman kan rago yace na Dafa masa yana so, cikin Lokaci kankani na zage na Dafa masa mai romo da yaji kayan kamshi kuma yaci da yawa tunda ko Taliyar da na Dafa da rana bai samu ci ba da Daddare ma shi na Dumama masa yaci da Burrdi.
Ni daman naman ganda bai Dameni ba ban ci wani da yawa ba, shiyasa ya kalleni yace"Yarinya baki san Dadi ba."
Mirmishi kawai nayi ban yi mgana ba Zama na da Assadiq zama ne na Mutumtu juna yadda ya ke tafiyar dani kamar kanwarsa nima sai na Dauke shi da Daraja sosai.
Koda yaushe muna tare da juna bamu cika Fira ba sai ta kama ammh yana tayani shara ko zuba ruwa banda girki ko wanke wanke domin yace bai iya ba ammh yana wanke bayi sannan in zai yi wanki ya had'a da nawa ya yanke dauraya kawai nake yi masa na Fita waje na shanya.
Ranar ko na fita shanya muka had'u da Ummi ta kalleni nima na kalleta kamar bazan yi mata mgana ba sai kuma na Duba Wani abu da yasa na Juya na yi mata sallama ta amsa a yamutse daganan na koma na cigaba da Shanyar kayan mu ni da shi ta tsaya kam ta na kallona kuma nasan bayan Fadila ta dawo sai ta gayamata.
Suna ganin mijina ammh kuma ba Fuskar da za su san wani abu akanshi kuma Assadiq ya gayamin tare suke sallah da mazajensu Ummi a masallaci anguwan nan.
Ammh iyakarsa da su gaisuwa shikenan.
Tun bayan auran mu sai wannan zuwan nasa suka taba waya da Amma tun bayan tafiyarta.
Sun gaisa sosai yace mata zamu zo mu gaisheta tace mu yi zaman mu.
Adda ce da aka bata su gaisa ta yi masa mganar ko ya sanar da Danginsa game da Hasiya? Sai yace mata Eh sun sani'.
Sai Adda tace"To tunda sun sani yakamata ka Dauketa ka kaita taga Ahalibka suma su ganta"
Sai ya amsa mata da Insha Allahu.
Tun ina saka ran zai ce min zai tafi har na sakankance.
Watarana in bamu jin dafa abinci sai yace na shirya muje mu ci abinci a waje Dalilin Assadiq na san wasu daga cikin Gidajen Abincin garin zariyan da abaya ban san su ba.
Kuma in zaman shurun ya yi mana yawa sai yace nazo mu yi kallo sai ya kunna mana kallo acikin karamar Na'urar computer dinsa ashe akwai kallo aciki.
Ba na Hausa ba ne Fina finan Sai dai akwai fassaran Turanci, shine ya ke min bayanin Abunda suke fad'i in muna kallo duk da Rabi da kwata ba na gane komai.
Ammh kuma ina jin dad'in haka dalilon haka mun samu sakewa da Sabo da juna sosai.


🌿 Ina manyan mata masu MATSALOLIN rashin Ni'ima Ina sabbabin aure Wanda basu juku yanda Mai gida zai sume ba😂Ina wayanda zasuyi sabbin aure
Nazo muku da magani SAHIHI ingantaccen TSIMIN TABAJE🤌🏽🥰😍 hmm uwar gida, amarya, tsoffin aure kuna Ina ko kuntsaya tsilla tsilla tohm maza kuzo nazo kusiya TSIMIN TABAJE 💃💃😂hajiya ta tunda kukaji na yaba wannan magani toh tabbas yakai inda yakai yanada matukar kyau, Yana saurin saukar da niima baya illa domin andafashine da saiwoyin da kuka San suna maganin dakyau... Hajiya ta 🙈wlh Mai gida zaiyi Santi zakiji dadi Kuma zakuzo ku godemun domin yanasa Gurin yayi dumi ya Kuma ciko miki da gaba Gurin Kuma zaiyi dadi zoyzoyy😂🙈💃Kuma duk afarashi kalilan akwai gorina 1k akwai galan, akwai jarka ga duk meso, hmmm duk Wanda yasha Sai ya Gode mun domin nice na baku tabbaci 💃😂kunsan banida burin daya wuce Inga anasaka Mai gida farinciki 💃😂🥰Toh kuzo kusiya zakuji dadi insha Allah Kuma Sai kun dawo.... muka hada miki maganin TSIMIN TABAJE sha'awa zaki koma kamar marka..game bukatar TSIMIN TABAJE ya kiramu tawa innan numbobin kamar haka
*Location* *Zaria and kaduna* *but nation wide delivery* *for more details 07062349732 or 08143450259* 💃💃💃





*Janafty*
*TMWBK2K013*

*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*


Mai_Dambu Candy world's and more. Zaa iya samun Tuwon madara da iloka, gullisuwa, aya mai sugar, gyada mai gishiri, sannan muna bada sari, muna kuma karban oda da aikin biki ko suna. Muna karban aikin donut da cincin..08130269641

Ranar kawai yace na shirya muje gidan Adda Fati mu gaisheta nan da nan na fara Murna, bayan la'asar muka tafi muna hanya ya kalleni ya na fad'in"Haka zaki je baki rike musu komai ba?
Sai nace"To me zan siya musu?
Kallona ya yi batare da ya yi mgana ba, sai da ya ga mun zo wani shago yace mu tsaya ya fita da kansa sai gashi ya Dawo da Leda cike da Biskit da Chaculet da Sweets.
Wani abu na bani mamaki game da Assadiq bayan kashe wayarsa da kuma rashin yin waya a gabana sai kuma yadda ya ke kashe kudi ahalin nasan ba shi da sana'a mai karfi asalima ya na karkashin wani ne.
Kuma a yanayin kashe kudinsa bai yi kama da wanda ke karkashin wani abu.
Duk da yace gwamnati na Biyansu ammh kudin da ya kashewa ya fi karfin kudin da ya ke da shi.
Na kasa yi masa mgana ganin kamar ba Hurumina ba ne
Adda Fati da Mijinta kamar su goyamu Adda Fati Bakinta yaki Rufuwa ita da Habiba da ta Dawo daga Islamiya.
Tare suka fita masallaci da Baban Hanif suka dawo suna falo suna Hira ni kuma muma ciki muna Hira da Adda Fati ta na faman tambayana ya yanayim zaman mu? Nace mata lafiya lau ko matsalan su Ummi ban fad'a mata ba.
Kallona ta yi kafin tace"Ya mganar zuwa dake chan garin na su?
Sai na kasa ce mata ban masa mgana ba sai kawai nace mata yace zamu je in ya samu Lokaci.
Adda Fati tace"Gaakiya ki takura masa ya kamata kuje ki ga yan'uwansa suma su ganki."
Sai na jinjina mata kai alamun to ina jinta ta na ta min bayanin Fa'idar haka ciki har da Tunanin kada mu zo mu fara tara zuru'a.
Sannan ta tambayeni ko a waya bai tab'a had'amu mun yi mgana da kakar tasa ba?
Nace mata a'a bai taba bani ba araina nace shi wannan wayar tasa ma ai ban taba ganinta ba koda yaushe tana jikinsa.
Achan falo ma haka Baban Hanif ya tasa Saddiq da Tambayoyi shi kuma ya na bashi amsa a takaice.
Tambayar da ta basa mamaki shine da Baban Hanif yace"Wani aiki ku ke yi ne kai da megidan naka?
Sadiq ya kallesa kafin yace"Gwari mu ke yi harkan gwari ne"
Baban Hanif ya kallesa ya na mamakin kalamansa shi dai a jikin Sadiq bai yi kama da mai gwari aikin Wahala ba.
Sadiq da ya Fahimci haka sai yace"Muna zuwa gari gari har kudu ma muna zuwa."
Sai Baban Hanif yace"Allah ya taimaka shi megidan naka anan garin ya ke?
Sadiq ya yi saurin cewa"A'a a chan kano ya ke."
Tun kafin Baban Hanif ya watso masa wata tambayar ya mike ya na fad'in nazo mu tafi kada mu yi dare a hanya mu kasa samun abun hawa.
Sai Baban Hanif ya tashi yaje kirana muna Tsaka da Hira da Adda Fati ya leko yace mijina yace na fito mu tafi.
Hijabina kawai na saka na fito Adda nata Godiyar tsaraban yara.
Har waje suka rakamu ita da Habiba da Baban Hanif.
Da kafa muka taka har bakin Titi sannan muka samu Adaidaita zuwa gida.
A hanya ya tsaya ya siya mana gashashiyar kaza da Madaran Holladian, muka koma gida muka ci sannan muka kwanta sai na lura kamar Assadiq yana cikin Damuwa yau ko kallon bai kunna mana ba ya kwanta ya rufe ido.
Ganin haka nima sai na shiga ciki na kwanta.
Sadiq ya dad'e bai yi barci ba ya na Tunanin wani abu tunda yan'uwan Hasiya suka fara damuwa da Sanin Danginsa yasan akwai matsala.
Shi gabadaya ma yan'uwan nasa Fushi ya ke da su tun abunda ya faru kafin tahowarsa.
Sun kikkirasa duka yaki Daga wayarsu, Umma ce kawai ya ke Daukan wayanta sai Abba sannan Sultana ma na kiran shi abun da ke ba shi mamaki sai ganin sakoninta ma su kama da na Soyayya da kulawa da ta ke Tura masa shi kuma bai tab'a kiranta ko sau daya ba.
Yasan shi ne karami ne acikin su ammh yasan yadda Mata suke jan Ragamar bata gida in dai suka yi yawa a waje.
Bazai bari su shiga rayuwarsa su takura masa ba, kowacce taje taji da gidanta da Mijinta da ya'yanta.
Sannan ya fara lura da in bai jajirce ba Ko auran Sultana ya yi su za su rika Tafiyar masa da matarsa shiyasa ya Tauna aya domin tsakuwa taji Tsoro.
Big sis ce ta Turo masa sakon ya yi hakuri ya kirata za su yi mgana shi kuma baya so Hasiya ta Fahimci wani abu Shiyasa sau tari ya ke barin wayarsa a kashe.
Sun yi mgana da Tahir sau biyu kuma bai taba sanin baya Gusai ya na zariya ba sun yi mganar zasu dawo zariya Lokaci d'aya.
Ya kwana da tunanin yadda zai tambayi Hasiya abunda ta ke so ta fara sana'a in ta samu jari so ya ke komai ya kare kafin yan'uwanta su gano abunda ya ke boyewa.
Sannan Tausayinta ya ke ji shiyasa har alokacin ya kasa aiwatar da Tsarinsa.
Washegari kuma Ramatu ta kirani tana gayamin Noor ba lafiya sai na gayamasa sai yace anjuma muje mu gaisheta
Kamar zuwan Adda Fati da Yammah mukaje gidan Ramatu cikin sa'a muka samu Nura ya dawo suka  had'e da Sadiq suna ta Hira ni kuma muka kule ni da Ramatu ita kadai na fad'a ma yadda muka kare da su Ummi.
Ramatu ta yi mirmishi kafin tace"Kin manta na taba fad'a miki gangariyan miji na nan zuwa gare ki Hasiya?
To shine Sadiq ina da tabbacin shine wanda zai zama bango gareki har Abada Hasiya kuma shi zai zama kariyar  kuma wanda zai tayaki wajen karb'an duka Kaddarorin ki."
Sai na kasa musama Ramatu saboda nasan gaskiya ta fad'a Assadiq mutun ne mai hange nesa da sanin Zahirin Rayuwa.
Nan ma sai Dare muka koma gida sai da muka ci abinci shinkafa da wake da Miya da Salat, tare duka muka ci abinci da su muna cikin cin abinci ne Ramatu ta kalleni ta na fad'in"k'awata ba ni shawaran wani sana'a zan fara Abban Noor ya bani jari"
Tun kafin na kalleta Assadiq ya kalleni domin yaji me zan ce, sai kuma yaji nace"To wani sana'a zaki fara?
Kai Tsaye tace"Shine na ke nemen shawaran ki"
Shuru na yi kamar me nazari kafin nace"kina da Fridge ko?
Sai ta dagamin kai sai na cigaba da Fadin"To ki fara saida Ruwan sanyi mana ki gani? Ko kuma ki had'a da Suya milk in ya amsu shikenan."
Ramatu ta yi jim kafin tace"Eh to zan gwada na gani kaji Shawaran Hasiya Abban Noor?
Nura na gefe yace"Sai ki gwada ki gani Allah yasa albarka."
Sadiq na gefe ya kalli Ramatu kafin yace"To ita ki tambayeta in ta samu jari wani sana'an zata fara?
Ramatu ta kalleni nima na kalleta sai na nuna kaina ina fadin"Wai ni?
Ta na Dariya tace"Hasiya mamman kona ba."
Cikin daga ido nace"Tab ai in na samu wasu kudad'e yanzu dubai zani na Saro zannuwa da kaya dogayen Riguna da su takalma ina so na zama yar kasuwa Sosai."
Ramatu ta yi dariya kafin tace"Lalle wa yahga Hajiyar Dubai."
Nura ya kalli Sadiq kafin yace"To kaji sai ka Shirya ka kusa zama mijin Hajiya."
Mirmishi kawai ya yi bai yi mgana ba daganan sai aka Rufe mganar sana'ar muna gidan har wajen goma saura sannan suka rakamu muka tafi.
Har na ma mamta mun yi wannan mganar sai washegari da rana ya kirani ya na zaune afalo.
Bayan na zauna a gabansa ya Tattara natsuwarsa ya fara fad'in"Da gaske kina son ki fara kasuwanci Hasiya?
Kai Tsaye nace"Sosai ina son na zama babbar yar kasuwa watarana"
Cikin jinjina kai yace"Baki sha'awar ki cigaba da karatun ki ne?
Sai na yi shuru ban yi mgana ba sai da ya kara maimaita tambayarsa sannan nace"In na samu damar haka bazan ki komawa makarantar ba."
Daganan bai karamin maganar ba ni kuma sai na Dauka kawai ya Tambayeni ne saboda hirar da muka yi a gidan Ramatu.
Shi kuma har ga Allah alkwarin da ya yi ya ke son cikawa in yace zai maidani makaranta lokaci ya kure sannan maganar kasuwancin da nace zan fara sai yaga kamar yafi sauki gwara dai ya fara bani jarin da zan fara kafa kaina kafin ya rabu da ni.
A daran ya kunna mana wani Turkish Film muna kallo muna zaune a saman kujera na zaman mutum biyu.
Na'urar na
Showing 54001 words to 57000 words out of 98628 words