su sark'a yan hannu harda na sawa a kai,kayan sun yi kyau sosae da ganinsu masu ingaci ne ba tagajan tagajan ba, su kansu kayan sun sak'u sosae musamman gwaggo ta kira kawu shi6ado ta fad'a mashi tana son kayan shi kuma yaba wani abokinshi sautu ya aiko mashi dasu jiya kawun ya bada sak'on Mota aka kawo ma gwaggon, wata k'arar farinciki Fanan tay ta mik'e tana nuna masu abunda aka aiko matan hajiya na dariya ta shiga yabawa cike da zumud'i ta sungumi ledar kayan tace bari taje ta gwado Hajiya ma ta mik'e tana Fad'in bari ta biyota tana son shiga toilet, ya rage daga ita sai shi a falon kowa yayi tsit gashi duk ta sha jinin jikinta kasancewar akan kujera d'aya suke, a hankali ta d'an juyo zata saci kallonshi karaf suka had'a ido dashi da alama dama kallonta yake, idasa d'agowa tay tana kallonshi tana motsa baki kaman zata ce wani abu sai kyakkyafta ido take still idonshi na akanta yana mata wani kallo ko kyaftawa baiyi hakan yasa duk ta dabarbarce ta fara yamutsa fuska kaman zata yi kuka kawae sai gani tay yay dariya har fararen hakoransa suka bayyana ya dan ta6e baki ya maida idonshi kan tv ita kuma ta sadda kanta k'asa ji take kaman ta rusa ihu, fitowa Fanan tay cikin kayan Tubarkallah ma sha Allah fad'in kyaun da tay 6ata lokaci ne Hajiya ta taimaka mata tasa komae tay kyau Over harda takalma masu tsini ta sawo ta tunkari Haisam tana cat walk idonshi akanta yana Murmushi Fatuu ma idonta na akanta tana kallonta da d'an Murmushi, tana isowa gaban Haisam ta wani jujjuya tana fari da ido tace "how do i look babe?" dage gira yay slowly yace "like a bride" dariya tasa tace "yeah it's true am ur bride" tana yin Maganar ta fad'a jikinshi tana dariya shima dariyar yake ta d'auki wayarshi ta fara yi masu selfie duk wannan abun idon Fatuu na akan tv tun sadda ta fad'a mashi ji tay bazata iya cigaba da zama ba tana niyyar mik'ewa Fanan ta nufota da wayar ta zauna gefenta ta d'aga alamar itama hoton zatayi da ita, ba yadda Fatuu ta iya dole ta tsaya ganin bata murmushi fanan tace "Smile Zarah" dole haka ta daure ta rink'a yin murmushin yak'e ta rink'a d'aukarsu, can Fatun tace mata tafiya zatayi lokacin islamiyya ya kusa dama gwaggo ce tace tana nemanta tace eh ta mik'e hannunta cikin na Fatun ta jata d'akin Hajiya bayan taba Haisam wayarshi, lokacin da suka shiga Hajiya na kwance akan gado Fanan ta nuna mata stool tace ta zauna, kit d'in kayan gyaran gashinta ta d'aukko ta aje a gaban Fatun ta d'aukko wata babbar leda itama ta aje a gabanta tace gasu nan tana tunanin kayan ciki zasu yi mata tayi amfani dasu ta janyo k'aton trolley d'inta ta bud'e tace ta k'ara dubawa in akwae abunda take so karta ji komae ta d'aukka, gaba d'aya Fatuu ji tay ta rasa mik'e mata dad'i kawae sai ta fashe mata da kuka, (Allah sarki Fanan baki san Fatuu ba wannan take bukata a wurinki ba), Sosae Fanan ta rud'e ta hau lallashinta tana cewa tayi shiru ai ba abun kuka bane Hajiya dake kwance ma tace mata tayi shiru ai ba wani abu bane tunda ita ta bata, da kyar ta daina kukan fatun tace mata ba abunda take so suma wanda ta d'aukkar matan ta barsu Fanan d'in tace a'a ai ita ta bata, ba yadda ta iya dole ta d'auki kayan harda kit d'in tay mata godiya harda Hajiya, tare suka fito ta rik'e mata kit d'in har lokacin Haisam na zaune Fanan tace mashi zata je ta dawo ya d'aga mata kai kawae, akan hanyarsu Fanan d'in ke ce mata zatai missing d'inta sosae amman dae ai zata zo bikinsu ko fatun ta d'aga mata kai kawae,lokacin da suka isa gidan gwaggo ta ga abubuwan data ba Fatun sosae tay mata godiya had'i da Addu'oi tay fatan Allah ya nuna masu Aurensu lafiya, bayan wani lokaci tay mata sallama gwaggon tace zata shigo su k'ara yin sallama da daddare, bayan sallan isha gwaggo taja Fatuu ba don taso ba suka je gidan, Washe gari da Safe misalin karfe takwas da wasu mintuna Fanan ta rafka sallama tana sanye da skinny jeans da riga long sleeve ta d'an saukko mata kanta ta yafa mayafi ta fito a Baturiyarta, fitowa gwaggo tay daga cikin Kitchen tana ganinta ta nufeta tana fadin "y'ata har an fito" tace mata eh zasu tafi, gwaggo tace "to Allah ubangiji ya tsare, mungode, mungode Allah ya k'arawa rayuwa Albarka yasa ki gama da iyayenki lafiya, ki gaida mana da yan gidan sai munzo biki in sha Allah" d'an side hug tay ma gwaggon tana Murmushi tace "nima nagode da kulawa granny" suna cikin haka Fatuu ta fito jikinta sanye da doguwar riga kanta ba kallabi duk maganganun da suke tana ji kasa jurewa tay ta fito Fanan na ganinta ta saki gwaggo ta bud'a mata hannuwa, nufarsu tay tana zuwa ta fad'a jikinta idanuwanta sun cicciko da kwalla har sun fara zubowa, d'agota fanan tay ta shiga share mata tana Fad'in ta daina kuka ai zasu ci gaba da communicating kaman da, horn d'in da akai a waje yasa ta saki Fatun tace babe na jiranta tare zasu tafi ta juya suka rakota bakin kopa anan suka tsaya don ita Fatuu bata da kallabi ita kuma gwaggo ba mayafi, bud'e kopar Motar Haisam yay shima yayi gayun k'ananan kaya ya gaida gwaggo tay mashi Allah ya tsare ita kuwa Fatuu kasa ce mashi komae tay ta bishi da ido har ya koma Fanan na d'aga masu hannu suma suna d'aga mata ta bud'e gaban Motar ta shige yaja suka tafi, wani irin sanyi jikin Fatuu yay gwaggo ma har ta fara jin kewarta, juyawa sukai suka koma cikin gidan.......

Wacece Fanan? Ya akai suka fara Soyayya da Haisam?

Domin karanta cikakken Littafin sai ku danna bulun Rubutun dake kasa ko kuma hoton dake kass πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

https://aihausanovels.com.ng/novel-document/a-sanadin-makwabtaka-book-2-complete-hausa-novel

πŸ‘†πŸ‘†πŸ‘†πŸ‘†πŸ‘†

*ASM Bk2007*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._
*πŸ’–A SANADIN MAKWABTAKAπŸ’–*
_*(Love and Destiny)*_



_*BY ZAINAB LALUHπŸ“²*_
~(Oumm Imam)~

Book 2

Bonus Page 7


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*



.....Fanan jikar Hajiyace wato d'iyar Hajiya Maryam ta lagos kuma itace babbar diyarta, acan baya lokacin da mijin Hajiya wato General Adamu zakee yay ritaya a Lagos suka fara zama acan ne kuma ita Hajiya Maryam ta had'u da mijinta Wato Dr Mohammed Abraham wanda babban likita ne da ya kware a aikinshi lokacin tana karatu a Jami'ar Lagos, shi kuma Senator Alee yana Katsina yana kula da harkokin kasuwancinsu, tun lokacin da aka haifi Haisam Hajiya ta kwallafa rai akanshi k'arshe dae har tay nasarar rabasu dashi duk da suma suna matuk'ar kaunarshi don yaro ne mai tsananin farin jini ga kyau da Allah ya yi mashi duk wanda ya kalleshi sai ya tanka hakan yasa kullum cikin yi mashi Addu'oi suke, sosae Senator Alee ya rarrashi matarshi Fateema ya nuna mata Mahaifiyarshi ce bazata ta6a cuta mashi ba kuma tunda Allah yasa tana haihuwar ko shekara mai zuwa sai ta k'ara haiho wani d'an ba matsala bane, da k'yar ya shawo kanta ta hak'ura yana shekara hud'u aka ba Hajiya shi ta saka shi a Makaranta, gatan duniya Hajiya tayi ma Haisam saidae bata bashi gatan da zai sangarce ba duk da dama shi ba mai suffar sangartattun bane a tsayenshi yake tun yana yaro gashi ko dariya bai cika yi ba in kaga dariyarshi to wanda ya sani ne sosae, yana shekara bakwae lokacin yana primary 1 don saida yay nurserys Hajiya Maryam ta haifi d'iyarta ta fari wato Fanan itama dae Tubarkallah badae kyau ba don jinin Mahaifinta ta biyo harma ta fi shi kyau sosae, Fanan irin rigimammun yaran nan ne ga kukan banza da wofi abu kad'an ta 6are baki gashi kuma bata son bak'in mutum hakan yasa bata cika sakin jiki da mahaifiyarta ba ko yaushe tana manne da Mahaifinta shi kuma gashi ba mazaunin gida bane sosae saboda yanayin aikinsa yana aiki a asibitin gwamnati kuma yana da babban private Hospital hakan yasa kullum cikin yi mashi rigima take gashi tayi k'ank'anta bare yace ya tafi da ita koma ya tafi da ita baida lokacin kulawa da ita saidae in barin aikin zaiyi, hakan yasa in ya barta gida tay ta yi ma Hajiya Maryam rigima data yi mata fad'a kuma ta idasa rikice mata, duk wannan abun Mutum d'aya ne ke controlling d'inta wato Haisam duk da shima lokacin yaro ne,duk rigimar da take da sunzo gidan tay arba dashi baka k'ara jin kukanta tana sonshi taita shishshige mashi gashi shi ba son yara yake ba wani lokacin sai Hajiya tay mashi Magana yake d'an sakar mata fuska har ya d'auketa kowa yasan tana shakkar Haisam hakan yasa Hajiya Maryam watarana taje gidan Hajiya ta rok'eta ta bari Haisam ya dawo gidansu, fir ta k'i amincewa tace itama ai don tana son zama dashi ta rabo shi da iyayenshi, wai ance tsakanin d'a da Mahaifi sai Allah K'arshe dae saida Hajiya Maryam tay nasarar raba Hajiya da Haisam da sharad'in duk Weekend nan wurinta zaiyi shi tace su duka ma zasu rink'a zuwa,sosae suka samu sauk'in rikicin Fanan bayan dawowar Haisam gidan duk in zaije Makaranta sai yabar sak'on in tayi rigima daya dawo a fad'a mashi aikuwa har ya dawo bata yin rigimar data yi niyyar farawa Hajiya Maryam zata ce daya dawo sai ta fad'a mashi sai tace ta bari, a lokacin komae na Fanan ya dawo kan Haisam shine yi mata wanka bata Abinci data ga yayi fushi duk sai ta rud'e ta fara bashi hakuri har sai yace mata yayi sannan zata warware da yake lokacin girmanta yafi shekarunta tana da wayo sosae ga baki, Haisam na primary 3 lokacin shekararshi tara da wani abu ita kuma Fanan ta kusa shekara ukku aka ba mijin Hajiya wato Adamu zakee Ministan tsaro bayan wani lokaci suka shirya komawa Abuja dama ba wani son zama Lagos d'in yake ba yafi son ya koma gida Arewa, Hajiya Maryam ta nuna abar Haisam nan ya k'arasa karatunshi Hajiya kuwa tace bai yuwuwa ai iyayenshi ma sai suce wani abu don haka k'afarta k'afarshi aikuwa Fanan ta sa rikicin sai ta bi bro haka take kiranshi sam Hajiya Maryam bata son d'iyarta tai mata nisa saida Dr Mohammed ya nuna mata ta barta su tafi da ita kawae in ba haka ba wani sabon rikicin ne tunda ta saba dashi in ta k'ara wayo sai ta dawo kuma in d'a take so zata iya daina planning d'in da take sai ta haihu dama so take sai Fanan d'in tayi wayo sannan ta k'ara haihuwa, ba yarda ta iya dole ta hak'ura aka tafi da ita Abuja aka saka su Makaranta tare da Haisam sam bata son zama class d'insu kullum tana zarya class d'insu Haisam sai ya kamata ya maidata, da yan class d'insu sun ganta tazo sai suce Zakee ga d'iyarka nan aita dariya shidae sai dae yay d'an Murmushi kawae, har lokacin shi ke mata wanka da sun koma gida ya bata Abinci kullum tana lik'e dashi tun yana jin ya takura harma ya saba, bayan tafiyarta da shekara d'aya Hajiya Maryam ta haifi Farha shima Haisam lokacin Mahaifiyarshi ta k'ara haihuwar yara biyu Laila da Nameer, Haisam na Junior Secondary Mijin Hajiya wato Gen Adamu zakee yay Accident ya rasu lokacin ba k'aramin tashin hankali iyalin suka shiga ba lokacin Fanan na primary 4, rasuwar mijin Hajiya yasa ta kasa cigaba da zama a Abuja ta yanke dawowa Katsina lokacin kuma Hajiya Maryam ta buk'aci Fanan ta dawo gida da taso ta turje aikuwa ta bude mata wuta dole ta koma Lagos shi kuma suka dawo Katsina yaci gaba da yin Senior Secondary lokacin kuma Mahaifinshi ya zama Senator, bayan ya gama secondary ya tafi kasar waje yin degree d'inshi na farko,akwae wani zuwa da yay Lagos lokacin yazo k'asar Fanan na Secondary skul tana ganinshi ta rungumeshi cike da farinciki suka ci Abinci tare da daddare bayan sun gama fira zai je ya kwanta tace mashi wai yayi mata wanka kaman yadda yake mata da d'an murmushi yay mata yace mata ai ta girma yanzu bai kamata yay mata wanka ba tace amman ai shi yayanta ne ba wani abu bane ganin ta turje kan hakan yasa ya zaunar da ita ya fahimtar da ita game da tsakaninsu na shi yayanta ne amman ba muharraminta bane kuma koda ma shi muharraminta ne yanzu takai wani mataki da bazai mata wanka ba tunda shi Namiji ne ganin ta zuba mashi ido yasa ya tambayeta ko bata san miye muharrami ba tace ta sani wanda bazai iya auren Mutum ba yace mata hakane, da bud'ar bakinta sai cewa tay yanzu shi zai iya aurenta kenan yana d'an Murmushi yace mata eh ai shi cousin d'inta ne ba ta sani ba tace eh ta sani,Washe gari bayan sun gama breakfast da yake Weekend ne taje part d'in da ya sauka ta iske shi yana kallo ta zauna kusa dashi itama tana kallon American film d'in da yake kallo, can aka nuno jarumin film din ya duk'a kan knee d'inshi yana rok'on jarumar zata aure shi ya mik'a mata zobe can ta amsa mashi da Yes ta mik'a mashi yatsanta yasa mata zoben ya mik'e suka rungume juna, juyawa Fanan tay ta kalli Haisam da idonshi ke kan tv ba zato ba tsammani kawae ta duk'a a gabanshi ya maido idonshi kanta yana kallon abunda tay murya kaman zatai kuka tace "Ya Haisam will u marry me pls?" dan bud'a mata ido yay alamar mamaki sai kuma yay Murmushi kawae ganin haka yasa ta fara yamutsa fuska kaman zatayi kuka tace mashi"plss answer me,will u marry me?" d'an lumshe ido yay ya jinjina kanshi, wata k'arar murna tasa ta fita daga falon da gudu ya bita da ido kafin ya maido kan tv yaci gaba da kallonshi, wurin Mommynta ta nufa lokacin tana d'akin Dad d'insu saida tay masu sallama sannan tasa kai tana ta dariya ganin haka yasa Hajiya Maryam tambayarta lafiya cike da farinciki tace Ya Haisam ne yace zai aureta yanzun nan, gaba d'aya suka bud'a idanu kafin sukai dariya suka ce suna tayata murna ta dace miji ta juya da gudu tana dariya, bayan fitarta Hajiya Maryam ta kira Hajiya ta sanar mata sosae tay farinciki tace ita dama tasan wannan shak'uwar inda zata kaisu kenan, tun daga wannan ranar Fanan ta koma yima Haisam kallon wanda zata aura, Bayan ya gama degree ya dawo Abuja ya fara aiki ita kuma Fanan ta gama Secondary tace ma Mommynta taji ana Maganar tafiyarta karatu ita dae aure take so tunda tana da wanda zata aura in sunyi auren tayi karatun, jin wannan Maganar yasa Hajiya Maryam ta kira Hajiya ta sanar mata game da zancen Fanan d'in ita kuma ta kira Mahaifinshi Senator Alee, Lokacin da ya kira Haisam d'in yay mashi Maganar auren da mamaki yace ai shi wannan lokacin wasa ne yake mata don baiyi tunanin da gaske take ba ganin ita yarinya ce kuma ya za'ai ai mata aure ma yanzu tayi k'arama, Senator yace yanzu dae bazai aureta ba kenan yace shidae yana mata son yan'uwantaka ne amman bana aure ba,sosae ya fahimceshi ya kira Hajiya ya gaya mata duk da bata ji dad'i ba amman tasan bazasu yi mashi dole ba lokacin ta kira Hajiya Maryam don ta sanar mata duk suna zaune a parlor bayan sun gaisa ne ta fara mata bayanin abunda Haisam yace sam Hajiya Maryam ta manta ma tana tare dasu Fanan d'in take wayar saida taji su Farha sun saka k'ara suna fad'in Sis Fanan ta fad'i sannan ta kai idonta kan Fanan dake baje k'asa kan carpet ashe tana jin abunda suke magana ta mik'e shine ta yanke jiki ta sume wata zabura Hajiya Maryam tay ta cillar da wayar tay kan Fanan, Hajiya nata hello hello sai Abraham ne mai sunan kakansu ya d'auka ta tambayeshi miya faru yace sis Fanan ce ta sume data ji suna waya da Mommy d'insu, rushing dinta sukai Hospital din Dad d'insu anan yasan abunda ke faruwa suka shiga bata agajin gaggawa koda ta farfad'o ta ganta a Asibiti ga iyayenta akanta sai ta fashe masu da matsanancin kuka tana Fad'in"Ya Haisam will not marry me why, why mom, Dad why? Am i ugly?....." haka ta dingi sambatu Hajiya Maryam harda kuka sai lokacin ta amshi wayarta ta kira Hajiya dama tana ta kira ba'a d'agawa cikin muryar kuka take sanar da ita halin da Fanan take ciki tace tana tunanin ta samu heartbreak ne gashi dama raunannar zuciya gareta, Hajiya na jin hakan washe gari sai Abuja ta zauna da Haisam da iyayenshi tace mashi miye aibun Fanan da bazai aureta ba ko yana da wadda yake so ne yace mata a'a shidae kawae bai mata son aure, tace to yayi hak'uri tunda ita tana sonshi ya daure ya aureta ko don a ceci rayuwarta kar a rasata saboda abunda bai fi k'arfin suyi mata ba yace shikenan zai aureta amman ba yanzu ba sai ya gama Masters degree d'inshi da zai tafi bada jimawa ba Hajiya tace wannan ai ba matsala bane tunda dae ya amince itama sai ta fara karatunta duk in suka gama sai ayi bikin in Allah ya kaimu,Washe gari Hajiya da Haisam harda Senator suka tafi Lagos duba Fanan d'in har lokacin tana cikin mawuyacin hali a Asibiti sai faman koke koke take, koda suka ganta gaba d'aya ta basu tausayi ba kaman Haisam da shi Mutum ne mai tsananin tausayi hakanne ma yasa ya amince da auren nata ba tare da an kai ruwa rana ba, gaishe da ita sukae sukai ma iyayenta ya mai jiki cike
Showing 24001 words to 27000 words out of 113043 words