ji da alama kowa yayi bacci don kusan k'arfe 1:30 na dare, har bakin part d'in da aka saukesu ya kaita ya manna mata kiss a goshi had'i da fad'in "Good Night" ta d'an yi mashi murmushi kafin ta juya ta shige shima ya nufi hayar fita, tana shiga parlon ta iske khairat kwance kan doguwar Sofa tana waya koda ta ganta ta shigo da sauri ta tashi zaune Fanan d'in ta nufeta ta fad'a gefenta ta zauna ta d'age kai sama ganin haka yasa khairat ce ma wanda suke wayan "Honey excuse me I will call back" daga haka tay cutting call d'in idonta kan Fanan tace "bestie where u from at dis time nata nemanki ban ganki ba I even call ur phone yana ringing baki d'aga ba" daga yadda take ta juyo da kanta tana kallonta ba tare data ce mata komae ba itama khairat d'in bin ta take tayi da kallo can idonta ya sauka a kan Fanan d'in da rabinshi ke bud'e k'ura ma gashinta ido tay sai kuma ta kai hannu ta ta6a da sauri ta sauke hannun ido waje ta ke kallon Fanan da itama kallon nata take far far da ido khairat tay tace "what am i seeing kar dae kice man he has taken ur pride tun baku bar Kasar ba?" Sigh Fanan tay ta furta "dat's what i wished.." gwalo ido khairat tay ta maimaita abunda Fanan d'in tace cikin d'aurewar kai ta nuna kanta tace "but d wet hair..." tura baki Fanan tay kawae, cikin k'aguwa Khairat tace "pls tell me d truth abunda nike tunani ya faru ko?" D'an guntun tsoki Fanan tay kafin tace "uwar gulma to ba abunda ya faru khairat it nearly happened but he said it's improper to do it in a hotel room yanzu kin ji ko sai ki kyale ni pls" bud'a baki khairat tay sai kuma ta kyalkyace da dariya can tace "ai da kun fad'a man na baku keys d'in guest house d'in Dad sai kuyi shagalin ku a can ni ina nan ina aikin nemanki ashe kina can kina enjoying" harara Fanan ta galla mata ba tare data ce mata komae ba khairat d'in ta sake cewa "U know what gara da ba abunda ya faru asirinku a rufe don yadda mijin nan naki yake k'akk'arfa I am very sure if to say it has happened definitely u would come back with bow legs" tana rufe baki Fanan d'in ta kai hannu ta fara bugunta sosae ta mik'e da sauri tana fad'in bafa ita ta kashe zomon ba.

Yana fita ya shiga Motan ya kai ta Parking space bayan ya parker ya d'auki d'ayar robar ice cream d'in da bata sha ba ya bud'e still akwae sanyi don lokacin da ya siyo shi a kankare yake a nutse ya fara sha don yunwa yake ji tun a Hotel d'in ma yaso su ci Abinci amman ganin dare yayi sosae yasa bai sa su tsayan ba, saida ya shanye shi duka sannan ya bud'e Motar ya fita ya nufi part d'inshi ta baya, yana shiga bedroom d'in ya had'a ido da Abbas dake kishingide jikinshi sanye da sleeping dress da alama bai dad'e daya kwanta bama yana ganin shi ya fara sakin wani shu'umin murmushi Haisam ya nufi edge d'in gadon ya zauna fuskarshi a sake Abbas yace "I thought can zaku kwana ai" d'age mashi gira yay ba tare daya ce komae ba, dagowa Abbas yay ya kai hannu gefen kafadar rigarshi inda jan bakin Fanan ya d'an goga ya bud'a ido yace "zargi na ya tabbata dae hope baka dae illata masu yarinya ba a Hotel H,zakee" hannu ya kai ya buge mashi hannu ya mik'e yana fad'in "We're Adult so we know what's right" daga haka ya nufi Toilet Abbas nata mashi dariyar shak'iyanci. Washe gari lahadi Abbas yaso su tafi to amman yana son ganin tashin su Haisam d'in hakan yasa yace ma su gwaggo sai washe gari in suka wace suma sai su d'au hanya tace Allah ya kaimu, Ranar Litinin Misalin k'arfe goma saura na safe su Haisam sun gama shirinsu tsab dam ba wani shiri bane sosae don daga su sai kayansu ita dama Fanan acan aka siya mata komae duk da gidan da zasu zauna Companyn da Haisam zaiyi aiki ne suka basu akwae komae a ciki amman duk da haka saida aka k'ara siya mata wasu abubuwan, Misalin k'arfe goma duk aka fito don rakasu Airport harda kakar Fanan da wasu daga cikin yan'uwansu da suka zo za'a tafi Farha ma taso ta bisu amman Hajiya Maryam tace ba yanzu ba sai in zata je sai su tafi tare gaba d'aya yan gidan dasu Abbas da gwaggo,kawu Amadu harda Saleem da Najeeb shima daga nan zai koma Lagos acan jirginsu zai tashi gobe dama bikin kawae ya kawo shi, Amarya Fanan na sanye da hadaddar jallabiya dark green ta fito mata da gasken ta sosae yayinda Haisam ke sanye da fararen suit bayan sun isa Airport d'in suka tsaya suna sake yin bankwana Farha sai kuka take yar uwa zata tafi suka rungume juna itama Fanan d'in hawaye take bayan ta saketa ta nufi Mommynta ta rungumeta sai lokacin tasa kuka sosae itama Hajiya Maryam d'in k'arfin Hali kawae take amman kad'an ya rage tasa kukan tana rungume da ita take k'ara jaddada mata fad'an da tayi mata game da rayuwar gidan Aure da biyayyar miji,haka dae sukae bankwana da kowa Senator ma ya k'ara yi ma Haisam nasiha kan Amanar Fanan da aka damka mashi ya tabbatar mashi da zai ruk'e Amanarta, saida ya rungume duk yan uwanshi su Laila Jidderh nata kuka haka su twins ya duk'a a gabansu yana rarrashinsu ya tabbatar masu in akae Hutu zai sa akawo su Jidderh na jin haka cikin muryar kuka tace "Big bro nima" ya d'aga kai ya kalleta da d'an murmushi ya jinjina mata kan, bayan ya mik'e ya nufi su gwaggo da Kawu Amadu yayi masu sallama duk sukai mashi fatan Alkhairi da godiya sosae ya kai idonshi kan Nameer dake ta sakin murmushi yace "Sarkin murmushi sai yaushe?" Yar dariya yay yace "ai ni nan zan zo in cigaba da karatu ba mun gama magana ba" jinjina mashi kai yay daga haka ya nufi Mahaifiyarshi ya kama hannunta duk ta shiga damuwa sai kace yau zai fara mata nisa, cikin breaking voice tayi mashi Addu'oi da fatan Alkhairi kafin suka rungume juna daga nan kuma Hajiya ya nufa ya tsaya gabanta suna ma juna murmushi ya kamo hannuwanta slowly yace "Thank u for everything Sweetheart, am gonna miss u....." bai ida ba ta fashe mashi da kuka ya jawota ya rungumeta sosae, yana matuk'ar k'aunarta kamar yadda take kaunarshi yadda yake jinta ko Mahaifiyar shi bai ji haka lokaci guda idanunshi suka canja yaso ta bishi amman ta k'iya ko jiya saida yayi mata Maganar to tama k'i zaman Abuja balle kasar waje, haka Fanan ma ta zagaya
tay sallama da kowa shi Dad d'inta ya koma Lagos amman shima ya mata Nasiha kafin ya wuce kuma shi ganinshi a wurinta ba matsala bane don US gidane a wurinshi, bayan Haisam yayi sallama da kowa yan'uwanshi sannan ya nufi Abokanshi na Amana sukae mashi fatan Alkhairi kafin ya juya ya tafi sai kuma ya dakata ya kira Abbas ya nufeshi ya tsaya gabanshi idonshi akanshi shima Abbas d'in kallonshi yake yana jiran yaji mi zaice can yace mashi "Abbas pls ka kula da ZARAAH, i entrusted her to u yarinyar ta damu da nisan da zanyi pls make sure bata yi maraicin YA HANDSOME ba" yana kai k'arshen Maganar yaji wani abu mai kaman kwalla na son taruwa a idonshi tunowa da yadda suka rabu da sauri ya d'an d'aga masu hannu ya juya Fanan da sauran masu tafiyan suka rufa masu baya anata d'aga masu hannu masu kwalla nayi, nima dae nayi kwallan Ya Handsome d'in mu ya tafi๐Ÿ˜ญMuna maka fatan Alkhairi.



Uhmmmm, an gama Takun Farko da Sabon salo yanzu saura kuma An yanka ta tashi, amman fa ba wani abu nike nufi ba face Kaza aka yanka ta tashin๐Ÿคฃ



_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wannan no 09013804524._

Domin karanta cikakken Littafin sai ku danna bulun Rubutun dake kasa ko kuma hoton dake kass ๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

https://aihausanovels.com.ng/novel-document/a-sanadin-makwabtaka-book-2-complete-hausa-novel

๐Ÿ‘†๐Ÿ‘†๐Ÿ‘†๐Ÿ‘†๐Ÿ‘†


*ASM Bk2021*
*๐Ÿ’–A SANADIN MAKWABTAKA๐Ÿ’–*
_*(Love and Destiny)*_



_*BY ZAINAB LALUH๐Ÿ“ฒ*_
~(Oumm Imam)~

Book 2

Bonus Page 21
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*






.....Suna komawa gida su Abbas suka fara shirin tafiya dama tun jiya kowa ya kimtsa kayanshi ba 6ata lokaci sukae sallama da kowa aka rakosu parking space bacin an had'a masu sha tara ta Arziki Senator har 50k yaba kowanne na shan ruwa a hanya Nameer ma uban kaya yaba Kawu Amadu harda sababbi dasu takalma a cikin madaidaicin trolley sosae yayi mashi godiya d'an zaman nan da suka yi sun shaku sosae ji yake kaman karsu rabu gwaggo ma saida tayi mashi godiyar dama tun jiya ya bashi kayan, su Hajiya,Mommyn Haisam Hajiya Maryam,Laila,Jidderh,twins duk suka rakosu ana ta sake yin bankwana Farha dae na ciki tana aikin kuka dama kuma ko ba kukan take ba ba lalle ma ta rako sun ba, Hajiya ji take kamar ta bisu to amman Senator ya hana yace ba yanzu zata koma ba sai ta huta gajiyar biki Saude tun ran Asabar ta wuce ita da wasu yan'uwansu Hajiya na Daura Hajiyar ta hadasu sanin bazata koma yanzu ba Nana tabi wasu yan wurin aikinsu yanzu daga gwaggo sai Amadu Feenah da Abbas sai su Abdul.


Tunda gari ya waye Fatuu keta faman farincikin su gwaggo zasu dawo har fuskarta ta kasa 6oye hakan dama duk kad'aicin su ya isheta kullum sai taje gidan tayi zaune, bata je Makaranta ba don kuwa jibi Laraba zasu fara Waec suna tashi bayan sunyi Karin kumallo Fatun tace ma Haulat tazo ta rakata taje ta gyara gida ta tambayi innarta tace suje, bayan sun koma gidansu Fatun zagewa sukae ba 6ata lokaci suka fara gyara ko'ina na gidan yay fes dashi bayan sun gama Fatuu tace su d'aura girki amman haulat tace mata ta bari sai d'an Anjima Abuja fa ba nan kusa bace in sukae da wuri zai iya dankarewa a cikin kula tace to su je bakin hanya su siyo Nama da zasu sa a Abincin haulat tace to, basu wani dad'e ba suka dawo suka zauna a Parlor suna kallo can Fatuu ta tuna da sauran cin cin d'in da gwaggo tay mata taje ta de6o masu suka had'a da lemu suna sha, bayan wai lokaci Fatun ta kira gwaggo ta tambayeta ko sun taho tace mata eh gasu a hanya ta shiga yi masu Addu'oi gwaggon na amsawa tana yar dariya don daga yadda taji muryar Fatun akwae tsantsar farinciki a cikin ta, tana gama wayar tace ma Haulat su d'aura girkin yanzu don suna hanya tace to ta mik'e suka nufi kitchen suka fara shirye shiryen abunda zasu dafa, zuwa Bayan Azahar sun gama dafa Abincin wanda Farar shinkafa ce da miya dama suna da cefane a cikin d'an fridge d'in gwaggo na kitchen harda Coleslaw suka had'a da suka je bakin hanya suka siyo harda kayan had'in shi saidae yanka su cabbage d'in kawae sukae basu ida hadashi ba gudun lalacewa ko mayonnaise din ta saki sun bari sai sun iso sai su had'a, bayan sun gama Fatuu ta tafi kai markaden Aya da dama sun gyarata don tasan gwaggo na son kunun Aya bata dad'e ba ta dawo suka hau had'awa sai kamshi ke tashi dama Fatuu ba dae iya Abinci ba komae ta koya a wurin gwaggo haka 6angaren na yan gayun ma duk ta koya a wurin Saude, zuwa k'arfe ukku duk sun gama komae haulat taci Abinci ta koshi ita kuwa Fatuu wai sai sun dawo ba yadda bata yi da ita ba amman tak'i ci k'arshe ta kyaleta tay kwanciyarta ta hau yin bacci ita kuwa Fatuu zaune tay duk bayan lokaci take kiran layin gwaggo taji sun kawo ina wani lokaci ta samu layin wani lokaci ace out of reach can dae da yunwa ta isheta taje ta zubo Abincin kad'an ta ci kafin ta wuce toilet tayo wanka lokacin data fito an fara kiran sallar la'asar ta yi Alwala ta wuce d'aki, ubansun leshi tasa riga da skirt sabbi dal farko kamar karta sa kayan don acikin kayan da Haisam ya yi mata ne sai kuma wata zuciyar ta raya mata in bata sa ba zubar dasu za'ai kuma shi ai ba sanin bata sa ba zai yi hakan yasa ta sanya kayan, tayi kyau sosae bayan tayi Salla harda yar light make up tayi yaushe rabo ita kanta taga kyaun da tayi tay tsaye a gaban mirror tana ta sakin murmushi kafin ta koma Parlor ta tashi haulat koda ta tashi bin Fatuu tay da kallon mamaki tace "k'awata kinga kyaun da kikae kuwa wllh sai kace Amarya" wani kallo tay mata mai kaman harara tace "ke kika d'aura man auren ko" haulat na dariya tace "Eh mana keda Ya Haisam" nan da nan fuskar Fatun ta canza ta daureta sosae Haulat na ganin haka ta hau bata Hakuri tana fad'in wasa take mata amman dae tana fata daga haka ta mik'e ta fita itama sallar taje tayi tana gamawa tayi wanka dama ta taho da kayan da zata canja, koda Haulat ta fita daga parlon lamo fatuu tay tana juya Maganar haulat d'in ta tana fatan ta zamo Matar Ya Haisam to ta ya ya? Fatun ta jefi kanta da tambayar ita yanzu ta riga ta fidda ran ma samunshi matsayin miji lokaci guda ta tuna da sakonshi data gani jiya da safe a ranta ta ayyana yanzu bai ma da lokacin kirana kada matarshi taji haushi haka ta dingi tunane tunane can da ta ga abun na neman yay yawa sai ta mik'e ta hau k'ara gyara gidan tasa turaren wuta, har Magrib ta gabato basu iso ba Fatuu na zaune jigum a falo har ta fara damuwa haulat na toilet bayan ta fito ta nufi Parlon k'arar tsayawar Mota da taji a kopar gidan yasa ta fasa shiga Falon ta nufi hanyar waje tana lekawa taga sune da sauri ta koma cikin gidan tana fad'in "Fatuu gasu sun iso...." tun kafin ta rufe baki Fatun ta fito da gudu kallabinta a hannu ko ta kan Haulat bata bi ba tay kopar gida daidai lokacin duk sun fito daga cikin Motar da gudu ta nufi gwaggo ta k'ank'ameta tana fad'in "ga gwaggota ga gwaggota" dariya sosae gwaggon keyi itama tana fad'in "ga Autata ga Autata" duk suka ba su Abbas dariya Haulat ma dariyar take tayi a gefe guda, Boot Amadu ya bud'e ya fara shigar da kayayyakinsu dama su kadae suka rage don an sauke Feenah Saboda tafi kusa da shigowa gari, bayan Amadu ya fito ne yace ma su gwaggon to su shiga ciki mana sai ta maida ita ciki ma kawae gwaggon na dariya tace ai sai ta maida tan daga haka ta juya ta kalli Abbas dake tsaye ya dafa kopar Mota ta shiga yi mashi godiya da Addu'oi da fatan Allah ya huce gajiya tace sai tazo k'ara yin godiya har gida a gaishe mata dasu Abdul yana dariya yace ai ba komae suka juya yana ta kallon Fatuu itama murmushi kawae take mashi ba tare data ce mashi komae ba Amadu ma yay mashi godiya sosae ya nufi gida har sun kusa shiga gida Fatuu ta juyo ta dawo ta tsaya gefen Motar tana kallon Abbas da har lokacin yake defe da kopar Motar yana mata Murmushi, shiru tay ta kasa mashi Magana don Haisam kawae take gani sai yan kyafcen kyafcen idanu take tana d'an motsa baki,

"Mom Zarah kina lafiya?" Jinjina mashi kai tay kafin a Hankali tace "lafiya lou kun dawo lpy?" Kai ya d'aga mata kafin yace "ya shirye shiryen Waec yaushe zaku fara ne?" Tace "jibi zamuyi paper d'in physics practical sai Islamic da yamma" jinjina kai yay ya d'an yi shiru tana bin shi da ido can taji yace "Ya damuwar ta rage ko?" d'an tura baki tay kaman bazata ce komae ba ganin ya kafeta da ido yana murmushi yasa tana tura baki tace "eh na daina damuwa ai shima ya yi Aurenshi ya manta dani da yana kira na amman yanzu ya daina" da alama abun na mata ciwo shi kuwa Abbas fad'ad'a murmushin shi yai cikin ranshi ya ayyana kishi kumallon mata ganin murmushin da yake yasa ta sadda kanta k'asa ita kanta bata san ya akai tayi Maganar ba ji tay ya kira sunanta ta d'aga kai ta kalleshi yace "kiyi hakuri amman ba haka H,zakee yake ba shi mutum ne mai damuwa da wanda ya damu da shi in dae yasan kuna gaisawa ya jika shiru yana tuntubar mutum yaji ko lpy ke kanki ba hakanan ya daina kiranki ba hidima ne yayi yawa amman nasan da ya zama well settled zaki ji daga gareshi ke ai yar gatan shi ce kina d'aya daga cikin mutanen da ya damu dasu sosae hakan ma ne yasa ko yau kafin ya bar Kasar saida yay Maganar ki" d'an bud'a ido tay ya jinjina mata kai alamar tabbatar mata da abunda yace kasa jurewa tay tace "to miya ce game da ni?" Yana murmushi yace "ya bani Amanarki ne yace kar na bari kiyi maraicin shi" zaro ido tay sai kuma tay yar dariya tace "to sai ka dawo gidan Hajiya kenan" dariya kawae yay itama tay shiru tana maimaita Maganar da Abbas d'in yay cikin ranta har taji sanyi don da tayi tunanin ya manta da ita ne,

Showing 69001 words to 72000 words out of 113043 words