mik'a hannu ya d'auki abincin nata ya k'ara mata cikin nashi ya maida mata tana dae ta kallonshi bayan ya aje ya kalleta yace yar rigen cinyewa zasuyi tana jin haka ta waro ido alamar mamaki tana guntse Murmushi wato abunda ta ta6a yi da Hajiya a gabanshi shine yace suyi da alama dae duk rayuwarsu da ita bai manta ba, alama yay mata na su fara ta kai hannu ta d'auki Fork d'in ta fara ci, tun tana ci a hankali har ta fara sauri sai gashi ta wuce shi ganin hakan yasa ya fara d'iba da yawa saidae rashin sabo da yin lomar yasa da ya kai Abincin wurin bakinshi duk sai ya zubo Allah ma yasa riga mai duhu ce a jikinshi daba k'aramin 6aci kayanshi zasu yi ba, Fatuu ko mi zatayi in ba Dariya ba sosae take kyalkyata mashi dariya ba 6ata lokaci sai gashi ta cinye nata lokacin nashi da saura da d'an yawa, aje fork d'in yay yana kallonta sai faman Dariya take mashi harda d'an kwantawa bata ta6a tunanin zaice suyi hakan ba, baisan ko shi kadae ke ganin hakan ba amman ba k'aramin kyau dariya ke mata ba hakan yasa sai yay ta kallonta wani lokacin in tana yi,hannu ya kai kan kujera ya d'aukko wayarsa yana dubawa can ya d'ago yay mata alamar ta matso da hannu ta d'an matsa kusa dashi kawae sai gani tay ya d'aga wayar ashe Camera ya shiga da d'an mamaki ta juya ta kalleshi don tasan ba ma'abocin son yan d'auke d'auken hotuna bane, alamar ta kalli Camera d'in yay mata da ido ta juya har zai d'auka kawae tasa dariya ganin taliya a gaban rigarshi a haka ya d'auki hoton kuma yay kyau sosae bayan ya aje wayan yace ko zata idasa sauran Abincin nashi tay mashi wani kallo tace Allah bata yarda ba bashi yace ai yar rigen ba dole shima ya cinye ya jinjina mata kai yaci gaba da ci har ya cinye, bayan ya sha tace lemun fa yace ya bar mata daga haka ya mik'e alamar zai tafi itama ta mik'e suka fito daga falon tare saida taje ta sanar ma gwaggo ta fito sukae sallama sannan suka fita tare, A daidai shagon Amadu ya tsaya yace mata ta koma dare yayi tace to ya juya ya tafi tay tsaye tana kallonshi yayin da sautin busar sarewa na wak'ar india ke tashi bada k'ara ba sosae daga cikin shagon Amadu lokaci guda idanunta suka d'an ciko da kwalla da sauri ta maidasu ta juya ta shige gida. Yana isa part d'inshi wayarshi tay k'ara ya duba mai kiran yaga Hajiya ce bayan yay picking take tambayarshi k'ara fita yay bai shigo yaci Abinci ba yace mata yaje gidansu Zarah ne kuma yaci Abinci acan daga haka sukae ma juna saida safe ya wuce Bedroom bayan ya rage hasken parlon, yana shiga ya aje wayar kan side drawer ya wuce cikin laundry duk da bai jima da yayi wanka ba bayan ya dawo gym saida ya k'ara yin wani saboda Abincin daya zubar mashi a jiki, sanye da bathrobe ya fito yana tsane gashinshi da wani farin short towel ya nufi cikin Bedroom din, shiryawa yay cikin Sleeping dress yasa turare ba mai k'arfi ba don su kansu kayan da ya sa sakin k'amshi suke ya goga roll-on kafin ya nufi wurin switch ya kashe hasken d'akin ya kunna bedside lamp guda daya ya haye gadon yana kallon ceiling lokaci guda zuciyarshi ta fara tariyo mashi abunda ya faru tsakanin shi da Fatuu, Murmushi kawae yake saki yana jin zuciyarshi Fresh can ya kai hannu ya d'aukko wayarshi,hoton da suka yi da ita ya bud'o ya k'ura mata ido yana kallon yadda ta washe baki tayi Dariya dimples d'inta sun lotsa sosae, murmushi kawae yake saki kafin ya maida wayan ya aje ya lumshe ido.....................
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wannan no 09013804524._
Domin karanta cikakken Littafin sai ku danna bulun Rubutun dake kasa ko kuma hoton dake kass ππππ
*ASM Bk2014*
*πA SANADIN MAKWABTAKAπ*
_*(Love and Destiny)*_
_*BY ZAINAB LALUHπ²*_
~(Oumm Imam)~
Book 2
Bonus Page 14
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
.......Tana komawa cikin gidan Falo ta nufa anan ta iske gwaggo zaune ta bud'e Akwatunan duka ta rafka uban tagumi tana ta kallon kayan sai kace lefe koda Akwatunan basu da yawa amma kud'in su dana kayan ciki zasuyi na wasu akwatinan lefen da suka fisu yawa itama Fatun tsaye tayi cike da Al'ajabin ganin uban kayan don ba abunda babu na buk'atar mace da ake sakawa a lefe kama daga d'inkakkun kaya da wanda ba'a d'inka ba,Cosmetics Undies takalma da dae sauransu, da alama dae bakin gwaggo ya mutu ta kasa cewa komae sai jinjina kai kawae take can ta kalli Fatun tace ta kama sukai d'akinta tace to ta matsa gwaggon ta tashi suka maida su d'akin nata, sai lokacin bayan gwaggo ta fita ta zauna ta fara dubawa nan take ta fara ayyana ina ma ace lefen aurensu ne a hankali siraran kwalla suka fara gangaro mata k'arshe ma sai ta kife kanta kan kayan ta shiga raira kuka ba mai sauti ba,
Washe gari da safe yazo d'aukarta don kaita Makaranta yana yin horn biyu ta fito cikin shiri ta zagaya ta bud'e kopar ta shiga bayan ta rufe kopar ta juya suka had'a ido ya jingina kanshi da headrest, da d'an Murmushi ta gaishe shi ya amsa fuska sake yace "How was ur nyt?" ta bashi amsa da "Alhamdulillah" ya jinjina kai daga haka yaja Motar suka tafi saida suka biya aka d'auki Haulat kaman kullum kafin suka wuce, ba laifi ta d'an saki jiki yau jefi jefi yake mata Magana tana bashi amsa Haulat dae nata bin su da ido acan k'asan ranta tana ayyana Fatuu ta warware ne ko ya akai ta saki jiki haka, bayan ya aje su ya basu kudin break tana Murmushi ta amsa tayi mashi godiya har zai ja Motar ya tsaya ya kirata bayan taje side d'in da yake ya tambayeta karfe nawa zasu tashi ne tace sai yamma yace to zaizo ya daukesu, akan hanyarsu ta zuwa Class ne Haulat ke tambayar Fatun game da warwarewar da taga tayi tace zata fadi mata in sunje aji, saida akai break ne ta bata labarin yadda sukae dashi sosae taji dadi da bata fad'i mashin ba ta kuma yaba da kirkin haisam d'in daya damu da damuwarta har haka ta tayata farincikin kayan data ce ya siya mata saidae bata ji dad'in jin Fatun bazata bikin ba tace mata "amman Fatuu miyasa zaki k'i zuwa bikin Ya Haisam ne fa ni kaina da za'a barni wllh ina son zuwa saidae nasan babanmu bazai barni ba amman ke tunda nasan su gwaggo ma zasu ai da kinje kawae tunda dae kin hakura dashi"
"Don na hakura ce maki akae na daina sonshi ne Haulat, har yanzu ba abunda ya canja kawae ba yadda zanyi ne shiyasa gwara ma kar naje naga abunda zai k'ara tarwatsa man Zuciya" ta k'arasa Maganar da damuwa kan fuskarta haulat tace ta fahimceta daga haka bata k'ara ce mata komae ba game da hakan bayan La'asar Haisam ya dawo ya d'aukesu, lokacin daya ajesu ya wuce gida yana zuwa bakin Gate Officer ya tsaidashi bayan ya tsaya ya nufo Motar lokacin ya sauke glass d'in,
"Barka da dawowa Yalla6ai" kai ya jinjina mashi yaci gaba "dama kana da bak'o ne" tambayarshi yay ina bakon yake ya nuna mashi can gefe da hannu ya d'an lek'o kanshi ya kalli direction d'in da Officer ke nunawa, wani dattijo ne ya manyanta sosae cikin shiga ta kamala yana tsugunne gaban mashin d'in shi Jincheng yana ganin fuskar Haisam ya mik'e yana kallonshi da d'an Murmushi, maida kan Haisam yay yace ace ya shigo daga haka yaja Motar ya shige, lokacin da Haisam ya fito daga cikin Motar dattijon ya shigo yay mashi alamar ya aje mashin d'in cikin wurin, da sauri ya nufo shi bayan ya parker mashi d'in nashi ya d'an rankwafa yana kokarin gaishe dashi ya mik'a masa hannu suka gaisa kafin yace su shiga ciki yace to saida ya koma ya d'aukko wata leda gari yayi zafi a jikin mashin d'in kafin ya bi bayanshi suka nufi part d'in Haisam, suna shiga ya bi parlon da kallo baki bud'e tunda yake bai ta6a shiga irin falon ba shi ko ganin irinshi ma a tv bai ta6a ba ga ni'imtaccen sanyi had'i da daddadan kamshi da ke kaima hancinshi da sauran sassan jikinshi ziyara, nuna mashi bangaren Armchairs yay alamar ya zauna ya nufi wurin ya zauna a takure, shiru suka yi Haisam bai mashi Magana ba shima haka sai dae faman murmushi yake can ya fara Magana yace "Yalla6ai baka gane ni ba ko?" Kai Haisam ya d'aga mashi alamar eh,
"Allah sarki ay dayake lokacin da tsawo sosae, Sunana Malam Garba kuma nine mutumin daka ta6a taimako ka biya masa kud'i a caji Office shekaru kusan ukku da suka shud'e tun lokacin naso nayi maka godiya sosae saidae ban samu halin hakan ba don baka d'aga waya dana rok'i Officer ya kiraka dama saida ya fad'a man bazaka d'aga ba karshe ya nuna man don Allah kai man in gode ma Allah kawae" d'an dakatawa yay Haisam dae nata kallonshi fuskarshi a sake don yanzu ya gane shi,
Malam Garban ya d'aura da fad'in "Wato Yalla6ai sanadiyyar taimakon da kayi man na samu bud'i sosae, da yar trader na bud'e ma yarona habu Allah yasa ma abun Albarka yanzu ta Zama k'aton shago Alhamdulillah yanzu ba matsalar Abinci a gidana sannan karatun yara ma ana kamantawa yadda ya dace shi kanshi wanda yay silar zuwana caji Office d'in Allah ya shiryar dashi ya daina d'aukar kayan Mutane yanzu ya natsu sosae suke Kula da shagon ni kuma naci gaba da sana'ata ta faci wadda dama injin d'inne ya lalace na daina sakamakon taimakon kudi da kayi man na canja wani wannan dalilin ne yasa na kasa hakuri don ban manta da abunda kayi man ba saboda ba abune da zan iya manta ba dama Officer ya fad'a man a wurin kakarka kake da zama tun wanccan lokacin hakan yasa ban sha wata wahala ba wurin nemo ka don ita d'in sanannace, a tak'aice dae Yalla6ai Nagode, Nagode Allah Ubangiji ya saka maka da mafificin Alkhairinsa ya dawwamar dakai cikin Farinciki kaman yadda kake saka bayinsa Farinciki, Allah ya jik'an Magabata ya raya maka zuria......" kasa karasawa yay sakamakon muryarshi da ta karye idanunshi suka cicciko da kwalla",
Sigh Haisam yay Calmly yace "ai ba wani abu bane ka d'auka rabonka ne a hannuna ba sai ka damu ba" yar dariya yayi yana kokarin mayar da k'wallan yace "duk da hakan ai ance yaba kyauta tukuici, ko don dakon rabon da kayi ai na gode maka" d'an murmushi Haisam yay baidae cemashi komae ba can ya mik'e ya nufi Fridge ya d'aukko lemu da glass cup ya dawo saida ya d'aukko c-table bayan ya tsiyaya ya aje mashi yace bismilla ya sha yay godiya kafin ya daukka ya fara kur6a, bayan yasha kaman rabi ya ajiye ya kai hannu gefenshi ya d'ago da ledar daya zo da ita yace "yalla6ai wannan daga cikin kayan shagonne su Omo, Sabulu Tolen paper (toilet paper) da dae sauransu na kawo a ba iyali" still da murmushi kan face d'inshi yace "Ok angode sai dae a kaima Hajiya"
"Af,af d'ana ba dae ba iyalin ba?" ya tambaya da d'an mamaki shiru kaman bazai yi Magana ba sai kuma yace "Yea but Next week ne zanyi auren" ruke ha6a yay yace "iko sai Allah kace da sati mai zuwan nazu dana taras ana tsaka da hidima kenan",
"Ba anan ne za'ai ba Abuja ne" idon Malam Garba a kanshi yace "Allah sarki Allah ubangiji ya kaimu ya nuna mana, aikuwa yakamata nima inje d'aurin auren nan"
"No, ba sai kayi hakan ba" ya bashi amsa a takaice yace "d'ana ba dae baka son naje d'aurin auren naka ba" da sauri yace mashi a'a kawae basai ya takura kanshi ba in yayi mashi Addu'a ya isa yay yar dariya yace" shikenan tunda kace hakan amma wllh ba wata takura ai Alhamdulillah Allah ya bud'a, Addu'a kuma kullum cikin yi ake wllh ba zancen ganin idonka ba aduk sallar da zanyi ta Farilla kota Nafila kana cikin Addu'oi na ko bama a salla ba" sosae Haisam yaji dad'in Maganar yace mashi ya gode,
Shiru suka d'anyi can Malam Garban yace "Yalla6ai bari in barka ka huta ka dawo aiki kuma na rik'e ka, saidae in ba damuwa ina son in gaisa da hajiyar taka,amsa mashi yay da Owk ya kai hannu gefenshi ya d'auki wayar shi yay Sending call, Tk ya kira saida ya tambayeshi yana gida yace mashi eh yace yazo part d'in nashi, bada jimawa ba sai gashi ya shigo da sallama ya gaida Haisam kafin ya juya ya gaida bak'on umarnin kaishi wurin Hajiya ya bashi yace to Malam Garban ya mik'e bayan ya dau ledan yace bari akai ma Hajiyan Haisam ya d'aga mashi kai, saida ya tsaya bakin kopa ya k'ara mashi godiya da Addu'oi sannan ya fita,suna fita Haisam din ya kira Hajiya tunkan tay mashi Maganar ya baizo yaci Abinci ba as usual ya rigata fad'in ga bak'o nan Tk zai kawo daga haka ya katse kiran ya mik'e ya nufi hanyar Bedroom.
Lokacin da suka shiga parlon Hajiyar na zaune kan 2 seater idanunta sanye cikin glasses ta juyo tana amsa masu sallamar da suka yi Tk ya nufeta yace ga bak'o nan inji Ya Haisam ta jinjina mashi kai ya juya ya fita ta maida idonta kan Malam Garba da yay tsaye tace "ka zauna mana kayi tsaye" fuskarshi d'auke da faffad'an murmushi ya amsa mata ya nufi one seater ya zauna Matar da yake gani a talabijin ko yajita a Radio yau gashi gata ba k'aramin dad'i ya ji ba,bayan ya zaunan ya d'an sunkuya yana gaishe da ita ta amsa fuskarta a sake shiru ya biyo baya can yaji tace "to bak'o daga ina don ban wayeka ba" tay Maganar tayi mashi k'uri ta cikin gilashin, gyara zama yay ya fara mata bayanin kanshi da abunda ya had'a shi da Haisam,
"Allah sarki da yake bamu ta6a ma yin Maganar dashi ba tunda ba fad'in abu yake ba in yayi" jinjina kai yay yace "Allah Akbar kaji mai yi don Allah, Allah ya saka da mafificin Alkhairinsa ya k'ara sutura" Hajiya ta amsa da Amin tana murmushi tace "ai Malam Garba da baka wahalar da kanka ba ma" da sauri yace "wllh Hajiya taimakon da yay man ne ya tsaya man a raina har mafarkinshi nike in ban zo nayi mashi godiyar ba bazan samu natsuwa ba" yar dariya hajiyar tayi ya fara bata labarin irin bud'in d'aya samu sanadiyyar taimakon da Haisam d'in yayi mashi tana ta fad'in Allah sarki an gode ma Allah, can ya mik'e ya kai ledar kayan gabanta yace ga irin kayan shagonne ayi amfani dasu ta kai idonta kan ledar tana fad'in harda hidima haka to an gode, komawa yay ya zauna yayi mata zancen bikin Haisam daya fad'i mashi tace eh in Allah ya kaimu juma'a mai zuwa ne da tun satin daya wuce ma zasu tafi to wai akwae uzurorin da bai kammala dasu bane saboda ba zai dawo nan ba to yanzu sai in Allah ya kaimu jibi zasu tafi yace ashe da rabon zai iskesu tace aikuwa, kokarin mik'ewa ya fara zai tafi da sauri Hajiyar tace "Malam Garba ya zaka tafi ko ruwa baka sha ba mun tsaya munata Magana bansa an kawo maka ba ka zauna sai ka sha ruwan zumunci tukunna, komawar yayi don bai iya yi mata gardama a ranshi kuwa yanata jinjina kirkinta yadda ta sake mashi sai kace dama sun san juna, Saude ta kwala ma kira tun kafin tazo cikin falon ta bata Umarnin kawo mashi ruwa da Abinci ta juya kitchen, bada jimawa ba ta kawo kayan Abincin cikin babban tray saida ta kinkimo sofa table ta kawo gabanshi sannan ta d'aura tray d'in tay Serving nashi bayan ta gaishe shi tace aci Lafiya yay mata godiya Hajiya ma ta mik'e tana fad'in bari ta bashi wuri ya samu sakewa ya tabbatar ya ci ya koshi ya amsa mata da to yana dariya, sosae yaji dad'in Abincin don Saude badae iya Abinci ba Musamman farfesunta in Mutum nasha kamar ya cinye da hannunshi don dad'i da wannan ta siye hajiya, bayan ya gama Saude taje ta sanar ma Hajiya ta fito don suyi sallama ta bashi kud'i tace ya sha mai yay mata godiya gami da Addu'oi ya tafi, Malam Garba bai tashi shan mamaki ba saida ya je parking space don d'aukar Mashin d'inshi nan ya iske Tk ya kawo mashi kwalin taliya da Macaroni harda yar galan d'in mai baki bud'e ya bi kayan da kallo kafin ya sauke idanun kan Tk dake ta washe mashi baki tun kafin yace wani abu ya riga shi fad'in Hajiya ce tace a kawo mashi kawae sai yasa ma Tk kuka yana fad'in wad'annan wane irin Mutane ne haka dama har yanzu ana samun Mutane masu tsananin kirki haka Tk yace "Wllh haka suke ni kaina nan daga Almajiri aka mayar dani d'an gida ba abunda ba'ai man wanda ake ma d'a Abinci,Sutura,Karatu da dai sauransu har iyayena ma ba'a barsu ba" waro ido Malam Garba yay jin wai shi Almajiri
Showing 48001 words to 51000 words out of 113043 words
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wannan no 09013804524._
Domin karanta cikakken Littafin sai ku danna bulun Rubutun dake kasa ko kuma hoton dake kass ππππ
https://aihausanovels.com.ng/novel-document/a-sanadin-makwabtaka-book-2-complete-hausa-novel
πππππ

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17 Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38