zai sanar da ke da kansa."
Da wannan kalaman Amma ta katse wayar ta barni sake da baki sai maganganunta suka sarkeni na kasa gane inda ta dosa.
Me ta ke nufi da cewa kada na matsama kaina da son sanin abunda ba'a so na sani ba? Ko ta san wani abun da mu bamu sani ba ne?
Ita ko Amma ta yi hakane saboda d'inke wata baraka abunda Fatin ta saka Hasiya ta yi gaggawa ne kuma shi gaggawa aikin shedan ne in a auransu gaggawa ya shiga bai kamata a zaman su kuma gaggawa ya shiga ba, a bi komai a sannu in sha Allahu alheri ne zai faru sannan kuma zai faru a yadda Ubangiji ya Tsara Faruwarsa ne.
Maganar Amma yasa na binne mganar acikin raina na kuma cire yakinin ko Assadiq ya zo bazan masa mganar Ahalinsa ba, na bi mganar Ammaa zan jira lokacin da ya kamata na sani zan sani.
Ranar asabar aka kawo Amarya kusa da Dakin Ummi mai suna Fadila.
Yar cikin samaru ne a irin gidajen ma su kudin anguwan.
Fadila irin yamatan ne ma su kaud'i da Son karya sannan ga fariya da wulakanci tare da renin arziki.
Mijinta ma'aikaci ne a CVN a Abuja ya na gini bai gama ba ne yasa ya kama Haya kafin ya kamallah gidansa.
Fadila Farar mace ce Doguwa mai jikin mata ta na da kyau irin kyau mai Daukan ido sosai, iyayenta ma su kudi ne shiyasa kayan Dakinta ma sun taka na Ummi a komai da komai.
Tun ranar litini da Daddare da muka shiga ni da Ummi ganin Daki na tabbatar ma da kaina Amarya Fadila bata karb'eni ba.
Fuskarta ba Fara'a ta amsanin gaisuwa sannan ta na ta min kallon kasa kasa a wulakance.
Ammh ta amsa ma Ummi cikin Sakewa ko ma daga ganin yan'uwanta duka Dakin Ummi suka yi mu'amalansu kafin su watse na Fahimci wani abu.
Wannan rayuwar kwarya tabi kwarya ne in kana da shi sai ayi da kai in baka dashi kuma kai da banza duk d'aya ganin haka yasa ban kara shiga Dakinta ba.
Kuma ta shiga Dakim Ummi sannan ta bata Su kayan Fulawa ammh ni ko abunda ba'a so bata bani ba.
Ummin ce ma ta sanmin a nata sai ta boyemin da cemin Fadilan ce ta had'ama waje d'aya tace ta dibarmin aciki.
shuru kawai na yi mata ammh mganar gaskiya ko a fuska wanda ya ke yi da kai zaka sani.

*****

Har su Sadiq suka samu Hutu bai samu Sararin kara komawa wajen Hasiya ba sai ranar da zasu tafi.
Tahir zai wuce Daura shi kuma zai tafi Gusai.
Da safe sun gama shiryawa duk da ya na kiran Hasiya a waya lokaci bayan lokaci yana jin lafiyanta yasan bai kamata ya tafi batare da yaje ya ganta ba tunda zai jima kamar wata daya haka kafin su dawo.
Ya rasa wata karya zai ma Tahir ya samu ya je ya dubata sai dakyar ya samu karyan zai je ya ciro kudi yanzu zai dawo sannan ya samu ya yi wuf ya fita yaje ya hau mashin.
Da misalin karfe 9am na safe na Ranar jumma'a ya kwankwansa ma Hasiya kofa.
Ina cikin barci naji ana Bugun kofa sai kuma kasala da barci yasa na kara komawa sai kuma naji wayata na Ringing cikin barci na lalubota kasan Filo ban ko Duba mai kiran ba kawai dauka na yi na saka a kunne.
Sanyin muryansa ce ta Dake ni sanda ya ke fad'in"Ina kofar dakin ki."
Da haka ya katse wayar ai sai na wartsake na Diro daga kan gado da Sauri dagani sai rigar barci tun ta gida ce duk taji jiki sai na Rarumi Hijabi na saka sannan na fito nazo na Bude masa kofar dakin lokaci daya ina Murza idanuwana.
Yana Tsaye kofar d'akin sanye da Riga da wando ma su ruwan kasa ya sanya Jaket baka a saman kayan sannan hannayensa suna cikin Aljuhun wandonsa.
Na fahimci ya na son tsarin wannan Shigar sannan koda wani Lokaci yana jin dadin sanya hannayensa cikin Aljuhun wandonsa.
Hanya na ba shi Lokaci d'aya ina fad'in"Sannu da zuwa."
Ba amsa ba sai da ya shigo ciki sannan yace min yauwa.
A tsakiyar falon muka Tsaya bai ko Zauna ba ya juyo ya na kallona.
Ni kuma ina shirin juyawa zuwa kitchen ko ruwa na kawo masa a tunanina daga tafiyar suke yanzu suka shigo garin

"Hasiiyaa."

Sai naji ya kirani cikin Taushin muryansa tsayawa na yi kafin na juyo ina fad'in"Na'am!
Kai tsaye yace"Dawo nan gaba na."
Ba musu na dawo gabansa na Tsaya ammh kaina na kasa ina wasa da Hijabin jikina da Hannayena da ke cikin Hijabin.
Na wani lokaci ya tsaya ya na kallona ya rasa abunda zai ce min.
Sai kuma chan ya nisa kafin yace"Jiya da Daddare muka dawo garin Hasiya. Kuma yanzu ma wata tafiyar ta kama mu yanzu."
Kai tsaye na kallesa kafin nace"Yau? To zuwa ina?
Sai da ya ja Numfaashi kafin yace"Zuwa Gusai."
Mirmishi na yi kad'an kafin tace"Allah ya kiyaye hanya."
Kudi ya fiddo cikin Aljihunsa ba zato kawai naji ya riko hannuna ta cikin Hijabin ya jawo shi waje karo na Biyu da Fatayen Hannayenmu suka kara had'uwa waje d'aya.
Dukkanmu sai da muka ji wani yam! Dumin Hannuna ya gauraye da Sanyin hannunsa.
Duk da yaji yanayin ammh bai maida kai ba sai ya sakamin kudin da ke hannunsa a cikin hannuna ya matse Lokaci d'aya ya na fadin"Ki kuka da kanki kin ji ko?.
Sai na samu kaina da gyad'a masa kai ammh na kasa mgana.
Hannunsa guda d'aya ya saka ya Dago habata lokaci daya ya na kallon kwayan idanuwana.
Cikin wani yanayi yace"Akwai kayan abinci ba su kare ba ko?
Kai na kara gyad'a masa ina so ya sakeni saboda ji na yi idanuwana sun ciko da kwallah suna shirin zubowa.
Ba shawara da ni kawai naji hawayen sun fara gangarowa saman kumatuna.
Wad'anda na rasa ko hawayen kewarsa ne ko na tafiyar da yace zasu kara yi ne?
Shi kuma hawayena su suka kara sakashi ya shiga wani yanayi har ga zuciyarsa da niyar ya lallasheni ya jawoni jikinsa ya Rungumeni, lokaci d'aya ya na shafa kaina zuwa bayana da Sigar lallashi.
Kansa ya kwantar saman kaina ya na fad'in"Sorry. Am sorry SIYA..!"
Ya ke fad'a cikin wani irin Taushin murya da sigan kuma lallashi.

Bansan ya akayi muka samu had'uwar gangar jiki ba, na dai ganni Tsamo tsamo a saman kirjinsa, ya na faman lallashina.
Bansan cewa bayan haduwar gangan jiki mun samu na zuciya ba, sai da naji nima na bude hannayena da na jimke kudin nan na Rumgumesa ta baya Lokaci d'aya ina sakin kukana.
Jin ina kuka yasa ya fara bubbuga bayana ya na fad'in"Shii.! Shii!
Alamun na yi shuru mun jima a haka na lumshe a tsakiyar kirjinsa ina shakan kamshin Turarensa.
Kafin naji ya dagoni idanuwana suna lumshe ne da hawaye ina ji ya saka Tattausan hannayensa ya sharemin hawaye lokaci d'aya ya na Fad'in"Ki daina kuka na baki tabbacin bazan jima ba zan dawo."
Kai na kara daga masa shi kuma sai ya rike hannayena ya na kara fadin"Ki kular min da kanki za mu rika yin waya ko?
Cikin muryan shagwaba da bansan yaushe na iya ba nace"To ba kai ba ka kirana ba."
Da Sauri yace"Zan rika kiran ki in sha Allahu."
Sai na jinjina kai kafin nace"Alkwari.!
Mirmishi ya saki mai kayatarwa kafin yace"Cikawa.!"
Ina shirin kara mgana wayarsa dake cikin Aljihu ta Dauki neman agaji da Sauri ya sakeni ya fito da wayar ya na ganin sunan tahir ya yi gaba lokaci daya ya na fad'in"Mu je ki rufe kofar zan tafi."
Jikina a sanyaye na bi bayansa sai da ya fita sannan ya juyo ya na min mirmishi hannu ya d'agamin nima sai na Daga masa sannan ya juya ya tafi.
Sai da naga Fitansa daga get sannan na rufe kofar na dawo falo na zauna ina Bude kudin hannuna.
Bansan cewa ina kuka ba sai da naga saukan digan hawaye saman kudin hannuna masu yawa da bansan adadin su ba.
Sadiq kuma ya na fita sauri sauri ya kara samun mashi ya hau ya koma Samaru ko da yaje Tahir ya gaji da jiransa sai masifa ya ke yi ya na fadin a ina ya tsaya?
Kai tsaye Sadiq yace"Layi ne acikin bankin"
Cikin mamaki Tahir yace"Banki kuma?
Sadiq yace"Banki naje saboda ina da matsala da Atm dina."
Da haka ya kashe bakin Tahir suka dauki jakunkunan su.
Suka kulle dakin, sannan suka yi sallama da yan makaranta da suke tare da su.
A tare suka je tasha Tahir ya samu motar katsina shi kuma Sadiq ya hau ta zamfara.
Allah ya taimaki su Tahir motarsu ba ta kai awa ba ta cika shi ya fara yin gaba.
Sadiq kuma sun bata Lokaci kafin motarsu ta cika duba da yanayin da mike ciki na Tsadar rayuwa mutane ba'a tafiye tafiye kamar baya sai wanda ya zame ma Dole.
Suna tafe a Hanya Sadiq na kujeran Tsakiya ya na kallon gefen hanya ta wajen glass ammh Hasiya ce da kukanta ke gilmawa ta cikin Idanuwansa da Tunaninsa.
Sannan dumin jikinta har a lokacin bai bar jikinsa ba sai ya ke jin kamar har alokacin ya na Rumgume da ita ne.
Shi dai har suka isa zamfara ba komai acikin zuciyarsa da Tunaninsa sai HASIYA.!
Ba wannan zumud'in da ya ke shiga in zai zo ganin gida.
Sannan kunya da nauyi sun gama lullubesa kwata kwata zuwansa gusai wannan karon ya sha bambam da zuwan da ya saba yi a baya.




*Janafty*
*TMWBK2010*

https://chat.whatsapp.com/GoRzZ7ZgslV2alO5hYGAnj
*BOJUWA HERBAL'S BY SURAYYA DEE*!

*Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Saiwowin maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Gaban ayu*.
*Hakkin daka gangariya*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*.
*Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya*
*08032773332*
*Ana dafa GIMBIYAR KAZA da tattabarun garari*.


Shi dai yasan ya sauka a tasha kuma ya samu mashin zuwa anguwansu.
Bayan mai mashin ya saukesa ya biya shi kudinsa sannan ya dauki Jakarsa da ya zubo sauran kayan da ya ke son ya kyautar da su in zai koma sai ya tafi da wasu daga gida.
Jikinsa ba kwari ya karisa jikin get din gidansu ya kwankwansa.
Mallam Tajudeen ya zo ya bude karamar Kofar ya na ganin Sadiq ya washe baki ya na fad'in"Yallabai barka da zuwa."
Ba wannan Annurin da zumud'in a Fuskar Sadiq yace"Mallam Tajudeen na same ku Lafiya?
Ya amsa masa Lokaci d'aya yana kokarin karban Jakar hannun Sadiq.
Shi kuma sai ya hanashi ya na dan mirmishi yace"Har gobe ni d'alibinka ne kuma mai biyayya a gareka."
Ya na fad'in haka ya sawo kansa cikin Haraban gidan.
Sai dai me? Gabansa ne ya yanke ya fad'in hango Abba da ya yi a haraban gidan Jingine jikin Motarsa.
Yana sanye da Shadda har da babban Riga waya ya ke yi, sai faman daga Hannu ya ke yi lokaci d'aya ya na ta saba hab'an gefe da gefem Babban Rigansa.
Kunya da wani irin nauyin jiki da na zuciya suka lullube Sadiq da ya sa kafafunsa suka kasa daukansa zuwa ga Abba.
Cak ya tsaya ya kasa gaba ballatana baya sai kawai ya zabi ya tsaya domin ba shi da karfin gwiwan fuskanta Abba a daidai lokacin da yasan ya ci Amanarsu ya aikata babban al'amari batare da saninsu ko amincewarsu ba.
Mallam Tajuddeen ya daga Murya ya na fad'in"Alhaji ga Magajin gida ya iso fa."
Abba da ke waya yaji sanda Mallam Tajudden yace ga magajin gida ya iso.
Da Sauri ya juyo ya na kallon Sadiq cikin wani yadi mai ruwan kasa shara shara har ana ganin shatin Vest din jikinsa.
Sai dai ya na tsaye kansa a sunkuye kamar wanda ya yi ma Sarki karya.
Da sauri Abba ya ba ma Alhaji Jibril hakuri da fadin"Mu yi mgana anjuma Alhaji magajin gida ne ya iso yanzu."
Dagachan bangaran Alhaji Jibril yace"Au ya dawo ne? Shine ba Labari Alhaji?
Abba ya yi dariyan jin dadi lokaci daya ya na kallon Sadiq yace"Kasan halinsa zuwan bazata ya ke mana ni kaina jiya mun yi waya da shi, ammh bai Sanar dani yau ya na tafe ba, ba ri na gansa zan kiraka."
Daga haka ya katse kiran cikin Sauri ya fara takawa wajen Sadiq ya na Fadib"Abubakar..!"
Dalilin da yasa ya dago kenan shima ya fara takawa zuwa wajen Abba suka had'u da Sauri Sadiq ya rankwafa ya na gaida Abba shi kuma sai ya Rumgumosa ya na fad'in"Maraba da magajin gida maraba da Shalelen Innani."
Mirmishin ya ke Sadiq ya yi ya na kokarin kara sunne kansa yau dai Abba ya zama Surukinsa.
Shi ko Abba bai ma lura da shi ba Rikesa ya yi ya na fad'in"Shine baka gayamin yau zaka dawo ba? Da ka fadamin da na tura maka Direba ya Dauko ka."
Sadiq ya yi mirmishi kafin yace"Abba shiyasa ban gayamaka ba, meyasa da girmana sai na saka an bama wani wahala ya tashi daga Gusau zuwa zariya kawai domin ya Dauko ni?
Abba yace"Ka isa ne kada ka manta kai magaji ne kuma shi Magaji ya na da komai."
Sadiq ya yi shuru bai yi mgana ba ammh a ransa fad'i ya ke yi a gusau Sadiq ya ke magaji a zariya kuma Abubakar ya ke.
Dafa kafad'arsa Abba ya yi kamar wani abokinsa sannan Lokaci d'aya ya karbi jakar hannun Sadiq ya na fadin"Ina Attahiru?
Sadiq yace"Ya wuce Daura Abba."
Abba ya jinjina kai ya na fadin"Allah Sarki."
Sadiq ne yaga Abba na jansa zuwa Shashen Umma yasa ya kallesa ya na Fad'in"Abba ba fita zaka yi ba?
Abba yace"Masallacin jumma'a zani Direba na ke jira yaje Dauko yara nan daga makaranta."
Da Sauri yace"Abba to bari na shirya sai na tuka ka muje ko?
Kallonsa Abba ya yi Lokaci d'aya ya na bubbuga kafad'arsa kafin yace"Da zan so hakan Magaji."
Sadiq zame jikinsa ya yi daga na Abba Lokaci d'aya ya na karban jakar kayansa ya na fadin"Bani minti goma Abba."
Ya fad'a ya na wucewa bangaransa, Abba ya bi shi da kallon kaunar da Allah kad'ai yasan iyakarta Tsakaninsa da Sadiq.
Ya na da makulin Shashensa tare da key din dakinsu na zariya ya had'a waje daya ya na jin shashen a Rufe ya Dauko key din ya Bude ya shiga.
Ko'ina Tsab kamar ya na nan ya Tabbata kullum ake gyara masa bangaransa Saboda Halinsa na zuwan bazata.
Kayan hannunsa kawai ya ijiye ya shiga wanka saboda kada Abba ya gaji da jiransa.
Abba ko Umma ya shiga kwalama kira daga Haraban gidan da karfi"Salamatu. Salamatu.."
Da sauri ta fito a firgice ba ita kad'ai ba Hatta Mama itama sai da ta fito.
Dukkansu a tsorace har suna had'a baki wajen fad'in"Alhaji lafiya?
Ya na mirmishi jin dadi yace"Magajin gida ne ya dawo"
Umma ta washe baki ta na fad'in"Auta na? Ya na ina?
Abba ya nuna mata bangarensa da baki ya na fadin"Ya shiga ciki ya shirya yau tare zamu tafi masallacin jumma'a."
Umma ta saki kayattacen mirmishi kafin tace"Auta ya kyauta ya dawo Lokacin da gidan gabadaya ya yi kewarsa."
Abba yace"Barin ma Innani ko jiya sai dai tace wai magajin gida ko lafiyarsa lau? Sulaimanu bazaka je ka duba mana shi kagani ba."
Umma ta yi dariya kafin tace"Ina ruwan Innani."
Mama na gefe karamin Tsaki taja a ranta ta na mamakin yadda suka Damu da yaron da bai damu da ya zauna da su ba.
Ta na jin haushin yadda Daga Umma har Abba basa iya boye kaunar Sadiq ko a gaban waye.
Ballatana Innani da zata iya yin komai a kan Sadiq ciki har da Tozarta sauran ya'yan gidan gabadaya.
Suna nan Tsaye sai ga jar mota kirar Vibe ta shigo gidan Direba ne ya Dauko su siyama daga makaranta.
Motar na gama parking a Haraban gidan suka Firfito.
Siyama ce kan gaba Sai Sultana kowacce dauke da Jakarta.
Salima kuma na baya ta na yaukinta da ta saba.
Wajen su Abba suka karisa ganinsu dukkansu a haraban gidan kamar wani abu ya faru.
Direba ne ya kariso ya rankwafa Lokaci d'aya ya na fadin"Yallabai ka yi hakuri mun samu cunkoso ne a hanyarmu ta dawowa.".
Abba ya saki kayattacen Mirmishi kafin yace"Kada ka damu garba Magaji ya dawo tare zamu tafi masallacin"
Garaba ya washe baki ya na Fadin"Maraba maraba ina yi ma magajin gida maraba da dawowa."
Siyama ta ware ido ta na kallon Umma kafin tace"Umma Yaya Sadiq ne ya Dawo?
Umma ta gyad'a mata kai ta na yar Dariya ,Tsalle ta daka kafin ta saki ihu ta juya ta na fad'in"Sultana Yaya Sadiq ya dawo wayarmu tazo."
Mirmishi kawai Sultana ta yi mata ba ta yi mgana ba.
Salima ce ta saki tsaki kafin tace"Yara sai kun shiga SS2 ko za'a siya muku waya"
Siyama ta balla mata Harara kafin tace"Ina ruwanki damu? Ke ai kina SS1 a ka siya miki, kuma lokacin muma bamu yi mgana ba."
Salima da Saurin harzuka ta kalli Abba ta na fad'in"Abba ka ganta ko? Rashin kunya zata min"
Abba na Dariya yace"Siyamar Abba ki kyale Salima kin ji ko? Yayanku zai siya muku waya in sha Allahu kafin ya koma."
Mama ta tabe baki kafin tace"Ku wuce ku je ku cire kaya ku huta ko?
Suka amsa mata da Toh.
Sultana ce a baya su kuma sun yi gaba suna Rigimansu na sako zuwa Shashen Mama ita kuma ta nufi bangaran Umma.
Daidai Lokacin Sadiq ya fito ya na kokarim saka links din Rigar shaddar da ke jikinsa mai ruwan Dark Blue dinkin zamani da Hula kube wacce ta hau saman aikin kayan sannan kafarsa cikin Budaden Takalmi Kalan brown sabo ne yau ya taba saka shi sannan agogon Hannunsa ma Brown ne na Fata mai kyau da yarari.

Hankalinsa na kan Links din da ya ke Sakawa shiyasa bai ga su Siyama ba.
Abba da Umma kuma kamshin Turarensa suka fara shaka shi ya sanar musu wanzuwarsa a wajen.
Umma kallonsa ta ke yi cikin Alfahari.
Sadiq na Dabam ne acikin zuciyarta duk da ba duka Rayuwarta ta yi tare da shi ba ammh akwai karfafan alaqa tsakaninta da Abunda ta Haifa.
Abba ma cikin Tarin alfahari ya ke kallonsa ya na jin wani annuri acikin ransa da Allah ya ba shi Sadiq a lokacin da ya riga ya fidda rai da Samun magaji.
Mama kuma kallonsa ta ke yi ta na auna kwarjininsa ba ta isa ta ce ga wani abu na rashin d'a da ya taba Had'a ta da Sadiq ba, bai taba nuna mata bambamci Tsakaninta da Umma ba, bai taba nuna bambamcin Tsakanin ya'yanta da ya'yan Umma ba.
Zuciyarta ta kasa jin Haushinsa Saboda Tarin kyakyawan Dabi'unsa.
Siyama da Salima
Showing 39001 words to 42000 words out of 98628 words