zaki iya yin wani abu bai kamata ayi mata aure ba" sauke ajiyar zuciya Hajiya tay tace "kagane su a wurinsu hakan daidai ne don haka suka saba za6a ma yara miji ...." Katseta yay "amman ita ba a wurin su take ba ai why za'a mata haka? U ave to do something sweetheart I think is part of ur work right?" D'an guntun murmushi mai sauti Hajiya tay tace "abunda nike son ka gane wannan family issue ne kaman yadda na fad'i maka haka suke ma yaran su yanzu inna ce in shiga Maganar ba lalle in yi nasarar hana yi mata auren ba in kuma aka yi nasarar to kuwa mahaifin nata ne a matsala kamar yadda na fad'i maka d'azun hakan ne ma yasa ita Fateema ta nuna ta Amince don fitar da mahaifinta daga halin da yake ciki" fuska a kwa6e yake saurararta bayan ta gama yace "so now u mean there's no way out dole ayi mata auren?" Hajiya tace "to ya za'ai in haka Allah ya kaddaro dole sai anyi mata auren sai dae ai fatan Allah ya zaba abunda yafi zama Alkhairi, ita kanta Fateemar ta ban mamaki wllh ban yi tunanin zata yi k'arfin hali har haka ba to amman nasan ba yadda zata yi ne bata son mahaifinta ya shiga matsala ne Saboda ita, yanzu tace sati mai zuwa mahaifin nata zai zo d'aukar ta yanzun nan ma ta kawo man kud'i da ya turo mata don ta sayi kayan kitchen" shiru bai ce komae ba har saida hajiyar tace ko shima ya fara baccin ne sannan ya yi magana yace Allah yasa hakan yafi zama Alkhairi ta amsa da Amin daga haka su kae sallama tace ya gaishe da Fanan, tun bayan da suka gama wayar still yay hannunshi dake ruk'e da wayar ya d'an dafa ha6arshi da shi kwata kwata bai ji dad'in Maganar auren ba sosae ran shi ya 6aci don har fuskar shi ta bayyana hakan, ya dau lokaci a hakan mutsu mutsun da Fanan ta fara yi ne yasa shi kai idanun shi kanta slowly ta fara bud'e nata idanun kafin ta ware su a kan fuskar shi tana ganin yanayin fuskar tashi ta yunk'ura ta tashi zaune shi kuma ya d'age kan nashi yana facing sama duk a tunanin ta Saboda rigimar zuwa Asibitin da ta gama yi mashi ne hakan yasa ta kai hannu ta kamo hannun shi guda a sanyaye tace "babe are u angry with me?" Shiru bai ce komae ba bai kuma d'ago ba cikin breaking voice ta kuma cewa "am sorry for dat son da nike maka ne yasa am eager to ave child wit u..." Kwalla ne suka taru a idonta tay shiru sai lokacin ya d'ago ya bita da ido kawae, shi kan shi bai san miya sa Maganar auren Fatun ta dame shi ba, sosae yake jin ba dad'i a ran shi da k'yar ya d'an yi mata guntun murmushi yace kar ta damu ba wannan ke damun shi ba, cike da kulawa ta tambayi abunda ke damun shi kawae sai ce mata yay bai jin dad'in jikin shi ne da sauri ta matsa ta fara tatta6a jikin nashi wai ko fever ce shi dae bai ce mata komae ba can ya fara k'ok'arin tashi yace zai je ya kwanta itama mik'ewa tay ya kai hannu zai d'auki laptop d'in ta rigashi d'auka bayan ta rufeta suka nufi bedroom d'in shi yana shiga ya kwanta dama shima sleeping dress ne a jikinshi, Fanan duk ta damu don tunda suka yi aure bata ta6a ganinshi a cikin irin yanayi haka ba yawanci in taga canji tattare da shi ta tambaye shi zai ce ya gaji ne ko kan shi na mashi ciwo yanzu kuma ta fahimci kamar yana cikin damuwa ne, cike da kulawa ta zauna a gefenshi ya kalleta tace mashi ko ta had'o mashi coffee ko tea ya d'an girgiza mata kai alamar a'a tace to miya ke damun shi ta d'aukko mashi magani tun da taji ba fever a jikin shi d'an murmushi yay mata ya kai hannu ya jawo ta ta hawo gadon sosae a hankali ya furta "am Ok" da yar damuwa tace "are u sure?" Lumshe mata ido kawae yay ta kwantar da kan ta a chest d'in shi tana shafa lallausar sumar dake kwance a wurin da hannunta guda akai akai take d'aga ido ta kalli fuskar shi ya rufe idonun shi hakan yasa tay tunanin yay bacci a wani bangare na zuciyarta kuma she's thinking what makes him so worried sanin shi ba abu kadan ke sa a ga damuwar shi ba, jin saukar numfashin ta a saman chest d'in shi yasa shi gane tayi bacci slowly ya ware idanunshi dama yayi hakan ne don bai son taci gaba da tambayan shi abun da ke damun shi gashi ya kasa sanar da ita zancen Auren da za'a yi ma Fatun don baison ma yin maganar, a nutse ya kai hannu ya janyeta daga jikinshi ya tashi zaune ya had'e hannuwan shi ya d'aura habar shi sam ya rasa ma tunanin da zai yi ba kamar da Hajiya ta nuna ba abunda za'a iya yi a hana su yi mata auren can ya sauke hannuwan ya kai hannu kan side drawer ya d'auki wayar shi saida ya gyara ma Fanan kwanciya ya lullu6e mata rabin jikinta da duvet ya rage hasken d'akin sannan ya juya ya fita, Parlor ya nufa ya zauna kan kujerar da ya tashi ya fara kokarin kiran layin Fatuu........




_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268._

Domin karanta cikakken Littafin sai ku danna bulun Rubutun dake kasa ko kuma hoton dake kass πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

https://aihausanovels.com.ng/novel-document/a-sanadin-makwabtaka-book-2-complete-hausa-novel

πŸ‘†πŸ‘†πŸ‘†πŸ‘†πŸ‘†



*ASM Bk2026*
*πŸ’–A SANADIN MAKWABTAKAπŸ’–*
_*(Love and Destiny)*_



_*BY ZAINAB LALUHπŸ“²*_
~(Oumm Imam)~

Book 2

Bonus Page 26
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*





.........Tana zaune kan darduma ta gama salla tana lazimi a d'akin Saude wayarta dake aje a gefen katifa ta fara ringing, a hankali taja jiki ta matsa ta kai hannu ta d'auki wayar ta duba mai kiran nata, Jim tay ganin sunan Ya Haisam ya bayyana kafin tayi picking ta kai kunne, shiru sukae gaba d'aya kaman bazasu yi Magana ba can Haisam d'in ya kira sunanta "Zaraah" har saida gabanta ya d'an fad'i jin yanayin da ya kira sunan nata cikin shaky voice tace "N..na'am Ya Haisam ina wuni" bai amsa mata ba ta sake cewa "Ya Aunty Fanan" sai lokacin yace "she's fine" shiru suka d'an k'ara yi kafin yace "I heard u'r going to get married right?" Har saida ta had'iye abu cikin karewar murya tace mashi eh,
"Kin hak'ura da zama Doctor kenan?" d'an runtse ido tay lokaci guda kuka yazo mata tace "Ehhh.. " yana jiyo sheshshekar da ta fara yi a hankali, d'an yamutsa baki yay kafin yace "Why are u crying, ba kina so ba shiyasa kika amince" cikin kuka tace "a'a Ya Haisam wllh bani so ba ni da yadda zan yi ne in ban amince ba Baffana zai shiga matsala ne Baban shi Ard'o zai tsine mashi yanzu haka ma duk yan gidan sun juya masu baya Saboda ya nuna bai so ayi man Auren shiyasa kawae na Amince don in taimake shi" sosae yake jiyo sheshshekar kukan nata yanzu slowly ya runtse idonshi ya d'age kan shi sama boiling from inside, ba k'aramin abu ke k'ona mashi rai ba amman wannan Al'amarin sosae ya ta6a mashi zuciya ba kamar yanzu da yake jiyo kukan ta ya fahimci itama abun ya ta6a mata zuciya sosae, sun dau d'an lokaci haka kafin ya sauke nannauyar ajiyar zuciya ya kira sunanta ta amsa yace "is Ok, I get u so stop crying and pray for d best" jinjina kai tay kaman yana ganinta sai kuma tace to daga haka yace mata zai kwanta su dare ne yanzu tace mashi sai da safe, koda suka gama wayar zaune yay a wurin bai tashi ba still kan shi a d'age yake saidae ya bud'e idanunshi ya k'ura ma ceiling ido da alama tunani yake, suna gama wayar taci gaba da kukan da take yi wanda ba na komae bane face tabo da Haisam ya fama mata, a cikin ran ta take ayyana da ta aure shi duk da yanzu bata shiga wannan halin ba tunda ba wanda zai ce ai zai mata aure tana cikin haka Saude ta shigo don tace mata ta fito ta ci Abinci ta iske ta haka da sauri ta zauna gefen Katifar ta janyo kan Fatun saman cinyarta ta shiga tambayarta lafiya cikin kuka take fad'in ita bata son auren nan, sosae ta ba Saude tausayi don Hajiya ta fad'i mata zancen Auren da za'ai ma Fatun, lallashinta ta shiga yi tana mata Nasiha har sai da tayi shiru sannan ta kama ta ta kaita toilet don ta wanke face d'in ta bayan ta gama ne suka nufi Parlor. Kullum gidan Hajiya take wuni ba laifi gwaggo na d'an sake mata amman ba wani sosae ba, ranar Friday da safe Baffanta ya kirata ya sanar da ita game da zuwan shi ranar lahadi in Allah ya kaimu yace mata akwae wani Abokin shi da zai kawo shanaye kasuwar charanchi ranar lahadin in zai koma sai su tafi tare koda akwae kayan da za'a d'auka tunda Motar tashi babba ce, wata irin kyerma jikinta ya fara yi a dabarbarce take amsa mashi bayan sun gama wayar zaune tay tana ta zare ido ya dae tabbata auren za'ai mata ji take tamkar ana zare mata lakar jikinta ta d'au lokaci a haka kafin da k'yar ta mik'e taje ta sanar ma gwaggo to itama dae ta girgiza da jin zancen amman bata nuna ba kawae sai ce mata tay Allah ya kaimu bata ji komae ba da yanayin yadda gwaggon ta bata amsa don tama saba da yadda take mata Magana yanzu, bayan ta fito ta koma d'aki gyale ta yafa ta nufi gidan Hajiya lokacin da ta je hajiyar na bedroom d'inta da sallama ta shiga ta amsa mata da murmushi gefenta ta baza wasu takardu da alama tana duba wani abun ne, gaida ta Fatuu tayi ta nuna mata gefenta tace ta zo ta zauna bayan ta zauna ne hajiyar ta tambayeta lafiya ta ganta sukuku nan da nan idanunta suka kawo ruwa tana kyakkyafta idanu don kada su zubo murya na rawa ta fad'i mata game da zuwan baffan nata itama hajiyar Maganar ta dake ta tay shiru can kuma sai tace Allah ya kawo shi lafiya Fatuu ta amsa da Amin yayin da kwallan da take ruk'ewa suka fara zubowa Hajiya ta fara lallashinta had'i da yi mata Nasiha mai tsuma jiki sosae taji ta samu natsuwa.

Washe gari Asabar Fatuu da ta je islamiyya ta yi ma k'awayenta bankwana had'i da neman yafiyar su duk sunyi mamakin jin zancen Auren don ba wanda ya san da Maganar har Malaman su ma sun yi mamaki sun kuma yi mata Addu'oi har Malam Nazifi na cewa bata fad'i da wuri ba da an yi mata sauka amman ko bayan ta tafin in sha Allahu zai sa ayi mata bai amshi hadda ba a lokacin sai kawae yayi masu Wa'azi game da rayuwar gidan Aure da yin biyayya ga miji sun sha kuka ita da k'awayenta yan ajin su da aka tashi har saida suka rakota har gida, tunda ta dawo take k'umshe a cikin d'aki ko Abinci ta kasa ci Alwala kawae ke fiddo ta haka ma gwaggo kowa dae yana cikin matsananciyar damuwa, bayan sallar la'asar ne tana zaune kan abun salla wayarta tay ringing ta mik'e taje bakin gado inda take ajiye ganin hajiya ce yasa ta d'auka da sauri bayan ta gaishe ta ta tambayeta tana gida ko ta tafi islamiyya tace mata tana gida tace to ta zo yanzu ta amsa da to, dama akwae hijab a jikinta wucewa kawae tay bayan ta lek'a ta sanar ma gwaggo hajiya na kiranta ta d'aga mata kai kawae, a Parlor ta iskesu ita da Saude da Tk ga wasu manya manyan kwalaye guda biyu dake a bud'e shak"e da kayan amfanin kitchen gaida su tayi su duka suka amsa mata fuska a sake hajiya ta nuna mata kayan tace "Fateema ga kaya nan ki duba in akwae abunda kike so wanda babu sai ki yi Magana, can waje a bayan Mota akwae freezer da gas cooker ba'a shigo dasu ba kar ai wahalar sake fitar dasu kuma" mutuwar tsaye Fatuu tay tana ta zare ido ganin uban kayan dake gabanta wai kuma nata ne, ganin bata da niyyar dubawar yasa Hajiya ce ma Saude ta firfito mata da kayan ta gani ta amsa da to ta duk'a ta fara fiddo kayan, ba abunda babu da zaka samu a kitchen d'in yan gayu tun daga kan kaya masu amfani da wuta da sauran kayan amfani a cikin d'ayan kwalin harda rantsattsun zannuwan gado da labulaye sai daga baya ne ma Fatun ta lura da k'aton kwalin plasma TV dake can gefe itama Hajiyar tace tata ce she was completely speechless sai bin komae take da ido Hajiyar ta tambayeta akwae sauran abunda take so wanda babu girgiza mata kai kawae tay don ta kasa Magana ganin abun take tamkar a mafarki tana cikin hakan Hajiya ta mik'o mata kud'i tace "ga wannan kud'in da kika kawo man ne Yayan ki ne ya turo da kud'i aka siya maki komae sai ayi wani amfanin da su" idanu raurau ta kalli hajiyar tace ta kar6a mana sai kawae ta saka mata kuka Hajiya tace "Fateema wannan koke koken yayi yawa zai iya ja maki wata matsalar ina mun gama Magana dake?" Kai ta d'aga mata tace to tayi shiru sai lokacin ta yi mata godiya Hajiya tace ma Tk ya tashi su maida su cikin Mota a had'a da sauran akai can gidan ya amsa da to ya mik'e Saude ma ta tashi ta kama mashi suka fara fita da su, gaba d'aya da Sauden da Fatuu aka tafi lokacin Amadu na shago Tk ya parker hilux d'in Hajiyar duk suka fito Amadu na ganin su shima ya fito suka fara kai kayan ciki, jin anata kacaniyar shigo da kaya yasa gwaggo fitowa tana yin arba da kayan tay turus tana bin su da ido Fatuu ce ta nufe ta ta tsaya a kusa da ita a sanyaye tace "wai Hajiya ce tace a kawo Ya Haisam ne ya turo da kud'i aka siya ga wanda na kai mata tace a yi wani abun da su" ta kai Maganar tana mik'a ma gwaggo kud'in hannunta a hankali tace ta ruk'e a hannunta, lokacin Saude ta k'araso ta gaishe da gwaggon da d'an murmushi ta amsa mata tayi mata godiya, bayan an gama shigo da komae su Tk d'in sun tafi Amadu ya fara firfito da komae cike da mamaki yana dubawa itama gwaggo idonta na akai lokacin da ya gama ya d'ago ya kalli Gwaggo yace "Naira dae tasha kashi a wurin nan wannan ai an kashe million koma fi, ji wannan k'atuwar freezer da gas cooker don Allah ga plasma ma babbar" ajiyar zuciya kawae gwaggo ta sauke kafin a hankali tace an gode Allah ya saka da Alkhairi Amadu ya amsa da Amin ganin tana niyyar juyawa ta koma d'aki yace ba za'a shiga dasu bane ta dakata tace tunda tafiya za ai dasu su kauda su gefe daga haka ta shige d'aki bada jimawa ba kuma sai gata ta fito sanye da hijab ta nufi gidan Hajiya don yin godiya, da daddare lokacin Fatuu ta gama komae ta kwanta tay tunanin yakamata tayi ma Ya Haisam godiya duk da bata son Auren taji dad'in kayan don ko d'iyar wasu masu kud'in ce iyakar abunda za'a mata kenan, lokacin da ta kira dawowar shi kenan daga Masallaci sallar Asuba a edge d'in gado ya zauna yay picking call d'in bayan ta gaida shi ya amsa ta shiga yi mashi godiya yace ba wani abu shiru suka d'an yi jin kaman tana kuka yasa shi fara lallashinta suna cikin hakan Fanan ta shigo jikinta sanye da jalbab da alama itama sallar tayi zama tayi kusa da shi tana sauraran yadda yake Magana cikin kwantar da murya har saida ta d'an yi mamakin da wa yake Magana haka, sosae ya kwantar mata da hankali kafin sukae sallama yay mata Allah ya tsare hanya yace sai ya sake kira, yana cire wayar Fanan ta tambaye shi wacece yake lallashi haka bin ta da ido yay ganin ta kafe shi da idanu alamar amsa take jira yasa shi d'age mata gira yace "kishiyar da zan maki ce" wani kalan kallo ta jefa mashi ta d'aure fuska tamau can kuma sai ta ce "Babe I hate dis kind of jokes" murmushin gefen baki yay ya ja jiki ya jingina bayanshi da heardboard yana cigaba da kallonta ta wani sha murr ita ala dole bata son zancen kishiya ganin baida niyyar yi mata bayani yasa ta k'ara tambayarshi da wa yake wayan sannan yace mata Zaraah ce with surprise tace to mi ya faru taji yana lallashinta haka sai lokacin ya sanar mata zancen Auren da za'ai mata itama ta nuna bata ji dad'in hakan ba k'arshe tace Allah yasa hakan yafi zama Alkhairi. Washe gari da safe lokacin da ta je gaida gwaggo tace mata ta shiga makwabta tay masu sallama tace to, duk inda taje da an ji zancen Auren sai anyi mamaki jin abun kwatsam akai tayi mata fatan Alkhairi harda masu bata kud'i amman ta k'i amsa daga baya ta wuce gidan su Haulat lokacin da ta sanar ma innarsu haulat
Showing 87001 words to 90000 words out of 113043 words