na Masara ne yaji zogale sai kamshi ke tashi, tare ta zubo masu a babban plate don tasan ko ta zubo masu kowa da nashi karshe Fanan din sai tace a had'a masu, sosae taji dad'in dambun duk yadda Fatuu taso k'in ci da yawa ta hanata tace in bata cin abinci sosae koda ta samu lafiya karfin jikinta bazai dawo ba, ba yadda ta iya haka ta rink'a turawa ba don tana wani jin dadinshi ba, koda suka cinye gwaggo tace a k'aro masu cewa Fanan tayi eh sam bata nuna bak'unta kai kace yar 'uwarsu ce ma, k'in ci Fatuu tayi bayan an k'aro tace ita ta koshi dole ta kyaleta taci gaba da ci ita kadae, tana cikin ci Hajiya tayi sallama gwaggo dake zaune itama tana cin dambun ta mik'e da sauri ta fita tana Fad'in "Maraba da Hajiya" ta amsa mata da yauwa tana nufota Saude na bayanta itama gwaggo tayi mata sannu da zuwa ta gaisheta da fara'a ta amsa mata tace su shigo, suna shiga idon Hajiya ya sauka kan Fanan da ta tura dambu a baki tana mata dariya Hajiya ta ruk'e ha6a tace "Oh su shanshani kafan yawo ana nan ana kwalama ashe, to Allah ya jikanka dambu ki dai bi a hankali in ba haka ba ya shaqe ki" tayi Maganar tana kokarin zama kan kujera gwaggo dake Dariya tace "Mutum da gidansu ai ba kwalama take ba" Fanan d'in ta gyad'a kai alamar atoh,nuna ma Saude kujera gwaggo tayi tace ta zauna tayi tsaye ta nufi wurin ta zauna, gaisawa suka shiga yi suka yi mata ya mai jiki tace da sauki kallon fatuu dake zaune kan carpet gefen Fanan tayi shiru tace "Oh sannu Fateema kinji, Allah ubangiji ya yaye maki wannan lalura baki d'aya ki huta wannan zuwa Dam bai yi dad'i ba sam" gwaggo dake d'an Murmushi tace "to ya za'ai haka Allah ya kaddara" hajiya tace "hakane amman dae da sauki sosae ko?"
"Eh jiyane dana dawo dae na iske abun yayi tsanani har tana kirjinta zai 6are to sai nayi mata Addu'oi na kuma je wurin Malam tanimu na fad'a mashi halin da ake ciki shine ya bukaci ruwan zam zam yayi mata Addu'oi yau da safe aka amso tasha na shafa mata kaman yadda yace Allah cikin ikonsa ta samu sauki sosae wllh" gaba d'ayansu duk suka girgiza kai alamar tausayawa ita dae Fatuu zuru tayi tana binsu da ido don ta fahimci ciwon da suke tunanin yana damunta, mik'ewa gwaggo tayi tace bari a zubo masu dambu Hajiya ta tambayeta na miye tace na Masara ne tace to a zubo masu kad'an don ta kwana biyu bata ci shiba, wuri daban daban ta zubo masu ita da Saude Hajiya na ganin haka tace maimakon ta zubo masu wuri guda sai sun cinye masu abinci dama ga wata acicin nan sai turawa take Fanan na jin haka tasa dariya suma duk dariyar suke, bayan sun gama Hajiya ta tambayi gwaggo bazata aiki bane yau tace tana son zuwa amman tana tunanin yanayin jikin Fatuu don jiya yadda ta dawo ta sameta hankalinta ba k'aramin tashi yay ba, Fanan na jin haka tace taje aikinta zasu zauna tare Hajiya tace "to ku taho can gida mana in ta dawo ba sai ta dawo ba" girgiza kai Fanan tayi tace "ban komawa fushi nake da Babe" Dariya Hajiya tayi tace "Saboda yau yak'i zuwa dake aikin kika yi fushi dashi" kai ta d'aga alamar eh, tace "hum dama dae zaki iya duk cika baki ne" gwaggo dake dariya tace "ai y'ata kishinki yake shiyasa bai je dake ba" bayan sun gama gaba d'aya suka nufi gidan Hajiya...........

Domin karanta cikakken Littafin sai ku danna bulun Rubutun dake kasa ko kuma hoton dake kass πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

https://aihausanovels.com.ng/novel-document/a-sanadin-makwabtaka-book-2-complete-hausa-novel

πŸ‘†πŸ‘†πŸ‘†πŸ‘†πŸ‘†



*ASM Bk2004*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._
*πŸ’–A SANADIN MAKWABTAKAπŸ’–*
_*(Love and Destiny)*_



_*BY ZAINAB LALUHπŸ“²*_
~(Oumm Imam)~

Book 2

Bonus Page 4


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*



Koda suka je zama sukayi a parlor suna kallo suna fira sai dae Fatuu bata wani saki jiki sosae ba sama sama take Magana ganin yanayinta yasa Hajiya tace taje d'akinta ta kwanta Fanan ta kama hannunta suka tafi, kwantawa tayi saman gadon Hajiyar Fanan kuma ta wuce Toilet don tayi wanka lokacin data fito har bacci ya kwashe Fatuu itama kayan shan iska tasa ta kwanta gefenta tana son ta kira Haisam don taga missed call d'inshi lokacin data fito daga toilet amman sai kawae ta daure ta kyaleshi wai don yasan tayi fushi, tana ta latsa wayarta har bacci itama ya kwasheta, sai da akayi la'asar Hajiya ta shigo yin salla ta tashesu suma suyi sallar, da daddare bayan isha suna zaune a falo Fatuu duk ta k'agara ta koma gida don bata son Haisam ya dawo tana gidan, har cewa tayi zata tafi Hajiya tace ta bari in Dijen ta dawo ai zata kira ita kuma Fanan cewa tayi ta kwana anan kawae mana ita dae murmushin yak'e kawae tayi, suna zaunen Haisam ya shigo da sallama duk suka d'aga kai suka kalleshi Hajiya ta amsa mashi yayin da k'irjin Fatuu yay mata wani irin bugu tana yin arba da fuskarshi sai dae kuma ta kasa daina kallonshi wani irin fresh taga yayi mata, nufosu yay Fanan ta kauda kanta yana ganin haka yaja ya tsaya Hajiya dake kallonsu na masu Murmushi don tasan yadda sukai da Fanan d'in da safe, juyawa yay zai koma da sauri Hajiya tace "ka rufa man asiri ban shirya yin jinya ba daga kawo man ziyara" ita kuwa Fanan d'in mik'ewa tayi da sauri sauri gudu gudu ta nufeshi tana zuwa ta fad'a bayanshi ta k'ank'ameshi ta yadda bazai iya cigaba da tafiya ba, ruk'e hannuwanta yay ya juyo yana kallonta ta zo6ara baki ya kai hannu ya d'an ja lips d'inta ta saki yar k'ara sai lokacin yay Murmushi ya kama hannunta suka nufo cikin falon, wani irin abu Fatuu taji ya tokare mata k'irji nan da nan zuciyarta ta karye taji kwalla na niyyar zubo mata da sauri ta juyar da kanta ta kalli tv, gefen Fatuu inda ta taso ya kaita ta zauna shi kuma ya zauna saman hannun Sofa har lokacin suna ruk'e da hannun juna kallon Hajiya yay ya gaidata ta amsa tana Murmushi a hankali ya juya ya kalli Fatuu daidai itama ta juyo saida ta had'iye wani abu mai d'aci kafin da k'yar ta iya gaidashi ya amsa yay mata ya jiki tace da sauki, maida kallon yay kan Fanan yace ta gama fushin Hajiya tace "to ai ni bansan wane ma irin fushi ne wannan ba" turo baki Fanan tay ta kwantar da kanta gefen jikinshi tace ita dama ba fushi tayi dashi ba ai, Hajiya tace to kanta dai ta k'aryata ba ita ba duk suka yi dariya, janyeta yay ya mik'e yace zaije yay wanka baiwar Allah Fatuu daurewa kawae take ita kadae tasan abunda take ji yanzu ta tabbatar ma kanta ba k'aramin son juna suke ba, kasa jure zaman tayi ta mik'e tace zata je gida tasan yanzu gwaggo ta dawo Hajiya tace ta lura dae gidan take son tafiya to ta bari taci abinci Fanan ma tace ta bari in sunci dinner sai su rakata ita da Babe Hajiya tace lokacin ma tasan dijen ta dawo, kasa yi ma su musu tay ta koma ta zauna bada jimawa sosae ba Haisam ya shigo ya shirya cikin jallabiya dark ash mai gajeren hannu yana shigowa Fanan ta mik'e ta kama hannun Fatuu tace mashi suje table Zarah nason tafiya gida jinjina kai yay suka nufi dining area da tun bayan gama sallar isha Saude ta shirya komae, kaman yadda suka saba haka suke cin abincin baiwar Allah Fatuu daurewa kawae take idonta akan abincin gabanta da Fanan ta zuba mata ji take kaman ta rushe da kuka, bata wani ci da yawa ba sai faman jujjuya cokali take can ta mik'e tace ta k'oshi fanan tace ta daure ta k'ara bata ci sosae ba tace amai take ji ne hakan yasa Hajiya tace ta k'yaleta fanan d'in tace to ta jirasu a falo su gama ta d'aga mata kai kawae, a tare suka rakota suna ta hirarsu irin ta masoya har wani d'an fad'a mashi a jiki take, lokacin da suka k'araso kopar gidan su biyu suka shiga shi ya tsaya a waje zai jirata, gwaggo bata dad'e da shiga gidan ba suka shigo fanan na dariya tace ta maido yar ajiya tak'i ta kwanan mata itama gwaggon dariya take tay mata godiya sosae ta tafi, kallon Fatuu dake zaune kan kujera tayi tace mata ya jikin ta amsa mata da sauki ta mik'e zata wuce d'akinta gwaggon tace ta tsaya ta zubo mata Abinci sai taje ta kwanta tace taci acan daga haka ta wuce d'akinta tana shiga ta nufi gado ta fada samanshi tayi rubda ciki sai lokacin kukan da take ta rik'ewa ya samu zubowa,wani irin son Ya Handsome take ji acikin ranta bata da buri yanzu sai na auranshi to amman ta yaya shi da baisan ma tana yi ba gashi yanzu tabbas ta gasgata Maganar Haulat na ba k'aramin son juna suke ba shida Fanan, sak'e sak'e taci gaba da yi tana neman mafita har gwaggo ta lek'o ganinta haka yasa tayi tunanin tayi bacci ne shiga tayi cikin d'akin tay mata Addu'oi duk fatun na jinta bayan ta gama ta gyara mata kwanciya lokacin da zata fita daga d'akin ta kashe mata hasken wuta kafin ta fita.

Tun daga wannan ranar Fatuu bata k'ara yadda wani abu ya kaita gidan Hajiya ba don ta fahimci in taga Haisam k'ara shiga mawuyacin hali take, k'iri k'iri ta hakura da ganinshin abunda bata ta6a tunani ba a rayuwarta wato guje ma ganin Ya Handsome d'inta mutumin da ko tafiya yay a k'agare take daya dawo don duk sai tajita ba daidai ba in bai nan, duk abunnan ba wanda ya fahimci halin da take ciki su a tunaninsu lalurar da suke zato ke damunta ita gwaggo bata ma san cewa Fatun bata san da Maganar baikon dake tsakaninsu ba sanin irin shak'uwar dake tsakaninta dasu duka bama kamar Haisam, itama kuma Fanan bata san Fatun bata sani ba, Ranar Asabar ya kama kwanan Fanan shidda da zuwa Fatuu na cikin d'akinta don yanzu ta d'aura aure da zaman d'aki ba kaman in gwaggo bata nan in tana nan ne wani lokacin inta matsa mata take zuwa Parlor ta kunna tv saidae sunan tana yin kallonne amman hankalinta na wani wuri tunane tunane sun zamar mata jiki duk tazama wata so silent Magana saita kama take yi, shigowa gwaggo tayi da sallama ta d'aga kai ta kalleta kafin a hankali ta amsa mata ta nufi gefen gadon ta zauna fatun ta yunk'ura ta mik'e zaune,
"Sannu ya karfin jikin?" amsa mata tayi da sauki, tace "Yanzu ya kike jin jikinne ina yafi damunki?" shiru ta d'anyi idonta akanta kafin a hankali tace "ba ko ina" itama gwaggon shiru tay kaman mai nazarinta hakan yasa Fatun duk'ar da kanta tana wasa da yatsunta,
"In ba abunda ke damunki yanzu miyasa kika k'i sakin jikin ki kaman da?" da yar damuwa tay Maganar, damm gabanta ya d'an fad'i ta d'ago idanunta har sun canja kala a sanyaye tace "kawae banjin dad'in jikinne kaman ba nawa ba" jinjina kai gwaggon tayi tace "a hankali zaki warware amman wannan k'umshewar da kike cikin d'aki hada shi ke k'ara maki rashin dad'in jikin, ki daure ki rink'a sakin jikin kina fitowa" kai ta d'aga mata tace Allah ya bata Lafiya daga haka ta mik'e zata fita sai kuma ta tsaya ta juyo tace "ko gidan Hajiya ki daure ki rink'a zuwa kinga yarinyar nan Fanan kullum sai tazo dubaki duk ta damu da halin da kike ciki in taga kinje zata ji dad'i, da zaki iya ma kiyi d'an wani abu ki kai mata nasan zata ji dad'i sosae taga kema kin damu da ita kaman yadda ta damu dake" wani irin fad'uwa gabanta yay hakanan ita bata tsani Fanan ba amman data ji muryarta ko anyi Maganarta sai gabanta ya fad'i ganin gwaggon ta kafeta da ido ne yasa tace to mi zata yi mata, tace "yauwa to ko wainar fulawa ce akwae komae na yi kije waje wurin Amadu sai ki amso kwai nasan ba k'aramin dad'inta zata ji ba tunda ita ba ruwanta komae ci take" ta k'arasa Maganar tana nufar kopa, zaune tayi tay shiru bayan gwaggon ta fita, ba wai wainar ke bata son yi mata ba kawae ita gidan Hajiyar ne bata son zuwa don karshenta zata tado ma kanta wata matsalar ne can dai ta saukko daga kan gadon ta fita, ba tare da 6ata lokaci ba gwaggo ta taimaka mata wurin had'a k'ullun wainar ta yi shi mai d'an yawa yadda suma zasu ci, suya Fatuu ta fara cikin Kitchen gwaggo kuma ta yanka mata cabbage da sauran kayan ci, bayan ta soya mai d'an yawa gwaggo tace tay sauri ta shirya ta kaimata ita bari taci gaba da yin suyar, wanka taje tayo har ta wuce kitchen gwaggo ta kirata tazo bakin kitchen d'in ta tsaya tace "nace ko ki saka kayan data kawo maki dinnan suna nan na saka maki acikin kayanki" kai kawae ta d'aga mata ta wuce, kayan na nan yadda suke cikin leda tunda ta kawo su Fatun bata ta6a su ba, d'aukar ledar tayi ta koma bakin gado ta zazzagesu ta fara d'agasu tana dubawa, sari kala ukku ne riga da wando da mayafinsu rigar iya gwuiwa ce sai kuma doguwar riga har k'asa itama kuma tana da wando da mayafi kayan sun matukar had'uwa daka kallesu zaka gane ainihin na india ne sun mata kyau saidae yanayin da take ciki yasa ta kasa yin murnar kayan dama kwanaki can baya Haisam ya ta6a kawo mata irinsu kala biyu da yaje Lagos yace Fanan tace a bata sai yanzu ta fahimci dalilin dayasa yake yawan zuwa Lagos wani lokacin harda wurin Fanan yake zuwa in tazo,wasu sky blue ta d'auka zata sa ta mayar da sauran cikin ledar,bayan ta gama shiryawa tsaye tay gaban mirror tana kallon kanta kayan sunyi mata kyau sosae sai salki stones din jiki ke saki ba don yanayin da kayan suka risketa aciki ba da ba abunda zai hana har rawar india tayi,jiki a sanyaye ta yafa mayafin kayan ta nufi kicin bayan ta sanya takalma masu d'an tudu don bata saka flat shoes shiyasa ma bata dasu sai yan na sawa a tsakar gida, lokacin data je kicin d'in gwaggo har ta had'a wadda zata kaimata tana ganinta ta washe bakin jin dad'in ganin yan matanta yau ta fito tsaf da ita duk da ba wata kwalliya tayi ba iya mai kawai ta shafa sai kayan data sa sosae ta shiga yabon kayan tana sunyi mata kyau sosae ita dae shiru tay tana bin ta da ido, d'aukko mata kwanon dinner set mai d'an girma dake a rufe gefe tay tace gashi nan ta kaimata.

Kasancewar Weekend ne gaba d'ayansu suna zaune a falo duk kaya ba masu nauyi bane a jikinsu Haisam da Fanan na kan 3 seater ya jingina a k'arshen kujerar Fanan kuma na kwance ta d'aura kanta kan kafafunshi Hajiya na akan 2 seater gaba d'aya idanunsu na akan tv suna kallon wani Indian film a Bollywood Fanan d'ince ke fassara masu abunda ake cewa don ta iya indiyanci sosae Musamman akwae lokacin da suka ware suna koyonshi acan, da yar sallama ta shigo Falon saidai ba wanda ya jita hakan yasa ta tsaya idonta akan Haisam wani abu take ji na bin jikinta ga zuciyarta dake bugawa da sauri da sauri ta kasa d'aga kafarta ta idasa shiga ciki kaman ji yay idanu na yawo a kansa hakan yasa ya d'an juyo suka had'a ido da ita shima kallon ya bita dashi from head to toe kafin ya tsaida idon cikin nata suna kallon juna can taji cikin cool voice dinshi yace "Zaraah ki shigo mana" Maganar da yay ce tasa duk suka juya suka kalli entrance d'in koda Fanan tayi arba da Fatuu tsaye da sauri ta yunk'ura ta mik'e ta nufeta ganin haka yasa Fatun nufo cikin falon suka had'e gaba d'aya ita da kwanon da take ruk'e dashi ta had'asu ta rungume tana Fad'in "am so so Happy Sis Zarah kin samu Lafiya sosae" d'agowa tay ta amshi abunda ke hannunta ta rungume a hannunta guda d'ayan kuma ta kama hannunta suka nufi ciki, a Sofa d'in da suke zaune ta zaunar da ita can d'ayan gefen ita kuma ta zauna tsakiya ta aje kwanon k'asa gabanta,
"Hajiya Ina kwana" ta fad'a a sanyaye hajiya dake kallonsu tana Murmushi tace "Lafiya lou Fateema kin yi kyau sosae, ya k'arfin jikin?" da sauki ta amsa mata kafin ta juya ta gaida Haisam da shima kallonsu yake ya amsa fuska a sake yay mata ya jiki shima tace mashi da sauk'i,maido idon tay kan Fanan da ta d'aura hannunta guda kan k'afafunta tana ta sakar mata Murmushi, itama gaidata tayi ta amsa tace mata tayi kyau sosae godiya Fatun tayi mata ta kayan tace basai tayi wannan ba takai hannu ta zame gyalen kanta ganin yadda gashin yake ba gyara tace mata tasan saboda bata lafiya ne bata gyara ba yanzu tunda ta samu sauk'i yakamata a gyara zatafi jin dad'inshi ita dai jinjina mata kai kawae take,
"To ke an kawo man abu kin tasa a gaba ki mik'o man in ga mi na samu haka" Hajiya dake kallon fanan ta fad'a aikuwa a hak'ik'ance tace "ba naki ne ba nawa ne" yar dariya hajiya tayi tace "hak'ilo, yanzu yaushe kika ji ance naki ne" kallon Fatuu tayi tace ita ta kawo mawa ko
Showing 12001 words to 15000 words out of 113043 words