zama cutuwa garesu.
Na auna yadda zan kashe kaina ta Sigogi da Dama ammh kuma na kasa aiwatarwa duk wanda ya fad'omin a rai sai naji bai kwantamin arai ba har Tunanin na Rataye kaina nayi sai kuma na fasa ina Tunanin ya Amma zataji in na kashe kaina? Sannan zan mutu kafira ce ranar gobe kiyama Allah ya sanyani acikin Wutan Jahannama.
Tuna haka yasa na watsar da Tunanin kashe kaina na fara tunanin nema ma kaina mafitan da zata sakani nayi nesa da dukkan rayuwar mutane gabadaya.
Tun wajen goma na Safe na ke kuka har aka kira sallar azahar ban daina kuka ba, abunka ga jar Fata gabadaya Fuskata ta kumbura ta yi jajir sannan kuma Idanuwana ma sun shige ciki kaina kuma sai saramin ya ke.
Da na mike zan shiga tiolet na Dauro alwala sai da na Dafe bango saboda jirin da naji ya kwasheni.
Hakanan na Dauro alwala na zo nan falo na shinmfida sallaya na tada sallah ina sallar nan ina kuka hawayena kuwa da an tara dan karamin Botiki tsab zai cika saboda yadda suke zuba ba Control.

Bayan na idar na koma na zauna kawai na jingina da kujera, na kasa ma addu'a na kuma rasa irin addu'an ma da zan yi sai kawai na koma na yi shuru ina jin cikina na kugin yunwa.
Daman jiya da Daddare ban yi abinci ba taliyar da na Daface tayi saura sai naci da daddare.
Shine da Safe na tashi na Dafa shinkafa da wake ko ci ban tsaya yi ba na fita kaima Ummi, shine suka Fahimtar dani cewa ni Annoba ce maganina sai Allah.
Ba ni da karfin gwiwan cin wani abincin bakina kuma ya yi takaf kamar wacce ta tashi jinya.
Shiyasa ban yi wani yunkurin tashi na taimaki kaina ba, a raina nace in yunwa ce ta kasheni ban mutu kafura ba in dai ko hakane bazan kara cin abinci ba ballatana na sha Ruwa har sai Ubangiji ya Dauki raina domin na gaji da wannan rayuwar.
Ina jin ana ta sake kiran wayata ammh yadda jikina ya nemi ya fara saki ne yasa ban ko iya jirgirtawa kusa da wayar ba, ballatana nasan wake kira a tunanina ko Adda Fati ne ban taba Tunanin Assadiq zai damu ba, ballatana har ya cigaba da kiran wayata a kai a kai ba.
Wayar ta na yankewa naji ana bugamin kofa, ko ina iya tashi ma da karfin jikina bazan tashi ba domin Tunanina ya gama gayamin su Ummi ne sun dawo ne domin su kara cin zarafina kamar yadda suka yi a farko.
Ina jin ana bugun da karfi sai kawai na kara fashewa da kuka.
A fili na furta"Innalilillahi wani'inna ilaihirraju'un ni Hasiya yaushe zan huta daga wannan bala'in ne? Daga wannan sai wannan?
Haka na ke fad'a a fili ina gunjin kuka lokaci daya ina had'e kaina a gefen kujera kamar wata marainiyar da ta rasa komai, Eh mana marainiyar ce mana tunda ba ni da Uba sannan ba ni da wani bangon abun jingina na.
Kamar wasa sai naji kuma ana Buga kofar dakina kuma ana Kiran sunana.
Shiyasa na mike a kasalance kamar zan fad'i, na nufi kofar dakin na bude da Niyar na yi shuru har su ummi su gama fad'in abunda za su fad'i su tafi.
Sai dai kuma me? Ina bude kofar ban tsaya kallon wajen ba na juya baya na ina sharan hawayena.
Sai jin tattausan muryansa na yi ya na fad'in"Hasiya me ya faru? Amma ce ciwonta ya tashi?
Da sauri na juyo muka had'a ido Hudu da shi ban taba Tunanin ganinsa ba.
Yana sanye cikin Riga da wando,Rigar Ash ce mai ruwan kasa sannan akwai Dogon Hannu,sannan sai bakin wando a jikinsa,sai karamin akwatin Trolley a hannunsa da jakarsa goye a bayansa.
Na kasa mgana illah kallonsa da na ke yi wasu hawayen na kara ambaliya a saman Fuskata.
Shi kuma daman ashe bugawar kofata da ya dinga yi da karfi ya fito da su Ummi Daga Dakunansu suna ta kallonsa ita da Fadila, shiyasa ya yi saurin shigowa cikin Dakin Lokaci d'aya ya maida kofar ya kulle.
Ni kuma da gudu na koma falo na zube a kasa ina gunjin kuka, cikin tashin Hankali ya sauke akwatin hannunsa lokaci d'aya da jakar bayansa ya Nufeni.
Duk a Tunaninsa wani abu ne ya samu Amma zuciyarsa na fatan Allah yasa ba ta rasu ba ne.
Tun sanda ya kirani yaji ina kuka kuma yana ta kara kira ban Dauka ba sai hankalinsa ya tashi, Baisan ya akayi ba kawai ya fara shirya kayansa ba shi dai yaji ya kasa natsuwa abunda ransa ya kawo masa wani abu ya samu Amma ko na ciwo ko na Mutuwa.
Yaji hankalinsa ya tashi, ya kasa samun natsuwa da sukuni, ya san cewa Hasiya ba ta da wani abunda ta ke kaunar bayan mahaifiyatan rasata ko wani abu ya sameta babban tashin Hankaline a gareta.
Shiyasa ya shirya tahowa Zariya batare da shawara da ko zuciyarsa ba Ruhinsa ne kawai ke jansa zuwa ga Hasiya.
Abba ma baya gida Umma ce kad'ai ya samu ya yi ma sallama itama sai da ta yi ta nanata tafiyarsa har dai ta kare ta baya ce zai jima a gida ba wannan karon? Kai tsaye yace mata daga wajen da ya ke hidimar kasa ne suka Kira shi, Umma dai ba yarda ta iya illa rakasa da addu'an Allah ya tsare.
Innani da mama bai samu shiga bangaransu ba tsabar yadda ya matssu ya gansa a zariya suna mota ji yake yi kamar ya yi tsuntsuwa ya gansa a gaban Hasiya.
A gabana ya duka cikin Damuwar da ta bayyana har a saman fuskarsa sannan ta nuna kanta a cikin muryansa, Cikin wani yanayi ya fara kiran sunana.

"Hasiya.. Hasiya."

Ina jinsa na kasa amsa masa saboda kukan da ya ke murkukusan raina a lokacin, ganin ban amsa kiran da ya yi min ba yasa ya saka Hannuwansa ya Dago Fuskata da ta kumbura ta yi jajir saboda kuka ya na kallona cikin sanyim murya yace"Me ya faru? Amma ce?
Ya fad'a lokaci daya yana bubbuga kumatuna idanuwana na Runtse sai ga hawaye sharr, sun sake zubomin cikin shakewar murya nace"Amma na lafiya, ba ita ba ce ni ne."
Daganan sai kawai sai na kara fashewa da kuka wannan karon harda Sauti kamar wata karamar yarinya.
Cikin damuwa ya tarairayoni a jikinsa ya na fad'in"Me ya same ki Hasiya? Ko baki da lafiya ne?
Ya ke fad'a ya na kokarim kama Fuskata da hannayensa duka Biyun ni kuma ina zillewa kokarina na koma kasan tayels din na kwanta na cigaba da kukana, shi kuma ya hanani sai Faman Rikeni ya ke yi, ya na kuma ta maimaitamin tambayan me ke damuna? Ko ba ni da lafiya ne?
Dakyar na yarda ya rikeni dakyau a cikin jikinsa, sannan fuskata na cikin Tafukan Hannayensa cikin tashin Hankali a muryansa ya kira sunana "Hasiya.."
Dakyar na bude kumburarrun idanuwana ina kallonsa cikin Muryansa mai cike da Sanyi yace"Gayamin me ke faruwa? Wani abu ne ya same ki? Ko baki da lafiya me?
Sai kuma hawaye sharr, kamar an bude famfo, ina kokarin kara zille masa ya kara rikeni gam ya na fadin"Me ya faru Hasiya?
Cikin kakkausan murya da alamu ya fara gajiya da jiran amsata.
Sai da na bud'e idanuwana jajir ina kallonsa ido cikin ido sannam muryata a shake nace"ASSADIQ...."
Sai kuma na kasa karisawa cikin kosawa yace"Menene Hasiya?
Cikin kuka nace"Ka sake ni. Don Allah ka sakeni Assadiq."
Gabansa ya yi wani Rugugu ya fad'i kuramin ido ya yi a ransa sai ya fara Tunanin ko dai nasan shirinsa ne na sakina nan da Lokaci kad'an?
Yana wannan Tunanin na katseshi da cewa"Gwara ka sakeni saboda ina son ka tsira da lafiyarka. Ban taba jin fargaban kada wani abu ya samu wani ba irin yadda na ke fargaban kada wani abu ya sameka ba"
Cikin ido muke kallon juna kafin yace"Me ya kawo wannan mganar kuma?
Kwace jikina nayi na koma gefe na jingina da kujera ina kuka cikin kukan na fara gayamasa abunda ya Faru Tsakanina da su Ummi na karishe da Fad'in"Ba na son wani abu kaima ya sameka shiyasa gwara ka sauwake min ka yi tafiyarka ka rabu dani Tun kafin wani abu ya sameka.

"Ba abunda zai sameni face abunda Ubangijina ya kaddaramin Hasiya."

Haka yafad'a lokaci d'aya ya na kallona cikin Kaushin murya kafin ya taso daga inda ya ke yazo gabana ya zauna ya tankwashe kafafunsa kamar mai Daukan karatu wanda har gwiwar kafafunsa na dukan gwiwan kafafuwana.
Cikin Kaushin murya ya bud'e murya ya kira sunana "Hasiya."
Na amsa masa cikin dashewar murya kafin naji yace"Dago kanki ki kalleni ina so zan yi miki mgana ne, kuma ina so ki bude kunnuwanki dakyau ki Saurareni."
Ya fad'a ya na kallona kai tsaye sannan Fuskarsa ba Fara'a ballatana a yanayin muryansa na Fahimci babu wasa acikin mganarsa.
Dagowa na yi ina kallonsa ina mai Tattara duka hankalina garesa.
Cikin Tattausan lazafi yace"Hasiya waye ya Hallice mu?
Kai Tsaye nace"Allah ne ya Hallicemu?
"Waye mahallicin sammai da kassai?
Nan ma na amsa masa da cewa"Allah ne"
Ya kara cewa"Waye Mahallicin Tsuntsaye da Dabobbi?
Cikin mamaki wannan karon na kallesa sai na ga da gaske ya ke tambayoyinsa ba wasa a saman Fuskarsa.
Ni kuma tambayar ce na raina musu ai ko yaro dan shekara uku yasan Allah da abunda ya ke tambayana.
Shi ya katseni da fadin"Kin yi shuru"
Da sauri nace"Duka Allah ne Mahallicin komai da komai da ke cikin wannan Duniyar sannan shi ke da Duniyar gabad'aya da abunda ke cikinta."
Cikin jinjina kai yace"Good. To kinsan haka Hasiya meyasa ki ke tunanin ke ce ki ka yi sanadiyar rasa Dukiyar mijin ki na farko? Sannan me yasa ki ke tunanin ke ce da alhakin Jinyar mijin ki na biyu?
Sai naji na kasa mgana na yi tsuru ina kallon kafafuwana ina wasa da yatsun hannayena.
Ganin na yi shuru yasa ya cigaba da fad'in"In dan har kinsan Allah ne Ubangijin duniya da abunda ke cikinta to ya kamata ki daina bari Tunanim mutane na Gurbata naki Tunanin Hasiya.
Duk Abunda ki ka ga ya faru da bawa daga Rabbil Izzati ne shi ke da ikon aikata duk abunda ya so a kuma Lokacin da ya so sannan wani abu bai isa ya samu Dan Adam ba, face abunda Allah ya kaddara masa cikin Kaddarorinsa."
Maganganunsa sun shigeni matuka da suka sanyayamin jiki.
Cikin nadamar tunanin da na yi na kashe kaina na Dago idanuwana da suka cika da kwallah ina kallonsa kafin yace"Ba ni na ce ba Assadiq mutane ne ke fad'in haka a kaina Tun kafin ma na girma. Ana zargin ni ce Silar karayan arzikin Baba sannan ni ce silar mutuwarsa sannan ni ce Silar lalacewar Rayuwarmu har da Ciwon Amma da bayajin mgani."
Sadiq ya yi shuru ya na kallona ina ta sharan kwallah kafin yace"baki amince da amsarki ta farko ba kenan Hasiya?
Da Sauri nace"Na amince wlh."
Kai Tsaye yace"Ke musulma ce kin shaida Allah Ubangiji ne sannan Annabi Muhammadu salallahu alaihi wasallam Manzonsa ne ko?
Nan na d'aga masa kai, cikin taushin muryansa ya cika da fad'in"Kin kuma amince da karban kaddara mummuna ko kyakyawa daga Ubangijin ko? Sai na kara gyad'a masa kai da Sauri ya rike hannayena cikin nasa hannayen muna masu kallon juna kafin cikin Muryansa mai yanayin kashe jikin mace yace" To ki sani wannan al'amarin daga Allah ne, sannan Faruwarsa kuma ta Sanadin ki, shine kaddara mummunan da ake mgana Hasiya, in kika yi hakuri zaki cinye Jarabawarki in kuma ki ka kaza to zaki fad'i daga wannan Gwajin da Ubangiji ke miki Saboda Auna imanin ki."
Amma ta sha zaunar da ni ta yi min nasiha ammh mganganun Assadiq sun kara sanar da ni wani abu, sannan sun kara Budemin ido sosai na Fahimci Ubangiji shi ke da Alhaki da duka Rayuwar duniya da Komai da ke cikinta.
Sai kawai na fashe da kuka ina Fadin"Allah na Tuba Astagfirullah na tuba Allah dazu fa har tunanin kashe kaina sai da nayi Assadiq"
Ido ya bude da Sauri ya na kallona kafin cikin Daga murya yace"Ke baki da hankali ne? Kinsan hukuncin wanda ya kashe kansa ko? Wutar Jahannama Khalidina Fiha Abadan Hasiya."
Jikina na rawa na kara Jimke hannuwan Assadiq ina kara fadin"Ai nace na Tuba bazan kara ba Assadiq."
Cikin Kaushin Murya yace"Kada ki kara wannan Tunanin komai ya yi Tsanani mganinsa na wajen Ubangiji duk sanda wani abu ya so ya gusar miki Da tunani ki ambaci Allah shi zai kawo miki dauki a daidai wannan Lokacin kin ji ko?
Sai na samu kaina da gyad'a masa kai ina zubar hawaye.
Cikin muryan kuka nace"Ka yi hakuri."
Cikin Tausayina da ya cika Kirjinsa ya Saki hannayena, sai ji na yi saman Fuskata ya na sharemin hawaye cikin sanyin murya yace"Ki daina kuka ba abunda zai faru sai alheri kin ji ko?
Sai na samu kaina da gyad'a masa kai ammh hawaye na sun ki daina Fitowa da kwarmin idanuwana.
Kawai batare da zato ko tsammani ba sai na kara tsintar kaina saman Kirjin Assadiq a karo na biyu.
Lokaci d'aya hannayensa a bayana ya na Bubbugawa kad'an kad'an alamun lallashi da ban baki.
Ni kuma na samu waje sai na kara baje kaina a saman kirjinsa ina shakan kamshin Turarensa da ya fara sanyamin natsuwa.
Ban sani ba har barci barci naji na neman kwasata ammh yunwar cikina bata barni ba sai ji nayi cikina na kuka Kuwwyaahh..!
Kunya ta kamani sai na fara kokarin Dago kaina sai ya sakeni jin na daina kuka.
Ya na kallona yace"Cikin ki ke wannan kukan?
Cikin kunya na daga masa kai da Sauri yace"kina da Ulcer sannan ki na zama da yunwa ko?
Sai na kasa ba shi amsa saboda kunya illah fara kokarin mikewa da nayi, ammh sai jiri ya kwasheni da yasa na kusa Fad'uwa sai da ya mike ya tareni ya na fadin"Kin gani ko?
Zaunar da nayi ya yi a kan daya daga cikin kujerun falon ya na fadin"Bari na sama miki ko ruwan zafi ne ya warware miki ciki"
Cikin sanyin murya nace"Na dafa abinci ya na nan cikin tukunyar da ke kan gas."
Bai kara cewa komai ba ya shiga kitchen din da kansa.
Ni kuma ganin haka yasa na mike dakyar duk da ina ganin jiri na Kwashe jakarsa da akwatinsa da ke nan Tsakar daki na kai masa cikin Dakina.
Ina fitowa muka Had'u da shi ya fito yana ganina yace"Ba na ce kada ki tashi ba?
Da sauri nace"Kayanka na shigar maka da su ciki."
Sai ya kalli inda ya watsar da kayan yaga ba su sai kuma ya Dawo da kallonsu kaina na cire Hijabin jikina karemin kallo ya yi yana ganin Ramar da nayi.
Ni kuma ganin kallon da ya ke min yasa naji kunya na koma na zauna da Sauri ina Rarraba idanuwana kamar wacce ta yi karya.
A saman kaina naji mganarsa" Gas bai kare ba ne har yanzu?
Dagowa nayi ina kallonsa kafin nace"Ya kare ranar da Habiba ta zo na bata cikin kudin da ka barmin taje ta sakamin"
Kamar zai yi mgana sai kuma ya fasa ya koma kitchen din.
Daman Dubu goma ya barmin kayan miya kawai nake siya da shi sai gas din da ta cikomin, sauran kudin na nan cikin Wadrope dina.
Gas din ya kunna ya saka Ruwan zafi sai da ya jira ya tafasa sannan ya Juye ya zuba min a wani karamin kofi.
Ruwan Bombita ya had'amin na fara sha saboda ya warware min ciki tunda ina da Ulcer ba na shan Lipton.
Sai bayan na sha ne na ji na Fara Dawowa daidai sannan ya zubomin shinkafa da wakem da na Dafa na ci shi kuma yace sai ya yi wanka da ya shiga ciki yaga ba Ruwa a bambon makewayi sai ya fito ya na tambayana ban samu almajirin da zai fara zubamin Ruwan ba ne?
Nace masa ban samu ba ni na ke zubawa da kaina.
Kai tsaye yace"Shiyasa duk kika rame salon muje gaida Amma ki sa tace ba na kula da ke."
Mirmishi kawai na yi ban yi mgana ba ammh a raina sai da nace ita kanta Amma tasan tun chan daman ni Ramammiya ce.
Assadiq da kansa ya zake ya rika Fita chan wajen Famfo da botikai ya na Dibomin ruwa da na gama cin abincin nace ya kawo botiki d'aya na tayasa sai ya hanani yace naje na kwanta na Huta.
A lokacin a wajen Famfon ne kuma ina da Tabbacin daga Ummi har Fadila suna leken mu ta windunan su.
Ya Dauko Botikai biyu a Hannunsa da Ruwa na matsa masa ya bani guda d'aya kai tsaye ya kalleni kafin yace"Ba na ce ki je ki kwanta ki Huta ba ne?
Zan yi mgana ya Dakatar da ni da cewa"Ba na son gaddama ki je ki kwanta."
Jin abunda ya fad'a yasa na juya shi kuma yabi bayana zuwa cikin Daki.
A falo na kwanta yace na tashi na shiga ciki bani da yarda zan yi tashi nayi na koma ciki na kwanta.
Daman ya gama cika na Tiolet sai na Kitchen ne ya ke cikawa.
Kamar ko ya sani barcin nake ji ina kwanciya sai barci ban farka ba sai Hudu saura.
Naga abun mamaki Assadiq bayan Ruwa Sai da ya sharemin daki tas ya goge kuma ya kunna Turaren wuta daman jiya da yau dakin bai ga shara ba, na iskesa har ya yi wanka ya sauya kaya zuwa jallabiya ya na falo a saman kujera ya yi barci.
Kunyar duniya ta kamani da naga har kitchen ya gyaramin sai dai bai yi min wanke wamke ba na ga dai shima yaci abinci tunda ga Filet dinsa nan alamun ya ci ba da jimawa ba.
Kunya ta saka na koma ciki nima na zuba Ruwa a botiki na yi wanka Tunda garin akwai rana.
Sai bayan na fito wanka ne ina Daure da zanin wanka na Daure gaba ya shigo Dakin.
Da Sauri na yi kasa da kaina ina Raruman Hijabin da zan sanya.
Bansan ko ya kalleni ba muryansa naji ya na fadin"Zan yi alwala."
Ni dai har sai da ya dauro alwala ya fita sannan na iya sauke Numdashin da na rike da Sauri na shafa mai na saka Wata Doguwar rigata na Atamfa.
Daman na yi alwala sai nima na Tada sallah na idar kenan naji shigowarsa kamar ya shiga kitchen sai na tashi na leka sai naga Pure water ne ya siyo sai ruwan gora da bakin lemu katan daya sai Fanta ya na Dauka zuwa Kitchen.
Da sauri na Fito bai sani ba ya Dauki Katan din bakin lemun zuwa Kitchen ni kuma
Showing 51001 words to 54000 words out of 98628 words