kallon hajiya Fatuu tay data kafeta da ido kaman zatayi murmushi ta sunkuyar da kanta ta d'aga ma Fanan d'in, yar k'ara tasa tace to gashi nan Sis Zarah tace nata ne, ruk'e ha6a Hajiya tayi tace "Wato dae Fateema an rabamu ko, ada Ya Handsome ya shiga tsakaninmu yanzu kuma ga wannan acicin ai shikenan zasu barni dake ne" yammm taji jikinta yayi jin Maganar Hajiya ta zasu barta da ita dama k'arfin hali kawae take zama a gurin, d'aukar kwanon Fanan tayi ta bud'e kamshin wainar ya daki hancinta har saida ta d'an lumshe ido sai dai bata gane minene ba hakan yasa ta juya ta tambayi Fatuu sunanta tace mata wainar fulawa,
"Wasu kuma suna ce mata kalalla6a wasu suce waina gira ko alallagira wasu ma yar cana suke cewa" suka ji Hajiya ta fad'a, bud'a ido Fanan tayi jin wasu sunaye ta fara k'okarin maimaitawa tace "K...kal...kallalla6iya..." tunkan ta rufe baki suka sa dariya gaba d'ayansu ita dae Fatuu d'an Murmushi kawai tay Hajiya tace "Da alama dai za'a maimaita na taliyan hausa" da sauri Fatuu ta juya ta kalli Haisam suka had'a ido ya saki Murmushin gefe tunowa da ranar data kawo mashi taliyan hausa mai daddawa sanin Murmushin kona miye yasa itama tayi kafin ta juyar da kan,
"Idan baki ci ki mik'o man nan k'amshinta duk ya cika man hanci" hajiya ta Fad'a idonta kan Fanan, da sauri ta girgiza kai tace ai ko bata ci sai taci abunda Sis Zarah ta kawo mata, d'aukar kwanon tay ta nufi dining Hajiya tace bata ci anan tace zata d'aukko fork ne,
"Shine sai kin tafi da ita wato kar ki barma kura ko" d'an d'aga murya tay tace eh cinye mata abunta zatayi, ta sake cewa to wayace mata da fork ake ci hannu ake sawa bazata ji dad'in cinta da fork ba jin hakan yasa ta wuce dining area ta wanko hannunta ta dawo, daga inda Hajiya take ta fara nuna mata yadda zata ci ta nade d'aya da kayan cin acikinta ta dangwala yajin kamar yadda hajiya tace ta tura baki ta fara taunawa, d'an bud'e ido tay lokacin da ta cinye ta yarfa yatsa tace "it's so yummy" dariya hajiya tayi ta juya ta kai sauran ta hannunta bakin Haisam ya kalli abunda take bashin kaman bazai bud'e bakin ba sai kuma ya bud'e ta saka mashi ya gatsa ta janye sauran ta tura baki hajiya dake kallonsu tace "Fateema dai duk ta koya maku kwad'ayi, shima kwanaki a waya naga wainar fulawar ta burgeni nasa Saude tayi mana ita da rana ina tunanin shi ayi mashi wani abun yaci sai ce man yayi wai zai cita nayi mamaki don nasan ba lalle in ya ta6a ganinta ba balle ma ya iya cin dana tambayeshi dama yasanta ne yake ce man ai da Salla da ban dawo bane ta kawo mashi ita nan ya fara cinta" dariya Fanan keyi tana taunar wainar ita kuwa fatuu a hankali ta d'ago ta kalli Haisam da d'an Murmushi suka sake had'a idon gaba d'ayansu Maganar Hajiya ta tuno masu da can baya sallar farko data fara yi dashi lokacin daya dawo ta rink'a kawo mashi abinci har ya rink'a yi mata lesson lokacin ya koyi cin wainar don farko data kawo mashi cewa yay bai iya cinshi ba saida yaga kaman bata ji dadi ba har zata tafi yace ta kawo yaci tace mashi ita ba fushi tayi ba tunda bai iya ci ba bari taje zata kawo mashi wani Abincin amman yace karta damu zai ci don ta gaya mashi musamman don shi ta soya dama kuma saida gwaggo tace mata ba lalle fa in ya iya cin ta ba wannan dalilin ne yasa ya daure yaci amman kuma sai yaji dadinta musamman data kasance ba abinci ce mai nauyi ba tun daga nan duk in ta kawo mashi yana ci, janye idonta tayi ta maida kan tv kaman tana kallo saidae a can k'asan zuciyarta wani iri take ji tunawa da rayuwarsu ta baya rayuwa mai cike da nishad'i daidai da rana d'aya bata ta6a tunanin komae zai sauya haka ba tsakaninta dashi,
"To sarakan son kai sai ci kuke kun barni da shak'ar kamshi da alama cinyewa zakuyi ma ba tare da kun bani ba ko" Hajiya tayi Maganar idonta akan su Fanan dake dariyar Maganar Hajiyar tana niyyar ba Haisam wadda ta gutsira ya girgiza mata kai yace ta kai mata cike da tsokana ta mak'e kafad'a alamar bazata bata ba Fatuu data juyo ta kalleta tunda hajiya tayi masu magana ganin abunda tayi yasa ta mik'e idonta akan Hajiyar tace bari taje tayo mata wata, da sauri Fanan ta kamo hannunta tace wasa take zata bata ba sai ta k'ara wahalar da kanta ba ta mik'e ta tunkari Hajiyar ta aje kwanon gefenta itama ta zauna tace to gashi nan su ci yar harararta tayi tace ita da bata da masoyi ko to itama a bakin zata bata tasa dariya tace wannan ai ba matsala bane ta d'aukko ta fara bata itama tana cigaba da ci, daga inda take bayan ta cinye wainar bakinta tace ma Haisam "Babe we need to go 4 an outing sis Zarah zata k'ara jin dad'in jikinta" tana rufe baki Hajiya tace "ba dai Ajiwa Dam d'in zaku je ba?" yadda tayi Maganar har saida taba Fanan dariya ta girgiza mata kai alamar a'a, tace "ato ai naji kina ce mashi ne kina son zuwa wurin da kika ga hotunansu nayi zaton can kike nufin kuje ince to kuje ku kad'ai banda ita a samu ma ta idasa dawowa daidai" sunkuyar da kai Fatuu tayi cikin ranta ta ayyana koda ma ance za'a can d'in ba zuwa zatay ba don yanzu Ajiwa Dam na d'aya daga cikin Wuraren da bata fatan k'ara zuwa fit ya fice mata arai ya kuma shiga cikin tarihin rayuwarta ko hotunan datayi a wurin bata son gani, tana son ta tafi gida amman tasan sai gwaggo tayi Maganar dawowarta da wuri gashi bata son taga tana sa gwaggon damuwa, kiran sallar Azahar ta tadasu gaba d'aya suka tafi yin salla bayan sun gama ne kuma Saude ta sanar ta shirya Table lokacin da Haisam ya dawo gaba d'aya suka nufi Dining din harda Fatuu da suka matsa mawa duk da tace masu ta koshi taci waina amman Fanan tace taci ko kadanne ai suma sunci wainar ba yadda ta iya, ita ta fara tashi tace ta koshi don ba k'aramin karfin halin zama take tana kallon yadda suke ciyar da junansu ba Fanan tace ta jirata a parlor inta gama zata gyara mata gashinta ta amsa mata da to kawae, bayan sun gaman visitor room ta kai Fatun taje dakin Hajiya ta daukko wani dan babban kit ta dawo lokacin data bud'e ba komai ne aciki ba sai uban kayan gyaran gashi da mayuka, nuna ma Fatuu dake zaune gefen gado stool din gaban mirror tayi tace tazo ta zauna, bayan ta zauna ta fiddo stretcher ta fara mata stretching sosae take yaba kyaun gashin Fatuu da yake cike gashi baki wuluk duk da na Fanan d'in yafi shi tsawo saidae baida cika, sosae ta gyara mata shi sai shek'i yake ta d'aukko wayarta ta fara masu hotuna ta rink'a masu styles da gashin kansu iri iri, dole Fatuu ta saki ta rink'a yin yadda duk tace mata tayi sosae hotunan su kai kyau ba kamar daya kasance ita gashinta brown na Fatuu bak'i bayan sun gama yin hotunan ta maida komae cikin kit ta maidashi Bedroom din Hajiya ta iske hajiyar kwance tana bacci hakan yasa data dawo tace ma Fatuu su kwanta suma su huta ba kowa a Parlor tace mata to kawae, zuciya nason mai kyautata mata duk da halin da Fatuu take ciki sam ta kasa jin tsanar Fanan din hakanne ma yasa wani lokacin bata iya yi mata gardama, har aka kira la'asar suna bacci ringing d'in wayar Fanan ne ya tasheta ta duba screen din taga Haisam ne ke kira bayan ta dauka ya tambayeta tana ina ne ya shigo har Bedroom bai ganta ba ta fadi mashi suna bacci ne a visitor room yace su tashi suyi salla ta shirya tace to don ta gane shirin zuwa gym yake nufi, tashi tay ta koma Bedroom d'in Hajiya within few minutes tayo wanka ta fito,shiryawa tayi cikin workout outfit riga da wandonta Ash colour rigar tight long sleeve ce irin mai dogon hannu ta kamata sannan iyakarta tsakiyar cikinta sai wandon shima skin tight ne dogone ya kai har kasan rigar sun matukar fiddo mata da dirinta kuma tayi kyau sosae hijjabai guda biyu ta d'auka ta koma d'akin da Fatuu take har lokacin bacci take dama tana fama da karancin baccin yan kwanakin nan, tashinta tay ta bud'e ido tana kallonta da Murmushi tace mata ta tashi lokacin salla yayi ta d'aga mata kai kawae ta saukko, lokacin data fito Fanan din ta kabbara salla don tayi Alwala a toilet hijab din data gani ajiye ta d'auka tasa itama ta kabbara sallar, bayan ta gama saida ta jira Fatuu ta gama sannan ta sanar da ita zasu tafi Gym ne ko zata k'ara kwanciya tace mata a'a gida zata tafi hakan yasa suka fito tare Fanan ta shiga d'akin Hajiya ta maida hijjaban tasa takalma sneakers farare ta d'aura farar jacket kanta kuma ta rufe shi da veil Ash kalan kayan tayi kyau har ta gaji, sallama tayi ma Hajiya tace adawo lafiya ta fito lokacin Fatuu na zaune kan kujera a Parlor tana ganin ta fito ta mik'e ta nufeta suka fita tare suna fitowa cikin harabar gidan Haisam ma ya fito cikin shirin gym hannunshi guda rataye da katuwar jakarshi abunda Fatuu ke ji duk ta ganshi shi taji gashi ta kasa barin kallonshi har ya k'araso inda suke Fuskarshi a sake yana kallonta Fanan ta kai hannu ta curo jakar ta rataya shi kuma ya nufi Parking Space don ya fiddo bike din lokacin Fatuu tace ma Fanan ta tafi gida ta dafa Shoulder d'inta tace in ta dawo zata zo kai kawae ta d'aga mata ta nufi hanyar gate, tana karya kwana bayan ta fito gate d'in gidan bike d'insu ya taho taja gefe don su wuce, dukkansu sun sa helmet a kawunansu Fanan na goye da katuwar jakar suna zuwa inda take Fanan ta d'ago mata hannu suka wuce fuuu,tsaye tayi a wurin tana bin su da kallo har suka yi nisa kafin suka 6ace ma ganinta, kasa d'aga kafafunta tay taci gaba da tafiya, da k'yar ta matsa ta jingina da fence a cikin zuciyarta ta ke ayyana Ya Handsome baisonta bai ta6a sonta ba yanzu ne ta k'ara gaskata hakan don ta gano dalilin dayasa bai ta6a goyata a bike d'inshi ba tunda suke, duk in ta nuna tana son su hau shi in zasu fita sai yace Mota zasu hau ko kuma in yaga kaman bata ji dad'i ba yace ba yanzu ba ashe duk don kar jikinsu ya had'u ne sai yanzu ta fahimci hakan ganin da suka wuce gaba d'aya Fanan na kwance a bayanshi ta sakala hannuwanta a cikinshi, wani 6angare ne na zuciyarta yace kawae ki cireshi a ranki tunda baison ki yayin da wata zuciyar kuma tace yanzu shikenan sai ki hakura dashi duk irin son da kike mashi ina kike tunanin zaki samu wani kamarshi, wasu kwalla ne masu zafi suka fara gangaro mata ta shiga yin kuka ba tare da sauti ba don ta rufe bakinta da tafin hannunta guda,can bayan wani lokaci tasa hannu ta fara gogewa kafin da k'yar ta d'aga k'afafunta da suka yi mata wani irin nauyi ta fara tafiya, tana karasowa kopar gidansu har zatai kwana sai kuma ta tsaya kaman mai yin tunani can ta mik'i hanya taci gaba da tafiya..............,
Domin karanta cikakken Littafin sai ku danna bulun Rubutun dake kasa ko kuma hoton dake kass ππππ
_Destiny may be delayed but cannot be changed......_
*πA SANADIN MAKWABTAKAπ*
_*(Love and Destiny)*_
_*BY ZAINAB LALUHπ²*_
~(Oumm Imam)~
Book 2
Bonus Page 5
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
........gidansu Haulat ta nufa tana zuwa bakin lungun ta hangota ta taho jikinta sanye da Uniform d'in islamiyya hakan yasa taja ta tsaya suna kallon juna har ta k'araso gabanta tana kallonta ganin yanayin fuskar Fatun yasa da yar damuwa tace "kawata ya jikin har yanzu?" gyad'a mata kai tay idanunta sun cicciko da kwalla tace "kiyi hakuri don Allah in sha Allahu komae zai wuce ki dawo kaman da wllh Allah ne shaidata bana jin dad'in halin da kike ciki Fatuu, dake nike kwana nike tashi kullum Addu'ata Allah ubangiji ya yaye maki abunda yake damunki" ta k'arasa itama idanunta sun ciko, shiru Fatun tay kaman bazata ce komae ba sai kuma Haulat taji tace "Yanzu Haulat ki fad'i man ya zanyi in daina jin son Ya Handsome" a sanyaye tay Maganar, ajiyar zuciya Haulat ta sauke kafin ta dafa shoulder d'inta tace "shi so matsalarshi kaman ciwo ne farat d'aya yake shiga amman sauki sai a hankali ba kaman yadda yay maki mugun kamu,amman ba ina nufin bazai barki ba saidae a halin da kike ciki yanzu son Ya Haisam bazai iya barinki farat d'aya ba ba kaman da yake kina ganinshi, dole sai kinyi yak'i da zuciyarki sosae duk yadda zata rink'a azalzalarki kan sonshi ki daure ki cije kar ki biye mata in akwae abunda Ya Haisam d'in ya ta6a maki wanda ya 6ata maki rai ki rinka tunano shi duk in ta ayyana maki wani abu game da sonshi........" katseta Fatun tayi tace "ni bai ta6a man komae ba na 6acin rai, kawae dai abu d'aya ne banji dadinshi ba shine yadda ya 6oye man tsakaninshi da Aunty Fanan ni nayi zaton soyayyar yan'uwantaka ce kawae tsakaninsu kinga dana sani koda ke baki sani ba lokacin da mukayi Maganar yana sona da zan fad'i maki yana da wadda yake so" shiru Haulat tayi yayin da cikin zuciyarta take ayyana cewa koda ma ya ta6a yi maki abunda ya 6ata maki rai a halin da kike ciki bazaki ji haushin shi ba, a fili tace "to ki daure kiyi kaman yadda nace maki da farko sannan ki dage da Addu'a don ba abunda yafi karfinta in sha Allahu zaki ga komae ya wuce kaman ba ayi ba" jinjina mata kai kawae Fatun tayi, da d'an Murmushi Haulat tace "kinyi kyau sosae" godiya tayi mata tana son tayi mata Murmushin itama amman ta kasa ta kama hannunta tace suje kada ta makara, akan hanyarsu ne Haulat ke tambayarta sai yaushe zata dawo islamiyyar tace mata ta kusa, a daidai kopar gidansu suka rabu Fatun ta wuce ita kuma Haulat tay tsaye har saida taga shigewarta sannan ta girgiza kai,ba k'aramin tausayi take bata ba duk tayi sanyi sai kace ba Fatuu ba daka kalli fuskarta zaka fahimci she's in serious grief, juyawa tay saida ta gaishe da kawu Amadu kafin ta wuce. Lokacin data shiga gidan bata ga gwaggo ba har Parlor da d'akinta ta duba bata ganta ba hakan yasa ta wuce d'akinta ta haye gado ta fad'a duniyar tunani,tana son ta daina jin son Ya Handsome saidae son nashi ya rinjayi hakan acikin zuciyarta, dama don ta tabbatar ma kanta da baisonta ne yasa take jin gara ta daina son nashi ta huta amman a yanzu bata da burin daya wuce taga ta aureshi wani irin son shi zuciyarta ke azabta mata dashi, a hankali ta kai hannu ta goge kwallan dake zubo mata, mik'ewa tay ta zauna tsakiyan gadon ta d'aga hannu idonta na kallon sama a fili tace "Ya Ubangijina Allah ka yaye man damuwata ka cire man abunda nake ji acikin zuciyata na son Ya Handsome tunda bai sona...." fashewa tay da kuka ta shafa kafin ta koma ta kwanta tana sheshsheka a haka bacci ya kwasheta, sai gab da sallar Magrib gwaggo ta shigo gidan dama makwabta ta shiga dubiya ganin takalman Fatuu a bakin kopa yasa ta gane ta dawo ta nufi d'akin ta d'age labule, ganinta kwance tana bacci yasa ta shiga ta tasheta tayi salla,bayan Sallar isha saiga Fanan lokacin sun dawo daga Gym yau ma Abubuwan ci ta kawo mata kamar rannan ta sanar da ita gobe around 12 ta shirya zasu fita gari kaman tace bata zuwa amman kuma a gaban gwaggo ne hakan yasa ta amsa da to kawae, tare da gwaggo suka ci abubuwan da ta kawo masu ba don tana jin dad'insu ba sai don gwaggon ta matsa mata, bayan sun gama ta bata wanda aka d'ibar ma Amadu ta fita ta kai mashi bayan ta dawo saida ta watsa ruwa ta canja kaya zuwa na bacci sannan ta kwanta sai faman sak'e sak'e take aranta kaman ko yaushe don sam bata jin bacci saboda tayi na yamma koda gwaggo ta shigo yi mata Addu'a isketa tay idonta biyu tace to in ta tashi yin baccin ta tabbatar tayi ta amsa mata da toh.
Washe gari tun bayan data yi breakfast ta tattara kayan wanke wanke tayi tana niyyar yin shara gwaggo tace ta barshi zatayi hakan yasa ta koma tay kwanciyarta, wuraren karfe sha d'aya da wasu mintuna gwaggo ta lek'a dakinta ganinta kwance yasa tace mata ba zasu fita bane tay kwance ta daure ta tashi ta shirya ta amsa mata da to, bayan ta tafi ta yunkura ta mik'e zaune ta zuro kafafunta k'asa har cikin ranta bata son fitan don tasan dole taga Ya Handsome kuma duk inta ganshi ita kad'ai tasan mi take ji, wani dan Murmushin takaici tay wai yau itace ke gudun ganin Ya Handsome, da k'yar ta mik'e ta nufi wardrobe d'inta ta cire kayan jikinta d'aura towel tay ta wuce Toilet, bayan ta fito mai kawae ta shafa tasa undies ta zumbula doguwar riga ta koma
Showing 15001 words to 18000 words out of 113043 words

https://aihausanovels.com.ng/novel-document/a-sanadin-makwabtaka-book-2-complete-hausa-novel
πππππ
*ASM Bk2005*

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6 Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38