kwashe koma zuwa bangaran Umma.
Suka kuma ja Fathihatu tare da su, Siyama da Sultana suka gyara wajen sannan suka ce Zahra'u ta zo su tafi, sai suka koma Shashen Mama suka zauna.
Salima kuma Dakinsu ta shige abunta bata ko zauna  a falon ba, inda su Siyama ke zaune suna taba hira ba.
Mubarak kad'ai aka bari da su Abba afalon sai su Umma da ke chan gefe suna ta hira da Hajiya Murjanatu.
Innani gyangad'i ta fara ta na zaune sai Alhaji Jibril yace ko zata shiga ciki ne ta kwanta.
Innani na jin haka sai tace bakomai ba barci take yi ba kuma da gasken barci take ji ammh kada ta tashi a yi wata mgana bata sani ba ne.
Kamar ko ta sani taji Alhaji Jibril na Tambayan Abba cewa bai ga Abubakar sadiq ba ko baya nan ne?
Kafin ma Abba ya ba da amsa Innani ta yi zaraf tace"Magajin gida ai ya na chan wani gari ne ma Salamatu?
Ta fad'a ta na kallon Umma wacce sai alokacin ma taji mganar.
Cikin alamun tambaya tace"Waye Innani?
Innani tace"Wai magajin gida ya ke tamnbaya nace ya ma wani gari ne?
Umma ta yi mirmishi kafin tace"Ya na chan Zariya ya na Hidimar kasa Innani."
Innani ta washe baki ta na fadin"An yi ko haka ya na chan zariya abun shi gidan sai ya yi ba dad'i da bayanan ka san shi ai na Innani ne in dai yana gidan ne to bai da wata uwa da ta wuceni nan ne wajen zamansa barci kawai ke kaisa bangaransa."
Alhaji Jibril yace"Allah Sarki."
A ransa ya na mamaki kamar Alhaji Sulaiman ace dansa ma ba'a waje ya yi karatu ba? Kuma wai ya na zariya ya na Hidimar kasa sai abun ya yi masa wani iri.
Sai dai bai yi mgana ba kamar an tambayi innani ta tsinke da labarin cewa Magajin gida zai auri Sultana an kusa bikin ma.
Abba ya kalleta cikin mamaki ba Halin ya yi mgana.
Alhaji Jibril kuma da mamaki ya kalli Abba na neman karin bayani.
Sai Abba ya gyara zama ya na fad'in"Sultana diyar kanwata ce da ta rasu nan ta ke wajena ita ce mu ke so mu had'a auran su da Magajin gida in sha Allahu."
Alhaji Jibril ya had'iye wani miyau mai daci ya kasa mgana ita ko Innani fad'i take yi wata yarinya nan mai kokari da suke ta kai da kawo ita da yar uwar ta? Wata mara kaurin jiki doguwa haka ita adole sai Alhaji Jibril ya ganeta.
Sai ya yi mata yake ya na fadin"Ma sha Allah wannan tunani ne mai kyau Alhaji Allah yasa muna raye."
Innani da karfi tace"In sha Allahu ma muna raye za'ayi auran magajin gida da Sulsana."
Alhaji Jibril ya Dukar da kai ya kasa mgana Umma ce ta juya ta na ma Hajiya Murjanatu bayanin had'in Auran Sultana da Magajin gida da ke chan zariya ya na Hidimar kasa ammh ya kusa gamawa ya Dawo gida.
Abba kuma ya na ta ma Alhaji Jibril magana sau yaga kamar ya d'an Shiga damuwa.
Cikin mamaki yace"Alhaji nace ko lafiya?
Alhaji Jibril ya sauke Numfashi cikin Damuwar da ta bayanna har saman fuskarsa.
Cikin wani irin sauti yace"Shikenan kawai Alhaji."
Abba yace"Shikenan me ya faru? Ka fad'amin mana?
Alhaji Jibril ya kara sauke Numfashi kafin yace"Alhaji mganar bata da amfani mu bar ta kawai."
Shi kuma Abba ya Dage sai ya gayamasa ko wata mgana ce.
Jin ja'in jansu yasa hankalin su Umma ya dawo kansu.
Har da Innani wacce tace"Fad'i damuaarka Jibrilu kamar yadda ka Daukeni uwa haka nima na Dauke ka d'a kamar Sulaimanu."
Alhaji Jirbril ya kalli Matarsa Hajiya Murjanatu itama sai ta kallesa cikin mamaki Saboda ta kasa gane ma'anar kallon na shi.
Sai kuma ya koma ya sunkuyar da kansa kafin yace"Had'uwar kasuwanci ne ya had'amu da Alhaji Sulaiman ammh jinsa na ke yi kamar Dan'uwa na jini Shiyasa na yi Tunanin na kara karfafa alaqar mu ta hanya aurattaya a tsakanin ya'yan mu."
Innani ta washe baki ta na fadin"To miye abun damuwa? Ga mu nan da yaran mata a gida sai shi dan wajen naka ya duba ga Salima da Siyama ni da zai ji shawara sai ya zabi Siyama Domin tafi yayar Hankali da natsuwa kunga shikenan ma sai a had'a bikin su rana d'aya da na magajin gida da Sulsana."
Kallonta kowa ya yi ya na mamakin ko gama mgana Alhaji Jibril bai yi ba har Innani ta yanke mgana.
Shi kuma Mubarak da yaji komai har ransa yaji dadi daman kuma kila Rabon auran shi da Salima ne ya had'a Abba da Baba suka san juna.

Maimakon yaji Alhaji Jibril ya karbi mganar Innani sai kawai yaji ya na Fad'in"Ba Mubarak na ke mgana ba Innani ina mganar Yar wajena Zahra'u da d'an wajen ku Abubakar Sadiq."
Sai falon ya Dau shuru kallo ya koma kan Alhaji Jibril.
Innani ko ta na jin abunda yace ta wani yamutsa fuska kafin tace"Wani Abubakar Sadiq din da wata Zahra'un?
Da sauri Mama tace"Magajin gida dai Innani da kika sani Sadiq."
Innani ta rafka salati ta na tafa Hannu har da wani cire gilashinta ta kare ma Alhaji Jibril kallon sama da kasa sannan ta maida gilashin nata lokaci d'aya ta na fadin"Ammh kai a wani gari a ka haife ka?
Ta fad'a ta na wani yamutsa Fuska
Alhaji Jibril cikin Ladabi yace"Ni haifaffan garin Zariya ne Innani aiki ne ya kawoni kaduna har kuma na yi aure na tara iyalai."
Innani ta wani tabe baki kamar taga kashi kafin tace"Ba shakka. Hala baka jin bayanin da na yi maka ba ne? Naga alamun baka gane bayanin namu ba ne bari na yi maka gwari gwari shi magajin gida da ka ke mganar a had'a shi da wannan Gajerar yar taka da matar sa wannan yar fara yarinyar Doguwa sulsana itace wacce zai aura ba domin ma Magajin gida yace a dakata ba ai da yanzu kila ma an samu Rabo."
Kunya ta kama Abba da su Umma na kalaman Innani da suka yi Tsauri.
Ita kuma Innani tunda taji yace yarsa ta san wannan gajeran ce tunda yar mai Tsawon da auranta har da ya'yanta.
Hajiya Murjanatu ko bakinciki ne suka mata runbdgu lokaci d'aya yasa ta kasa mgana illah kallon mijinta da take yi cikin Tuhuma meyasa baban bintu ya ke raina mata wayau ne haka? Ta yaya zai yanke Hukunci kan yarsu ammh bazai sanar da ita ba.
Sai da yazo ya yi mganarsa kuma ba ta samu karbuwa ba daga baya kuma cin zarafi na neman biyowa baya
to cin zarafi mana Innani tace gajerar yarsa da kushen Halitta a lamarin kenan.
Alhaji Jibril kuma ya kasa kallon matarsa ballatana su Innani ko da akazo wannan gabar bai ji ya karaya ba.
Sai ma kara Rusuna kai da ya yi ya na fad'in"Ai shiyasa da naji haka na so na Binne mganar a rai ku ka matsa har sai na sanar da ku."
Innani ta kallesa a rene  sai taji bala'in haushinsa take ji wato daman ba Domin Allah ya ke wannan ladabin ba saboda ya samu biyan bukata ne lalle aiko sai dai  ya bi wani sarkin.
Mubarak kuma Mamansa ya kallah itama ta kallesa sai dai ba su da ta cewa a yanzu tunda ba su da wannan Hurumin.
Abba ne ya yi Saurin cewa"Bakomai Alhaji Jibril na yaba da karamcinka. magajin gida kuma mijin mace hud'u ne bayan ya auri Sultana zai iya karawa da Ita Zahra'un."
Innani na jin haka bata bari ma ya Rufe baki ba ta saka musu kuka mai had'e da ihu.
Har da kurma ihun wayyo Allahta ta shiga uku.
Abba da su Umma suna Rige rigen isa gareta domin jin abunda ya sameta.
Ammh sai Innani ta cire gilashinta ta fara goge hawaye da Haban zaninta Lokaci d'aya ta na fad'in"Shikenan Sulaimanu shikenan zai saka a yi ma Susalana kishiya itama a kashe min ita kamar yadda aka kashe min kuluwata."
Ta karishe fad'a ta na mai kara fashewa da kuka kamar wacce ake yankata.
Umma ta kalli Abba shima ya kalleta Hajiya Murjanatu ta isa gaban Alhaji Jibril a sannu ta na fad'in"Me ka ke shirin aikatawa Baban Batul?
Kallonta ya yi kafin kai tsaye yace"Abunda kunnen ki yaji miki Murjanatu."
Da haka ya kauda kansa, Abba ko da su Umma suna ta faman lallashin Innani ammh taki daina kuka.
Kara fad'i ta ke yi za'a kashe mata Sulsana kamar yadda kishiyoyo suka kashe mata Kuluwarta.
Abba ya kalleta ya na fadin"Innani ki daina da Fad'in haka Hauwa fa lokacinta ne ya yi ba kasheta abokan zamanta suka yi ba fa."
Innani ta dago da idanuwanta da bata wani gani ta zabgamasa harara kafin tace"Matsa ka bani waje kai me ka sani? Kai dai a yi sha'ani kawai ammh a ranar gobe kiyama akwai tarin Hisabai a gaban Ubangiji ko tawa da Shitu kad'ai ta isa b'ata lokaci."
Mama ta so ta yi dariya ammh ta Daure ammh sai da ta juya baya ta na tarin karya.
Abba ya jinjina kai kafin yace"Shikenan naji ki bar mganar na nan don Allah."
Innani tace"Ta ya zan bar magana kana neman kace za'a yi ma Sulsana kishiya tun ma kafin ta shiga gidan?
Sulaimanu anya kana so ka gama da duniya lafiya ban sallamaka ba.?
Umma ta yi saurin taran Innani da cewa"Haba Innani bai kamata ba."
Kawai sai Innani ta cigaba da kukanta shi kuma Abba kunyan Alhaji Jibril yasa yace"Innani addini fa ya bamu damar auran mata sama da d'aya Hudu ya ce mu yi in muna da Hali."
Innani ta dago ta na kallonsa ranta bace tace"Wlh ko bayan raina a ka yi ma jikata Sulsana kishiya ban yafe maka ba Sulaimanu."
Ba su Abba kad ai suka zaro ido ba hatta da Alhaji Jibril da Hajiya Murjanatu.
Abba ya kalli Innani kafin yace

"Innani.."

Bai karisa ba ta katse shi da daga masa Hannu Lokaci d'aya ta na fad'in"Da wanda ya biya Sadakin da wad'anda suka zo daurin auran dukkan su Allah ya tsine musu ba su da albarkata kai har da shi magajin gidan inda ya sake ya yi ma jikata Kishiya ba ni ba shi har abada ni da shi uban kowa ya yi ta kansa."
Ai ta na fad'in haka sai jikin su Umma ya yi sanyi su san ta gama mgana Tunda har magajin gida bai Tsira ba.
Alhaji Jibril ya yi shuru ya na wani nazari kafin Daga bisani kamar an zabure sa ya mike zuwa gaban Innani ya Durkusa ya rike hannuwanta.
Ita kuma cikin masifa tunda ba gani take yi ba tace"Waye wannan kuma?
Da sauri yace"Ni ne Innani.".
Sai da ta ji muryansa sannan ta Saurara ammh fa ya sha harara da tabe taben baki.
Cikin Ladabi yace"Innani kada ki damu tunda baki so ba wanda zai yi ma Jikarki kishiya ko bayan ranki in sha Allahu"
Ba kunya ba komai Innani ta washe baki kafin tace"Ko kai fa? Ka ga dai an riga an ba shi ita kuma dangi kowa yasani nace maka ma ba domin magajin gida yace a dakata ba da yanzu kila har da rabo."
Alhaji Jibril yace"Bakomai Innani in Lokacin ya yi a sanar damu in sha Allahu zamu zo."
Innani tace"In sha Allahu kuwa Allah ya yi albarka kada ka damu kaji ko? Ba domin Sulsana ba ce da Tuni mun amimce ammh kada ka damu ka Siyama nan da Salima wannan Saurayin d'an naka ya zab'i daya acikin su sai a yi had'in zumuncin ba shikenan ba."
Alhaji Jibril yace"Shikenan ko Innani yadda kikace haka za'a yi"
Innani ta washe baki ta shiga saka masa albarka.
A daidai Lokacin aka fara kirayen kirayen sallar la'asar yasa mazan suka tafi masallaci matan suka yi na su a gida.
Suna dawowa Alhaji Jibril yace za su tafi Abba yace ya zata kwana za su yi sai gobe yace yau zasu koma sai kuma wani jigon.
Umma tace in sha Allahu suma suna nan zuwa tunda su sun fara zuwa saura su.
Hajiya Murjanatu yake kawai take yi ammh abun na cin ranta ta kosa su bar gida taji Dalilin Baban Batul da na aikata musu wannan Tozarcin.
Innani ko harda ita a masu rako ta na ta Allah ya shi albarka ammh ta tafka musu tsiya saboda son kanta.
Umma ta ba ma su zahra'u kyatan Turaman atamfofi da Turare sai Batul da bama Takalmi.
Mama kuma ta ba ma Fathihatu Kyautar Turaren wuta mai kamshi zuwan maiduguri.
Kamal kuma Abba ya basa kudi da baisan adadin su ba shi da Batul.
Karfe hud'u da rabi suka bar Haraban gidan Alhaji Sulaiman bayan Alhaji Jibril ya bama Innani kudi da yawa da su siyama duk ya rabama 5k kowacce ammh ban da Salima wacce ke cikin Shashen Mama bata ko Fito ba.
Duk da Mubarak yaso ya kara ganinta ammh har suka bar haraban gidan bai ga ko mai kama da ita ba.

Suna fita daga gidan ko anguwan Hajiya Murjanatu bata bari sun fita ba ta kalli Abba da ke gabam Mota Inda Mubarak ke driving tace"Baban Batul me nake jin ka aikata ne haka?
Ko waiwayowa bai yi ba cikin Kaushin Murya yace"Murjanatu ba anan ya kamata mu yi wannan mganar ba. So behave u self kina gaban yaran mu ne"
Sanin haka yasa sai ta danne mganar ammh abun na cin zuciyarta.
Abun takaicin ma su ke da ya mace ammh su suke kai tayi ana musu wulakanci kuma tasan haka kurum Baban Batul bazai aikata haka ba sai yasan ya na hangen riban da zai samu akan hakan.

Su Surayya kuwa sai bayan Tafiyar baki suka samu labarin abunda ya faru a falon Innani.
Sajida ta yi karaf tace"Haba mama Umma ai gwara da Innani ta hana. Tsakani Allah ba na son ganin kananan yara da kishiya duk sai kiga abun ba tsari aciki."
Daman Umma ke shaida musu yadda abun ya wakana a shashen Mama.
Kowa dai sai tofa na shi ya ke Allah yasa Sultana na shashen Innani abunta in abun Innani kuma na kusa ta kwashe yadda akayi ta fad'a mata shi yafi komai ma sauki.
Surayya ta kada kai kafin tace"Sadiq bai da Tsarin auran mace fiye da d'aya."
Sa'ima tace"Ba shi da hayaniyar da zai iya ma wannan gaskiya wannan karon ina bayan Innani."
Mama ta yi dariya kafin tace"Kai Innani akwai karfin hali wai har ta na cewa gajerar yarsa."
Gabadaya suka saka Dariya Salima na gefen Umma tace"Ba karya ta fad'a ba yarinya is too short ta yi ma Bro gajarta da yawa yadda ya ke gint d'inan"
Umma tace"kun dai yi son kai kamar yadda Innani ta yi kun so Sulsatana kun ki Zahra'u."
Sa'ima tace"Umma daman ai so so ne ammh son kai yafi ko Surry?
Surayya tace"To daman mu ai Sultana ce tamu yadda bazamu so a yi mana abokam zama ba sai dai in kaddara haka itama mu ke mata wannan Fatan"
Umma tace"Ai shikenan mgana ta kare. Ammh fa Innani tace in ya na so a had'a zumuncin ne ga Siyama ga Salima wanman saurayin babban yaron nasa ya zo ya zaba acikin su."
Mama ta kada  baki tace"Sai dai Salima domin siyama ta yi masa kankanta."
Salima na jin haka tace"Mama wata Salimar?
Umma tace"Salima Sulaimam Shinkafi.".
Salima ta mike ta na Tura baki Lokaci daya ta na fad'in"Tab ni fa ba yanzu zan yi aure ba karatu zan yi.".
Tafad'a ta na tura baki kafin ta bar Falon.
Sa'ima ta bita da fad'in"Ki yi fatan Innani tace a'a in kuma tace Eh! sorry ki yarinya."
Gabadaya suka kwashe mata da Dariya sanin Halinta da Ra'ayinta na sai ta zama ma'aikaciyar gwammati ko za ta yi aure.



🌿 Ina manyan mata masu MATSALOLIN rashin Ni'ima Ina sabbabin aure Wanda basu juku yanda Mai gida zai sume ba😂Ina wayanda zasuyi sabbin aure
Nazo muku da magani SAHIHI ingantaccen TSIMIN TABAJE🤌🏽🥰😍 hmm uwar gida, amarya, tsoffin aure kuna Ina ko kuntsaya tsilla tsilla tohm maza kuzo nazo kusiya TSIMIN TABAJE 💃💃😂hajiya ta tunda kukaji na yaba wannan magani toh tabbas yakai inda yakai yanada matukar kyau, Yana saurin saukar da niima baya illa domin andafashine da saiwoyin da kuka San suna maganin dakyau... Hajiya ta 🙈wlh Mai gida zaiyi Santi zakiji dadi Kuma zakuzo ku godemun domin yanasa Gurin yayi dumi ya Kuma ciko miki da gaba Gurin Kuma zaiyi dadi zoyzoyy😂🙈💃Kuma duk afarashi kalilan akwai gorina 1k akwai galan, akwai jarka ga duk meso, hmmm duk Wanda yasha Sai ya Gode mun domin nice na baku tabbaci 💃😂kunsan banida burin daya wuce Inga anasaka Mai gida farinciki 💃😂🥰Toh kuzo kusiya zakuji dadi insha Allah Kuma Sai kun dawo.... muka hada miki maganin TSIMIN TABAJE sha'awa zaki koma kamar marka..game bukatar TSIMIN TABAJE ya kiramu tawa innan numbobin kamar haka
*Location* *Zaria and kaduna* *but nation wide delivery* *for more details 07062349732 or 08143450259* 💃💃💃



*Janafty*
*TMWB2K009*


*TMW is a paid Novel, Pay 500 for regular or VIP N1K, Via 0552179550 Jamila Umar Gt bank, 09069067488*

*BOJUWA HERBAL'S BY SURAYYA DEE*!

*Akwai kaya masu kyau a cikin farashi mai sauki*
*Saiwowin maganin sanyi*
*Saiwowin Tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza*
*Saiwowin dahuwar tattabaru*
*Gumba*
*Tsumin kwakwa*
*Y'aya'n gadali*
*Hadadden daka*.
*Tsugunno mai sa a matse*
*Goran tula*
*Goran tula syrup*
*Garin goran tula*.
*Maganin gyaran nono*.
*Zuma ta mussaman*.
*Tsumi*.
*Gaban ayu*.
*Hakkin daka gangariya*.
*Da sauran kayayyaki na mussaman da basu da illah*.
*Domin kuwa asalin Saiwowin ne da ake kawo su daga Chad*.
*Abu mai kyau shi ke siyar da kansa ku tuntube ni dan samun naku kayan cikin sauki da mututantawa. Ina aikawa ko ina a fad'in tarairaiyar Nijeriya*
*08032773332*
*Ana dafa GIMBIYAR KAZA da tattabarun garari*.


Kaduna.
Da daddare.

Hajiya Murjanatu tunda suka isa gida lafiya ta ke kokarin su kad'aice da Baban Batul domin su yi mgana ammh yaki bata wannan damar.
Suna dawowa ya shige dakinsa ya kuma ce kada kowa ya zo ya damesa ya na bukatar Hutawa ne.
Ko Tea dinsa na dare zahra'u ta kai masa, sai dare bayan ta sallami yaran ta isa dakin nasa tunda har Fathihatu a nan zata kwana sai gobe mijinta zai zo ya dauketa.
Abun na cin ranta ta kasa fad'a musu Mubrak ne kad'ai ya sani shi kuma ba shi da tacewa kan abunda Baban na su ya riga ya aikata. abunda bata sani ba ne shi bai ga illar hakan ba sai ma ya ke ganin shi kila a gaba maganar Baban nasu zai iya zame masa alheri watarana.
Ta isa dakin nasa da shirin barcinta ammh ta dora zani da karamin Hijabi saman kayan barcin jikinta.
Ko da ta shiga ta iske shima ya sauya kayan jikinsa zuwa jallabiya mai saukin kauri ya na zaune gefen gado ya dora kafafunsa saman gado.
Sai kurb'an tea dinsa ya ke yi hankalinsa kwance.
Ta na shigowa ta cire zanin da Hijabin sannan ta haura saman gadon ta zauna kusa
Showing 33001 words to 36000 words out of 98628 words