fi Sarari bayan ya yi wanka ne ya Kira Sultana yace mata ya Dawo ta kawo masa abinci.
Shine kafin tahowarta ya samu ya Kira Siya tunda ta na makale a ransa baya so su yi tafiyar Dare gwara su isa cikin Lokaci.
Sun yi sallama kenan ya na zaune falon Abba gajiya duk ta kamasa har yanzu DogomnTuki bai gama zama ajikinsa ba.
Dogon wando ne a jikinsa sai karamar Riga mai gajeren Hannu.
Sanda Sultana ta yi sallama ta shigo bai yi niyar Dagowa ba sai dai kamshin da yaji ya shiga Hancinsa ne yasa ya Bude ido da Sauri ya na Bin inda kamshi ya fito da kallo.
Sultance a tsaye a gabansa ta ci gayu Cikin Materila din yinin Biki hannayenta sun sha jajayen kunshi Ta kashe dauri ga shi an yi mata makeup wanda ya yi mata kyau sosai.
Mayafinta itama Coffea ne ammh kuma karami ne.
Hannayenta Dauke da Farantin abincin nasa da ruwa da lemu.
Har ga Allah bai san ya shagala da kallon Sultana ba sai da yaji ta na masa Sannu da zuwa.
Sannan ya farga da Sauri ya basar ya na gyara zamansa.
Cikin shakewar murya ya amsa mata ya na satan kallonta kasa kasa ta na Duke tana zuba masa abinci.
Sai da ta gama sannan taja Center table din dake falon ta Dora masa komai sai kuma ta kallesa cikin mirmishi kafin tace"Bismillah."

Ba musu ya matso domin ko karyawa bai yi ba, mahaukaciyar yunwa ya ke ji.
Ya fara cin abincin kenan ta zuba  masa ruwa a wani karamin kofin Tangaran ta na Shirin mikewa ya kalleta da Sauri ya na fad'in"Abba fa? Ban gansa ba?
Cikin yanayin maganarta tace"Abba ya fita Tun Safe."
Kai ya jinjina kafin yace"To miye na taro Biyu? Ba gobe  ne Daurin auran ba?
Mirmishi ta yi kafin tace"Yaya Sadiq Ya Mubarak fa yace an ana gama Daura aure za'a tafi da Anty Salima"
Sai da ya Cinye abincin bakinsa sannan yace" shine daidai ammh wannan taron duk shirme ne."
Ita dai sai mirmishi ta ke yi baya so ta tafi Saboda kwaliyarta ta yi masa kyau.
Sai ya fara hasaso irin kwaliyar a Fuskar Siya di'nsa.
Har baisan sadda mganar zucci ya Fito Fili ba yace"Wow Beatufull."
Saboda har ya hango kyan da Siya zata yi in da itace ta yi wannan kwaliyar.
Sultana ko ta zata da ita ya ke ta Rufe fuska da tafukan hannayenta ta na Fadin"Thanks Yaya Sadiq."
Sai a lokacin ya fahimci aikin da ya yi sai bai karyata kansa ba ya kalleta ya na fadin"kin yi kyau ya zama dole Abubakar ya biya tukwaicin wannan adon."
Sai jin dad'i ta ke yi ta na masa wani Fari da ido lokaci daya ta na yarfa Hannu.
Bai sallameta ba har ya gama cin abinci sai janta da Hira ya ke yi , anan kuma wajen ya tura mata 5k ta acct dinta yace Tukwaicin gayun da ta yi Sultana zuciyarta kamar Farar Takarda Saboda Haske.
Ba ta bar Falon ba sai da Siyama ta kira wayarsa ya na Dauka bayan sun gaisa tace masa Sultana tazo yan makarantarsu zasu tafi.
Dalilin da yasa ya sallameta kenan, ta koma cikin gida shi kuma saboda mata sun yi yawa bai ko yarda ya Fita ba sai chan da yamma da baki suka fara Raguwa yan gari.
Sannan ya sake wanka ya saka Shadda mai Ruwan kasa, kayan da zasu saka Gobe Farare ne Tahir ne ya matsa masa shi ya Tura ma kudi ya siya musu shaddar tunda yace yasan inda zai kai musu d'inki.
Sannan Abba ma ya dinka musu su biyu, sannan ya dinkamusu har da su Baba Sammani, da sauran yayen su maza matasa har da Baban Sultana Mallam Datti.
Sai Dare Abba ya Dawo gidan a masallaci suka had'u da Sadiq sai bayan sallar Isha'i suka baro masallacin zuwa cikin gida.
Sai lokacin sauran yan'uwansa suka gansa Shashen Innani ya fara Shiga gaida Mutanen Shinkafi.
Da ya ga Innani sai da ya yi Dariya har ya na Rike ciki.
Ga uban Gwagwaro da ta maka a kanta ga gilashi, sai kuma wani Uban mayafi mai kauri mai kama da Bargo da ta yafa sannan ga wata jaka kamar ta wamzamai tace na Tara kudin Biki ne ai ba'a zo a tafi haka ba kuma Hidimar nan dai Sulaimanu ya yi ba Suwaiba da Danginsa ba ahto gwara dai a rika yi ana Tausayama Sulaimanu.
Abba na gayamasa maganar gwagwaro Innani sai da tace in ba'a nad'o mata ba  sai ran kowa ya baci sannan Dakyar ya hanata Dauko masu Kidan kwarya ammh tace bikin Sulsana da Magajin gida taga Uban da zai hana makid'a shigowa gidan nan
Abba ba ya son Bid'a su ma walima kad'ai Amarya da kawayenta tare da yan'uwanta suka yi.
A daram Sadiq har shashen Mama ya shiga ya yi mata Allah ya sanya alheri yan'uwanta suka fara zolayansa da Ango gaba tuna shima na shi kamar Gobe ne shi dai baya mgana sai dai ya yi mirmishi.
Shaahen Umma ne yaji daman bai Shiga ba cike da yan'uwansa mata da kawayen Amarya da su Sultana.
Ya na shigowa suka Dau Ihu suna Fadin"Ga angon Sultana Fari mai farin Aniya."
Duk yadda yaso ya zille suka hanasa suka Takura masa sai sun yi Hotuna haka ya tsaya suka yi ta Daukan junansu har da Amarya Salima da ta sha kyau kamar ba ita ba.
Daga karshe Sajida tace"Ku matsa ku bama Magajij gida waje shi da Amarya su sha Hoto."
Hararanta ya yi bai samu zarafin mgana ba suka Turo Sultana gefensa suna Daukansu Hotuna suna Dariya.
Sajida har wani Had'a jikinsu ta ke waje daya ya make hannunta ya na fadin"Sajida."
Dariya ta yi masa har da gwallo sai ya rasa yadda zai yi da ita.
Karshe dai har rike kugun sultana sai da suka saka ya yi da ya gaji ne ya hade rai yace"Kai nagaji."
Surraya tace"Bakomai akwai na gobe mai Hoto na nan zuwa."
Shi dai sulalewa ya yi ya gudu sai a bangaren Abba yaga Umma suka gaisa Hidima ta yi musu yawa.
Sai da Safe ya samu zuwa ya gaisa da Iyayen Sultana wato Matan Mallam Shitu kenan.
Rana  bata karya sai dai Uwar Diya taji kunya karfe Sha biyu da Rabi na rana aka Daura auran Salima Sulaiman Abubakar Shinkafi da angonta Mubarak Jibril Mamman.
Akan Sadaki mai Daraja.
A masallacin kusa da su In da Abba ke sallah aka Daura auran.
Daurin auran da ya sami Hallatan manyan baki kama daga abokan kasuwancin Abba yan anguwa, Mutanen Shinkafi dangin Umma da Mama Mazajen ya'yansa da Sauran su
Sai Tawagan Ango daga Kaduna suma gayya Guda bayan Tawagan Uban ango shima sai wanda dai ya gani.
Sadiq daman Shigar Farare suka yi shida Tahir da sai ana gabda ma Daurin auren ya iso garin Sadiq na mamakin Tahir komai yace ba shi da Lokaci kamar majalisan Dinkin Duniya.
Daga nan reception din da Abba ya shirya suka je suka yi, Dagachan angwaye suka rigasu dawowa saboda Daukan Hotuna da Had'a Hadan Tafiya da Amarya.
Hayaniyar gidan ta ishi Sadiq shiyasa yace ma Tahir su zauna a Restaurant din nan su Huta.
Ga shi ya na son Kiran siya ba Dama, Tun jiya da suka yi mgana ta gayamasa sun sauka lafiya.
Basu baro Wajen ba sai da Abba ya kirasa yace yazo gidan yan'uwansa na nemansa za'a tafi da Amarya.
Koda ya zo duk suna haraban gidan ga Motoci ne birjit na tafiya kaduna.
Hotuna suka yi har da su Umma da Abba da Mama da su Baba Sammani.
Har da su Goggo Husai.
Su Mallam shitu da wasu sauran jama'an ana gama Daurin aure kamar Mota Biyu suka koma Shinkafi.

Salima ta sha kuka daman Nasiha tuni Abba sun yi mata sauran yan'uwanta ma ba'a bar su a baya ba.
Da har ance a kaita bangaren Innani sai aka ji ta na masifan a fitar mata daga Shashenta zata kulle ne kaduna garin gwamma zata je kai amarya.
Kuma wlh duk sai da aka fita ta saka wata yarinya kanwar Sultana ta saka mata kwad'o a kofar falonta.
Kuma saboda matam baban Sultanan ne yasa tace zata rufe shashenta.
Tunda suka zo Bikin nan Innani ke bala'i ta na Habaicin wani Hisabin dai sai a lahira.
Sai gata da jakarta Tun na saudiya nan, ta cikata da kaya ta ci Atamfarta ta yinin biki zanin nan a kauri ga uban Daurin da ta Guma a kanta ga gilashi ta na tafiya ta na Dingisa sanda.
Ba wanda bai yi Dariya ba a yi mgana kuma tafara tsine tsine.
Abba da su Umma sun yi sun yi Innani ta yi zamanta kai Amarya  tace Uban kuturu ya yi kad'an sai taje gwara taje ta saka ido Bikin jikarta ne.
Sadiq da aka so ya yi mgana wannan karon bai yi ba da kansa ma ya saka Innani a motar amarya yace ta je ta Raka Salima dakinta.
Umma zata yi magana ya kalli su Sakeena ya na fadin"Ku kula da ita in kun isa chan."
Sai kowa ya gyada kai Innani ko sai lekowa ta glass ta ke ta na kwararama Sadiq addu'a.
Daga Siyama, Sultana sai kawayen salima guda biyu a dakin Umma kuma Sadiya da sa'adatu Sai Sajida, Dakin Mama kuma Sakeena da Saliha da Shahida Sai Umma sai Kanwar Mama sai Goggo Husai da matar Baba Sammani, sai matar Baban Sultana da Innani bata ga shigar ta Mota ba da tace tace in taje Allah ya tsine mata.
Sa'ima da Surayya da Suba'atu sai gobe zasu taho da sauran mutane da wasu kayan.
Karfe Biyu da wani abu na Rana Motocin Amare suka Dauki Hanyar kaduna.
Daman Alhaji jibril tun daga Wajen Reception suka wuce.
Suna tafiya ba Dadewa Tahir yace zai tafi  sadiq bai damu ba yace a sauka lafiya.
Shima bai ma san tafiyarsa ba bangaransa ya koma ya na kiran wayar siya ammh bata Dauka ba, sai ya yi Tunanin kila ta na cikin Hayaniya ne

******

Ni ko ba biki ne ya yi biki ba da yasa ban ji kiran wayar Assadiq ba.
Wayar ta na cikin Jaka kuma Adda Fati na bama ajiyar Jakar da Safe kuma basa nan suna makota gidan suke wai aikin abinci.
Ita da Adda Rukayya ni dai nace ba na jin dadin na yi kwanciyata Dakin Zahra'u.
Yaran gidan ma sai da muka zo na san su wlh, da ya ke kuma ba son mutane suke yi ba Daga yan'uwan matar gidan kad'an sai mu Dangin megidan Daga Zariya.
Ita naji ma ana fadin a gidansu take nata taron ita uwar bikin, gidan sai bai wani cika ba sai mutane kad'an masu Shigowa.
Abinci ma a wani waje aka Dafa sai dai aka kawosa a dafe kawai aka fara ci.
Na samu sakewa kad'an Tunda matar gidan ta na da Kirki ita da ya'yanta Yan zuwa Bikin ne marasa Mutumci wato ya'yan su Baba tanko da Baba Saminu daga Zariya.
Ina ga ko ba su so mu zo ba ne bansanin mu su ba, ni dai tunda na samu Zahra'un ta jani Dakinta sai Washegari na fito.
Hajiya Murnajatu sai godiyan kudin da Adda Fati ta bata ta ke yi mana.
Bata gane mu ba sai da Adda Fati ta yi mata bayani sannan ta gane mu.
Shi ko Baba Jibril din ban san ko ya gane mu ba, mun dai gaisheshi da Safe da suka Shigo gidan suna gabda Tafiya Daurin aure.
Angon ma daga nesa na ganshi ni ko a Hanya muka had'u bazan iya ganesa ba.
Su zahara'u sun yi sha'aninsu sun yi gayyar kawayensu ba laifi, sai bayan La'asar Su Baba Jibril suka dawo ni kuma sai a lokacin na yi wanka na Saka Atamfata.
Tunda sai da na jira su Adda Fati suka Dawo kayammu na wajen su.
Su ne ke shiga cikin yan'uwa ni kam sanin bakin fenti na yasa na ke sahale kaina a gefe.
Ina dakin zahara'u in nagaji da kwanciya na mike da ya ke ina al'ada ba na sallah Shiyasa.
Ina ji da yammah ana karadin Saukan Amare daga Gusai ban fito ba.
Sai bayan mangariba Adda Fati ta leko tace nazo muje Za'a raka Amarya gidan ba na son zuwa sai nace su je kawai ba na jin dadi.
Har ga Allah ban so zuwa ba sai da Fathihatu ta shigo Daukan abu ta ganni kwance cikin Fara'a ta min mgana ko lafiya?
Nace mata lafiya lau sai kawai tace na tashi mu karisa gidan Amarya.
Na kasa yi mata musu sai na tashi na saka mayafi, jakata ce har yanzu ta na Hannun Adda Fati na ganta a hannunta sanda tazo min mganar tafiya raka Amarya.
A motarta muka tafi ni da ita gidan duk ya watse sai kalilan duk jam'ar na gidan Amarya.
Ashe ba Nisa tafiya kad'an muka yi sai gamu mun iso gidan a waje ta faka Motar sai a ka kirata a waya, ta tsaya ta na mgana sai tace na Dauki wata karamar kula muje gata nan zuwa.
Sai na yi gaba saboda sha'ani sabon get din gidan ya na Bude ne ina Turawa na shiga.
Haraban gidan akwai haske tar kamar an kuna gen ne ko kuma kila wuta ne domin naga anguwan ko'ina da haske.
Ina shiga gidan na rasa ina zan nufa Tunda Kofar falon da na gani kamar a Rufene kuma ina jin hayaniya daga ciki.

Bansan ta inda Tsohuwar nan ta Bullo ba ganinta kawai na yi a gabana, yadda ta ke dogara sandar hannunta ne yasa na tabbatar bata gani.
Kamar kila Motsi taji sai ta fara fadin"Waye anan ne?
Cikin mirmishi nace"Ni ce iya."
Innani ta yamutsa kafin tace" ni sunana Innani yar nan nace ko cikin yan'uwan mijin ki ke ne ko?
Sai na amsa da Eh da Sauri tace"Taimaka min ki Dubamin gilashina karfen nasara ba Tabbas daga Fitowa ai na sha iskar Ubangiji ya na fuskata ya fad'i daganan ne na nema na rasa."
Da toh na amsa mata ta na nuna min inda tabi da sandarta ni kuma na Duka ina Dubawa sai ga shi na ganshi kusa da kofar falon.
Na dauko mata na goge mata na karisa gabanta na saka mata shi fuskarta ina fadin"Iya ga shi nan na gano miki."
Innani jin gilashi a Fuskarta yasa ta kara gwale ido ta na kallona.
Nima ita na ke kallo abun mamaki Irin kayan da ke jikinta nima shi ne ajikina.
Kafin mu samu Zarafin mgana dagani har Tsohuwar da tace sunanta Innani wata mata ta fito da Sauri.
Ta na Dube Dube ta na ganin mu sai ta Sauke Numfashi.
Da ya ke na juya baya bata fuskata ba sai ta kariso ta na fadin"Saliha ashe Innani na tare da ke? Na tsorata da na Duba ciki ban ganta ba."
Juyowa na yi muka had'o ihu hudu da ita sai da mukaji wani iri.
Kallona ta ke yi nima ina kallonta cikin mamaki.
Innani ce ta tabe baki kafin tace"Wata Salihar? Yaran da tunfa muka zo ban kara ganin su ba, wata yar mutumci ce ta taimakeni kin ji yar nan Allah ya yi albarka."
Ta fad'a ta na Dafa kafad'ata, Umma ta kalleni ta kara kallona nima na kalleta sai kuma na sunkuyar da kaina ina gaisheta ta amsa cikin Sakewa kafin tace"Ayya to mun gode"
Da kai ma amsa mata Hannun Innani ta kama suka wuce ammh ta waiwayi ta kalleni nima kuma ina ta kallonta har suka shige cikin Falon.
Kila ta na mamakin kayan jikina ne, ni kuma Muryanta ne naji ta yi kama da na wacce na sani.
Sannan kamminta ne ya yi kama da na wanda na sani Ammh na kasa tuna komai.
Sai kawai na Cigaba da Tsayuwa ina jiran Wacce muka zo tare.
bazan iya Shiga gidan ni kad'ai ba Tunda bansan kowa ba.


Mata muntashi tsaye mu yaki infection (sanyi) Wani ciwone Mai nacin gaske Wanda idan kikayi wasa xaihanaki jindadin Aure Sannan maganin shi saikin daure da nacin shanshi Akai Akai toh kufito🤌🏽 KUSAI TSIMIN TABAJE DOMIN MUNA DAFASHINE DA INGANTATTUN SAIWOYI MASU AMFANI AJIKI DAKUMA LAFIYA, CIWON SANYI, SANYIN MARA, BASIR DASAURANSU INSHA ALLAH DUK WANI CIWO INDAE NA SANYINE ZAIZO KARSHE DA YARDAN ALLAH KIDAE KIDAURE KIDUNGA SIYAN TABAJE KIJEFI TSUNSTU GOMA DA DUTSE DAYA💃💃💃
Akwai infection Wanda yake nuna kanshi Akwai Kuma kurman infection Wanda baxaki San kinada shiba Amma yanacan yana Miki illa domin duk kyan Kayan mata baxakiga aikinsu ajikinki ba ko Kuma sumiki aiki bayanda akaso ba
Anason duk bayan wata 1 mace tasha maganin infection sbd samun lafiyar jikinta
Alamomin shi sune
Fitar farin ruwa
Kaikayin gaba/ko kuraje
Jin zafi yayin sex
Daukewar ni'ima
Daukewar sha'awa dadai sauran su
Kafin kifara Shan maganin mata yakamata ki fara Shan maganin infection
Ina Yan mata Budurwa kema Yakamata kidinga Shan maganin infection Dan kariya da lfy ki karsai kinyi Aure infection ya Riga yamiki illa Baki saniba Allah y bamu lfy y karemu Ameen 🙏



*Janafty*
*TMWBK2019*

*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*

Mai_Dambu Candy world's and more. Zaa iya samun Tuwon madara da iloka, gullisuwa, aya mai sugar, gyada mai gishiri, sannan muna bada sari, muna kuma karban oda da aikin biki ko suna. Muna karban aikin donut da cincin..08130269641

https://chat.whatsapp.com/I7uxPXgtPKBHnVQjaEbRlE


Na dad'e tsaye bayan shigewar matar nan da tsohuwar da ta kira kanta da Innani ciki kafin Fathiha ta shigo.
Ganina tsaye yasa ta rike baki ta na fadin"Kina tsaye? Me yasa baki shiga ba?
Mirmishi na yi mata ammh ban yi magana ba sai ta yi gaba ta na fad'in"Muje."

Ni kuma jin haka sai na bi bayanta har zuwa cikin kayattacen Falon Amarya da yaji komai na kayan more rayuwa masu kyau da inganci.
Sai dai me? A falon ma duk da akwai wasu daga cikin yan'uwan uwar ango akwai na Amarya aciki ma su sanye da irin kayana.
Mamaki sai ya kara kamani suna kallona nima kamar yadda na ke kallon su, cikin mamaki Sa'adatu da ke falon ta kalleni ta na fadin"Laa Sadiya ga irin ankon mu?
Ta fad'a ta nuna ma wata da ke kusa da ita wacce ke latsa wayarta.
A tare suka kara kallona kafin ma na yi mgana Fathihatu ta kalli kayan jikina kafin tace"Laa iri d'aya kuwa ni ban lura ba."
Sadiya tace"Yar'uwan ku ce?
Fathihatu ta gyad'a ta na fadin"She is a Cousin."
Sannu dayar tace min ta farkon kenan Sadiya nima na amsa mata da Sannu, dayar wayarta ta cigaba da latsawa.
Wurga ido na fara yi ina neman su Adda ban gansu a falo ba sai na Fara Tunanin ko sun koma gida ne.
Sai wata cikin dangin Ango tace sauran suna d'ayan dakin suna ta sallah.
Sai Fathihatu ta jani zuwa Dakin da Amarya ta ke ciki tunda ga Hayaniya nan muna jiyowa.
Ni ban
Showing 84001 words to 87000 words out of 98628 words