ta rafka tagumi itama ta zauna gefenta ta dafa Shoulder d'inta tace "bak'on naki ya iso Fatuu" kallonta tay ta fara d'an ta6e baki alamar zata fara kuka yadikko ta girgiza mata kai tace "Don Allah Fatuu ki yi hakuri ki fawwala ma Allah komae, shi mai ji ne kuma mai gani yafi kowa sanin halin da kike ciki don haka ki dogara da shi na tabbatar zai baki mafita ya za6a maki abunda yafi Alkhairi gare ki" d'aga mata kai tay ta kama hannunta ta mik'ar da ita, gaban mirror ta kai ta tasa ta ta shafa powder har jan baki tace ta shafa amman ta k'i tasa lip glow kawae yadikkon ta gyara mata d'aurin kallabin ta ya zauna sosae gashin ta dama ta lankwasa shi ya fito yay tum a baya, golden brown gyale mahad'in kayan ta yafa haka takalma ma sosae tay kyau duk da ba wani make up tay ba, tun da ta fito ta nufi hanyar soron k'irjinta ke bugu tamkar ana mata luguden ta6are hakanan take jin tsananin fargaban zuwan ganin abun take kaman almara ba gaske ba wai wurin wanda zata Aura nan da sati biyu zata je, da yar sallama ta shiga lokacin da ta k'arasa ko cire takalman k'afafunta bata yi ba tun a bakin kopar kamshin turaren da ya baza a jikinshi ya d'aki hancinta, a d'arare ta idasa shiga idonta a kan shi yana zaune akan kujerar da Ard'o ke zama ya sadda kanshi yana latsa wayarshi yana sanye da shadda brown wanda ta hau da fatar jikin shi sosae anyi mashi irin fav d'inkin Haisam wato senator style saidae basu amshe shi kaman yadda suke amsar jikin Haisam ba don yanayin halittar jikin ba d'aya ba, bai sa hula ba hakan ya bayyanar da sumar shi dake a lallank'washe hannunshi sanye da brown wrist watch, ba laifi shigan tay kyau kana ganin shi kaga wayayyan d'an boko, tsaye tayi daga d'an can nesa bayan ta shigo tana kallon shi tana haka su Mino suka shigo da kayan Abinci suka nufi gaban shi suka aje had'i da gaishe dashi kaman bazai amsa ba sai kuma yace "lafiya" ba tare da ya d'ago ba balle su samu Arzik'in kallo suka juya suka fita, sun d'auki lokaci a haka sai da ya mula ya sha iska sannan slowly ya d'ago ya sauke mayatattun idanunshi tamkar na mai jin bacci akan Fatuu dake tsaye a gaban shi, kallo suka bi juna da shi tun bayan da ya d'ago Fatuu ke mashi kallon sani hakanan taji kaman ta ta6a ganin shi to amman a ina? Shine abun da take son ta gano, wani irin jarababben kallo yake bin ta dashi from head to toe tsam ya mik'e walking slowly toward her, a gabanta ya tsaya har saida Fatun tay stepping back Saboda yadda ya k'ure mata, a hankali ta kai idanunta kan fuskar shi lokaci guda k'irjinta yay wani irin bugu tuna inda ta ta6a sanin shi d'an buda ido tay sai kuma da sauri ta sadda kan ta kasa,

"Why am I having d feeling dat I know u somewhere??" taji husky voice d'in shi ta fad'a wato shima ashe yaji ya santa wani wurin, K'in d'agowa tay gaban ta naci gaba da fad'uwa wani irin mugun tashi hankalinta yay ganin shi matsayin Mutumin da zata aura, "Hey!" taji ya fad'a da d'an d'aga Murya a hankali ta d'ago duk ta kame kanta sai zare ido take ya k'ara kankance idon shi yana kallon ta da alama so yake ya tuna inda ya santa can bayan d'an lokaci kawae sai gani tay yay wani kalan murmushin mamaki ya d'an kya6e baki kafin ya furta "Wonders Shall Never End, so u'r My Wife to be!!!" bin shi da ido kawae take sai faman sakin Shu'umin Murmushi yake.........




_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268._

Domin karanta cikakken Littafin sai ku danna bulun Rubutun dake kasa ko kuma hoton dake kass πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

https://aihausanovels.com.ng/novel-document/a-sanadin-makwabtaka-book-2-complete-hausa-novel

πŸ‘†πŸ‘†πŸ‘†πŸ‘†πŸ‘†


*ASM Bk2029*

*πŸ’–A SANADIN MAKWABTAKAπŸ’–*
_*(Love and Destiny)*_



_*BY ZAINAB LALUHπŸ“²*_
~(Oumm Imam)~

Book 2

Bonus Page 29

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*





.......Juyawa yay walking majestically ya koma inda ya ta so ya zauna idon shi a kanta,

"zaki ta tsayuwa ne?" Ya tambaya had'i da d'age mata gira wani kuka cikinta ya fara yi, kaman k'wai ya fashe mata a ciki ta fara moving zuwa gefe inda wata kujerar take ta zauna tana cigaba da kallon shi, "From all indications kema kin gane husband to be en naki ko?" wani wahalallan miyau ta had'iya bata dae ce komae ba,

"I ave been wondering wata kucakar Dad ya sama man matsayin Mata a Wannan tsukukun k'auyen ashe ba kucakar bace mara kunya ce mai zagin iyayen Mutane" still bata ce mashi komae ba yaci gaba "But duk da haka am so happy Dad has made a right Choice for me, it's nice meeting you my lovely wife" bakin Fatuu fa ya mutu murus ba kamar da ta ga irin murmushin da yake saki tasan ba har zuciya yake fad'ar abubuwan da yake fad'i ba,

"Kin bi ni da ido ko baki farin ciki da ganin husband en naki bane shiyasa ko Welcoming dina bazaki ba balle in sa ran za'a gaida ni, koda yake I know who my wife to be is ba lalle in ta iya gaida Mutane ba" d'an motsa baki tay sai kuma ta sunnar da kai katsa yayin da a cikin ranta ta furta innalillahi Wa'inna ilaihir raji'un, sam ta kasa bud'e baki tace wani abu don ba k'aramin Al'ajabi ne ya kamata ba, a hankali ta saci kallon shi taga still kallon ta yake hakan yasa ta idasa dagowa cikin trembling voice tace "ina wuni an zo lpy" d'an tafa hannu yay yace "Wow what a sweet voice, lafiya lou wife hope na same ki lpy?" tabdijan ya gama kashe Fatuu da mamaki duk yadda tay zaton zai mata ba haka take gani ba ganin tayi kasak'e tana bin shi da ido yasa ya d'age mata gira yace "Wife Kaman ke baki farin cikin gani na a matsayin wanda aka za6a maki ba ko" murya a hard"e tace "a'a nayi" jinjina kai yay yace "To ya Katsina fatan kin zo lafiya" tana d'an kikkafta ido tace mashi lafiya lau yaci gaba "dama ina ji ana cewa Katsina akwae beautiful babes masu ilimi da wayewa yanzu na shaida haka even though ke d'in asalin yar nan ce amman su suka maida man ke yadda nike son wife ena ta kasance" ya k'arasa yana wani juya yaudararrun idanun sa, sunnar da kanta tay k'asa don Maganar tashi ba wanda ta tuno mata sai Haisam Saboda shi ne ya maida ta yadda take,

"na fa san kina Magana so ki daina acting as if baki magana ko yana maki wuya, ki saki jiki ki kuma bud'a baki ki man magana kaman ranar da kika zage ni" da sauri ta d'ago ta kalle shi ya bud'a mata ido d'an yamutsa fuska tay cikin breaking voice tace "ni fa ba zagin ka nayi ba kuma Kaine ka fara zagi na ai" Shegen murmushin shi ya saki yace "kika rama kuma ko, anyway ai baki ji nace kin yi laifi ba ya wuce koma kin yi ai Amarya bata laifi if u wish yanzu ma zaki iya zagi na I won't feel offended" ya ilahi ya rabbil alamen mutumin nan nema yake ya tarwatsa ma Fatuu zuciya, shiru suka d'an yi sai faman k'are mata kallo yake can yace "Wife ina buk'atar ruwa or I should serve myself ?" a hankali ta juya ta kalleshi sai kuma ta mik'e ta nufi gaban shi ta duk'a ta fara kokarin zuba mashi lemu hannunta har d'an rawa yake, bayan ta zuba ta d'ago da niyyar bashi taga gaba d'aya hankalin shi na a wani wuri a jikinta hakan yasa ta d'an d'ukar da idonta don taga abunda yake kallo ashe saman boobs d'inta da sukae fam fatar wurin fari fat da ita ya kafe da ido yana kallo sakamakon wuyar rigar da yake a bud'e sosae, da sauri ta ja gyalen ta rufe wurin hakan ya sa shi dawo wa cikin hayyacin shi ya kalleta da murmushi kafin ya kai hannu ya amshi glass cup d'in had'i da furta "thanks my beautiful wife" mik'ewa tay ta koma ya bi bayanta da kallo har ta zauna sannan ya kai cup d'in baki ya fara sipping lemun saida yasha kaman rabi sannan ya ajiye ya kalleta ta d'ukar da kanta tana d'an wasa da yatsunta taji ya d'an yi gyaran murya hakan yasa ta kalle shi yace "Wife miye labari" d'an watsa hannu tay tace "babu" yace "What about preparations na bikin mu?" Kaman bazata ce komae ba sai kuma tace "ana yi" gyara zama ya d'an yi yace "Ok dame dame zaku yi ne?" tace "ba komae" d'an buda ido yay alamar mamaki yace "Haka zaku yi bikin ba wasu programs kaman zaki auri enermy en ki" ido kawae take bin shi da shi yaci gaba "koda yake baki da Friends anan ko?" Kai kawae ta d'aga mashi ya jinjina nashi,

"To yanzu kaman nawa kike buk'ata na abunda kike ganin zaki yi like gyaran jiki and so on" ya tambaya, tace "zanyi ba sai ka bani ba" yar dariya yay ya d'an shafi sumar shi yace "Ashe wife en nawa Hajiya ce" shiru bata ce komae gaba d'aya sai taji ta k'agara ma ya tafi kota koma ciki don gaba d'aya kanta a d'aure yake bata da natsuwa,

"Gobe sister d'ina zata zo zaku je wurin tailor zai taking measurement naki sai ki shirya" kallon cikin ido tay mashi yace "let me have ur digits so dat lokacin da zasu zo sai in sanar maki" karanto mashi phone number d'in ta tay bayan ta gama ya kira jin wayan na ringing ba anan ba yasashi tambayar inda wayan take tace tana cikin gida yace to in ta koma sai tay Saving harda fad'i mata sunan shi Khalid ya tambayi nata tace mashi Fateema yana murmushi ya furta "Fatima Zaraah" har saida kirjinta ya buga damm, ganin yana kokarin mik'ewa yasa tace bai ci Abincin ba yana wani kashe mata ido yace he's Ok bai jima da ya ci Abincin ba but next time in ya zo zai ci daga haka ya mik'e itama tana ganin hakan ta mik'e ya nufo in da take ya tsaya suna facing juna ya kafeta da mayaudaran idanunshi seductively ya furta "Hope ban yi laifi ba da ban ci ba kar next time a ki dafa man don nasan girkin ki must ba as hot as u'r" wani dam dam k'irjin ta ke yi ganin yadda yake mata Magana ba zato ba tsammani sai ji tay ya kawo hannu ya janyota ya had'e jikinsu a gigice ta shiga kiciniyar kwace jikinta saidae ta kasa a rud'e tace "Don Allah ka sake ni kar wani ya shigo fa ayi tunanin wani abu nike yi" gaba d'aya ya zuba ma lips d'inta ido yadda tay Maganar ba k'aramin tafiya tay da shi ba kokarin had'a face d'in su yake a kidi'me Fatuu ta tattara duk k'arfinta ta tura shi tay baya ta fad'a kan kujerar da ta tashi, wata yar iskar dariya ya saki yace "Wife zaki ji ma kan ki ciwo fa and miye abun rud'ewa haka kaman na aikata wani abu ba daidai ba, ko basu yi informing naki an biya sadakin ki bane?" Kasa cewa tay komae sai numfashi take fitarwa da sauri da sauri duk ya gama tsorata ta, still dariyar yake yace "I forgot wife en tawa Secondary graduate ce but at least be romantic Babe" daga haka yasa hannu a cikin Aljihun rigarshi ya fiddo rafar yan dubu dubu guda biyu ya d'aura mata akan cinyarta kafin ya sake sa hannu a aljihun ya fiddo farin glass ya sa a fuskar shi yana murmushi yace sai sun sake had'uwa daga haka ya fice, Mutuwar zaune Fatuu tay tama rasa tunanin da zata yi akan shi da k'yar ta iya yunk'ura wa ta mik'e jikinta har lokacin rawa yake ta nufi cikin gidan a kan hanya ta had'u da Mino tace mata taje ta kwaso kayan abincin da suka kai tace to, a Falo ta iske yadikko zaune tana ganinta tay mata Murmushi tace har ya tafi ta d'aga mata kai kafin ta wuce cikin d'aki tana shiga ta cillar da takalmanta ta cire gyalen shima ta wurgar ta haye gadon sai zare ido take tunani kala kala acikin ranta ba kamar akan had'a jikinsu da yay hakan yasa ta fara shakkun anya ba gaskiya bane yana neman mata in ba haka ba mi zai sa daga fara haduwar su yau ya had'a jikinsu bama wannan ba kadae har fa kusan had'a bakunan su yay ba don ta samu ta fizge ba, wata zuciyar kuma ta ayyana mata ai yace don an biya sadakin ta ne to amman ai ba'a d'aura masu aure ba ko, gashi sam ta kasa yadda da yanda ya sake mata sai take ganin kamar akwae dalilin hakan, tana ta zancen zuci har Yadikko ta shigo bata sani ba saida ta zauna ta kira sunanta sannan ta kai idanunta kan ta, tambayarta tay lafiya dai ko taga ta shigo ta kwanta ko wani abun ya faru ne ta k'ak'alo murmushin yak'e tace mata a'a lafiya lou,

"To Allah yasa dae kun fahimci juna yayi maki kuma" d'an ta6e baki Fatuu tay a sanyaye tace "koma bai man ba yadikko ya zanyi dole ai in Aure shi ko" shiru tay tana kallonta gaba d'aya tausayinta take ji don daga yanayin ta sai taga kaman bai mata ba, tambayarta tay ya akai taga bai ci komae ba Fatun tace "Yace ya k'oshi sai ya sake dawowa zai ci" jinjina kai tay tace mata to ta taso suje ta ci farko taso ta k'i tace ta k'oshi saida Yadikkon ta matsa mata sannan ta saukko lokacin ta nuna mata kud'in da ya batan na abubuwan da zata yi tace to ta ruk'e a wurinta. Da daddare tana cikin yin shirin kwanciya sai ga kira ya shigo wayarta koda ta duba bata gane mai kiran ba hakan yasa tak'i d'agawa taci gaba da abunda take sai gashi an sake kiran, zama tay bakin gado ta d'aga ba tare da ta ce komae ba on the other hand taji ance "Wife ko kin yi bacci ne" rass gabanta ya buga jin muryarshi sai lokacin ta tuna da d'azun ta bashi no dinta har ya kira yace tay Saving, sake maimaita tambayar da yayi mata yay sai lokacin tace mashi a'a yanzu zata kwanta,

"Gani na kasa bacci Saboda tunanin ki wannan shi ake kira da luv at first sight all I need in ji ki gefe na hope kema hakan?" shiru tay mashi har saida ya k'ara tambayar tata sannan ta tura baki tace "a'a" tana jiyo sautin dariyar shi yace "Don't worry Babe zan koya maki yadda kema zaki rink'a jin hakan game da ni" shirun dae ta k'ara ita duk ta fara tsorata ma da shi haka ya dingi yi mata kalaman soyayya harda tambayarta wace tarba zata mashi a first night d'in su ita dae a tak'aice take bashi amsa wani wurin kuma ta mashi shiru jin shiru shirun nata yay yawa yasa shi tambayar ko ta fara jin bacci ne tace mashi eh yace bari ya barta ta kwanta harda cewa tayi bacci mai dad'i kuma tayi mafarkin shi shima zai yi nata ita dae shiru tay mashi tana niyyar cire wayar taji sautin wani matsiyacin kiss da yay mata har cikin dodon kunnanta da sauri ta cire wayar ta k'ura ma screen d'in ido kirjinta na beating very fast can ta runtse idanunta sai ga kwalla sun fara zubowa ba kowa ne ya fad'o mata a rai ba face Ya Haisam ji take inama shine yake nuna mata so haka ba wannan ba da take tunanin duk k'arya ne da biyu yake mata hakan ba don yana sonta tsakani da Allah ba, tana ta tunane tunanenta har bacci yay awon gaba da ita,

Washe gari bayan sun kammala yin breakfast ta gyara d'akin sai ga kiran shi wai ya kira ya ji ya ta tashi tace mashi lpy Lou anan yake sanar da ita ta shirya around 1:00 za'a zo atafi da ita ta amsa da to, lokacin ta sanar ma yadikko ita kuma ta kira Baffanta a waya ta gaya mashi yace to ta dawo lafiya ta so ace Mino ta dawo daga Makaranta ta rakata, wurin karfe d'aya saura tana cikin shiryawa yadikko ta shigo cikin d'akin ta sanar da ita game da zuwan wadda tazo tafiya da ita wato Sadeeya tace to, doguwar rigar shadda sabowa dal acikin irin kayan da Haisam yayi mata Navy blue tasha aiki blue da fari yayi kyau sosae ta sa yan kunne da sark'a sai Agogo duk silver sai farin mayafi haka takalma ma high heels ne farare ta d'auki yar clutch dark blue, a saman kujera Sadeeya ta zauna ita da wata yarinya da zata yi shekara bakwae da suka zo tare tana sanye da jeans da t-shirt kanta sanye da hula da bayanta ya d'an yi tudu alamar gashin ta a fake yake, itama Sadeeyar a shekaru zata yi shekara 25 zuwa 26 itace k'anwar Khalid ta biyu, ta farkon wato Yayar Sadeeyar tayi Aure, a ABU Zaria Sadeeya ke karatu itama fara ce saidae bata kai Khalid haske ba sannan ita da Chairman take kama duk da ta
Showing 99001 words to 102000 words out of 113043 words