"Akwae Account da yace man a bud'e maki so ki fad'a a gida zuwa gobe da safe sai muje kafin ku fara exams d'in" taji Abbas d'in ya fad'a idonta akanshi ta d'an tura baki tace "Account d'in me kuma?" Da murmushi yace "Bank Account mana yana bukata ne nasan Saboda ya samu sauk'in turo maki kud'i ne" yamutsa fuska tay kaman zatai kuka tace "to ai ya bani kud'i masu yawa da zai tafi ni bani buk'atar wasu kud'i" Abbas yace "ke da zaki cigaba da karatu aikuwa kina buk'atar kud'i sosae Mom Zaraah our future Doctor, ai dama kin bishi can kin yi karatun cikin sauk'i" wani kallo tay mashi tace "kam Matarshi taga na lik'ewa mijinta ta koro ni, nima bazan ma je ba" dariya yasa ganin yadda tay Maganar kafin yace bari ya wuce Magrib ya kusa ya tambayeta tana da passport guda biyu tace eh ganin yana k'ok'arin shiga Mota tace "Ya Abbas ka tsaya kaci Abinci sannan ka tafi" dakatawa yay ya kalleta yace mata kar ta damu sun ci Abinci a hanya kuma gida zai koma zai ci acan" tura baki tay a shagwa6e ta langa6ar da kai tace "ni dae don Allah ka tsaya kaci nifa na dafa shi" k'ura mata ido yay yana murmushi acikin ranshi yake ayyana yanzu ya gane dalilin da yasa suka shak'u da Haisam sosae sam in kana magana da ita baka jin ka k'osa komae nata nada burgewa katse mashi tunani tay da fad'in "Ya Abbas zaka ci ko don Allah?" Sigh yay yace "Ok ki zubo man in tafi dashi sai in ci a gida yanzu Magrib ya kusa amman fa bada yawa ba" washe baki tay alamar taji dad'i tace to ta juya da sauri ta d'aura kallabin saman kai ya bi bayanta da kallo har ta shige hakanan shima yana son ta da Haisam don ba k'aramar fahimtar juna za'a samu ba tsakaninsu ba ita kanta yanzu yadda akanshi ta fara sanin so to ba lalle ta so wani Namiji har ta samu natsuwa da shi kaman haisam d'in ba to amman yasan kasancewarsu tare matsayin ma'aurata ba k'aramin abu bane gashi yasan Haisam baida ra'ayin mata biyu saidae hakan ba matsala bane don yasan Mutane masu irin ra'ayin nashi wanda yanzu suna da mata fiye da d'ayan amman kuma ita kanta Fanan zata iya zama shamaki kan hakan don Ya fahimci ba k'aramin kishi zatayi ba a k'arshe ya yanke duk hakan k'aramin abu ne a wurin Ubangiji in dai ya kaddaro masu zama ma'auratan, rungume da Warmers babba da k'arama ta fito sai Leda yar babba ruk'e a hannun ta sak'o robobin kunun Aya da Coleslaw tana ta washe mashi baki ta nufeshi bud'a ido yay lokacin data k'araso yace "Mom Zarah wannan ai kin kwaso man Abincin yayi yawa" bata ce komae ba ta bud'e kopar baya ta saka Warmers d'in da ledan bayan ta rufe tana dariya tace "ai ba naka bane kai kadae harda Abdul da Aunty Feenah na zubo mawa in kuka ci ina jira ka fad'i man yayi dad'i ko bai yi ba" yana dariya ya jinjina mata kai kawae ta juya tana ce mashi sai Allah ya kaimu yace Ok zai kirata ya fad'i mata time da zasu fita daga haka ya shige Motar ya tafi.

Tana shiga d'akin gwaggo ta nufa lokacin tana cikin cin Abincin da Haulat ta zubo mata ta nufeta ta zauna ta jingina da jikinta a Shagwa6e take fad'in "shine kuka je kukai zaman ku bacin tun ran Juma'a aka d'aura Auren baku damu da kun bar ni ni kadae ba ko" dakatawa gwaggo tay tana dariya tace "to ayi hakuri auta kamawa tay nima duk na damu da rashin ki kusa amman kuma dae ai nasan ba ke kadae na bari ba ko" tura baki tay haulat dae nata dariyar yadda Fatun keta shagwa6a, yabon Abincin gwaggo ta shiga yi da yadda suka gyara gidan tace sunyi kokari sosae hakan yasa ta warware ta fara dariya cike da tsokana gwaggo tace "shiyasa bani da wani shakku akan ku in ku kai aure" turo baki Fatun tay tace "in dae tay aure" gwaggo tace "kema ai zaki yi ne ko an dingi karatun ne ba ranar gamawa?" Tace "ai kona gama ni bazan yi aure ba" da sauri gwaggo tace "ba Amin ba ban fata in ma kina cikin karatun Allah ya kawo Nagari ai aurar dake zanyi kawae Kya idasa a d'akin mijinki" shiru tay kawae cikin ranta tana ayyana da nasamu wanda nike so ma kafin in fara karatun zanyi aure na kallon haulat tay suka had'a ido tay mata Murmushi ita kuma ta tura mata baki, Bayan Magrib duk sunyi salla gwaggo ta kwala masu kira suka shigo d'akin suka zauna ta janyo wata katuwar jaka cikin kayan da suka zo dasu ta tura ma Fatun tace "ga sak'on Yayanki nan tunda bazaki tambayeshi ba da Auntyn taki Amarya, d'an kallon juna sukai ita da Haulat cikin kama kai tace "ai na tambayi ya Abbas ne fa shiyasa banyi maki Maganar ba" gyad'a kai tay Haulat ta kai hannu ta bud'e jakar wadda ta bikin ce mai d'auke da sunayensu a cikinta ma duk tarkacen souvenirs ne da aka rarraba a bikin kaya jibgi guda sai kace d'an gidansu ne yay auren ai ko d'an gidansu ne bazata samu rabin su ba ma, wata k'atuwar Calendar Haulat ta fiddo ta bud'e har bata san lokacin data furta "Wow! Gaskia sunyi matuk'ar kyau wllh" gwaggo ta amshe da fad'in "ah ai ba'a cewa komae Haulat sai Mutum ma yaje hidimar abun sai san barka wllh amman an yi matuk'ar kokari kowa yabo da fatan Alkhairi yake masu" Haulat dake murmushi tace "Allah ubangiji yasa Alkhairi ya basu zaman lafiya" gwaggo ta amsa da Amin Fatuu ma ta amsa a hankali duk jikinta yay sanyi lakwas, mik'a mata Calendar d'in Haulat tay kaman bazata amsa ba sai kuma ta amsa ta zuba mata ido Haisam kawae take kallo sun yi kyau iya kyau hoto ukku ne a jiki babba na sama sai biyu a k'asa gefe da gefe sunyi shiga daban daban ta Alfarma dake nuna mawadatan Mutane ne ko ina Fanan tayi dariya shi kuma d'an Murmushi yayi wuri d'aya ne yay yar dariyar da har dimple d'inshi ya lotsa da sauri ta mik'a mata Calendar din jin kwalla na niyyar taruwar mata a idanu, Haulat taci gaba da fiddo abubuwa harda jakunkunan kwali suma masu d'auke da pic dinsu gwaggo ta sake janyo wata jakar ta fiddo yan buckets masu kyau guda ukku suma dai na bikin ne tace ma Fatuu ga kuma sak'on Hajiya suma haulat ce ta bud'e marfinsu d'aya dublan ne d'aya cincin da doughnuts d'ayan kuma Alkaki ne da cake gwanin sha'awa d'an murmushi tayi ta tambayi gwaggo ita sai yaushe zata dawo tace bata sani ba amman zata d'an kwana biyu, suna haka Amadu ya shigo ya zauna hiran bikin ya shiga yi masu harda pictures da Vedios ita dae Fatuu zugudum tayi Haulat nata washe baki tana tsuma had'i da yabawa sai faman zuzuta bikin yake da gidansu ya Haisam d'in da gaba d'aya garin Abujar don sun fita da Nameer ya zaga gari dashi bama sau d'aya ba gaba d'aya jikin Fatuu yayi weak lokaci guda ta yanke tun farko sunyi kuskuren da har sukae tunanin Haisam zai so ta don kwata kwata ba ajinta bane ma, sai da akayi isha Haulat tace zata tafi gida gwaggo ta d'ibar mata abubuwan bikin tace ta kai ma Innarta ta kuma bata kud'i farko K'in amsa tay saida gwaggon tace yaushe suka fara wasa irin haka sannan ta amsa tayi godiya itama Fatuu ta d'ibar mata komae cikin nata ta rakata har gida koda innarsu taga abubuwan da aka bata sosae tay godiya har tana zolayar Fatuu tana cewa da yake fa gwaggo ta dawo gashi nan tana ta fara'a yanzu ita dae yar dariya kawae tay daga baya tay masu sallama haulat ta rakota bakin lungu ta tafi, da wuri gwaggo tay bacci ita kuma sam baccin ya k'aurace ma idanunta tay zaune saman gado ta tasa Calendar d'in tana sake kallo bata yi kuka ba saidae wata irin kewar Haisam d'in take ji k'arshe ta kwanta hannunta kan fuskarshi tana shafawa tana d'an murmushi mai ciwo tunowa da abubuwa da dama a haka dae har bacci yay awon gaba da ita.Washe gari tana cikin yin Breakfast Abbas ya kirata yace wurin 11 zai zo ya d'auketa ya d'an shiga Jami'a ne tace to sai lokacin ta tuna bata ma fad'i ma gwaggo ba dama suna tare a falon ta sanar mata godiya ta shiga yi da yima Haisam d'in Fatan Alkhairi tace tay sauri ta shirya kar lokaci ya k'ure yazo ta 6ata mashi lokaci ta amsa to ta mik'e, kafin lokacin ta gama shiryawa cikin doguwar rigar Atamfa ta d'an yi yar light make up k'arfe 11 saura yan mintuna yazo ta yafa gyalen da suka hau da kayan da takalma ta d'auki yar jakarta ta fita saida ta lek'a tace ma gwaggo sun tafi sannan ta nufi wajen, lokacin data isa bakin Motar kwankwasa glass tay ya bud'e yana sanye da jeans da t-shirt ta d'an lek'a tana murmushi tace gaba zata shiga ko baya sosae ta bashi dariya jin tambayar da tayi shima ya tambayeta a Motar ya Handsome ina take zama ta nuna mashi gaba yace to nan zata zauna sannan ta bud'e Motar ta shiga tana yar dariya ta gaidashi tay mashi ya gajiyar hanya ya amsa sannan yaja suka tafi, basu wani 6ata lokaci mai tsawo ba a Bank d'in aka gama mata komae bayan sun fito gari ya d'an zagaya da ita saida ya tabbatar ta warware sosae dama Abbas d'an barkwanci ne sosae yake ta saka ta dariya har tambayarshi tay game da Abincinta yace yayi dad'i sosae Feenah ma da Abdul sun yaba har santi sukae sosae ta washe baki can tace to in mark zai bata nawa zai bata, d'an jimm yay sai kuma yace "zan baki 95%" d'an jujjuya kai tay tace "Gaskia Ya Abbas ban yarda ba ka cike man 5 marks d'in kawae mana ba kace har santi su Aunty Feenah sukai ba" yana dariya yace "No bazan baki 100 ba da dai a gidan mijinki kika yi shi confirm kin cancanci 100%" d'an murmushi kawae tay bata ce komae ba, a wani Eatery ya tsaya yace suje suci Abinci batare data musa ba tace to suka nufi ciki ya tambayi abunda zata ci bayan sun zauna tace "Burger and ice cream" yar harara ya wurga mata kafin yace "I mean Abinci ba kayan kwad'ayi ba" tace "to ai suma Abincin ne tunda ana koshi" girgiza kai yay yace ta dai fad'i Abinci a shagwa6e tace "ni dai su nike so inna koma gida naci Abincin...." Tun kafin ta rufe baki ya fara girgiza mata kai kaman zatai kuka tace "Wayyo bafa haka Ya Haisam ke man ba dana fad'i abunda nike so yake man kuma kace Amanata aka baka fa" dariya sosae yasa yace shikenan yaja ma kanshi dama bai fad'i mata ba dariya itama take yasa akawo mata abunda take so d'in shima ya fad'i abunda za'a kawo masa, bayan duk an kawo masu suna cikin ci wayar Abbas dake gefenshi ta fara ringing ya kai idonshi kan screen d'in yana ganin mai kiran ya dakata yana murmushi ya kai hannu yay picking kafin ya karata a kunnanshi yace "Latest Ango Mutanen US....." Jin hakan yasa Fatuu ta kalleshi da sauri............




_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wannan no 09013804524._

Domin karanta cikakken Littafin sai ku danna bulun Rubutun dake kasa ko kuma hoton dake kass πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

https://aihausanovels.com.ng/novel-document/a-sanadin-makwabtaka-book-2-complete-hausa-novel

πŸ‘†πŸ‘†πŸ‘†πŸ‘†πŸ‘†


*ASM Bk2022*
*πŸ’–A SANADIN MAKWABTAKAπŸ’–*
_*(Love and Destiny)*_



_*BY ZAINAB LALUHπŸ“²*_
~(Oumm Imam)~

Book 2

Bonus Page 22
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*






.......wayar Abbas dake gefenshi ta fara ringing ya kai idonshi kan screen d'in yana ganin mai kiran ya dakata yana murmushi ya kai hannu yay picking kafin ya karata a kunnanshi yace "Latest Ango Mutanen US....." Jin hakan yasa Fatuu ta kalleshi da sauri yaci gaba da fad'in "Mutanen Waje ya gajiyan hidima da tafiya" Haisam d'in ya amsa mashi da Alhamdulillah cigaba da fira su kae har Abbas d'in na tambayar shi lokacin da zai ci gaba da aiki yace sai Next week Abbas yace "Allah ya kaimu" amsa mashi yay da Amin ya d'an yi shiru Abbas d'in yace "gani tare da Mom Zaraah mun dawo daga bank an bud'e Account d'in amman mun tsaya Eatery muna cin Abinci" yar dariya Abbas d'in yay jin amsar da Haisam d'in ya bashi yace to, daga haka ya cire wayar Fatuu dake kallonshi lokaci guda ta yanke a ranta koma yace a batan ko bai ce ba, ita dama tasan ya daina damuwa da ita ne kawae don yayi Amarya tana cikin zancen zucin taga Abbas ya mik'o mata wayarshi yace gata, bin shi da ido tay yace "Vedio call ne zaku yi da Ya Handsome d'in ki" yay Maganar yana yar dariya jiki mace ta mik'a hannu ta amshi wayar kafin ta kalli screen d'in har saida gabanta ya d'an fad'i da suka had'a ido dashi, yana zaune kan leather sofa ya d'an kishingid'a jikinshi sanye da armless data bayyanar da suffarshi abunka da zuciya tuni Fatuu taga ya canja mata yayi mata wani irin Fresh, bin shi da ido tay ta kasa ce mashi komae Abbas dae ya ci gaba da cin Abincin shi,

"Zaraah ina wuni" ta ji cool voice d'inshi ta fad'a, d'an tura baki tay ta d'auke idonta don tasan da biyu yace haka can ta sake kallonshi taga still kallonta yake cikin shaky voice tace "..ina wuni, an je lpy" shiru yay mata ta fara yamutsa fuska ta k'ara gaidashi ya k'ara yin shiru d'an tura baki tay kaman zata sa kuka tace "to kayi hakuri" wani d'an guntun murmushi yay dama da biyu yak'i amsawa just yana son ganin reaction d'in da face d'inta zatai displaying, bin shi da ido kawae tay can yasa hannu ya shafi beard d'insa yace "ina fushi dake" da sauri tace "to mi nayi maka?"

"An d'aura man Aure but u couldn't call and rejoice wit me" d'an motsa baki tay ta sadda kai tabbas bata kirashi ta taya shi murna ba kuma har Haulat saida tace mata ta kira shi amman ta k'iya, d'agowa tay a hankali still kallonta yake duk ta kame kanta cikin rawar murya tace "to don Allah ka yi hak'uri Ya Haisam dama inata so in kira" d'an ta6e baki yay baice komae ba ta tura mashi baki fuskarta a yamutse alamar ya tanka amman yak'i cewa komae sai kallonta yake kawae sai da ya ga dama sannan ya tambaye ta ya Exams tace mashi Alhamdulillah yay mata fatan Alkhairi ta amsa sai lokacin ta tambayeshi ya Aunty Fanan yace tana lafiya daga haka yace zasu yi magana ta d'aga mashi kai ta mik'a ma Abbas wayan yana amsa yace "wai ina Amaryar ne ta barka kai kadae zaune"? Ya bashi amsa da tana Bedroom cike da jan Magana Abbas yace "d'anyen aure amman kai kana Parlor ita tana Bedroom ko har kun fara fad'a ne" yar dariya Haisam d'in yay jin wata magana ta Abbas d'in sai kace wasu k'ananun yara wai har sun fara fad'a sigh yay yace mashi tana hutawa ne bata jin dad'i, d'an buda ido Abbas yay kafin yace "Subhanallahi mi ya same ta ne naga lafiya lou ku ka tafi" bin shi da ido yay kawae Abbas d'in ya k'ara tambayar shi abunda ya same ta yasan in ba fad'i mashi yay ba bazai k'yaleshi ba hakan yasa shi ce Masha is Nausea daga tafiyan da sukai amman duk da haka saida Abbas d'in yace "amman dama tana hakan naga ta saba hawa jirgi sosae fa" ya k'are Maganar yana guntse dariya Haisam d'in yace zasu yi magana da sauri Abbas yace "No yakamata mu gaisa ai muyi mata ya jiki ga ma Mom Zarah itama zata gaidata" ya d'aga ido ya kalli Fatuu yace "Auntyn ki ce bata lafiya zaki gaidata ko?" Tura mashi baki tay yay yar dariya ya maida idon kan screen d'in yace ma Haisam Zarah zata mata sannu ya kai mata laptop d'in ya amsa da Ok kafin ya yunk'ura ya mik'e, had'add'an Bedroom ne mara hayaniya sosae komae na cikinsa fari ne tass sai d'an ratsin baki kadan a wasu wuraren, tana kwance ta kudundune cikin lallausan farin bargo ya tunkareta saida ya aje laptop d'in ta kalli can gefe kafin ya fara tada Fanan d'in a hankali ta fara motsi kafin ta yaye bargon daga fuskarta suka had'a ido, yar harara ta wurga mashi tana kokarin rufe fuskar k'asa k'asa yace Abbas ne zasu mata sannu shi da Zarah wani kallo ta wurga mashi tun kafin tace wani abu ya riga ta fad'in it's connected yay mata nuni da laptop d'in da ido, shiru tay ta fasa yin Magana ganin bata da niyyar tashi yace mata "sit up" d'an yamutsa fuska tay dama fuskar duk a harmutse take tay jajir abunka da fara ga idanunta ma sun d'an kumbura da gani dai tasha kuka gashin kanta ma duk ya harmutse haka lips d'inta ma sun d'an kumbura suma, cikin disasshiyar murya tace "but u know I can't am feeling pain al over my body" kallonta kawae yake yana tuna gumurzon da suka sha da ita wanda gaba d'aya ita taja har yay losing control yasa ta jigata sosae sam baiji dad'in hakan ba don da bakinta
Showing 72001 words to 75000 words out of 113043 words