bani itace kawai babu komai. Hakan yasa naji babu daɗi gaskiya. dan harna nuna masa. Mutum ne shi mai matuƙar sauƙin kai ga iyalansa. sai ya zauna ya dinga bani haƙuri damin nasiha akan wani abun barinsa a yanda yake yafi muhimmanci fiye da tonasa. Nanma dai haƙura nai na barsa badan naso hakanba, sai daga bayane na samu Mama maryam da maganar dan abin ya kasa barin zuciyata. A ranar yazo nan gidan, sai dai bansan mi suka tattauna ba, da ya koma gida kuma ban tambayesa komaiba”. Umm-Anum ta sauke numfashi da share hawayen dake gangaro mata, wanda su Bilkisu ma kukan suke a hankali. Ƙafarta mai ciwo taɗan miƙe da cigaba da faɗin,
   
            “A daren wata juma'a dake dai-dai da cikar Abdul-aziz shekara ɗaya da wata ɗaya akan kujerar mulki sai yay baƙi bayan sallar isha'i, tunda naga har ya yarda zaiga baƙin na tabbata masu muhimmanci ne, dan a ƙa'ida shugaban ƙasa baya irin wannan zaman musamman ma da daddare, kuma a cikin gida, gidanma a falonsa. Inason tashi na bisa naga wanene Jawaad dake fama da zazzaɓi ya hanani tashi dan yanata faman kuka, haka na haƙura nai amfani da telephone nai kiran su Wasila dake ɗakinsu, dan suna a tare damune kowa ya sani. Rahma ce ta ɗaga wayan, a cewarta Wasila tayi barci. Umarni na bata akan tasaka akaima baƙin Abdul-aziz abin sha, idan kuma suna buƙatar wani abu sai a haɗa da shi. Ta amsamin da to na katse kiran. Kusan mintuna arba'in da yin haka harma na manta ina jiran shigowarsa ne kawai sai ga Rahma ta shigomin a wani iri. Faɗa na fara mata, dan basa shigowa ɗakinsa inba da wani babban daliliba. Cikin rudin da take ciki tace, Kiyi haƙuri Yayah, wlhy wani abune ya sakani a ruɗani, zomuje ɗakinki kiji dan ALLAH kada Yah Abdul ya shigo. Ban musa mataba nabi bayanta muka fita, ina goye da Jawaad da yay barci a bayana”.
       (Yayah wai dan ALLAH mi su Alhaji Sadi keson Yah Abdull yayi ne yaƙi?). Ban ganemba Rahmah miya faru?. (Ruwan da kikace na saka a kaimusu saina iske ma'aikatan sunata faman aiki, kinsan kuma Yaya bason kowa yay masa aiki yake ba wani lokacin, shinefa na ɗauka da kaina nakai ruwan, to saina iske Yaya Nasir, Alhaji Ali da Alhaji Kokino tare da shi, sai dai kafin nai sallama naji wani furuci na Yaya Nasir daya saka bayan na gaishesu na ajiye ruwan na sake laɓewa, dan tundafa na shiga falon kan Yah Abdull a ƙasa alamun ransa a ɓace yake. Kinsan minaji kuwa?) kaina na jinjina mata a lokacin. (Ta cigaba da faɗin Yaya Nasir naji yana faɗin, “Amma dai Abdul-aziz kasan baka isa sanin sirrinmu ba sannan ka bijire mana, bafa wai dan bama sonka bane muke jawoka jikinmu, duk yanda kake tunanin mulkin ƙasarnan yafi ƙarfinka saika ɗaura ɗammarar da muke nuna maka, dan mulkin ƙasarnar baya buƙatar GASKIYARKA ko ƘWAZONKA balle son TALAKAWANKA”.  Murmushi Yaya Abdull yayi yana girgiza kansa, cike da ladabi yace, “Yaya dan ALLAH mu ajiye maganarnan, indai nine kusa a ranku abinda naji na gani a can wajen na barsa wlhy, kuma har abada bazan taɓa furtashi ga waniba koda kuwa ace Bilkisu ce ko Mama ko Jawaad. Amma hakan bawai yana nufin zan barku kucigaba da zama akan wannan hakalarba, kuji tsoron ALLAH, karku.........” da sauri Yaya Nasir ya ɗaga masa hannu, “Bama buƙatar ji”. Murmushi Yaya Abdull yay kawai yaɗan girgiza kansa, “Shikenan Yaya na bari, ALLAH ya ganar daku gaskiya idan kunada rabonta. Sai dai gaskiya koda zan haɗe wannan maganar a cikina bazan iya barin Sadi ya cigaba da sarrafa mugan ƙwayoyi ana cutar talakawa naba, dolene kodai ka rufe kamfaninka na sararafa magunguna, kokuma ni nasaka kwamitin bincike a kansa ƙarƙashin hukumar lafiya.......” a fusace Alhaji Ali (Dad) yace, “Mi kake nufi Abdul!? Kenan zaka iya mana SARAN ƁOYE (littafina na zafafa 2021🤗😋) kenan bayan kasan mu duka nan munada hannun jari a wannan kamfanin hatta da kai kanka ka sakama ɗanka hannun jari zaka aikata hakan kuma?”. “Babu wani maganar Saran Ɓoye Alhaji Ali, inda Saran Ɓoye zan muku da bazan fito na faɗa muku ba ai, sannan da kake maganar na sakama Jay hanun Jari a ciki ALLAH shine shaidata bansan abinda kukeyi a ɓoyeba kenan ai, nidai ABINDA KE CIKIN ZUCIYA ta (Littafin Rano a Zafafa 2021🤗😋) na fito na faɗa muku, dan ALLAH ya kukeson nayi? Ku kune garkuwata, a wannan tafiyar, amma kundawo kuna meman sakani cikin SIRAƊIN RAYUWA (Littafin Huguma a zafafa 2021🤗😋) kuma? Dama kun dafamin bayane domin kuyi amfani dani wajen cimma burinku ko mi? To wlhy! Wlhy! Wlhy!! Kunji sau uku, bazan taɓa cutar da talakawana danna faranta mukuba, bakuma zan taɓa nisanta kaina da UBANGIJINA saboda ku ba, sirrinku kuwa zan riƙe, domin wanda ya halicceku na kallonku, nayi imani da KIBIYAR AJALI.....(Littafin Miss Xoxo na zafafa 2021🤗😋)  sulke baya tareta saita gitta wataran, duk abinda yay farko zaiyi ƙarshe. Karku sake zuwamin gida akan wanan maganar daga yau na rufeta, kuma har gaban abada bazata sake tashiba insha ALLAH”. Kallon tsoro suke masa sosai, Alhaji Kokino zaiyi magana Alhaji Ali ya hanashi, shinefa na taho ganin Yaya zai fito). Ajiyar zuciya na sauke da cigaba da kallon Rahmah tamkar a jikinta zan samu amsoshina, fassara maganganunta nake amma babu wadda na iya samawa fassarar data dace, haka na haƙura na barta ta tafi ɗakinsu saboda farkawar da Jawaad yayi baban yaji kukansa ya shigo. Ban tambayesaba a ranar sai bayan sati kusan ɗaya, sai dai ko uffan baice daniba balle na samu amsa, haka na cigaba da masa naci daga ƙarshe yace karna sake damunsa akan abinda bai shafeniba. Ranar haka muka yini ran kowa a ɓace ni da shi”.
      Ta sake share hawayenta tana shaƙar numfashi da ƙyar, saida Gambiya ta bata ruwa tasha sannan ta cigaba.
        Tun daga wannan lokacin na fahinci abubuwa sun ɗauki zafi tsakanin Abdul-aziz da su Sadi, sai dai yaƙi faɗa min komai duk yanda naso ji, kamar yanda yay alƙawari ya saka kwamitin bincike akan kamfanin magunguna na Sadi, wanda abin bai nisaba aka ƙwace kamfanin batare da am bayyanama duniya mi aka gano a cikiba, sai dai abin mamaki ko sati biyu ba'ai da amsarba aka maida masa abinsa. daga wannan lokacin kuma yanayin yanda Abdul-aziz ke gudanar da mulki ya fara canja taku, baya iyayin komai sai abinda su Sadi sukace, ikon ALLAH dai talakawan ƙasa basu fahimci hakanba sai mu dake a kusa da shi sosai. Hankalina ya tashi sosai, dan ko shawara na bashi akan abu ko Baba da Mama maryam suka bashi sai yace ba hakaba, ga abinda Sadi da Ali sukace, ma'ana dai yafi yarda da nasu. Cikin wata guda duk ya susuce komansa ya koma ƙarƙashin ikonsu, mulkinma dai tamkar sune suke yinsa bashi ba, dan komai akan ikonsu yake gudana, sai sunce yayi yakeyi, wanda kuma sukace kar yayi komai muhimmancin abun bazai yisaba. Tun yana ciwo a tsaitsaye harta kaisa ga kwanciya, da ƙyar ya amince Doctor yazo ya dubashi a wata ranar laraba, a gwajin farko aka gano ciwon hawan jini tattare da shi, sannan zuciyarsa na barazanar kamuwa da ciwo kuma. Hankalina ya tashi, na dinga masa kuka da roƙon ya sanarmin abinda ke damunsa ko shawara na bashi, amma yaƙi. Bayan kwana biyu ya cigaba da ƴan harkokinsa yana nunamin ya warke, amma ni nasan akwai wata a ƙasa tunda nasha ritsashi yana hawaye, sannan idan ya zauna shi kaɗai zaka samesa yayi jigum yana tunani. Sai kuma rama da ya ketayi a tsaye wadda Baba da Mama maryam suka kasa haƙuri suma sai da suka tambayeni ko lafiya?. gudun karsu tashi hankalinsu nace babu komai kai kawone kawai irin na shugabanci da kuma ɗan zazzaɓi da yay na kwana biyu. Sun masa addu'a daga haka muka bar maganar.
         Bayan kamar sati shida da tashinsa daga wannan ciwo sai ya ƙara kwanciya, wannan itace kwanciyar data zama ajalinsa, a ranar bai fita office ba duk da kasancewar ranar aikice, yanama da meeting da gwamnoni, amma hakan ya gagara. Wajen yamma sai ga Sadi Kokino da Ali sunzo sun dubashi, ban kawo komai a rainaba na barsu daga su sai shi, ina ɗakina inama Jawaad shirin islamiyya sai ga Rahma da gudunta, sai dai tama kasa magana, hannuna kawai taja muka fito zuwa ɗakin da Abdul-aziz yake kwance. Sai dai muna kawo ƙofar ɗakin su Sadi na fitowa. Kallon Rahmah suka dingayi cikin wani yanayi daya sakani faɗin, “Lafiya kuwa? Miya faru?”. Cikin shashantar da zancen suka shiga gaisheni da tambayar jikinsa, tare da ɗorawa da faɗin ya kamata a sanar dan a fita dashi ƙasar U.S yaga likitan daya san aikinsa. Ban musa musu hakanba, dan nima ina buƙatar lafiyar mijina, na raɓasu na shige ɗakin sai na tadda Abdul-aziz a lulluɓe har fuskarsa, nai saurin matsawa na janye bargon. Ajiyar zuciya na sauke ganin idanunsa biyu, sai dai da alama hawaye yakeyi, amma jin motsina yay saurin sharewa ya maye fuskarsa da murmushi. Zama nai kusa dashi ina jera masa sannu, na shiga karanto addu'a kuma ina tofa masa kamar yanda ya buƙata, dan ya faɗamin jikinsa na masa zafi kamar ana hura wuta.
         Indai taƙaice muku a wanan dare  bamuyi barciba sam, washe gari muka wayi gari jikinsa ya rikice, da yayi tari sai jini, tun yanayi a ɓoye harna farga da hakan, sai dai ya hanani na faɗama kowa, a cewarsa zasu tafi asibiti gobe idan ALLAH ya kaimu zai samu sauƙi insha ALLAH. Badan hankalina ya kwantaba na yarda.
      Zuwa bayan sallar la'asar baba yaje gida ƴaɗan watsa ruwa dan tare damu ya yini sai ga Alhaji Ali (Dad) Alhaji Sadi Kokino, Alhaji Nasir (Uncle Nasir) da wasu mutane biyu daban saniba sunzo dubashi wai. Da yake muna falon ɗakin da yake kwance sai nace su shiga yana ciki, caraf Rahma ta riƙemin hannu tan girgizamin kai hawaye cike da idanunta amma ban fahimtaba, duk zatona damuwar ciwon nasane kawai, dan ita da Wasila tunda gari ya waye suke kuka, amma da yake Rahma tafi Wasila wayo a lokacin sai nata yafi yawa. Suna shigewa ta miƙe zaram ta kama hannuna tana nunamin ɗakin, mamaki abin ya bani na hau mata faɗa akan bata da bakine?. Har sannan bata tankaminba, kanta dai taketa faman jujjuyamin da fusgar hannuna muka zagaya ta Window.
        Ban taɓa ganin tashin hankali mai muni irin na wannan ranaba, dan kuwa zagaye muka hangi su Alhaji Kokino akan Abdul-aziz, sun lulluɓa masa wani jan ƙyalle suna wani kalar yare da su kaɗai suka san mi suke faɗa, duk yanda naso ɗaga ƙafa naje cikin ɗakin dagani har Rahma mun gagara hakan, a gaban idanunmu Nasir ya shiga zubama Abdul-aziz wani ruwa yana surkulle, sannan ya hau kansa yay....ya ya...yay fasiƙanci mafi muni da shi”. Umm-Anum ta ƙare maganar da fashewa da wani irin matsanancin kuka mai cin rai da zuciya, numfashin ta sai sama da ƙasa yake tamkar zata shiɗe.
      Tsitt falon yayi babu maiyin koda ƙwaƙwaran motsi, da alama dukansu sunyi suman zaune ne.
     Umm-Anum dake kuka tamkar ranta zai fita ta cigaba da faɗin, “Yana kuka da roƙonsa karya aikata masa wannan aiki maimuni, ga aman jini yanayi amma sam Nasir bai sauraresaba, sai da ya biya buƙatar zuciyarsa Ali ma yayi, Kokino ma Yayi. Duk muna kallonsu ni da Rahma, sai dai ko motsin kirki mun gazayi balle wani yunƙuri har suka fito suna kuka. Fitowarsu tayi dai-dai da dawowar baba tare da Mama Maryam. Sai ji kawai mukai suna faɗin Abdul-aziz ya rasu. Iya abinda naji kenan ban sake sanin mi nake cikiba sai a Saudia, shima ban tuna komaiba makamancin hakan sai shekaran jiya dana farka tamkar mai barci naga Anuwar da Abbunsu tare dani............✍
     

__________________
ZAFAFA 2021
_______________

             Masoya naku taurarinfa sun sake dawowa da sabon salo a 2021.

       Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
  
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

Kwace wannan kodai itama su Dad sun ƙwamusheta ne🤣, na barku a gidan Alhaji babba kunata jira, yo sakawa sukai nimafa akai kidnapping ɗina, da ƙyar na fito a inda suka ɓoyeni😪🚶🏻🚴🏼.

Ku fara da waɗanan kafin na ƙara editing sauran na turo muku da safe idan ALLAH ya kaimu💃🏻. Yanzu kam mankaina ya tsiyaye sai an ɗura wani😣😪😫🚶🏻🚶🏻.
[2/17, 7:31 AM] Suwaiba: __________________
ZAFAFA 2021
_______________

             Masoya naku taurarinfa sun sake dawowa da sabon salo a 2021.

       Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
  
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

Page 62

....................Wani irin tsuma jikin Jay ya keyi irin wanda kowama bai taɓa ganiba, idanunsa sunyi masifar rinewa abun tsoro, duk wata gaɓa ta jikinsa ta sake buɗewa, ƙwanjinsa ya kumbura hakama jijiyoyin kansa dana dukkan sassan jikin nasa. Da sauri Alhaji babba daya fahimci komai zai iya faruwa a wajen dan yasan wanene jikansa da zafin zuciyarsa. yay azamar riƙo Jay ya rungume a jikinsa, duk da neman ƙwacewa da ya keyi bai sakesaba. sai ma taimaka ma Alhaji babba da Uncle Sulaiman yay suka danne Jawaad ɗin yanda bazai iya tashiba duk yanda yaso hakan. Kuka kawai ya fashe dashi dan zuciyarsa tai masifar kaiwa maƙura, Alhaji babba ma kuka ya keyi. ya kalli su Dad yana faɗin, “Amma Ali ka cuceni, yanzu kunsan da wannan zaluncin da kuka aikata amma harka iya zuwa neman auren Rahmah a wajena?”.
        Cike da tashin hankali da tsoron Jawaad dake a cikin idanunsu ƙarara Dad yace, “Munyi hakane domin rufe sirrinmu, dan bayan mun gama aikata abinda bokanyarmu tace ga Abdul-aziz sai kawai mukaci karo da Rahama da Bilkisu a bazata duk suna kallonmu ashe, duk da munsan asirin dake tattare damu bazai bari su iya komaiba a kanmu hakan bai hana  hankalinmu mummunan tashi ba, a take muka aika ɗan aike wajen bokanya, mukuma mukabi ayarin masu kukan mutuwa da jimami. Kafin a gama kammala haɗa gawar Abdul-aziz muka sake samun ɗan saƙo daga bokanya akan bilkisu da Rahmah. andai rufe bakin Rahmah kamar yanda bokanya ta faɗa har abada bazata sake tuna abindama ta ganiba balle wani ma yaji daga gareta, Bilkisu kuwa babu yanda za'ai bakinta ya rufu sai dai ta haukace, hakan kuma bazai tabbata ba sai idan data farka za'a bata ruwan tsafin da bokanya ta aiko dashi. Musan mu bazai yuwu muyi hakaba, dan haka Nasir ya kawo dabarar zuwa ga Humaira (Mom) da Mama (Mama Atika) dan ya sakasu suyi mana wannan aikin ta hanyar daya dace tunda suma akwai nasu burin akan dukiyar Abdul-aziz........”
      Kuka mama atika da Mom suka fashe dashi. mama Atika tace, “Wlhy ALLAH ne shaidarmu baku sanar mana akan hakan zakuyima Bilkisu asiri ba, Nasir ya samemu lokacin da aketa shirin fita da gawar Abdul-aziz, mukuma isowarmu kenanma babu jimawa. Yace muyi ƙoƙarin bama bilkisu ruwan maganin, ta hakane kawai zamu sami damar mallake duka dukiyar da Abdul-aziz ya tar.......” sai kuma ta kasa ƙarasawa ta fashe da matsanancin kuka. Uncle Nasir ya kalleta shima yana kukan,
         “Ki ƙarasa mana mama, ai duk kece silar komai, kece kike mana huɗuba akan karmu yarda kowa ya fimu a ƴaƴan baba, kece kika saka ƙiyayyar Abdul-aziz a ranmu, a cewarki an auro uwarsa a bayan baya amma ɗanta yazo yafi kowa arziƙi a gidan harda ƴaƴanki, bayan kuma mune ya dace muyi wannan arziƙin saboda kece matar baba ta farko, mukuma mune ƴaƴan farko a gidan. A dalilin wannan huɗubar taki na jefa kaina a halaka, tun bana ɗaukar huɗubar Alhaji Ali da Alhaji Sadi har suka fara tasiri a raina, nidai burina kullum na wuce Abdul-aziz arziƙi dan na faranta miki rai. hakan yasa duk muguntar dasu Alhaji Sadi suka kawo shawarar a aikatama Abdul-aziz na dinga biye musu, har takai sunyi ƙokarin jawo Abdul-aziz cikin tafiyarmu, dan har wajen bokanya an kaisa da yaudarar zata bashi maganin sammune saboda magautan siyasa. Ko'a hakanma saida ya tirje, nine naita lallaɓarsa harya amince ya bimu, koda yaje yaga abinda muke nufin ɗorasa a take ya bijire mana ya kuma nuna ɓacin ransa mai tsanani akan hakan. Sai dai zukatanmu sun rigada sun bushe a lokacin. gani muke kamar zai tona mana asirine. dan haka muka gaza ƙyale rayuwarsa ta huta, duk wani burinsa na aikata alkairi ga talakawansa mun daƙilesa ta hanyar asiri da muzgunama rayuwarsa, kowane aiki munyi bake-bake a kansa tare da handame dukiyar da aka keɓe danyin ayyukan, daga ƙarshema bokanya ta bamu tabbacin jinin Abdul-aziz zai taimaki tafiyarmu, dan haka muyi amfani dashi, kafin hakan kuma dolene muyi fasiƙanci dashi. Jinin Abdul-aziz shine jini na farko da muka fara salwantarwa, dan da duk abinda zamuyi na tsafi da jinin dabbobi mukeyi. Amma nasarar da muka samu da jinin Abdul-aziz yasa burikanmu sake faɗaɗa, muka fara sadaukar da makusantanmu. Mama da humaira sune suka ɗurama Bilkisu maganin
Showing 237001 words to 240000 words out of 249282 words