mata kai alamar eh, kuka ta fashe mashi da shi tana fad'in ashe bata hak'ura ba har yanzu fushi take da ita, side hug Amadu yay mata ya shiga rarrashin ta yana tayi hakuri a hankali komae zai wuce yasan dole zata zo ne koda bayan anyi auren ne can ta d'ago tace mashi Hajiyar Sanata fa itama bazata zo ba, da yar damuwa yace mata Hajiya bata lafiya ciwon kafafu take yanzu ko wurin aiki ma ba zuwa take ba amman taso ta zo koda taji gwaggo bazata zo ba har fushi tay da ita, sosae ya rarrasheta ya nuna mata tayi hak'uri wannan jarabawa ce daga Allah, kiran sallar Magrib yasa shi tashi yace mata ta koma ciki zai je yay salla ya dawo, zaune tay a cikin d'akin tana cigaba da matsar k'walla sai daga baya ta tashi ta nufi cikin gidan lokacin da taje d'akin su a k'urya ta iske Haulat na yin salla itama taje tayo Alwala tazo gefenta ta kabbara salla, bayan sun gama Haulat ta kalleta da Murmushi tana ganin yanayin fuskar Fatun tace "K'awata lafiya dai ko, idanun ki naga sun canja kuma dama naga har rama kin yi" kaman zata sa kuka tace "Haulat baki ji Auren dole za'a man bane?" da yar damuwa Haulat tace "naji Fatuu lokacin da innata ta kira waya can Nijar ta sanar da ni na matuk'ar girgiza da jin zancen tun lokacin nike kokarin kiran ki amman bata shiga daga baya ne na kira kawu Amadu ya fad'i man komae, na matuk'ar tausaya maki Fatuu wllh Allah ne shaida har kuka nayi sosae nace Ashe ba rabon dae kiyi karatu kuma ki auri wanda kike so" kuka sosae Fatuu ta fashe dashi tasa hijab d'in jikinta ta rufe bakinta don kar sautin ya fita itama Haulat kwallan ta fara yi ta shiga rarrashinta tana cewa tayi hakuri kowa a rayuwa da kalar kaddarar shi ita kuma wannan ce tata, cikin kuka tace "Haulat za'a man Aure ba tare da gwaggo ta zo ba Saboda tana fushi dani don na amince aman auren, nima don banda yadda zan yi ne amman wllh ban son Auren nan....." sosae taci gaba da yin kuka suna haka yadikko ta shigo a rud'e ta shiga tambayar ko lafiya Haulat tace ba komae Saboda gwaggo bata zo bane nan itama tasa baki suka cigaba da rarrashin ta tare suna ce mata dole gwaggo zatai fushi yanzu amman zata saukko ko ba yanzu ba, sai da aka kira sallar isha suka tashi suka yi Bayan sun gama ne Yadikko ta nuna mata kayan da su Haulat suka zo dasu Manyan bokitan su cin cin da dublan ne dasu zannuwan gado da labulaye harda kayan gara su buhun shinkafa biyu katan d'in Taliya da Macaroni suma bibbiyu jarkar Mai su gishiri Man shanu da sauran su dae bin kayan da ido kawae tay ba tare da ta ce komae ba, tana gama nuna mata tace bari taje wurin Yaya ta d'aukko kayan lefenta da shiru har yanzu ba'a maido su nan ba, lokacin da Yadikkon taje bayan sun gaisa da wad'anda suke d'akin ta sanar ma Yaya ta zo d'aukar kaya ne, wani kallo ta jefa mata cikin harshen fulatanci tace to cinye kayan zasu yi da har sai an biyo sahu d'an murmushi had'i da d'an ta6e baki Yadikko tay tace dama daga gidan su Angon ne ake ta kira ana son aji ko akwae abunda baiyi ba kaman takalma da kuma d'inkakkun kaya anata ce masu bata gwada ba shiyasa tazo ta tafi dasu ta gwada amman bari taje sai a sanar masu har yanzu Amaryar bata ma ga kayan ba, tana fad'in hakan ta fara kokarin juyawa ta tafi Yayar ta tsaidata Fuska a murtuke tace ai sai su yi ta d'auka kuma dole za'a fitar ma da Mutanen gida nasu, ita dae Yadikko bata ce komae ba don tasan yanzu ace tayi rashin kunya kaman yadda aka saba cewa, guda biyu ta fara d'auka duk suna kallonta ba wanda yay yunkurin taimaka mata sai bayan da ta kai su daki ne ta dawo tare da Haulat da Mino suka kwashe sauran, bayan sun maida su can suka zauna don sake kallon kayan dama basu samu sun duba ba sosae da suna can, sosae Haulat ta shiga yaba kayan duk yadda akai da Fatuu tazo taga kayan ta gwada k'iyawa tay tace ai ba sai tasa ba tunda tailor ya gwadata, suna cikin kallo sai ga Kawu Amadu da Kamalu sun shigo yadikko tace yazo shima ya ga lefen sosae shima ya yaba saidae acan k'asan ranshi sam bai farin ciki da Auran ba kamar da Kamalu yay mashi bayani kan wanda za'a aura matan don shima ba so yake ba yafi son tay karatun ta kamar yadda shima yake da burin ya koma Katsina don yay karatu, bayan sun gama gani yadikko ta kawo ma Haulat Abinci da k'yar ta matsa ma Fatuu ta d'an ci suna gamawa Haulat ta shiga bathroom tayo wanka don a mugun gajiye take bayan ta fito tay shirin kwanciya itama Fatun ruwan ta watso bayan ta shirya ta hau gadon lokacin tuni bacci yay awon gaba da Haulat, Sam Fatuu ta kasa bacci sai faman sak'e sak'en mafita take rashin zuwan gwaggo ya dameta sosae ga Auran da shima bata son ayi can wata zuciyar ta ayyana mata ko ta kira Haisam ta fad'a mashi halin da take ciki game da wanda za'a aura matan sai kuma ta ayyana to in ta fad'i mashi shi mai zai iya yi mata tasan ba iya sa Ard'o ya fasa zai yi ba k'arshe ya bata hak'uri kawae dama a k'ule take dashi don kwata kwata ya daina kiran ta, haka taci gaba da yin tufka da warwara ta sak'a wannan ta kwance wannan har dare ya raba ba tare da ta ankare ba, can wuraren Asuba ta mik'e ta saukko daga kan gadon ta nufi inda akwatunan da tazo da su suke ta bisu da ido kaman mai nazarin wani abu kafin ta kai hannu ta d'aukko trolley d'in a hankali don kar ya saki sauti, k'asa ta aje shi ta bud'e ta sake d'aukko babban shima ta bud'e ta fiddo wasu kaya ta saka acikin trolley d'in ta d'aukko wasu takalma daga can gefe suma ta saka ciki duk wani abu da tasan zata buk'ata ta saka sannan ta rufe babban Akwatin ta maida shi inda yake ta d'aukko wata Handbag d'inta dake rataye ta bude kud'in da Khalid ya bata ne a ciki dama bata ta6a ko yar biyar ba ta curo su ta nufi akwatunan lefenta ta d'an bud'e d'aya daga ciki ta cusa kud'in kafin ta rufe ta dawo wurin trolley d'in ta rufe shi ta kai hannu ta d'aukko Hijab d'inta dake sagale jikin gadon ta saka har ta d'auki trolley d'in ta nufi hanyar fita sai kuma ta dakata ta juya tana kallon Haulat dake kwance tana bacci hakanan ta ji kamar bata kyauta mata ba in ta tafi ba tare da ta sanar mata ba, a hankali ta jingine trolley d'in ta nufi gadon ta hau a hankali tasa hannu ta fara tashin ta da yake haulat bata da nauyin bacci a nutse ta bud'e idanunta tana ganin Fatuu a gabanta ta yunk'ura da sauri da alamar mamaki akan fuskarta tace "wai har Asuba tayi kin ma yi salla kenan" a hankali Fatuu ta girgiza mata kai murya k'asa k'asa tace "Asuba bata yi ba Haulat" ganin yadda tay Maganar yasa itama Haulat yin k'asa da murya ta tambaye ta miya faru, shiru ta d'an yi tana kikkafta ido kafin tace "Gida zan koma" cikin rashin fahimta Haulat ta sake tambayar ta wane Gidan tace mata Katsina waro ido Haulat tay baki bud'e jin abunda tace Fatuu taci gaba da cewa "Haulat ban son Auren nan, ban so gwara in gudu kawae in dae aka ga bana nan ai dole a fasa" a razane Haulat tace "Amman Fatuu baki ganin lokaci ya k'ure saura fa yan kwanaki a d'aura auran ki miyasa tun farko baki nuna baki so ba sai yanzu" kuka ta fara yi k'asa k'asa tace "Saboda Baffana ne Haulat Kawu Amadu baya fad'i maki ba" kai ta d'aga mata tace eh ya fad'i mata taci gaba da fad'in "Yanzu ban son auran nan Haulat....." Katse ta tay tace "amman Fatuu kina ganin abu ne mai sauk'i fasa auran nan don kin gudu, ni a ganina kawae zaki jawo wata matsalar ne ki k'ara jefa su Baffa cikin wani tashin hankalin" Fatun tace "ai dama gwaggo bata so dalilin hakan ne yasa take fushi da ni don na k'i goyon bayanta nace na amince aman auren yanzu in naje nasan zata yi wani abun a fasa" shiru Haulat tay tana kallonta kawae ta lura ganin hakan take abu mai sauk'i can ta dafata tace "Fatuu ni a ganina ki hak'ura kawae tunda har an zo nan....." Cikin kuka tace "Allah bazan Aure shi ba in ba haka ba mutuwa zanyi don baki san wanene za'a aura man bane yasa kike cewa in hak'ura, Mashayi ne fa mai neman mata kuma..." Nan ta kwashe komai harda gidan gona da ya kaita da Maganin bacci da ya saka mata a lemu harda abunda yay mata jiya da yamma da ta dawo ta isketa ta zo, hannu Haulat tasa ta rufe bakinta cike da Al'ajabi kafin ta cire a sanyaye tace "Shikenan Fatuu in dai kina ganin gwaggon zata iya yin wani abu da zai sa a fasan kije" da sauri ta goge kwallan fuskarta ta juya zata sauka daga gadon Haulat tace "Amman Fatuu ni fa?" juyowa tay ta kalleta tace "ba sai ku dawo da kawu Amadun ba" gyad'a kai Haulat tay sai kuma ta sake cewa "amman lafiya lau zaki iya tafiya dare fa ne" jinjina mata kai Fatuu tay tace zata iya lafiya lou ba abunda zai sameta in sha Allahu daga haka ta idasa sauka ta nufi hanyar fita idon Haulat a kanta tana kallon ta cike da tausayi har ta kai hannu zata d'auki trolley d'in taji muryar Haulat ta kira sunanta juyawa tay ta kalleta ta saukko ta nufo inda take tana zuwa tace "bari mu tafi tare" da mamaki tace "amman haulat jiya fa kuka zo ko hutawa sosae baki yi ba ki kwanciyar ki daga baya sai ku dawo" girgiza mata kai tay tace su tafi ba komae har cikin ran Fatuu taji dad'in hakan, Hijab Haulat ta d'aukko ta saka ta maida kayan da ta cire jiya cikin jakarta dama ita kadae ta zo da ita ta d'auka Fatuu ma ta d'auki trolley a hankali tasa k'afa cikin Falon ba kowa sai k'annenta dake ta bacci kan shimfid'a dama cikin d'akin daga ita sai Haulat Yadikko na d'akin Baffa, cikin sa'a suka fito daga cikin d'akin gaban Haulat nata bugawa gaba d'aya a tsorace take suna fitowa Fatuu tay ma Haulat nuni da hanyar bayan gidan a hankali cikin rad'a tace ta can zasu fita bata kopar waje ba...........
*Uhmmmm, shin su Fatuu zasu samu fita daga cikin gidan kuwa? In sun fita zasu samu komawa Katsina? Gwaggo zata saurari Fatuu in sun samu komawar? Za'a fasa auran ko baza'a fasa ba???*
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268._
Domin karanta cikakken Littafin sai ku danna bulun Rubutun dake kasa ko kuma hoton dake kass 👇👇👇👇
*Uhmmmm, shin su Fatuu zasu samu fita daga cikin gidan kuwa? In sun fita zasu samu komawa Katsina? Gwaggo zata saurari Fatuu in sun samu komawar? Za'a fasa auran ko baza'a fasa ba???*
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268._
Domin karanta cikakken Littafin sai ku danna bulun Rubutun dake kasa ko kuma hoton dake kass 👇👇👇👇
https://aihausanovels.com.ng/novel-document/a-sanadin-makwabtaka-book-2-complete-hausa-novel
👆👆👆👆👆
********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.
Email > aihausabooks@gmail.com
******* FOLLOW US ******
Facebook: Ai Hausa Novels
Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels
WhatsApp Number: 08138873799
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafinmu ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38