jingina da bango tana nishi cikin jin jiki ta fara bashi labari tun farkon yadda akai ta fara sonshi dalilin Maganar da suka yi da Haulat har zuwa yanzu data je ta iske suna fira da Abbas, murus bakin Amadu ya mutu sai faman bin ta da ido yake sosae kuma yaji ta bashi tausayi don yasan wacece ita sam soyayya bata gabanta don wani lokacin shida kanshi yake ce mata in bata da saurayi taya zatai aure ta tafi ta basu wuri sai tace ai in tazama likita miji sai ta za6a,
"Na fahimci komae, kiyi hakuri kinji, naji dad'i da baki sanar dashi ba don ko kin gaya mashi ba abunda zai maki saidae ya baki hakuri tunda kinga saura kwanaki ma bikinshi kuma dama bai kamata ma kice mashi kina son shi ba duk yadda kike ganin kuna mutunci dashi sai wani abu ya ragu na daga mutuncin da yake kallonki dashi don mace da kunya aka santa balle ke da kike cikakkar bafullatana wad'anda aka sani da tantsar kunya, ba wani abu bane don mace tace tana son Namiji tunda ga misali nan akan Manzo (S.A.W) da Nana Khadija Allah ya kara mata yarda ta furta tana sonshi saidae ita a lokacin ta girmeshi kuma bazawara ce,shiyasa in budurwa ta furta tana son namiji sai ad'auketa mara kunya mara kamun kai duk da ba haramun bane"
"To Kawu Amadu ya zanyi da sonshi yana damuna baka ji yadda nike ji a kirjina ba, ba irin k'ok'arin da banyi in fitar da son nashi ko na huta amman kullum k'ara yawa yake wllh" ta k'arasa Maganar fuskarta sha6e sha6e da hawaye harda majina, Amadu dai sai kallonta yake abun gwanin ban Al'ajabi wai Fatuu ce so ya maida haka acikin ranshi yake fad'in nifa shiyasa ba ruwana da wata soyayya nafi gane ma in nemi kudi tunda naga sa Mutane hauka yake ga misali nan a gabana, a fili kuma sai ya mik'a mata hannu ta matso kusa dashi cikin sigar lallashi yace "na fahimci yadda kike ji amman ki daure ki cije ki fitar dashi zaki iya nasan ke ba raguwa bace kar ki bari sonshi yay galaba a kanki ya rusa maki mafarkinki na zamowa kwararriyar likita da muke burin yin Alfahari da ita bama mu kadae ba gaba d'aya k'asa zatai alfahari dake in kika dage, lokacin sai kiga Allah ya kawo maki wanda ma yafi shi" da sauri tay mashi wani kallo wanda ya fahimci kona miye yace "nasan Ya Haisam na dabanne samun irinshi zai matuk'ar wuya amman fa bawai baza'a iya ba shima ai cikin Mutane aka sameshi ko to tabbas akwae wasu irinshi wanda ma suka fishi komae, kyau, nasaba da sauransu ke dai kawae ki dage ki cimma burinki zaki ce nina fad'a maki zaki ga yadda maza da suka amsa sunansu zasu yi rububin samunki don kema d'in sarauniyace cikin mata Allah ya baki komae sai abunda ba'a rasa ba tunda mutum tara yake bai cika goma ba amman dae dole sai kinyi yak'i sosae da zuciyarki, sannan in kuma kika bari tay galaba akanki to kuwa zata kaiki ta baro ki ne, ki dage da Addu'a dare da rana nima yanzu tunda na sani zan tayaki da Addu'ar kar ma ki bari gwaggo taji wannan Maganar don ba lalle ta fahimce ki ba tana iya yi maki fad'a ma, kuma kar kiji haushin Haulat abunda ta fad'a maki nima kwanaki sai da nayi tunanin hakan har ina Addu'ar Allah ya tabbatar amman daga baya tun kafin in san da akwae wadda zai Aura na fahimci kawae kyautatawa ce, don haka mu bar ma Allah komae ki d'auka shi d'in ba rabonki bane don wata bata taba Auran mijin wata haka wani ma bai taba Auran matar wani kowa da wanda Allah ya kaddaro mashi matsayin abokin rayuwarshi in kuma shi d'in rabonki ne kina zaune ba tare da wata wahala ba zaki ga yazo ya aure ki har kita mamakin yadda akai hakan, kad'an daga cikin ikon Allah ne Abunda baka taba tunanin zai yuwu yasa ya yuwu, kiyi hak'uri kinji d'iyata kuma yar k'anwata" ya k'arasa Maganar had'i da jawota jikinshi ya rungumeta ta gefe tay lamo tana nazarin maganganunshi acikin ranta, yayin da shima a cikin ran nashi yake fad'in dole ya k'ara kiyayar so,
"Amman kawu Amadu inason in daina ganin Ya Handsome yanzu, don duk in na ganshi ciwon k'aruwa yake" yaji ta fad'a cikin sanyin murya,d'agota yay yana kallonta yace "Amman baki ganin zaiyi tunanin wani abun ace ya daina ganinki kwata kwata?"
"Eh nidae nafi son hakan kawae ai dama ya kusa tafiya ko" jinjina kai yay yace "shikenan daga yanzu zan rink'a taimaka maki har Allah yasa ki daina jin son nashi idan yazo d'aukarki da safe zan sanar dashi cewa Haulat tazo kun tafi nasan in akai haka sau biyu ko sau ukku zai yi tunanin ko kuna wani abunne a Makarantar yasa kike tafiya da wuri tunda yasan kun kusa fara jarabawa k'ilan ya daina zuwa, to amman bikin nashi fa bazaki ba?" da sauri ta d'aga mashi kai alamar eh, d'an Murmushi yay ya girgiza kai a ranshi yace rayuwa kenan wazai yi tunanin hakan zata kasance a tsakaninsu, komawa tay ta kwantar da kanta a kafad'arshi duk jinta take wani iri,shiru sukai na d'an wani lokacin kafin yace "nasan kina jin yunwa ko?" kai ta d'aga a sanyaye tace "amman ban iya cin komae bakina ba dad'i" yace "daurewa zaki fa karki illata kanki da yunwa su basu san ma kina yi ba kuma ba Abunda zasu fasa koda wani abu ya sameki, bari in kawo maki abu ki ci" ta d'ago daga kafad'ar tashi ya mik'e ya fita, bada jimawa sosae ba ya dawo dama saida ya kulle shagon ya shigo gidan har ya isketa a halin, k'aton biscuit da cup cake guda biyu ya d'aukko mata da lemu ya tasata gaba bayan yasa ta wanko bakinta saida taci sosae ta rage biscuit d'in bada yawa ba yace zaije yayo salla ta daure itama tayi tace to, saida ya gyara inda tay amai sannan ya tafi, ana idar da sallar ya dawo lokacin tana kwance akan sallayar yace taje tayi wanka zata ji dad'in jikinta ya rakata kar bakin toilet d'in bayan ta shiga ya shige d'akinshi, saida ya tabbatar ta gama shiryawa ya koma d'akin ya isketa akan gado tayi lamo ya shiga ya tambayeta akwae abunda take so tace mashi bacci take son yi amman yak'i zuwa, shiru ya d'anyi sai kuma yace mata yana zuwa ya fita, mashin d'inshi ya hau ya nufi bakin hanya can wani babban chemist yayi ma mai shagon bayanin kanwarshi ce ke cikin damuwa tana son yin bacci amman yaki zuwa in akwae Maganin da zata iya sha mara illa ya bashi yace mashi akwae ya d'aukko mashi,bayan ya dawo yadda ya barta haka ya isketa sai wurga ido take ya bata Maganin yace ta bari sai tayi sallar isha tasha tace mashi to tay mashi godiya yace ba komae shidae fatan shi ta cire damuwar a ranta tace in sha Allahu zata cire daga haka ya juya ya nufi Masallaci don yin sallar isha da aka fara itama ta mik'e ta fita tayo Alwala tazo ta kabbara sallar tana gamawa ta d'aukko maganin ta sha kafin ta haye gado, lokacin da Amadu ya k'ara dawowa wurinta har tayi bacci d'an Murmushi yay a fili ya furta "ciwon so ya kama manya,wato dae ashe ciwon nan da gaske ne, nifa na d'auka duk iskanci ne mutum yay shame shame wai shi ciwon so yake, to Allah ka k'ara kare mu da sharrin ciwon so Amin" daga haka ya kashe mata hasken d'akin ya tafi. Bada jimawa ba gwaggo ta dawo tana shigowa gidan d'akin Fatuu ta nufa bayan ta kunna globe ta hangota kudundune saman gado tana ta bacci a ranta ta ayyana yau da wuri akai bacci kenan ta juya bayan ta kashe hasken, tana fitowa tay kacibus da Amadu da ya shigo yana k'ara mata sannu da zuwa don yayi mata a waje,tace "Fatuu Lpy dae ko naga tayi bacci da wuri" da d'an Murmushi kan fuskarshi yace "Eh to da sauk'i tace man wai kanta na mata ciwo shine na bata Magani ta sha"
"Bata ma je islamiyya ba kenan" yace "a'a taje" jinjina mashi kai tay tana shirin nufar d'aki shima ya juya yaji ta tambayeshi Fatun taci Abinci kuwa yace mata eh taci daga haka ya fice itama taci Abinci
tayo wanka ta kwanta don a gajiye take.
Tun bayan da ya gama komae ya kwanta Maganar Abbas ke ta mashi kai kawo acikin ranshi, duk da bai gasgata ba amman kuma wani sashi na Zuciyarshi yana neman takura mashi da zancen, kwance yake jikinshi sanye da sleeping dress riga da wando farare masu laushi yana facing saman d'akin sai faman tunane tunane yake, ba Maganar data fi damunshi sai ta Abbas da yace ya sani yay breaking heart d'in yar Mutane, hannu ya kai ya shafi forehead d'inshi ya bar hannun ba tare da ya cire ba idanunshi a runtse ya fara tariyo rayuwarsu da Fatuu tun farko har zuwa yanzu,wani lokacin yay d'an Murmushi wani lokacinma yar dariya yake har hakoransa su bayyana a haka har ya gangaro zuwa girmanta gaba d'aya rayuwarta cike take da nishadi da wuya kaga tana k'unci, ko ta d'aure fuska na d'an lokaci ne zata washe kaga tana dariya, in bai manta ba zai iya cewa rabon da ya ga farinciki akan fuskarta tunda suka baro Ajiwa Dam ne, a hankali ya cire hannun dake dafe da goshinshi ya bud'e idanuwanshi, yunk'urawa yay ya tashi zaune ya jingina bayanshi da headboard ya kai hannu ya d'auki wayarshi dake kan side drawer, bayan ya bud'eta direct images dake a gallery d'in wayar ya shiga yay scrolling har zuwa inda pictures d'in da sukai a Ajiwa suke ya fara kallonsu da Murmushi akan fuskarshi, kai da kaganta a hotunan zaka fahimci tana cikin tsantsar farinciki ba kamar yanzu ba duk ta canja kamar ba ita ba, a hankali ya maida wayar inda ya d'aukko ya ajiye ya d'age kanshi sama yana jin wani iri a zuciyarshi lokaci guda ya ayyana in dae da gaske shine silar shigar Zaraah halin data ke yanzu bai ji dad'in hakan ba...........
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wannan no 09013n804524._
Domin karanta cikakken Littafin sai ku danna bulun Rubutun dake kasa ko kuma hoton dake kass ππππ
*πA SANADIN MAKWABTAKAπ*
_*(Love and Destiny)*_
_*BY ZAINAB LALUHπ²*_
~(Oumm Imam)~
Book 2
Bonus Page 10
_Destiny may be delayed but cannot be changed....._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
........Washe gari da Asuba Amadu da kanshi ya je ya tasheta tay salla yace ta tabbatar tayi Karatun Alqur'ani kuma tayi Addu'a sosae tace mashi to sannan ya wuce Masallaci shima, ba laifi taji dad'in jikinta hakan yasa ta fara yin shirin zuwa Makaranta tana gama sallar, lokacin data fita gwaggo na kitchen ta nufi can ta tsaya bakin kopa ta gaisheta don lokacin da take karatu taga gwaggon ta lek'a dakinta da fara'a ta nufota tana amsa gaisuwar tace "ya ciwon kan jiya dana dawo kina bacci Amadu yace man kina ciwon kai" d'an Murmushin yak'e tay tace mata ta samu sauk'i gwaggon tace "Oh ciwo dae ya taso ki gaba kwanakin nan daga wannan sai wannan Allah ya baki lpy mai d'orewa" sadda kanta tay ta amsa da Amin kafin ta d'ago tace mata zata tafi Makaranta da d'an mamaki gwaggon tace "Makaranta da wuri haka, ban tunanin bakwae fa ta k'arasa in ma tayi to yanzu ne" d'an sosa gefen kanta tay tana kallon gwaggon tace "ai zamu fara practical ne yau wanda zai fito mana a Jarabawa shiyasa nike son zuwa da wuri mu samu gaba yadda zamu ga yanda ake yi sosae" jinjina kai gwaggo tay cike da gamsuwa ta juya tana Fad'in bari to ta mik'o mata abun karin kumallo taci sai ta tafi,bayan ta amshi Breakfast d'in ta koma d'aki ta fara ci, ba wani da yawa taci ba ta maida kayan Kitchen lokacin gwaggon bata ciki ta bita d'aki tace mata zata tafi ta bata kud'i, dama koda Haisam ke kaisu tana bata isassun kudin tara da zata iya hawa ma Bus har tay break, saida ta lek'a d'akin kawu Amadu tace mashi ta tafi ya rakota har kopar gida yana k'ara tausarta akan ta d'age ta cire damuwa ta maida hankali kan karatunta, saida yaga tayi nisa ya koma cikin gidan, duk da bata jin k'arfin jikinta sosae haka tay ta sauri don kar Haisam ya isketa a kan hanya har ta k'araso lungun gidansu Haulat, lokacin da ta shiga d'akinsu bin ta da ido Haulat d'in tay ta kasa mata Magana saboda zullumin jin yadda sukae da Haisam jiya itama Fatun kallonta kawae take Haulat din tace mata ta zauna mana, bayan ta zauna gefen katifar itama ta zauna a kusa da ita can dae ta daure tace "kin fad'a mashin ne?" girgiza mata kai tay alamar a'a, wani sanyi haulat taji har saida tay d'an Murmushi kafin ta tambayeta ya akai bata fad'a mashi ba, farko shiru Fatun tay hakanan taji bata son fad'a mata hirar da ta iske suna yi hakanne yasa tace mata kawae ta d'auki shawararta ne shiyasa ta fasa Haulat d'in tace mata ta kyauta,
"Amman ya naga kin shiryo da wuri ko Ya Haisam dinne ya kawo ki?" girgiza mata kai tay tace" bashi ya kawo ni ba ni na taho,ban son ina ganinshi" cikin karyayyar murya tay Maganar idonta har sun ciko da kwalla Haulat ta dafata tace "na fahimta Allah yasa hakan yasa ki samu sassaucin abunda kike ji" a hankali ta amsa mata da Amin, tambayarta tay ko ta kawo mata abun kalaci tace mata taci a gida haulat d'in ta tashi ta fara shiryawa saida lokacin da suka saba tafiya yayi sannan suka tafi. Misalin k'arfe 7:30 Haisam ya parker a kopar gidan yay horn kamar yadda ya saba yi in ba kowa a waje, saida yayi sau wurin ukku sannan Amadu ya fito ya nufi Motar Haisam d'in ya sauke glass da Murmushi Amadu ya gaidashi ya amsa tun kafin ya tambayi Fatun Amadun yace mashi sun tafi tun d'azu, shiru Haisam d'in ya d'an yi sai kuma yace mashi Ok, Amadu yay mashi sai ya dawo ya amsa daga haka glass d'in ya d'aga sama ya rufe yaja Motar Amadu yabi bayan Motar da ido kafin ya d'an girgiza kai ya shige gida,
Koda suka je Makarantar Haulat na lura da ita sam bata wani saki jiki ba har gara ma lokacin da bata kaiga ganin Iv d'in ba ta d'an fara saki amman yanzu an koma yar gidan jiya, saidae tay shiru ko ta d'aga ma Mutum kai in yayi mata magana sai ta kama take bud'e baki tay Magana, ita kanta halin da take ciki na matuk'ar damunta ba kuma kamar hukuncin da ta yanke na daina ganin Haisam duk sai take jin wani irin kad'aici gashi zuciyarta sai tay ta ayyana mata fuskarshi bata da aiki sai tunane tunane,Haulat dae bata gajiya da k'arfafa mata guiwa, A ranar da daddare bayan tayi sallar isha ta fita waje wurin kawu Amadu yana ganinta yace "Juliet ya akai" yay Maganar yana yar dariya ita kuma ta d'an tura mashi baki ganin tay mashi tsaye yasa yace mata ya akai ne tace "dama bacci nike son yi na kasa shine nazo ka bani wannan Maganin na jiya" bud'a mata ido yay yace "ke kina son zama yar k'waya ne?" a sanyaye tace "a'a ba magani bane?"
"Eh magani ne amman in kika saba bazaki iya bacci ba sai da shi don haka ki je ki kwanta kawae baccin zai zo in sha Allah kiyi Addu'a" tana shirin k'ara yin Magana ta jiyo k'arar bike d'in Haisam ya dawo daga Gym aikuwa da sauri ta juya gudu gudu ta shige gida ta la6e cikin zaure tana lek'enshi har yazo ya wuce, sauke ajiyar zuciya tay ta d'an cije baki kafin ta nufi cikin gidan tana shiga d'aki ta haye gado ta kwanta tana ta tuna rayuwarsu da Haisam kwalla na gangaro mata duk ranta bai mata dad'i sai can dare ya nisa bacci yay awon gaba da ita. Washe gari ma sai ga Haisam yazo d'aukarta lokacin ta tafi Amadu ne ya lek'a ya k'ara ce mashi ai basu dad'e da tafiya ba ya amsa da Owk ya tafi, abu kaman wasa Amadu na cewa k'ilan in yazo sau biyu ko ukku ya daina zuwa sai gashi har ranar Juma'a saida yazo a wannan lokacin kunya ta gama rufe kawu Amadu hakanan yake daurewa yana ce mashi ta tafi shi kanshi ba don yana son hakan ba don sai yaga kaman ana wulakanta Haisam dinne wanda yafi karfin ai mashi haka,
Zaune take a aji duk ranta a jagule yake kukan zuci kawae take wanda akace yafi na fili rad'ad'i sanin yau saura sati d'aya Haisam ya tafi kaman yadda taji a bakin gwaggo don sam bata san Fatun ma bata zuwa gidan Hajiya ba a tunaninta in bata nan tana zuwa wani lokacin kuma tana fita da sunan zata can d'in gudun kar gwaggo ta gano bata zuwan amman data fita sai tay tafiyarta gidansu Haulat haka in Fanan ta kira waya tana amsa su gaisa don sosae take kiran layin gwaggo ta gaishe da ita wani lokacin ma in Fatun na d'aki data ji suna waya sai tay baccin k'arya, Haulat har ta gaji da bata
Showing 33001 words to 36000 words out of 113043 words

https://aihausanovels.com.ng/novel-document/a-sanadin-makwabtaka-book-2-complete-hausa-novel
πππππ
*ASM Bk2010*

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12 Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38