rufe bakinta da tafin hannunta, kokarin sauka daga kan gadon ya fara yi yana fad'in "bari inje in gayo ma su Dad baki lafiya kina kuka azo akai ki Hospital" da sauri ta kamo hannunshi tana girgiza mashi kai yace "kar naje na fad'i masu?" d'aga mashi kai tay alamar eh yace "to ki daina kukan don Allah" yadda yay Maganar kaman shima zai sa kukan, a hankali tace to ta daina ya kai hannu yana goge mata hawayen, da k'yar ta samu hawayen suka tsaya cikin muryar wanda yay kuka tace mashi ya Makarantar yace lafiya lou tace yana dae kokari ko yace eh sosae,shiru sukai na d'an lokaci can yace "Aunty Zarah yau bazamuyi game ba tunda baki lafiya ko?" kai ta daga mashi alamar eh yace "Allah ya baki lafiya sai mu yi" a hankali tace Amin suna cikin haka sai ga Abbas ya shigo d'akin Abdul na jin sallamarshi ya sauka daga gadon da sauri ya nufe shi yana fad'in "Daddy Aunty Zarah tayi kuka a kaita Asibiti" jinjina mashi kai yay ya nufi cikin d'akin ya tsaya gabanta yana kallonta kanta na kasa tunda taji Abdul yace tayi kuka, slowly Abbas ya kira sunanta ta amsa ba tare data d'ago ba hakan yasa yace ta kalleshi kaman bazata d'ago ba can ta d'ago da jajayen idanunta ta kalleshi duk ta kame kanta,
"In akwae abunda ke damunki banda ciwon da akace kar kiji komae ki fad'a man" da sauri ta girgiza mashi kai tama kasa yi mashi Magana, d'an Murmushi yay yace "to miyasa kike kuka?" murya na rawa tace "d...da dama jikin nawane bana jin dad'inshi..." shiru ya d'anyi kafin yace "an kai ki Asibiti ne?"
"A'a, amman Aunty Fanan tayi man Allurar zazza6i ta kwana ukku nama samu sauki sosae yanzu"
"Ko mu kaiki Asibiti to tunda kince jikin naki har yanzu bai maki dad'i" taji ya fad'a, da sauri ta girgiza mashi kai tace "a...ai gwaggo tace ciwon bana Asibiti bane tasa anyo man Addu'a a ruwan zam zam ina sha" shiru yay yana cigaba da kallonta hakan yasa ta sunkuyar da kanta don gabanta wani irin bugu yake mata ita tsoronta wai kar ya gano mike damunta ya fita ya fad'i masu, sigh yay yace mata Allah ya bata lafiya ta amsa da Amin ya kalli Abdul yace ya cire Uniform d'in jikinshi yasa kaya yazo zasu je Masallaci ya amsa da to, wani sanyi taji bayan Abbas d'in ya fita Abdul ya nufi wardrobe d'in kayanshi don ya canja kaya bayan ya d'aukko wanda zai sa ya juya yace ma Fatuu wai ta juya zaisa kaya bata san lokacin data saki dariyar da rabon da tayi irinta ta manta, kifa fuskarta tay jikin pillow tace bata ganinshi yasa ya amsa da to, bayan ya fita saiga Feenah ta shigo da Murmushi ta nufi Fatun tana tambayarta ya karfin jikin tace mata da sauk'i tace to ta tashi tayi salla ta amsa da to ta mik'e ta nufi toilet itama ta fice dama Fanan ta kai d'akinta tayi salla shine tazo wurin Fatun, suna dawowa daga sallar Haisam yace ma Abdul yaje ya kira Zarah zasu tafi, tare suka fito dashi ya ruk'o hannunta idonsu akanta hakan yasa duk ta dabarbarce ta sadda kanta k'asa har ta k'arasa cikin Falon ta zauna kusa da Fanan, Abbas ne yace ko zasu tafi sai taci Abinci sannan, ba yadda ta iya dole ta d'an ci Abincin da Feenah ta zuba mata, har bakin Mota suka yo masu rakiya Feenah tace ma Fanan in sha Allahu kafin ta tafi tana nan zuwa dan da suna hira tace mata upper Monday zata tafi tace to tana jiranta, sallama suka yi masu suka k'ara yi ma Fatuu Allah ya sawak'e Abdul ya d'aga mata hannu yana mata bye bye itama ta d'an mashi kafin ta bud'e Mota ta shige suma duk suka shiga yaja suka bar gidan...........
Domin karanta cikakken Littafin sai ku danna bulun Rubutun dake kasa ko kuma hoton dake kass ππππ
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._
*πA SANADIN MAKWABTAKAπ*
_*(Love and Destiny)*_
_*BY ZAINAB LALUHπ²*_
~(Oumm Imam)~
Book 2
Bonus Page 6
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
.......bayan sun baro gidan Abbas a wani Shopping complex ya tsaya dasu yace ma Fanan suje suyi shopping ta amsa mashi da owk ta bud'e Motar ta fita shima bud'e kopar side d'inshi yay har zai fita ya dakata ya juya ya kalli Fatuu dake zaune suka had'a ido,
"Ki fito zamuyi shopping" ya fad'a da cool voice d'inshi, girgiza mashi kai tay a hankali tace "ni bani buk'atar komae" wani kallo ya bita dashi da sauri ta sunkuyar da kanta kirjinta na bugawa da sauri da sauri,
"Let's go Zaraah" wani yamm taji a jikinta duk cikin masu kiranta da Zarah ba wanda ya kai shi iya Fad'a gashi da wani irin sauti mai dad'i sunan ke fita, d'agowa tay suka had'a ido kawae sai ta Fara yamutsa fuska tana ta6e baki alamar zatayi kuka dama har yanzu bata bar ta6e baki ba in zatayi kuka tun yarinta, still yay yana bin ta da ido sai far far take da ido don kada kwallan su zubo mata kawae sai yay wani murmushin gefen baki ya d'an girgiza kai ya fice daga Motar, zagayawa yay side d'in da Fanan take tsaye tana amsa waya tana ganinshi tace ma wanda suke wayan zata kira daga baya tay rejecting call d'in, ganin ba Fatuu tace mashi Zarah fa yace zuje kawae zasu d'aukar mata abunda ya dace ta amsa da Ok, sosae sukai shopping bayan sun gama aka zuba masu a shopping bags aka biyo su dasu, jakar da suka siya ma Fatuu kaya Fanan ta bud'e baya gefenta ta aje sauran kuma aka saka masu a boot daga haka suka shige Motan suka tafi,suna kan hanya jin shirun Fatun yay yawa yasa Fanan ta kira sunanta tana jinta tay mata shiru hakan yasa ta juya baya ta kalleta ganin ta langa6ar da kai gefe yasa tay tunanin bacci take, suna k'arasowa kopar gidansu ta bud'e Motar ta fita Fanan ma ta fito ganin bata d'auki kayan ba yasa ta tsaidata ta bud'e bayan ta d'aukko mata don tayi tunanin ko bata san nata bane har da ledan kayan da khairat ta bata, tana tsayen kafin Fanan ta d'aukko mata glass d'in gaban ya sauka Slowly, da sauri ta kai idonta wurin suka had'a ido dashi da yake akwae wuta globe din gaban shagon kawu Amadu ya haske wurin, ya d'an kwantar da kanshi jikin headrest kasa jure ma kallonshi tay ta sadda kanta k'asa lokacin Fanan ta mik'o mata jaka guda ita ta ruke mata guda tace suje, har lokacin idonshi na akanta ta juya kawae sai taji kaman bata kyauta ba don bai ta6a yi mata abu ba ba tare data gode mashi ba kuma hakan hud'ubar gwaggo ce, tsayawa tay Fanan ta juyo kafin tayi mata Magana tace mata zatai mashi godiya ne ta amsa da Ok tay gaba abunta, a hankali ta nufi Motar kamar wadda kwae ya fashe mawa a ciki ta tsaya gaban kopar tana kallonshi ba tare data ce mashi komae ba shima kuma baida niyyar tanka mata can ta bud'e baki da k'yar tace "Nagode Allah ya saka da Alkhairi" shiru kaman bazai tanka ba sai kuma taji yace "Ameen" k'okarin juyawa ta tafi ta fara yi taji yace "Zaraah?" wani mugun bugu k'irjinta yai dammn ta juyo a d'arare ta kalleshi gently yace "kina da wani problem ne?" a hankali ta girgiza mashi kai alamar a'a,
"Then why d change?" wani irin harbawa zuciyarta take ita tsoronta ma kar Fanan ta fito su tutsiyeta tare har su gano abunda ke damunta don a yadda take ji komae zai iya faruwa, "am talking to u zaraah why u look different?" baki na rawa kaman zatai kuka tace "b..ba..banjin dad'in jikina ne ba kasan ban Lafiya ba" shiru yay yana nazarin Maganar calmly yace "Ok i understand, ki fad'a ma grandma d'inki zamuje hospital tomorrow" da sauri ta d'ago ta kalleshi tace "ai ba ciwon Asibiti bane Addu'a ake man kuma anyo man ina sha" ta kai Maganar tana sussuna kai k'asa don wani irin kuka ne ke taho mata, Sigh yay yace mata zata iya tafiya Allah ya bata Lafiya da sauri ta amsa da Amin ta juya a harhard'e ta nufi gidan tana shiga zaure ta lafe a jikin bango ta tura gyalenta a baki ta fashe da kuka,can zuciyarta ta raya mata kar Fanan ta fito ta ganta haka da sauri ta goge kwallan ta d'auki ledan ta shiga cikin gidan, a bakin kopar Parlor ta hangi takalman Fanan ta jiyo muryarta ita da gwaggo hakan yasa ta aje ledar a gefe ta nufi hanyar toilet, jin motsi yasa daga cikin falon gwaggo ta tambayi waye tace itace zata shiga toilet ne, koda ta shiga kukan taci gaba da yi, ita kanta yanzu tsoron fad'i ma Haisam d'in take game da son nashi don ta yarda da Maganar Haulat ta zata jefa kanta a wata Matsalar ne,har saida taji gwaggo ta rako Fanan suna sallama sannan bayan ta tafi ta wanke fuskarta sosae ta d'auro Alwala ta fito cikin sa'a tana fitowa taga gwaggo ta kabbara sallar isha hakan yayi mata dad'i don bata son ta gano kukan da tay, itama sallar taje d'aki tayi bayan ta gama sosae tayi Addu'a kan halin da take ciki daga baya ta kwanta kan abun sallan, tana kwancen gwaggo ta d'aga labulen ta kira sunanta tace ko har ta kwanta, d'an d'ago da kanta tay tace mata eh ta gaji ne sosae bacci take son yi tace "to bazaki ci Abinci bane?" d'aga mata kai tay tace "eh banjin yunwa munci Abinci" jinjina kai tay tace to ta tashi ta hau gado kuma ta tabbatar tayi Addu'a ta amsa mata da to ta juya ta tafi, mik'ewa tay ta cire kayan jikinta har zata nufi gado taji kuma ruwa take son ta watsa ta nufi toilet bayan ta yafa mayafi a kanta, tun bayan data fito ta saka kayan bacci ta haye gado ta dasa sana'ar tunane tunanenta, tabbas tana son ya Handsome sosae to amman ta gane ba samunshi fa zatayi ba matuk'ar yana tare da Fanan yanzu ya zatayi, nan take ta gano bata da wata mafita da ya wuce tay hakuri dashi tayi yak'i da zuciyarta kaman yadda Haulat tace mata, yin wannan tunanin yasa ta saukko daga kan gado ta d'aukko Al'qurani ta fara karantawa acikin zuciyarta bayan wani lokaci ta rufe ta d'aga hannuwa harda kwallanta ta rok'i Allah daya cire mata son Ya Handsome, bayan ta gama ta mayar dashi cikin jakarta ta koma kan gado tay lamo tana cigaba da zubar da kwalla a haka bacci yay awon gaba da ita.
Washe gari data tashi ba laifi ta d'an ji k'arfin jikinta bayan tayi breakfast ta fara ayyukanta gwaggo nata jin dad'i duk in suka had'a ido sai tay mata d'an mumushi,da yake aikin safe take Fatun ta tambayeta mi zata dafa kafin ta dawo tace ayyukan bazasu yi mata yawa ba kuwa ko ta samu wani abun taci in ta dawo sai tayi Fatun tace ba komae zata iya, ta fad'i mata abunda zata dafa kafin ta tafi, tana ta ayyukanta tana tunane tunane har ta gama komae tayi wanka tay kwanciyarta, rashin zuwan Fanan ba k'aramin dad'i yay mata ba don ta fahimci duk in ta gansu su biyun k'ara mata ciwon suke,k'arfe biyu da wani abu gwaggo ta dawo lokacin Fatuu nata bacci abunta ba laifi yau ta samu bacci sosae bata tasheta ba ta wuce d'aki ta kimtsa kafin ta fito ta nufi Kitchen sosae taji dad'in ganin Fatun tayi Abincin lafiya lou ga Kitchen din tsaf a cikin ranta take godiya ga Allah da ya amsa addu'arta da take ma Fatun, sai wurin karfe ukku ta farka tayi mamakin irin baccin da tayi da har bata san gwaggo ta dawo ba, ana kiran sallar la'asar ta watsa ruwa tay salla ta fara shirin zuwa islamiyya, bayan ta gama ta lek'a d'akin gwaggo tace mata ta tafi islamiyya tana washe baki ta hau yi mata Addu'oi har da fitowa wai bari tayi ma yar autarta rakiya waje ta rungumo kafad'unta Fatun tasa dariyar da yaushe rabon da gwaggon taga tayi ta, Lokacin data je Haulat bata kai ga zuwa ba nan yan ajin suka hau yi mata ya jiki don Haulat ta sanar da rashin lafiyan nata, lokacin da Haulat ta shigo ajin suna had'a ido da Fatun ta nufeta da yar sassarfa ta duk'a ta dafata tana washe baki tace ta samu sauk'i kenan ta jinjina mata kai kawae, zama tay sosae taci gaba da k'arfafa mata guiwar tayi hakuri ta cire shi daga ranta ba tare da wani ya ji maganar da suke ba a haka har Malam ya shigo, bayan an tashi ma akan hanyarsu ta dawowa shawarwari taci gaba da bata ita dae saidae ta d'aga mata kai kawae duk da tana son amfani da shawarwarin saidae har lokacin ba abunda ya canja na daga son ya Handsome a cikin zuciyarta, bayan ta koma gidane gwaggo ke fad'i mata Fanan tazo tace da daddare zata dawo tace to kawae.
Gaba d'aya satin guje ma duk wani abu da zai kaita gidan Hajiya take in gwaggo tace taje da ta fito sai ta wuce gidansu Haulat, Fanan har Maganar rashin zuwan nata tayi don a tunaninta ta samu sauk'i tace mata islamiyya take zuwa da yamma da safe kuma ita ke aikin gidan, sosae ta fahimceta bata sa komae a ranta ba ita taci gaba da zuwa, ba laifi kuma Fatun ta d'an k'ara sakar mata jiki, a cikin satin Haisam ya kaita gidansu Khairat ta wuni bata samu kara zuwa gidansu Nana ba amman ita tazo harda k'annenta yan mata guda biyu suka kawo mata kaya harda atampopi don ranar Monday zata tafi, Feenah ma tazo itama ta kawo mata abubuwa d'inkakkun Material masu kyau da tsada kala biyu sai kayan kamshi su humra da kullacca har gidansu Fatuu taje ta k'ara yi mata ya jiki suka gaisa da gwaggo Abdul yaji dad'in ganinta tana ta mashi dariya har yana cewa da yasan ta samu sauk'i da yazo da tab d'inshi sun yi game, Feenah tace shi damuwarshi kenan game ko duk suka yi dariya gwaggo tace ina ruwan yaro, daga baya suka yi masu sallama suka tafi Fatuu ta rako su kopar gida, Ranar Friday da safe gaba d'aya Haisam da Fanan da Hajiya suka tafi Daura suka zaga dangi Fanan ta gaisa da su sai washe gari da yamma suka baro daurar suka biya Ajiwa Dam sosae wurin ya burge Fanan Hajiya ma taji dad'in zuwa wurin Fanan tay masu hotuna ba kamar ita da Haisam sai bayan Magrib suka dawo ta gaji sosae shiyasa bata je gidansu Fatuu ba sai Washe gari lahadi bayan sun gama breakfast ta shirya ta nufi gidan Harda tsarabar Daura, lokacin data je Fatuu bata nan tana islamiyya hira suka d'anyi da gwaggo tay mata godiyar tsaraba, Fanan d'in tace in ta dawo ace mata tana nemanta gwaggo tace zata fad'i mata da ta dawo, bayan Fatun ta dawo ta canja kaya gwaggo ta kirata ta sanar da ita sak'on Fanan na tana son ganinta har saida ta d'anyi jimm don rabonta da gidan Hajiya tun wanccan satin haka haisam ma rabon data sanya shi a idanunta tunda suka je gidan Abbas sosae take guje ma ganinshi ba kuma don bata son ganinshin ba, bayan taci Abinci tayi sallar Azahar Gwaggo tace mata taje kar Fanan d'in taita jiranta ba yadda ta iya dole tace to bayan ta fito zata tafi ne ta kirata ta bata wata leda dake k'ulle tace ta kai mata, tunda ta tunkari gidan kirjinta ke bugawa hakanan ta daure ta k'arasa har Officer nace mata kwana biyu dama tana gari ta amsa mashi da eh kawae ta shige, da zata wuce har saida ta kalli Corridor d'in shiga part d'in Haisam ta d'an girgiza kai tunowa da baya yanzu shi kanshi mai part d'in ma gudunshi take rayuwa kenan, lokacin data shiga Falon Hajiya gaba d'aya suna zaune harda shi Haisam d'in kamar ko yaushe dai Fanan na manne dashi jikinta sanye da rigar shan iska wadda iyakarta guiwa santala santalan k'afafunta dake jajur a waje kanta a bud'e tayi parking gashinta a tsakiya yayinda daga k'asa wani ke zube, shima Haisam riga armless ce ajikinshi da wando 3 quarter, tana yin sallama duk suka juya suka kalleta Fanan ta mik'e zaune tana mik'a mata hannu tana mata murmushi nufarta tay tana zuwa ta kama hannunta ta zaunar da ita gefenta, gaida Hajiya dake kallonta tay tace "Oh Fateema k'iri k'iri dae kinyi mana yaji ko?" d'an guntun Murmushi tay a sanyaye tace "a'a Hajiya na koma islamiyya ne da safe kuma dana yi ayyuka na gama sai lokaci ya k'ure" da k'yar ta k'arasa Maganar saboda fargaba, Hajiyar tace "ai lokaci kam na gudu wllh Allah ubangiji yasa mudace" ita da Fanan suka amsa da Amin, d'an juyawa tay ta kalli Haisam da idonshi na akan tv ta gaidashi shiru bai amsa ba saida Fanan tace mashi Zarah na gaidashi sannan ya d'an kalleta ya amsa kafin ya mayar da idon ta lura da yadda ya amsa mata duk sai taji dama bata zo ba kaman ma ta mik'e ta tafi hakanan dae ta daure dama ita yarinya ce mai tsananin k'arfin hali ba k'aramin abu ne kesata raunin zuciya ba, mik'a ma Fanan sak'on gwaggo tay ta amsa da farinciki tun kafin ma taga miye aciki lokacin data bud'e kayan Fulani ne Navy blue riga da zani da kallabi harda mayafi sai abubuwan ado
Showing 21001 words to 24000 words out of 113043 words

https://aihausanovels.com.ng/novel-document/a-sanadin-makwabtaka-book-2-complete-hausa-novel
πππππ
*ASM Bk2006*

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8 Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38