ya kira Hasiya yau da Safe kad'ai suka yi mgana ammh Tahir ya tsare ko'ina kuma baya so ya kirata a gabansa Saboda baya son wani surutu.
Sai da Daddare suka had'u da yayyen Tahir a bangaren Hajja suna ta Hira.
Sai da Hajja ta gaji ta fara gangadi sannan ta kora kowa dakinsa.
Sadiq cikinsa ya cika yau har Danwake ya ci da Dambu wanda kanwar Tahir ta kawo masa.
Sun gaji shiyasa suna kwanciya sai barci sai da safe bayan sun dawo sallar asuba sannan suka zauna suna Hira.
Acikin Hirar ne Tahir ya kalli Sadiq ya na fad'in"Wani shiri gareka kasan fa mun kusa yin sallama da garin zariya?
Sadiq na kwance ya yi shuru kafin yace"Wani shiri kuwa? Shiri ai na Ubangiji ne"
Tahir yace"Nasani. Mganar yarinyar nan? Kan rabuwarka wani taimako zaka yi mata kafin haka?
Sadiq ya mike zaune ya na fadin"Shine na rasa mafita har yanzu Tahir."
Tahir ya yi shuru shima ya na Tunani, Kafin ya yi magana Sadiq ya kallesa yace"Da na yi tunanin na saka ta a makaranta ta cigaba da karatunta sai kuma naga wannan ba mafita ba ne"
Tahir yace"Gaskiya ba mu da wannan Lokacin."
Suka yi shuru gabadayan su kafin chan Tahir yace"to ka bata jari ta fara sana'a mana ina ganin hakan ma taimako ne"
Sadiq ya yi shuru kafin yace"Nima na yi wannan Tunanin. To wata sana'a ka ke ganin ta dace ta fara?
Tahir ya balla masa Harara kafin yace"Ina zan sani? Ni ce zabiyar matar taka?
Sadiq yace"Sunanta Hasiya ba Zabiya ba."
Tahir ya yamutsa fuska kafin yace"What Ever. Sai ka tambayeta kaji ta bakinta ni nawa shawara ne"
Sadiq ya koma ya kwanta ya na Fadin"Nagode da shawara."
Tahir yace"Godema Allah."
Sadiq ya yi dariya kafin yace"In ka dawo gida wani abu zaka kama?
Tahir yace"Ba ni da wani zabi yanzu. Yaya kasimu yace ya yi magana a babban Sakandirin nan ta kusa damu zan kawo takarduna, in na samu shikenan in ma bansamu ba zan cigaba da siyasa a sannu a hankali."
Sadiq yace"Ban ji ka yi mganar cigaba da karatu ba?
Tahir ya yi shuru kafin yace"Uhm karatu yanzu ai sai da kudi Sadiq in na samu yadda na ke so zan cigaba in sha Allahu."
Sadiq bai ce komai ba, shima Tahir haka shi Sadiq sai ya yi kamar ya Fara Barci shi kuma Tahir sai ya cigaba da latsa wayar hannunsa.
Kwana uku ya yi a Daura sannan ya koma Gusai yaje kuma ya iske wata Sabuwar mgana ta kara ta shi.
Yan'uwansa mata sun yi taro akan mganarsa da Sultana.
Kuma wannan karon Umma ta goya musu baya sun kuma samu Abba da mganar shi kuma yace mgana ta na Hannun Sadiq duk abunda yace shi za'ayi.
Babu abunda ya ba shi Haushi sai wai ana mganar ko a nan shashen nasa za su iya zama da Sultana kafin ya samu aikin, Haushi ya kamasa ballatana da yaga gabadayansu sun had'u harda wad'anda ke nesa ma duk sun zo ko da suke gaba da shi ammh ai su mata ne ya na gaba da su a tsarin addini bai kamata su zo su zauna suce za su zama control a kan Rayuwarsa ba.
Ranar da ya dawo da Daddare suka shirya taron a falon Innani, sai dai ya bari duka sun gama maganganun su, ya na zaune gefe ya na kallonsu su Hujjarsu wai ya fara damuwa kuma suna Tunanin in ya yi auran zai samu natsuwa da kwanciyar Hankali.
Sai ya yi kamar yace musu shi ai ya riga ya yi aure sai kuma ya fasa.
Fuakarsa ya had'e ba ko Fara'a saboda ya na da wani abu guda d'aya ba ya son ka rika tsallake Hurumin da ba naka ba sannan ya tsani a shiga rayuwarsa.
Abun da yasa ya kasa mgana Har Umma ta ba da goyon bayan wannan karon Mama ma tace duka abun gidane to ba ta ga matsala in an yi auran yanzu ba, Innani daman Burinta kenan bakinta washe da wawulamta domin ta cire Hakoran Roban sai dasashi ba Hakora.
Sadiq bai yi niyar mgana ba sai da Abba ya kallesa yace"Kaji duka bayanan yan'uwanka menene Ra'ayinka akan mganar su?
Gyara zama ya yi kafin yace"Abba ni bansan kan wannan zaman ba, na riga na gama tsayawa a matsayata tuntuni."
Surayya tace"Wata matsayar kenan?
Kallonta ya yi ido cikin ido ya na mamakin Saboda kawai su shiga rayuwarsa yasa suka baro gidajensu suka zo nan su kwana saboda su yanke ma Rayuwarsa Hukuncin da suka ga dama.
Cikin Maganarsa ta kai tsaye yace"Ai na fad'a muku ba yanzu zan yi ba sai nagama Bautar kasa na kama aikin yi kilama har na fara masters dina."
Sai falon ya Dauki Shuru Abba ya juya ya na kalllonsu kafin yace"To kun ji na shi matsayar"
Umma tace"Ammah Abban siyama wannan ba Hujja bace. Kana da kudin da zaka iya rike su da shi da Sultana har ya'yansu meyasa zai ba da Hujjar da sai ya samu aiki.?
Sadiq ya kalli Umma kafin yace"Umma Kudin Abba ba kudina ba ne. Abba ne ya sha wahala ya tara kudin da guminsa kuma kada ku manta ba ni kad'ai ya Haifa, duk nan ya'yansa ne kenan ba ni kad'ai ke da iko akan dukiyarsa ba, Ya riga ya sauke Nauyin da ke kansa na ciyar da ni da Tufatar da ni, sannan ya ba ni Gudummuwa kan karatu ya sauke wannan Hakkin nasa, ko yau Abba ya Mutu komai da ya mallaka ba na wa bane ni kad'ai shima ya'yansa ya taramawa nima shiyasa na ke son ku barni na Tsaya da kafafuna kafin na Fara Tunanin Dauko wani nauyin a kaina."
Surayya ta bude baki kafin tace"Sadiq ni fa banga wata matsala a nan wajen ba. Abba ma mai iya baka gida ne kyauta wanda zaku zauna kai da Sultana."
A fusace yace"In ya bani gidan shi zai rika ciyar da matar tawa? Ko kuma ke zaki rika daukan Dawainiyar nata?
Rashin kunya ba Halinsa ba ne yasa gabadaya suka Dago suna kallonsa da mamaki.
Surayya ta nuna kanta lokaci d'aya ta na fadin"Ni ka ke gayama mgana haka Sadiq?
Karamin Tsaki yaja kafin yace"Kowaccen ku nan ta na da nata tsarin rayuwar. Ku yayyena ne nasan kun girmeni ammh kuma wannan ba shi zai baku damar shiga rayuwata yadda kuka ga dama ba. Mgana ta guda d'aya ce sai na samu aiki aure na da Sultana zai ta shi in kuma kun matsa ne sai ta yi aure sai ku nema mata wani mijin ammh ba dai ni ba."
Umma ta mike a fusace cikin tsawa tace"Abubakar.."
Shima cikin Daga murya yace"Umma me yasa su kika saurare su ni kuma kika kasa Fahimta ta?
Umma kallonsa ta ke idanuwanta na Cikowa da kwallah.
Innani tace"Na shiga uku ni Dije me nake ji haka?
Ta fad'a Lokaci daya ta na Dafe kirji sai kuma ta saka kuka ta na fadin"Wlh ko bayan raina wani ya Tada maganar auran magajin gida da Sultana ban yafe masa ba ko da kuwa Magajin gidan ne da kansa."
Sadiq ya kalleta a fusace kafin yace"To in dai kina son kada in tada wannan mganar ki fad'a musu su dakata da wannan mganar, zan auri Sultana bayan na samu aiki Fakat mgana ta karshe kenan."
Daga haka kawai ya fice a Fusace suka bi shi da kallo cikin mamaki.
Umma ta koma ta zauna ta na fadin"Me yaa samu yaron nan ne?
Mama tace"Ya jima ransa bai baci haka ba."
Sajida tabe baki tayi kafin tace"Duk su Umma suka ja, su suka fara nuna masa cewarsa da Ra'ayinsa na gaba da na kowa har ta su kansu."
Innani ta harareta kafin tace"Rufemin baki, duk ba ku ne kuka saka ya so yace ya fasa auran Sulsanan ba? To wlh ku ji dakyau abar mganar nan a bi abunda ya ke so saboda ba na so ya tada wannan alkwarin saboda haka Sulaimanu ka tsawarta ma da ya'yanka da matanka su fita Hanyar maganar Auran magajin gida da Sulsana a bari har Lokacin da ya samu aikin ko yaushe sai ayi auran ba shikenan ba."
Baki su Surayya suka saki suna kallon  Innani wacce yanzu yanzu ta sauya mganarta.
Tana ganin suna kallonta sai ta fashe da kuka ta na fadin"ko Aljanune suka shafi Magajin gida da ya ke tunanin fasa auran Sulsanan? Kuma ni dai nasan yana tsananin sonta."
Abba ya yi mirmishi kafin yace"kada ki damu Innani ba wanda ya isa ya Tada wannan mganar."
Sun cigaba da Tattauna mganar matan duk jikinsu ya yi sanyi barin ma Surayya abun ya Tsaya mata arai da Sadiq ya yi mata rashin kunya Saboda kawai ta yi mgana kan inganta Rayuwarsa.
Sai ta fara wani tunani ko dai ko dai?
Ta fara Tunanin akwai wani abu ke Boye wanda ba su sani ba.
Umma ma ranta ya baci ammh sai ta Danne ta Lallashi ya'yanta.
Har suna ikararin sun cire hannunsa a kansa yaje shi ya sani.
Allah yasa ma su Sultana ba su a wajen da shikenan sai taji wannan Dibar albarkar da Sadiq ya yi musu.
Gari na wayewa duk suka kama gabansu sai yan nesa aka bari irin su Suba'atu.
Saddiqa ko fad'a ta dinga yi ta na ba ma su Umma laifi da cewa su suka sangarta Sagir suka nuna masa Tun farko cewarsa da Ra'ayinsa na gaba da na su in da tun farko sun nuna masa cewarsu na gaba da banzan Ra'ayinsa da yanzu duk Hukuncin da suka yanke bai isa yace a'a ba.
Umma dai ba ta da bakin mgana Tunda tasan gaskiya suke fada.
Abba kuma ya kashe mgana da cewa za'ayi auran Sultana Lokacin da Abubukar ya so kuma ya kashe mganar baya bukatar yaji an kara taso da ita.
Sadiq yana shashensa Ransa duk ya baci meyasa su ke gaggawa ne? Ba su san matsalan da ya ke ciki ba ne shiyasa su ke kokarin kara sakashi cikin wata matsalar.
Ba niyarsa ya yi musu rashin d'a ba sai dai ya yi musu hakane saboda su yi Fushi su fita da Rayuwarsa su barshi ya tafiyar da ita a yadda ya ke ganin ta yi masa daidai
Kuma har ga Allah bai isa yace baya son Sultana ba sannan mganar tada alkawarin auran barazana ya yi ma Innani Saboda ita kad'ai ne makamin Nuclear da zai Harba ta isa garesu gabadayansu kuma ya yi nasara.
Gabadaya sai yaji gidan ya fita kansa in yaje gaida Umma fuska Daure ta ke amsa masa Abba kad'ai suke yar dad'i da shi.
Ita kuma Innani sai ta rika masa kukan ko bayan ranta in bai auri Sultana ba bata yafe masa ba.
Ranar ta ishesa yace"To karki yafe min mana, ai ba ke kika haifeni ba ko Tsine min kika yi bazan lalace ba Innani."
Ranar yini ta yi jan majina da an yi mgana sai tace"Makiya sun shiga tsakaninta da Magajin gida yau kiri kiri yace bata haifesa ba ko ta tsine masa bazai lalace ba."
Saboda Halin da ya ke ciki kwana Biyu bai kira Hasiya ba sai Ranar asabar da Safe ya kirata har sau hud'u bata Dauka ba.
Sai ya kyaleta bayan ya kwanta barci ya tashi sai ya kara kiranta sai ga shi ta Dauka.
Sai dai kuma a muryanta yaji kamar ta yi kuka, cikin tashin hankali ya mike zaune ya na fadin"me ya same ki?
Dagacham bangaran na kasa magana Saboda ko yaya na Bud'e baki zan yi magana kuka ne kawai zai tahomin.
Kawai sai na ce masa"Bakomai."
Kafin na katse wayar nan a tsakar Falo na zauna na had'a kai da Gwiwa ina ta rafzan kuka.
Kalaman Fadila kawai na ke tunawa Lokacin da ta ce min ni Annoba ce sannan Gobara daga kogi maganinta sai Allah.

Tun bayan zuwan Ummi gidan nan da kyakyawan mu'amalata tsakanina da ita bantab'a Tunanin watarana komai zai zama Tarihi ba sai da Fadila ta tare.
Ashe abunda bansani ba Diyar kanwar mahaifin Abubakar kawar Fadila ce itace tazo gidan ta ganni ni kuma bansanta ba,ballatana nasan cewa zata fad'i wani abu a kaina.
Ita ta kwashe komai na Rayuwata na baya ta gayama Fadila, daman kuma Tun farko jininmu ni da ita bai had'u ba da Ummi kadai ta ke huld'ar ni ko haduwa muka yi in na gaisheta sai ta ga dama ta ke amsawa bayan ta gama min kallon wulakanci.
Bansan ta gayama Ummi komai ba harda ma da karin karya sai da naga Ummi taja baya da ni, ta daina shiga Dakina ballatana mgana da ni, in ta dawo makaranta Dakin Fadila ta ke shigewa.
In na yi abinci na kai mata da Safe zan ganshi ta zuba shi a bola.
Sannan in nazo zan shiga Dakinta sai ta yi wuf ta fito ta kare kofa ko tayi min karyan fita zatayi ko tace mijinta ya na gida.
Kwata kwata daai ta sauya ba kamar yadda na santa ba.
Sai abun ya Dameni na kira Ramatu na Fad'a mata sai ta bani shawaran na sameta na yi magana ko wani Laifi na yi mata? Tunda zaman tare daman ya gaji haka.
Shine yau din bayan na gama abinci na zuba mata zan kai mata sai na same su kofar dakin Fadila suna zaune saman Cafet suna hira suna shan lemu gefe ga kololin abinci nan da alamu sun gama ci ne.
Na yi musu sallama ba su amsani ba sai da na kara sannan Ummi ta amsa.
Sannu da gida na yi musu sannan na mikama Ummi abincin.
Kamar bazata amsa ba sai ta karba a gabana ta mike ta isa wajen zuba sharan Fadila a kofar dakinta ta Juye shinkafa da wakenan a bola.
Sai raina ya baci na kalleta cikin mamaki kafin nace"Haba Ummi in bazaki ci ba ba sai ki gayamin ba, ai bai kamata ki zubar da abinci ba."
Kai Tsaye ta kalleni kafin tace"Gwara na zubar saboda kada ma wani yagani yaci ya ci ma kansa bala'i."
Baki sake na ke binta da kallo nan ko naji ta na zayyanamin har da fad'in an gayamata nice sanadiyar Mutuwar Mahaifina da Karayan arzikinsa.
Sannan na yi aure aure mazaje biyu duka sai da na Talauta su d'aya ma zaman garin sai da ya gagaresa.
Dayan kuma gabad'aya rayuwarsa ya kusa rasawa saboda ni.
Dole ne su daina rab'ata kada suma wani abu ya same su.
Maganganu na batanci da cin mutumci Fadila ta kalleni ido cikin ido tace ni Annoba ne kuma sunana Gobara daga kogi mganina sai Allah.
Sannan tace shima wannan auran da nayi ba'asan waye na aura ba shima ana Tunanin wani bala'in ne gagarumi zai samesa.
Ba na ganin gabana sanda na shiga daki sabida tashin Hankali da kuka, ina cikin kukan ne na samu kiran Assadiq.
kamar bazan dauka ba sai naga ya na ta kira na, sai na Dauka ina kokarin boye Halin da na ke ciki.


*BOJUWA HERBAL'S BY SURAYYA DEE*!

*Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Saiwowin maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Gaban ayu*.
*Hakkin daka gangariya*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*.
*Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya*
*08032773332*
*Ana dafa GIMBIYAR KAZA da tattabarun garari*.




*Janafty*
*TMWBK2012*


https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk

Ku zo ku yi sayayya tare da Yar Gidan Imam cikin aminci da kwanciyar hankali komai akwai harda kayan gyaran jiki hamshakan mata na supliments kala kala wanda ba su da illa, akwai kuma gagarumin haɗin mu na Arabian sabaya powder wanda babu kamarsa wannan ba irin sabayar da ki ka saba gani bace, kayan kicin dogayen riguna kuwa ba'a magana ke dai ki yi sauri ki shigo domin kwasar roman wadannan kayan.


Na jin sanda ya ke ta kirana da ta yanke kuma sai wani kiran ya biyo baya.
Gabadaya na rasa tunanin da zan yi kwakwalwata ta tsaya cak a waje daya zuciyata ta cunkushen da na kasa Sarrafa kaina ballatana nayi Tunanin wani abu.
Kuka na ke rerawa wanda ke fitowa daga karkashin zuciyata kuma ya ke amsar duka gangar jikina.
Tabbas na yaudari kaina in ina Tunanin kwanciyar Hankali da na samu a gidan Assadiq mai Dorewa ce, kuma na shagala da yawa matukar nayi tunanin abunda ke shafan Rayuwata zai iya gogewa har Abada.
Nasan duk abunda suka fad'a gaskiya ne ya faru a kaina sai dai abunda har yau bangane ba ne meke faruwa da Rayuwata ne? Anya ni mutum ce ko Aljanna? Amma tace ni ba mayya bace ammh meyasa abubuwa marasa dad'i basa tashi Faruwa sai abunda ya dangance ni ko ya matso kusa dani?
A d'an ilimin da Allah ya bani na dad'e da sanin babu mai yi sai Allah sannan Amma ta fad'amin Allah ne kad'ai ke da ilimin sanin gaibu ba Mutum ba sannan ta sha zaunar da ni ta fad'amin ni ban isa na rike kaddaran wani a hannuna ba duk abunda ya Faru da Abubakar ko da Salisu daga Ubangijin sammai da kassai ne, sai dai ya kasance kowani abu na duniyan nan akwai sanadin to ni ce na ke kasancewa sanadin duka al'amuran su.
Meyasa mutane ba su da Tunani ballatana saurin Fahimta irin ta Amma? Ko da ya ke sai na tuna da yar'uwata Adda Rukayya itama ba ta dad'e da daina kallona a matsayin Annoba ba, Mijinta kuma da Ahalinsa har gobe a bar gudu suke ganinaa.
Cikin satin nan naje gidanta ko awa Biyu ban yi ba na dawo gida Saboda Mijinta ya dawo sun shiga ciki naji ya na gayamata bayason ina zuwa masa gida saboda ya na son rayuwarsa sannan ya na son ya tsira da arzikinsa.
Bata ma san na fito daga gidan ba sai dai fitowa tayi taga na tafi har na kawo gida ina kuka na rasa ina zan Nufa Amma tamin nisa ballatana na samu kafad'anta na kwanta na sha kukana ta lallasheni sai na Dawo gida na kulle kaina acikin daki nayi kuka kamar raina zai fita.
Ban taba tunanin cewa Fadila na da alaaqa da Ahalin mijina na Farko ba. sai yau da ta ke fad'amin wacce ta sanar da ita komai game da ni.
Da dukkan zuciyata na ke kuka kamar raina zai fita a wannan Lokacin nayi Fatan Mutuwa ban san iyaka ba.
Na duba na hango sai naga ai banga amfanin Rayuwata ba in dai zan kasance Annoban da ke illarta da Mutane to rayuwata ba ta da wani amfani Tunda in dai ina Raye sai na zauna da Mutane kuma na
Showing 48001 words to 51000 words out of 98628 words