ne wanda ba kama ba alama ba don shi ya fad'a ba ma ba lalle ya yarda ba, cewa yay bari yaje ya k'ara yi mata godiya Tk yace ba sai yayi hakan ba ya tafi kawae su bama su cika son yawan godiya ba nan take ya tuna zancen SP acan baya hakan yasa ya hau mashin d'in Tk ya taimaka mashi ya d'aura komae har zai tafi ya dakata yace ma Tk don Allah in ba damuwa ya bashi lambar wayar Haisam yaji aurenshi ya kusa yana son in an dauran ya kira yay mashi fatan Alkhairi ya kasa tambayarshi ne d'azun yace Ok ya amshi yar wayarshi yay mashi saving lambar kafin ya mik'a mashi yanata shi mashi Albarka yaja mashin d'inshi ya tafi Farinciki fal cikin ranshi.(Allah ka had'a mu da Mutane irinsu Hajiyar Sanata ka bamu ikon sanya Farinciki a zukatan junanmu Amin)


Sanye cikin gym outfit ya fito daga cikin d'ayan d'akin hannunshi guda rataye da k'atuwar Sport Bag d'inshi yana fitowa daga cikin Corridor ya d'an bud'a idanu alamar mamaki idonshi akan bakin kopar shigowa, Fatuu ce a tsaye jikinta sanye da Uniform d'in islamiyya ya nufi wurin da murmushi don yaji dad'in ganinta hakan ya tabbatar mashi da ta warware itama d'an Murmushin take mashi yace islamiyya zata ta d'aga mashi kai ya nuna mata kujera taje ta zauna, mikewa yay ya aje jakar a gefe kafin ya nufi Fridge ta bi shi da kallo babbar robar lemu Fanta ya d'aukko ya dawo ya zauna kan hannun Sofa inda ya tashi ya mik'a mata ta kalleshi ya d'an d'age gira ya furta "u'r my guest now" tana murmushi ta amsa tace ta gode shiru ta d'an biyo baya ta sunkuyar da kanta tana wasa da hannun jakarta can ta d'ago taga ita yake kallo motsa baki ta fara a sanyaye tace "dama nazo in yi maka godiyar kaya tunda safe naso yi maka,Nagode sosae Allah ya saka maka da Alkhairi ya k'ara Arziki mai Amfani" d'an bud'a ido yay with a broad smile on his face da kaji yadda take Maganar cikin hankali zaka fahimci ta girma ba kaman da ba, cikin cool voice nashi yace "Ameen don kin cinye ma Amarya kud'in cin kayan dad'inta su kaza da kika ce ana ci" waro ido tay tana mashi wani kallo yasa dariya tana ganin hakan ta tura mashi baki sai kuma itama tayi yar dariyar, mik'ewa yay yace suje yayi dropping nata kar tay late tace to bayan ta saka lemun daya bata cikin jaka tabi bayan shi, lokacin da suka isa Parking space d'in duk a tunaninta Mota zasu hau amman sai taga ya fiddo bike bayan ya hau ya d'aura jakar a gabanshi yace mata ta hau amman sai tayi tsaye hakanan taji yanzu bata son hawan don tasan dole jikinsu ya hadu shi kanshi tasan ba so yake ba kawae don ya faranta mata ne, juyowa yay ya kalleta yace ta hau mana ta d'an yamutsa fuska tace ita tsoro take ji yace kada ta damu ba abunda zai faru ba gudu zai yi ba, ba yadda ta iya haka ta daddage ta hau tabi ta daddafe jikin mashin d'in yaja suka tafi, gaba d'aya a tsorace take don sai taga tayi sama sosae shi kanshi yaji a takure take hakan yasa yace ta rike shi da sauri ta kai hannu ta kama gefe da gefen rigarshi gadagam har saida ya d'anyi dariya don ya gama fahimtarta abunda bai kai ya kawo ba shike bata tsoro bata tsoron babban abu, a gefen gate d'in islamiyyar ya parker duk ba dalibai da alama duk an gama zuwa, kokarin sauka ta fara yi kwatsam ta tafi gaba d'aya zata kifa cikin zafin nama ya damkota ta dawo sama ta matuk'ar tsorata sai numfashi take fitarwa da sauri da sauri lips d'inta na d'an motsi haka idanunta ta rufe su gam ga dogayen eyelashes d'inta sai rawa suke sakamakon idonta dake kyerma still yay yana k'are mata kallo tunda yake da ita bai ta6a samun closeness da ita ba haka da har zai kalleta tsaf ba, ba komae yafi d'auke mashi hankali ba irin gashin idonta dake rawa sai kace irin d'iyar roba da ake saka ma batir, jin ta d'an samu natsuwa yasa ta fara bud'e idanun a hankali kafin ta ware su sosae har saida ta d'an tsorata da ganin fuskarshi kusa ganin ya k'ura mata ido yasa duk taji wani iri a hankali tace zata sauka don har lokacin yana ruke da damtsenta sigh yay kafin yace "am so sorry for dat" kai kawae ta d'aga mashi ya taimaka mata ta sauka ta nufi cikin Makarantar, yana kokarin tashin bike d'in ya tafi kawae sai ganinta yay ta lek'o karaf suka had'a ido tasa dariya ta juya da sauri ta koma shima dariyar yake a fili ya furta "U'r too much Zaraah" daga haka yaja ya tafi.

Washe gari Alhamis bayan ya aje su Makaranta tana kokarin fita ya tsaidata ya tambayeta yau ma sai yamma zasu koma tace eh, ganin ya d'an yi Jim yasa ta tambayi ko akwae wani abu yace da yana son zasu fita ne da rana,itama shirun tayi sai kuma tace to sai ta koma da an tashi ba sai ta tsaya lesson ba yace ba matsala tace eh ai dama past question papers ne ake fidda masu kuma duk ta iya yace Ok zai dawo lokacin tashin ya dauketa tace to, gaba d'aya sukuku take koda taje aji sam hankalinta bai a tare da ita sanin gobe ne Haisam d'in zai tafi ji take kaman ta bishi amman tasan tabbas hakan matsala zai k'ara zame mata gwara ta hak'ura kawae, ana tashi k'arfe biyu saura sai gashi ya zo d'aukartata Haulat ma tace binsu zatai ta tafi gida aka tafi da ita, bayan ya sauke Fatun tana shirin fita taji yace kada taci Abinci sosae yasan ita acici ce zasu ci in sun fita tayi yar dariya kawae ta fice shima murmushi yake ya nufi gida, tana shiga d'akin gwaggo ta nufa lokacin gwaggon na kwance tana bacci bata dad'e da ta kwanta ba bayan tayi sallar Azahar hakan yasa Fatun na shiga ta bud'e ido tace mata har sun dawo da wuri haka saida ta gaidata sannan ta sanar mata da zancen fitar da zasu yi tace to tay sauri taje ta shirya ta amsa da to ta fita, ko Abincin ma bata ci ba ta hau shiri ba tare da 6ata lokaci ba ta gama shiryawa cikin k'ananan kaya riga da skirt kayan roba ne hakan yasa suka kamata sosae shape d'inta ya fita sai ta d'aura After dress tay rolling veil d'in ta fiddo takalma masu tudu ta sa ba k'aramin kyau tay ba don ma kumatunta sun d'an fad'a, tana gamawa bada jimawa ba ta jiyo horn d'in shi saida ta lek'a don yima gwaggo sallama ta iske tay nisa a baccinta hakan yasa ta tafi kawae, zagayawa tay d'ayan side d'in Motar ta bud'e kopar ta shiga wani fitinannan kamshi mai tsuma zuciya ne ya bugi hancinta har saida ta d'an lumshe ido tana kokarin rufe kopar, juyawa tay suka had'a ido ta gaishe shi yay nodding kai tana shirin juya fuskarta ta kalli gaban Motar kaman daga sama taji ya furta "Kinyi kyau sosae" da sauri ta kalleshi with surprise ol over her face don bata tsammaci jin hakan ba saboda tunda suke da ita bai ta6a ce mata hakan ba ko a da saidae in ita ta tambayeshi tayi kyau in tayi gayu sannan yace eh ko in tasa kayan daya siya mata ta nuna mashi sai yace sun mata kyau, ganin ta k'ura mashi ido yasashi d'age mata gira yace "What?" da sauri ta girgiza mashi kai ta juyar da kanta yaja Motar suka tafi acikin ranta ta fara tunanin yadda yake mata abubuwa wanda bai saba yi mata ba can zuciyarta ta ayyana mata don ya sakata Farinciki ne kawae, ta juyar da fuskarta gefe tana kyakkyafta idanu don ta mayar da kwallan dake kokarin taruwa..........



_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wannan no 09013804524._

Domin karanta cikakken Littafin sai ku danna bulun Rubutun dake kasa ko kuma hoton dake kass πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

https://aihausanovels.com.ng/novel-document/a-sanadin-makwabtaka-book-2-complete-hausa-novel

πŸ‘†πŸ‘†πŸ‘†πŸ‘†πŸ‘†


*ASM Bk2015*
*πŸ’–A SANADIN MAKWABTAKAπŸ’–*
_*(Love and Destiny)*_



_*BY ZAINAB LALUHπŸ“²*_
~(Oumm Imam)~

Book 2

Bonus Page 15
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*





.........Wani babban Eatery mai kyau da tsari ya nufa dasu bayan ya parker Motar a wurin da aka tanada don haka a tare suka fito suka nufi ciki Masha Allah ya dae tsaru Fatuu sai d'an bin wurin take da kallo ta yadda baza'a ga k'auyancinta ba, wuri ya nuna mata suka zauna suna facing juna suna zama sai ga waitress tazo tana sanye da Uniform d'in wurin bak'in skirt sai riga milk tasa yar himar bak'a dama ma'akaitan wurin Mata da Maza ne, Haisam ta nufa cike da salo tace "Barka da zuwa Yalla6ai" ba tare da ya kalleta ba ya d'aga mata kai Fatuu ta zuba mata ido tana kallon ikon Allah don sai faman rausaye rausaye take, Menu ta mik'a mashi mai d'auke da lists d'in dishes dake garesu bai amsa ba yace ta kawo mashi Fried rice d'an d'aga gira tay jin yadda yake Magana tace "with Beef or chicken yalla6ai" chicken ya bata amsa a tak'aice sai kuma ta k'ara kanne murya tace "to yalla6ai itafa mi za'a kawo mata?" Shiru yay mata jin wata tambaya mara kan gado gata ba sai ta tambayeta ba Fatuu kam har saida tay kaman zatai murmushi cikin ranta take ayyana kyama yi ki gama, har saida ta k'ara tambayarshi sannan idonshi akan waya yay mata nuni da Fatun yace "ask her" d'an ta6e baki tay ta nufi Fatun suka had'a ido tana kokarin bata menu d'in itama tace ta kawo mata babban robar ice cream da shawarma tace Ok ta juya Haisam yay ma Fatun kallon k'asan ido ya furta "Wannan ne zai isheki?" Yar dariya kawae tay bata ce mashi komae ba, bada jimawa ba waitress d'in ta dawo d'auke da k'aton tray wurin Haisam ta fara zuwa ta aje mashi nashi kafin ta nufi fatuu, tana niyyar tafiya Haisam ya tsaidata ta kalleshi sai lokacin suka had'a ido dashi yace ta kawo mashi pepper chicken da soft drink sai ruwa cikin kashe murya ta tambayeshi kaman ya complete chicken ko half yace complete ta d'an juya ido ta furta Ok kafin ta tafi, har ta kawo mashi bai fara cin fried rice d'in ba bayan ta aje mashi tace aci lafiya ta juya Fatuu ta d'an ta6e baki tabita da ido, tana juyowa taga ya turo pepper chicken d'in gabanta ta kalli kazar sai kuma ta kalleshi taga yana sakin wani Murmushin gefe nan take ta gane mi hakan ke nufi dama tasan tunda tay Maganar kaza yace ko tana son ci ne tabbas sai ya siya mata, tura mashi baki tay yay mata alamar ta fara ci shima ya fara cin nashi a nutse, ita kuwa Waitress d'in wuri ta samu can gaba ta zauna ta fiddo wayarta tana lallatsawa can wata ma'aikaciyar ta shigo d'auke da tray ta kai ma wasu bayan ta aje masu ta juya da tray d'in anan ta hango d'ayar zaune ta nufi inda take tana zuwa ta dafa shoulder d'inta tace "Su Billy manya shine kika bar aiki kika zo nan kikai zaune ko" wani d'an iskan kallo tay mata tana d'an Murmushi tace "zaman dole nike zuciya ce taga abunda take so" bud'a ido tay jin abunda billyn tace sai kuma ta juya tana k'are ma wurin kallo nan take idanunta suka sauka kan su Fatuu,

"Kice bak'in Farar fata mukae,to ke burgeki sukae kenan shiyasa kikai zaune kina k'are masu kallo"? d'an juya ido Billy tayi tace "ya dae burgeni" da sauri d'ayar tace "yau naga ikon Allah daga ganin Mutum kuma kika sani ma wadda yazo da ita ko matarshi ce ko kuma budurwarshi" d'an ta6e baki Billy tai tace "I don't care ni dae yayi man ne baki ji dad'in voice d'inshi ba wllh, kuma ma ni ban tunanin wai ko matarshi ce ko budurwarshi nafi tunanin kanwarshi ce ma" d'ayar tace "kanwarshi kuma,haka kawae sai ya d'aukko kanwarshi ya zo da ita nan cin Abinci ko ba wani abu bane hakan ai nasan dae ba ita kadae ce kanwarshi ba",

"Ke baki san in kud'i sukae ma Mutum yawa ba komae yi yake, ba kamar su daga gani ba cikakkun hausawa bane nafi tunanin half caste ne kuma ai zai iya yuwuwa yafi ji da ita ne acikin k'annan nashi" ta6e baki d'ayar tayi tace "lallai aiki ya sameki to, ki tashi kici gaba da aiki ko inje in kai k'ararki" ta k'arasa Maganar tana kokarin tafiya billyn tay dariya tace "ai na gama da kowa ba abunda zanyi" gyad'a kai tay tayi gaba abunta ita kuma billyn taci gaba da lallatsa wayan tana satar kallon yadda Haisam yake cin Abincinshi a nutse bai ma san tana yi ba,

Fatuu na cikin shan ice cream idonta akan tv tana kallon maimaicin shirin dadin kowa da aka fara yi a tashar Arewa 24 hankalinta ya tafi har bata san sadda robar ice cream d'in ta kubce mata ba gaba d'aya ya zube akan after dress d'inta duk ta 6aci dashi da sauri ta mik'e tana d'an yarfa hannu idon Haisam a kanta suka had'a ido dashi ta d'an yamutsa fuska d'an ta6e baki yay tace mashi yanzu ya zatayi ya d'age gira yace "ni nasa ki sake shi" d'an tura baki tay kaman zatai kuka ya bita da ido yana d'an murmushi, duk abunda ke faruwa akan idon billy hakan yasa ta taso ta nufo su tana zuwa cikin kashe murya tace "Subhanallahi 6are maki yay ne?" Kai Fatuu ta d'aga mata tace bari ta taimaka mata ta ciro rigar Fatun tace to, ta kai hannu ta cire Billyn ta kar6a ta juya, duk sai kuma Fatun tajita wani iri da ba rigar don kayan ba k'aramin tighting nata sukae ba hakan yasa tay tunanin tabi bayan billyn in an wanke sai tasa, fita tay daga cikin seat d'in ta nufi hanyar data ga billyn tayi Haisam yabi bayanta da kallo, tunda suke bai ta6a kafeta da ido ya k'are mata kallo irin haka ba bare har ya fahimci yadda jikinta yake ya dae san ba ramamma bace kuma yana jin ana Magana kan structure d'inta kaman can baya lokacin da Najeeb yay Magana kan hakan, dressing d'in ba karamin fiddo mata da shape yay ba don har shatin undies nata ana gani kasantuwar kayan roba ne, a hankali ya d'an juya lokaci guda yay noticing gaba d'aya hankalin mutanen dake wurin ya koma kanta maida idon yay a kanta har takai tsakiyar wurin don kayan basu barinta sauri a hankali take tafiya d'an d'aga murya yay yace "ZARAAH" dakatawa tay lokacin da kiran ya sauka cikin kunnanta Slowly ta juyo ta kalleshi don tasan shine ya kirata da kai yay mata alamar tazo ta juyo ta nufo shi idanunshi a kanta har ta k'arasa kafin tace wani abu yace "Sit and wait for her zata kawo maki ne" d'aga mashi kai tay don dama da tana tafiyar ta lura da yadda ake kallonta alama yay mata taci kazar a shagwa6e tace ai tayi mata yawa yace taci wanda zata iya,
"To kai bazaka ci ba" ta tambayeshi, shiru ya d'anyi sai kuma taji yace taci in ta rage zaici bud'a ido tay tace "ba baka cin saura ba?" Yar harara ya wurga mata tasa dariya ta kai hannu ta fara ci, can saiga billy ta dawo maimakon ta nufi Fatuu sai ta nufi Haisam cikin salo tace "amm Yalla6ai na wanke rigan tana can na shanya under fan don ta bushe da wuri in zaku tafi sai ayi man Magana in d'aukko mata" Slowly ya d'ago da fararen idanunshi tar masu d'auke da bakar kwaya mai baki sosae ya d'aura a kanta har saida taji fad'uwar gaba fuska a sake ya furta mata "thanks" wani far tay da ido ta washe baki tace "u'r welcome" daga haka ya maida idon yana cigaba da cin Abincinshi tay tsaye tak'i tafiya tana kallon sumar kanshi dake ta kyalli tasha gyara duk abun nan idon Fatuu na kanta ta gama kasheta da mamaki kasa jurewa tay tace "kar ki sa ya kware fa" kaman daga sama billy taji Maganar hakan yasa ta juya da sauri ta kalli Fatuu dake kallonta fuskarta ba yabo ba fallasa cikin dabarbarcewa billyn tace "a....am ina jira ya gama ne in d'auke kayan kar nayi tafiya biyu ba wani abu ba" wani kallo Fatun tayi mata cike da rainin Wayo tace "ba zaki kawo rigan ba ai sai ki d'auka lokacin ko" da sauri tace hakane ta manta ne ta juya cike da jin kunya ta tafi, kallon k'asan ido yay mata ta tura mashi baki yay d'an murmushi kawae bai ce mata komae ba, bai cinye fried rice d'in ba Fatuu ta mik'o mashi pepper chicken d'in ya d'an ci kadan daga haka ya yagi tissue ya fara goge hannu da baki tana ganin haka itama ta yaga ta goge tana kokarin mik'ewa taje ta amso rigar yace ta zauna ya mik'e ya nufi cikin wurin don kunya tasa billy ta bar wurin a can daga ciki ya ganta yace ta d'aukko rigar ta amsa da Ok ya juya ya koma bada jimawa ba sai gata tana wani shan k'amshi ta mik'a ma Fatuu rigar da d'an murmushi tace mata ta gode ba tare data kalleta ba
Showing 51001 words to 54000 words out of 113043 words