mata, bayan kaman minti 30 suka dawo Fanan ce kawae ta shigo shi Haisam yana waje cikin Mota duk ciwon da Fatun keyi ya dameshi ganin lafiya lau suka dawo da ita amman har yayi tsanani haka, Artemether da paracetamol injection suka siyo, had'a allurar ta shiga yi bayan ta gama tayi mata har saida gwaggon tayi mamakin yadda ta tsaya tayi mata allurar don ita in zata yi mata wani lokacin sai tayi fama da ita da can ma da bata girma ba haka wani lokacin sai tasa Amadu ya ruke mata ita, bayan ta gama ta tambayi inda dustbin yake gwaggo ta mik'e ta amsa taje ta yado su ta dawo Fanan tace ma gwaggo yakamata taje d'aki ta shiga Net saboda sauro tace to, mik'ar da ita tayi suka nufi hanyar fita gwaggo na biye dasu ta tambayi ina d'akin da zata kaita gwaggo ta nuna mata dakinta suna shiga ta nufi gado da ita ta taimaka mata ta kwanta sai faman sannu take ce mata kai kawae take d'aga mata ita kanta Fatun bata san mi take ji game da Fanan d'in ba ita kawae abunda ya dameta shine Ya Handsome bai sonta ba zai Aureta ba, a hankali kwalla suka fara ziraro mata daga kwancen ta juya masu baya yadda bazasu ga Fuskar tata ba,
"Granny ni zan tafi Ya Haisam na jirana gobe in sha Allah zanzo in yi mata second dose" godiya sosae gwaggo ta shiga yi mata tana cewa Allah yasaka da Alkhairi ya bar zumunci ta amsa da Amin juyawa tayi ta dafa jikin Fatuu tace "Sis Zarah Allah baki lpy kinji" kai ta d'aga mata kawae ta juya ta tafi gwaggo tayi mata rakiya har zaure saida ta lek'a ta k'ara yi ma Haisam godiya kafin ta komo daki wurin Fatuu, a gefen gadon ta zauna tana kallonta yayin da take ta sak'e sak'e aranta game da silar ciwon Fatun tsoronta kar ace abunda take tunani ne sanin inda suka je ciwon na iya tasar mata, yin wannan tunanin yasa da sauri ta girgiza kai a fili tace "in sha Allahu bama shi bane" dafata tayi tace mata sannu ta d'aga mata kai ta tambayeta ko tana son wani abu ta girgiza mata kai alamar a'a tace "to tashi ki rage kayan jikinki bari in je in d'aukko maki wanda zaki canza" bayan taje d'akinta ta d'aukko mata kayan bacci da taimakon gwaggon ta tashi ta canja kafin ta koma ta kwanta gwaggo ta lullube mata rabin jikinta tasa mata Net.

Bayan sunyi parking Motar a parking space suka fito sukai ma juna irin rukon nan na turawa wato a sak'ala hannu suka nufi part d'in Hajiya, lokacin da suka shiga ba kowa a falon hakan yasa suka wuce bedroom dinta lokacin har ta kwanta amman bata yi bacci ba wutar d'akin ma a kunne take da alama jiransu take, jin motsin shigowarsu yasa ta d'ago ta kallesu suka nufeta suna Murmushi suka zauna a bakin gadon,
"Ai nayi zaton Zarah ta rik'e ki acan zaki kwana don nasan dole zatayi farinciki da zuwanki" da sauri Fanan ta girgiza mata kai da yar damuwa tace "Sis zarah ba lpy dat's why we stayed a bit long" yunkurawa Hajiya tayi ta tashi zaune da mamaki kan Fuskarta tace "Ba lpy kuma miya sameta" fad'i mata abunda ya faru Fanan din tayi harda uban aman da tayi Hajiya tasa salati ta kalli Haisam dake saurarensu tace "dama bata lpy kuka dawo" kai ya girgiza "No lafiyanta lou wai bayan ta shiga gida tace ma grandma d'inta tana jinta abnormal and kanta na mata ciwo sosae" jinjina kai Hajiya tayi da yar damuwa akan fuskarta tace "tohhh, Allah ya kyauta yasa ba mutanenta bane kuwa tunda anje wurin ruwa" cikin rashin fahimta duk suka kalleta Fanan ta tambayeta suwaye mutanenta,
"Jinn nike nufi" waro ida Fanan tayi a rud'e tace "Ajanu!" yadda tayi Maganar har saida Hajiya ta d'anyi dariya ta jinjina mata kai alamar eh,
"Dama tana dasu?" Haisam daya kasa hakuri ya tambaya, Hajiyar tace "Eh mana amman basu kada ita yanzu saidai su sata ciwo, tama dad'e gaskiya bata yi ciwon da take irin nasu ba" jinjina kai yay taci gaba da cewa "ai na Mahaifiyarta ne suka komo kan Fateemar amman basu cutar da ita gaskiya sai rashin ji da suka saka mata" wani d'an guntun Murmushi haisam d'in yay ya furta "the whole things make sense now",
"but su dama basu son aje wurin ruwa?" Fanan da duk alamun tsoro ya bayyanar mata ta tambaya dariya hajiya tasa tace "ai kinsan su ko ina akwae su ba iya wurin ruwan ba saidae akwae inda zaki ga sunfi zama kaman toilet to wurin ruwan ma matattararsu ce, kai bamma tunanin su ne gaskiya k'ilan dai ta de6o sanyi ne kawae shine ya tado mata zazzabin" jinjina kai Fanan tayi tace Allah dai ya bata lafiya hajiya ta amsa mata da Amin, mik'ewa Haisam yay yace zaije ya kwanta Hajiya tace "Allah ya bamu Alkhairi" kokarin mikewa Fanan ta fara yi tace bari ta rakashi yace tay zamanta tace ko bakin kopa ne, suna fitowa yace ta koma sai kawae ta jingina bayanta da bango tana mashi wani kallo mai cike da tsantsar kauna hannu ya kai ya d'an shafi cheek d'inta da wata irin Murya ya furta mata "I luv u Sweetheart" hannu tasa ta dafa hannun nashi tana Murmushi tace "dat's my breath babe" yar dariya yayi ya fara kokarin wucewa ta kamo hannunshi ta baya ya juyo da narkakkun idanu tace "Gud nyt nd Dream of me" lumshe ido yay kafin yace "Always" d'ago hannun tay tayi mashi kiss a bayan hannun kafin ta saki ya tafi, saida ya kai bakin kopar fita ya juya ya kalleta yay mata alamar ta shiga cikin d'aki da kanshi,blowing kiss tai mashi kafin ta d'aga hannu tay mashi bye bye ta juya ta shige..........

Domin karanta cikakken Littafin sai ku danna bulun Rubutun dake kasa ko kuma hoton dake kass πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

https://aihausanovels.com.ng/novel-document/a-sanadin-makwabtaka-book-2-complete-hausa-novel

πŸ‘†πŸ‘†πŸ‘†πŸ‘†πŸ‘†

*ASM2002*

*πŸ’–A SANADIN MAKWABTAKAπŸ’–*
_*(Love and Destiny)*_



_*BY ZAINAB LALUHπŸ“²*_
~(Oumm Imam)~

Book 2

Bonus Page 2


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*




..........Washe gari da suka tashi ta d'an ji sauk'in jikin nata kawae yanzu fargaba ce tafi damunta hakan yasa duk bata jin dad'in kirjinta bayan tayi sallar Asuba komawa tay tayi lamo kan gado sai sak'e sak'e take aranta, yanzu shikenan ta rasa ya Haisam, tana ji tana gani zai yi auranshi ya tafi ya barta, haka dai take ta tunane tunane tana matse k'wallan dake zubo mata ba tare da gwaggo ta ankare ba don ita duk tunaninta bacci Fatun ta koma, Wuraren k'arfe tara saura tazo ta tashe ta tayi karin kumallo, bayan taje tayo brush ta zauna don yin breakfast d'in saidai sam tama kasa cin komae don bata jin dad'in bakinta gwaggo dake zaune gabanta ta lura da hakan tace mata ta daure in taci sai tafi jin dad'in jikinta ta dai d'aga mata kai kawae, da k'yar ta d'an tuttura ta mik'e zata kwashe kayan gwaggon tace ta bassu taje ta kwanta in ta gama zata d'auke, bayan ta gaman ta kwashe komae ta kai Kitchen bata dawo d'akin ba saida ta had'a ma fatun ruwan wanka a toilet tace ta daure taje tayi ko ta ji k'arfi, d'akinta ta koma ta cire kayan jikinta ta d'aura towel ta yafa mayafi kafin ta fito ta nufi toilet walking slowly don duk jikinta ba k'arfi, bayan ta fito doguwar rigar material kawae ta zura ta haye gado taci gaba da tunane tunanenta,

Wuraren k'arfe 11 Fanan ta farka tun bayan sallan Asuba data koma tana saukko da k'afafunta k'asa idanunta suka sauka akan wata yar guntuwar farar takarda dake ajiye kan bedside drawer, hannu ta kai ta d'auki takardar tana duba rubutun dake jiki kamar haka,

_Went to work_
_Luv u_

Shine rubutun dake ajiki Murmushi ta saki sanin Haisam ne ya ajiyeta, baki ta kai paper d'in ta manna mata kiss had'i da furta Luv u too Babe,maidata tayi inda ta d'auketa ta ajiye ta wuce toilet don yin wanka bayan ta fito ta shirya cikin skinny jeans blue da farar top bayan ta gama shiryawa ta dauki wayarta ba tare data rufe kanta ba ta saki brown gashinta ya zuba gefe da gefen fuskarta ta nufi Parlor ganin ba Hajiya a falon yasa ta nufi d'akin Saude tana kwance kan katifa tana huta gajiyar aikin gidan data gama bada jimawa ba, zazzak'ar muryarta saude ta jiyo tana yi mata sallama hakan yasa ta tashi zaune da sauri suka had'a ido ta sakar mata Murmushi itama sauden Murmushin take mata don ba k'aramin burgeta take ba,
"Ina kwana" Saude ta gaidata ta nufo inda take ta zauna gefen katifar da Murmushi tace "kin tashi lpy ya aiki" tace "Alhamdulillah" shiru suka d'anyi kowa Murmushi ne akan fuskarshi can Fanan d'in tace "Hajiya ta fita?"
"Eh bata dad'e da fita ba taje wurin aiki ne" jinjina kai tayi sauden ta kuma cewa "ga breakfast can na shirya maki a kan table",
" Owk thanks",
"Babe ya shigo kuwa yayi breakfast?" ta tambaya tana kallon sauden,shiru ta d'anyi don bata gane babe d'in da take nufi ba gane hakan yasa fanan d'in cewa "I mean Ya Haisam" da sauri tace mata "eh ya shigo d'azun da shirin zuwa aiki ya shiga d'akin Hajiya kafin ya fito ya tafi,
"yayi breakfast?" kai ta girgiza mata "a'a ai bai yin breakfast yake tafiya gaskiya sai dai wani lokacin in hajiya ta matsa mashi yake dan yi shima dai kad'an" jinjina kai tayi tace "har yanzu baison cin abinci ko?" yar dariya Saude tayi kafin tace "eh to gaskiya yana ci amman fa ba sosae ba shima dai sai Hajiya ta matsa mashi yake d'an ci da d'an yawa" jinjina kai ta sake yi ta fara kokarin tashi Saude tace "Breakfast d'in zakiyi inzo in zuba maki?",
"No don't worry zanyi serving kaina"
"Don Allah ki bari kar aikin yayi maki yawa" d'an waro ido tayi alamar mamaki tace "miye ne aiki ciki just serving Myself ai kene mai yin aiki so just relax" tayi Maganar tana mata alamar ta kwanta da hannu ta juya ta nufi kopa Saude ta bita da ido tana Murmushi aranta take ayyana kirkin yarinyar yayi yawa sam ba halinsu d'aya da yar'uwarta ba, tana fitowa bata nufi dining don sai taji bata son yin breakfast d'in ita kad'ai, Bedroom d'in Hajiya ta koma ta d'aura boyfriend jacket bak'a mai d'an ratsin fari ta yafa d'an k'aramin bak'in gyale ta fito, gidansu Fatuu ta nufa wayarta ruk'e a hannunta tana zuwa bakin gate ta tsaya suka gaisa da su Officer tana ta Murmushi suma duk suka washe mata baki bayan ta wuce ne su kau yabonta, tana shiga gidan ta tsaya bakin kopa ta rafka sallama da zazzakar muryarta "Salamu Aleeikum" tana niyyar k'ara yin wata gwaggo ta fito daga cikin d'akinta tana amsa mata sallamar suna ganin juna suka saki Murmushi gwaggon ta nufeta tana Fad'in "Ah ya kika tsaya anan ki shigo mana y'ata" nufota tayi suka had'e a tsakar gidan d'an side hug tay ma gwaggo tace "ina kwana granny" da fara'a tace "lafiya lou y'ata ya gajiyar tafiya kuma"
"Babu shi" ta bata amsa gwaggon na niyyar ce mata su shiga falo tace "ina Sis Zarah ya jikinta fa" tace mata da sauki sosae tana cikin d'aki "owk bari in ganta" tare suka juya suka nufi d'akin gwaggo Fatuu da duk abunda suke tana jinsu tana jin sun nufo d'akin tayi saurin juyawa yadda baza'a ga fuskarta ba ta runtse idanunta sosae, suna shiga d'akin Fanan ta nufi gadon ta zauna a gefe ta kai hannu tace "Sis Zarah" shiru bata amsa ba hakan yasa ta kalli gwaggo tace ko tana bacci ne, ita kanta gwaggon ta d'anyi mamakin ganinta haka don lokacin da Fanan d'in tayi sallama tasan ba a haka take kwance ba idonta biyu har suna ma d'an Magana da ita, matsawa tayi gaban gadon ta kira sunanta da d'an karfi ba yadda ta iya dole ta amsa mata sanin gwaggon tasan ba bacci ta barta tana yi ba,
"Ki tashi ku gaisa da Auntynki da tazo nasan jiya ba lalle ma in kin gane wacece ba kina cikin ciwo" d'an jimm tayi kafin a hankali ta yunk'ura ta tashi zaune ta kalli Fanan dake ta faman yi mata Murmushi murya can ciki tace mata "ina kwana, anzo lafiya" hannu ta kai ta dafa shoulder d'inta tace "Lafiya, ya jikinki" amsa mata tayi da sauki tace Allah ya bata lpy, ganin yadda take ta faman yi mata Murmushi yasa itama da kyar ta d'anyi mata na yak'e,
"How are u Feeling Now?" ta tambayeta k'asa k'asa tace mata "da sauki sosae kawae bana jin karfin jikinne" still hannunta na asaman kafad'arta tace mata ta kwanta, komawa tayi ta kwanta dama bata so tashin ba cike da kulawa take kallonta kafin ta maido kallon kan gwaggo dake zaune ta tambayeta tayi breakfast tace mata eh ta d'an ci kad'an, fira suka shiga yi da gwaggon kai kace dama can sun saba tace ko ta kawo mata wani abu taci bata kaiga d'aura abincin rana ba tace mata a'a ta barshi can gwaggon ta mik'e tace bari taje ta d'aura girki fanan d'in tace mata ba damuwa bayan ta fita wayarta ta shiga latsawa tana yi tana d'an d'agowa ta kalli Fatuu can ta kai hannu ta dafa kafafunta tace "Sis Zarah am really worried about ur condition, Allah ya baki lafiya kinji" a hankali ta ware idonta kan Fanan d'in dake kallonta cike da damuwa wani iri taji don ita kanta bata ta6a tunanin zasu kasance haka da Fanan ba yadda suka shak'u sosae har ta k'agara ta ganta a zahiri saboda yadda take nuna mata k'auna bata ta6a tunanin zuwanta zai jefata a matsala haka ba, a hankali wasu yan siraran hawaye suka zubo mata tana k'okarin gogewa fanan d'in ta matsa da sauri tana Fad'in ta daina kuka zata samu lafiya bada jimawa ba in sha Allah wai akace rashin sani yafi dare duhu, wayartace ta fara ringing takai idonta kan screen d'in ganin mai kiran nata yasa ta saki Murmushin da tun bata d'auka ba Fatuu ta yanke wanda ya kirata, cikin murya mai cike da tsantsar kauna bayan ta d'auka tace,
"Hlo Babe, how Work?" ta tambaya, on the other hand ya bata amsa da lafiya kafin ya tambayi tana ina tace mashi tazo ganin Zarah ne ya tambayi ya jikinta tace da sauki,
"am on my coming back now" ya fad'a, d'an ware ido tay ta cire wayan daga kunnanta ta duba time kafin ta maida tace mashi amman still Working hours ne ya akai zai dawo yace saboda bata yi breakfast ba yar dariya tayi tace waye ya fad'a mashi bata yi breakfast ba yace a jikinshi ya ji, cigaba da fira sukae cike da kauna har ta tambayeshi ya taho da gaske yace eh yana driving ma suke wayan, duk Maganganun da turanci suke wayar fatuu na saurarensu a hankali ta juya ta kalli d'ayan bangaren d'akin ta shiga yin kuka sosae ta rufe bakinta da hannunta guda don kar sautin ya fita, har ya kawo kopar gidansu Fatun suna waya ta mik'e ta d'an ta6a kafafun Fatun tace zata je ta dawo, kai kawae ta d'aga mata ta juya da sauri ta fice, tana fita kopar gida taga Motarshi ta nufi d'ayan side d'in ta bud'e ta shiga suna had'a ido suka sakar ma juna Murmushi ya kamo hannunta ya rike yaja Motar da d'ayan suka tafi, suna shiga Falon Hajiya Dining suka wuce da kanshi yay serving nasu don shima bai ci komae ba awurin aiki cike da tsantsar kauna suka shiga ciyar da juna koda ya tashi komawa wurin aikin bayan sun gama marairaice mashi tayi wai ya tafi da ita gidan is so boring yace ai Hajiya bazata dad'e ba zata dawo amman ta k'iya dole yace taje ta shirya su tafi, bada jimawa sosae ba ta fito sanye cikin bak'ak'en Suit na mata kafafunta sanye da ankle strap farare irin takalman nan masu tsini sosae masu rufe diddigen k'afa da igiya sama da ake d'aure k'afa kanta ta yafa k'aramin bak'in gyale hannunta ruke da farar clutch bag data hau da rigar cikin da kuma takalmanta yayinda kunnanta ke sanye da yan kunne fashion silver masu matsiyacin kyau hannunta na hagu d'aure da agogon diamond sai d'aukar ido take ba k'aramin kyau tayi ba, idanunshi akanta ya d'an lumshe su yana binta da wani kalan kallo ta nufo shi tana tafiya irin ta wayayyun yan boko tana zuwa gabanshi ta tsaya tana Facing d'inshi tana wani kashe mashi ido yay d'an Murmushi kafin ya kai hannu ya kama kunnanta yace dama tazo da shirin takura mashi kenan ko ta fad'a jikinshi tana dariya a lokacin idanunshi suka sauka kan gashinta dake kwance kan gadon bayanta hannu ya kai ya cire gyalen ya nad'e gashin yadda bazai fito ba kafin ya d'agota ya fara nad'a mata gyalen, Allah sarki ashe ga inda Haisam ya iya nad'a gyale da Fatuu ke tambayarshi ya akai shi da yake namiji ya iya lokacin daya ta6a nada mata har tace kumatunta sunyi kaman an tura biredi, kama hannunta yay a nutse suka tafi.

Bayan Azahar Amadu ya shigo cikin gida daga Makaranta don yanzu a Poly yake Karatu don tuni ya kammala Secondary d'inshi kuma Haisam ne ke d'aukar nauyin karatun nashi shi da Tk don shima ya dasa HND bayan ya gama ND din da yake, d'akinshi ya bud'e don yanzu koparshi na a cikin gidan aka maidota lokacin da Haisam yasa aka gyara masu gidan sai aka
Showing 3001 words to 6000 words out of 113043 words