k'ara ma zauren girma, yana shiga d'akin gwaggo ta fito daga cikin Kitchen ganin kopar d'akin nashi a bud'e ne yasa ta kwala mashi kira tace ya dawo ne don bata ji shigowarshi ba, fitowa yay ya nufo inda take tsaye yace "Eh na dawo in ci abinci in d'an huta don sai k'arfe hud'u nike da lecture" kai ta d'aga yace "ba yau zaki fara aikin rana bane naga baki shirya ba kuma lokaci yayi" da yar damuwa tace "to na tafi aiki Fatuu ba lafiya, har yanzu fa jikinta bai mata dadi wllh ina lura da ita har kuka take tayi" ajiyar zuciya ya sauke yace "amma ba kince jiya har Allura an mata ba?'
"Eh anyi mata amman ai kasan ciwo ke shiga lokaci d'aya sauki sai a hankali ko, kuma ni wllh damuwata kar ace ciwon da nike tunani ne" sanin ko wane ciwo take nufi yasa Amadun cewa "in sha Allahu ba shi bane ma, amman ina ganin ki tafi aikin ni bari sai in fasa komawar kawae" tace "ayi haka bazaka samu Matsala ba?"
"A'a ba wata matsala dama komawar k'ila wa k'ala ce don ba lalle ma lecturer d'in yazo ba haka yake sai anata jiranshi ya kira waya yace bazai zo ba" jinjina kai tay tace "k'ilan uzuri ne ke masa yawa kasan hidindimun rayuwa, bari to in mik'o maka Abincin sai inje in shirya don ya kamata inje tunda yau Monday akwae tsare tsaren da zamuyi" tana k'arasa Maganar ta juya ta shige kicin,bayan ta mik'o mashi abincin ta zuba ma Fatuu ta kaimata saida ta matsa mata ta d'an tsakura tace mata ta k'oshi bata jin dad'in bakinta dole ta kyaleta ta hau shirin tafiya aiki bayan itama taci Abincin.

Lokacin da suka isa wurin aikin tun da suka fito daga cikin Mota ake ta faman binsu da ido dan duk wanda ya kallesu sai ya k'ara wasu da suka kafesu da idanu ko kyaftawa basa yi, da suka shiga cikin wurin wad'anda suka san Haisam da basu iya hakuri bayan sun gaisa dashi sai suce wai sabuwar Ma'aikaciya suka yi ne anan ya gabatar masu da ita a matsayin wife to be d'inshi, fatan alkhairi aka shiga yi mashi yayin da wasu ke fad'in perfect match har kiran Mutane aka rink'a yi suzo ga Fiancee d'in Zakee tanata fara'a take gaisawa da mutane, bayan sun gama gaisuwar Office d'in su Nana ya wuce da ita wanda babban Office ne don su hud'u ne aciki duk mata biyu matan aure ne sai su Nanar da wata sune marasa aure, Nana zaune tana lallatsa Computer jikinta sanye da doguwar rigar atampa gyalenta akan kafad'a taji an d'anyi knocking kopar kafin aka turota hakan yasa ta kai idanunta wurin, Fanan ce ta fara shigowa ai suna yin ido biyu da Nana zumbur ta mik'e ta dafe k'irji tace "innalillahi, wa innahu min sulaimanu wa inna hu bismillah..." tana rufe baki Haisam ya shigo tana ganinshi ta sauke nannauyar ajiyar zuciya don ta fahimci tare suke tace "Haba Zakee irin wannan ai sai ka fara shigowa kai da muka sani, ni wllh nayi zaton gamo nai yo kawae ana bud'e kopa sai inga Mutum irin wannan ta shigo tana man dariya" sauran yan Office d'inne suka sa dariya taci gaba da cewa "kad'an ya rage ban saki fitsari ba" ita dai Fanan Murmushi kawae take haka ma Haisam,
"Zakee bakuwa muka yi, daga ni dae sis d'inka ce ko?" tay tambayar tana kokarin zama ta nuna ma Fanan kujera tace ta zauna, maida kallonta tay kan Haisam tace "Zakee na tambayeka baka ban amsa ba" yace "Yea she's my sis and My wife to be also" waro ido Nana tayi da sauri ta kalli fanan d'in sauran abokan aikinta ma suka kalleta ita dai sai faman sakin Murmushi take, kallon Haisam Nana tayi tace "Haba mana shiyasa ba wata mace dake gabanka ashe ashe hurul ayn zaka aura, kace duk kallon gwaggon birai kake mana Zakee" gaba d'aya suka saka dariya harda Fanan, taci gaba "Tubarkallah ma sha Allah, gaskiya had'in nan yayi ba'a Magana, duk kun dace abokan rayuwa wllh Allah yasa Alkhairi ya kaimu lokacin musha biki ya kuma maida mu damshin ku duk da dai ita Amaryar tamu bansan halinta ba" Fanan na dariya tayi mata godiya tace ai duk halinsu d'aya Nanar tace to ta zauna anan ta tantance in halinsu d'aya, dole anan Office d'in nasu ya barta aikuwa sun sha fira da Nana harda ma sauran yan Office d'in sun matuk'ar yabawa da halinta na rashin ji da kai, sai gab da za'a tashi sannan Nana ta rakata Office din Haisam wanda babban Office ne mai d'auke da duk wani abu da zaka samu a hadaddan Office na babban ma'aikaci yana da dan falo wanda anan Secretary d'inshi yake, ana yin la'asar suka baro wurin aikin saida Nana ta rakota har Mota tace tana jiranta tazo mata wuni gida tace in sha Allah Babe zai kawo ta, saida suka biya shopping mall suka yi shopping yawanci duk kayan ciye ciye ne suka siya kafin suka nufi gida.

Tun bayan da gwaggo ta tafi aiki take kwance tana ta tunane tunanen rayuwarta da Haisam, a yanzu ne komai nashi ke bala'en burgeta a hankali take kai hannu tana goge kwallan dake zubo mata wanda sam ta kasa tsaidasu ga wani irin kadaici da take ji don tasan da yanzu tana gidan Hajiya ba kaman da gwaggo bata nan, da ta tuna yana tare da Fanan sai taji wani irin kunci a zuciyarta har wani zafi k'irjinta ke mata da kyar ta yunkura tayi sallar la'asar ko Addu'a ta kasa yi don ta rasa wace Addu'a ma zatayi, mik'ewa tay ta cire hijab d'in ta koma kan gado ta koma duniyar tunani tana ta juye juye tana goge kwalla, tana cikin wannan halin Haulatu tazo gidan a bakin shagon Amadu daya bude bayan ya dawo daga Masallaci ta tsaya ta gaidashi ta tambayeshi Fatuu na nan ko ta wuce islamiyya yace mata tana nan ciki kwance ai bata Lafiya tun jiya jin haka yasa ta nufi cikin gidan da sauri har tana yin tuntu6e a bakin kopar shiga, d'akin Fatuu ta nufa tana zuwa ta fad'a ciki da sallama ta nufi gadon Fatuu na jin sallamarta ta yunkura da sauri ta tashi zaune fuska jage jage da hawaye ga gashinta ya kwance yay mata rumfa, a rud'e Haulat ta nufeta tana Fad'in"Subhanallahi, wai ciwon har ya kai haka k'awata, ni wllh bansan baki Lafiya ba tun d'azun naso zuwa to sai innarmu ta tafi unguwa tabar man kula da gidan, yanzu ma islamiyya zani inata tunanin k'ilan ma kin tafi ina tambayar Kawu Amadu shine yake ce man wai baki lafiya tun jiya baku ma samu zuwa Daurar ba ko?" kaman jira Fatuu take tana jin ta fad'i hakan ta fashe da kuka mai sautin gaske ta matso ta kama hannuwan Haulat cikin kuka tace "Haulat na bani munyi kuskuren fahimta wllh" a kid'ime ganin yadda Fatun take a hargitse tace "kuskuren mi?"
"Ya Handsome bai sona Haulat, bai ta6a sona ba wllh" zaro ido Haulat tayi murya na rawa tace "a..amman ke ya akai kika san hakan ko kin mashi Magana ne ya fad'i maki hakan?" cikin kuka tace "a'a ashe wai yana da wadda yake so kuma ma har ansa masu rana da ta gama karatu za'ai aurensu,yauwa ba kinsan wannan Aunty Fanan d'in ba yar uwarsu mai karatu a india to itace, jiya muna dawowa muka iske tazo baki ga yadda ta rungumeshi ba da suka had'u shima baki ga yadda yake farincikin ganinta ba, da daddare suka zo tare wai kawo man tsarabar da muka yo, da tayi ma gwaggo bayanin kanta shine gwaggon tace ko itace akai masu baiko tace mata eh ashe ita gwaggo ta sani sun ta6a yin Maganar da Hajiya, Wllh Haulat baki ji yadda naji ba wani abu mai zafi kaman wuta naji a kirjina ga kaina da yayi wata sarawa nan da nan amai ya taho man baki ga aman da nayi ba kaman yan hanjina zasu fito kuma su duk sunyi tunanin ban lafiya ne har allura suka je suka siyo ita da Ya Handsome tai man" kasak'e Haulat tayi tana sauraranta kamar gunki gabanta na fad'uwa don duk gani take itace sanadin shigar Fatun halin da take ciki.....

Daidai gidansu Fatuu ya parker bike d'inshi Fanan dake bayanshi ta saukko jikinta sanye da workout outfit da alama Gym zasu tafi tare, Cire Helmet din dake kanta tayi ta mik'a ma Haisam ya amsa ta juya zata shiga gidan Amadu dake cikin shago yana ganinta ya fito da sauri don jiya da daddare bayan ya shiga gida gwaggo ta bashi labarin zuwan nata harda allurar data yi ma Fatuu, da Fara'a ya gaidata ta amsa yayi mata anzo lpy tana ta sakar mashi Murmushi, bayan ta wuce ya gaishe da Haisam kafin ya koma shago, tana shiga ta kwad'a sallama da zazzakar muryarta jin ba'a amsa ba yasa ta k'ara yin sallamar tana shiga cikin gidan a lokacin suka ji sallamar Haulat ta mik'e tana bari ta duba ita kuwa Fatuu tana jin sallamar ta gane ko wacece hakan yasa ta kwanta da sauri ta juyama kopa baya ta lullu6e fuskarta tana goge kwallar fuskar, d'aga labulen d'akin Haulat tayi ta lek'a kanta tana amsa sallamar saidae a susuce ta k'arasa amsawar baki bud'e take kallon fanan dake mata Murmushi ganin tak'i ce mata komae yasa tace mata "Sannu Gwaggo fa" a dabarbarce don bata yi tunanin zataji tayi hausa ba cikin yar in ina tace "g..gwaggo ta... ina tunanin ta tafi aiki" tace "Ok Zarah fa" da hannu ta nuna mata cikin d'akin alamar tana ciki ta nufo dakin har saida tace mata zata shiga kafin da sauri taja gefe ta shige, gadon da Fatuu ke kwance ta nufa ta zauna a bakin gadon cike da kulawa tace "Sis Zarah" shiru bata amsa mata ba ta d'aga kai ta kalli haulat tace "ko tana bacci?" da sauri tace "e..nima ban dad'e dana shigo ba na ganta haka"
"Ok amman ina son nayi mata injection ne zamu fita bansan ko zamu dawo da wuri ba" haulat da tayi mata k'uri tace "to bari in tada ta" matsawa tayi ta fara kwala mata kira ba yadda Fatun ta iya dole ta yunkura ta tashi zaune a hankali ta d'an kalli Fanan din ta sakar mata Murmushi tace "Sannu sis Zarah hope u'r feeling better" dan daga mata kai tayi kafin kaman an mata dole ta gaidata ta amsa had'i da dafa kafadarta tace bari tai mata second dose d'inta kai kawae Fatun ta d'aga mata ba tare da 6ata lokaci ba ta fiddo allurar da syringe daga cikin jacket din data rufe jikinta da ita ta had'ata tayi mata, cike da kulawa tace "zamu je Gym da Babe do you need something?" wani abu fatun taji ya daki kirjinta hakan yasa ta d'an kauda kanta ta girgiza mata Fanan din tace to ta koma ta kwanta Allah ya bata lafiya daga haka ta juya har takai bakin kopa ta juyo ta kalli Haulat tace "U'r Haulat right?" da sauri haulat ta d'aga mata kai kaman kadangaruwa Fanan d'in tace "I heard u'r Zara's best friend nayi farincikin ganinki" tayi Maganar tana mik'a mata hannu a d'arare haulat ta kama hannun wani kalan taushi data ji har saida ta had'iye miyau kutt, "zanzo gidanku in gaisa da mom naki in Zarah ta samu lpy" da sauri haulat tace mata to ta d'an yake baki ita ala dole Murmushi take, janye hannun tayi tace mata ta tafi, ai tana fita Haulat bata san lokacin da a zuciyarta ta furta "Bura ubannan Astagfurullah", juyawa tayi ta kalli Fatuu suka yi ma juna k'uri da alama wutar kowa ta d'auke, a sanyaye Haulat ta koma ta zauna ganin kallon da fatuu ke binta dashi idanunta sun cika da kwalla yasa tace " itace ko?" kai ta d'aga mata alamar eh, shuru sukai kowa da abunda yake sak'awa can Haulat taji Fatuu tace "Yanzu Haulat ya za'ayi" a d'an firgice Haulat tace "Uhyumm" matsowa Fatuu tayi ta kama hannuwanta kwalla suka fara zubo mata tace "Don Allah ki bani shawara Haulat yanzu ya zanyi, wllh inason Ya Handsome in ban aureshi ba zuciyata zata iya bugawa yanzu haka bakiji yadda nike ji ba kaman ana hura man wuta ga wani bugu da take man mara dad'i" tana kai Maganar ta d'ago hannun Haulat d'in ta d'aura kan kirjinta kwalla naci gaba da zubowa, wani wahalallan miyau Haulat ke had'ewa ta k'ura ma Fatuu idanu ba tare data ce mata komae ba,
"Haulat don Allah ki taimaka man kinga dama kin saba bani shawara in ina cikin mawuyacin hali kuma duk inkika bani tana man aiki don Allah ki fad'i man abunda zanyi yanzu?" nannauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin tace "kin yarda in na baki shawara tana maki aiki? Da sauri ta d'aga mata kai alamar eh, taci gaba "to zan baki shawara amman da farko ina mai baki hakuri akan halin da kike ciki don duk ni naja maki dana yanke hukunci ba daidai ba batare da nayi la'akari da wani lokacin ko a Novel d'in muna yin hasashe yazo bai zama gaskiya ba....." katseta Fatuu tayi "ki bar d'aura ma kanki laifi ai dama kince nima ina sonshi kuma bazan gane ba sai naga ina niyyar rasashi to abunda ya faru yanzu kenan ni dai ki bani shawarar kawae" wata ajiyar zuciyar Haulat ta kara yi kafin cike da k'arfin hali tace "Shawarar da zan baki itace.................
Domin karanta cikakken Littafin sai ku danna bulun Rubutun dake kasa ko kuma hoton dake kass πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

https://aihausanovels.com.ng/novel-document/a-sanadin-makwabtaka-book-2-complete-hausa-novel

πŸ‘†πŸ‘†πŸ‘†πŸ‘†πŸ‘†


*ASM2003*
*πŸ’–A SANADIN MAKWABTAKAπŸ’–*
_*(Love and Destiny)*_



_*BY ZAINAB LALUHπŸ“²*_
~(Oumm Imam)~

Book 2

Bonus Page 3


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*





"........KIYI HAKURI FATUU...." Fuzge hannunta tayi kaman wadda
Shock yaja tunkan haulat d'in ta rufe baki tana fitar da numafashi da sauri sauri tace"Hakuri! ya zaki ce in yi hakuri bacin na gaya maki ina sonshi,ni dai bazan iya hakuri ba Haulat ki taimaka ki gaya man yadda zanyi in ba haka ba na gaya maki zuciyata bugawa zatayi" nan da nan idanun Haulat suka ciko tabb da kwalla ganin wai Fatuu ce a wannan halin ita da sam so bai gabanta bata da burin daya wuce tayi Karatu amman lokaci guda komae ya canja so yayi mata mugun kamu, duk gani take laifinta ne hakan, kamo hannun Fatun tayi cikin karewar murya tace "da inada shawarar da tafi wannan da na baki k'awata don nima banson ganinki cikin irin wannan mawuyacin halin to amman ya zamuyi dole saidae fa hakurin tunda dai kinga har ansa masu biki",
cikin muryar kuka tace "to ko in fad'i mashi ina sonshi don Allah ya Aure ni nima?" D'an girgiza kai Haulat tayi jin wata Magana ta Fatuu wadda daga ji bata yi tunani wurin fad'inta ba,
Gyara zama Haulat tayi tace "duk da bansan ya kike ji acikin zuciyarki ba amman zan iya fahimta daga yanayinki tabbas nasan kina cikin mawuyacin hali, amman fa kisani in kika ce zaki hakan to fa ba k'aramin kuskure zaki yi ba kizo ki k'ara jefa kanki wani halin don karshe nasan ba samun biyan buk'ata zaki ba, ke da kanki kince yayi farincikin zuwanta sosae kinga alamar yana sonta kenan sannan yanzu a gabanki ta fad'i cewa an gaya mata ni aminiyarki ce wa kike tunanin ya fad'i mata hakan in ba Ya Haisam d'in ba, kinga kenan duk wani abu game damu yana sanar mata ko daga kanki ma ai zaki gane yadda ta sanki sosae tun kafin ta ganki a zahiri to baki tunanin in kin gaya mashi zai iya sanar da ita kuma in tasan hakan mi kike tunanin zai faru? Duk fa yadda kike ganin kaman tana da kirki wllh tasan da wannan Maganar za'a samu matsalane babba don ba yarda za'ai ace bata kishin Ya Haisam baima yuwuwa wllh kuma tana iya sanar da Hajiya k'arshe in Maganar ta dawo kunnan gwaggo mi kike tunanin zai faru? kiyi tunani Fatuu kowa na iya yi maki kallon mara hankali ma "

"Amman ai ba lalle in yaji irin wannan Maganar ba ya sanar da itan" k'ara girgiza kai Haulat tayi don ta fahimci Fatuu bata cikin hayyacinta shiyasa bata ganin hakan a wani abu tace "to kina tunanin in kin fad'i mashin Auren naki zaiyi, ni na tabbatar hakuri zai baki Ya nuna maki yana da wadda zai Aura kiyi tunani bafa zai ta6a aurenku ba ku biyu, ai ko danginsu ma bazasu ta6a yarda ba kar fa ki manta yar'uwarshi ce waye zai goyi bayan ayi mata kishiya a cikinsu bafa mai son kishiya Fatuu sai dole, duk da halin da kike ciki kar ki bari tunaninki ya gushe kizo kuma ki abunda zaki danasani ki daure ki cije ki yak'i zuciyarki ta fitar da Ya Haisam daga cikinta shine abunda yafi Alkhairi" bin ta da ido kawae Fatun keyi yayin da cikin ranta take juya Maganar Haulat d'in lokaci guda ta tuno da Farha da Abubuwan data rink'a yi mata lokacin data fara ganinta da kuma wani zuwa da suka k'ara yi yanzune ta gano dalilin da yasa hakanan ta d'auki karan tsana ta d'aura mata ashe kishi take taya yar'uwarta, ganin tayi shiru yasa Haulat cigaba da tausarta tana k'ara nuna mata had'arin dake tattare da abunda take tunanin yi na sanar mashi,

K'arshe dai saidae fasa zuwa islamiyyar Haulat tayi sai gab da Magrib ta bar gidan duk jikinta yay sanyi lakwas, Tun bayan da Haulat d'in ta tafi tay zaune saman gado ta had'e kafafunta ta d'aura ha6arta idonta akan bangon d'akin tana ta nazarin Maganganun Haulat tabbas tasan in har Gwaggo taji wannan Maganar
Showing 6001 words to 9000 words out of 113043 words