bakaga fitarta ba?". "Wlhy ban ganiba yarona, dan ita macece mai yawan barkwanci inhar zata fita a gidan nan kota shiga saimun tsokani juna, to a randa ta dawo da yake salla nakeyi sai ban kawo komai a rainaba, abinda ma ya ɗauremin kai da sukace su basu gantaba randa ta dawo ɗin". Shiru boss yayi alamar tunani, dan haka nikuma nace, "To amma baba a wannan daren kana tunanin zata iya fita?". "Gaskiya bazata iyaba ƴata, dan maman yara ma tana da ciwon ƙafa bata cikason yawan kai kawoba". "Hakan na nufin tana cikin gidan kenan kokuma an fita da ita a daren, ko kaine idonka bai nuna maka dai-dai ba?". "Wlhy bana ko tantama itace ta dawo da mangaribar nan, to ƴata wazai fita da ita kuma sai kace wata kaya batare da an gani ba?, shaiɗanin daya taɓa kwatanta hakama mijinki yasa an kaisa gidan maza ai". Murmushi nayi kawai, na ɗan juya na kalla boss ɗin dake saurarnmu sannan na maida ga baba, "Baba a wannan ranar mota nawa ta shiga gidan ta kuma fita bayan dawowar maman yara?". "Babu wanda yazo tunda Alhaji baya gari ma, sai wani yaro ɗan dogo baƙi mai dogon hanci da ya kanzo lokaci-lokaci idan Alhaji na nan, to ni a ranarma da yazo ɗin saida na sanar masa baya nan ai Alhaji, sai yace ai ya sani saƙo zai bama hajiya inji Alhajin. Daga haka ban sake tofa komaiba na barshi ya shiga ni kuma na shige ɗakina, to baifi mintuna goma sha biyar da shigaba ma naji yana horn nazo na buɗe masa ya fice". "Kasan sunansa baba?" "A'a gaskiya ƴata, ban saniba wlhy".
Waya boss dake saurarenmu ya ɗauka ya shiga daddanawa, kafin ya miƙama baba wayar yana faɗin, "Shine wannan?". Amsa baba yay ya kalli hoton, cikin jinjina kai da murmushi yace, "Tabbas shine kuwa ɗana". "Baba ka tabbata?". "Babu tantama a zancena". "Shikenan mun gode, bara mu maida kai, sai dai zamu iya dawowa gareka a ko wane irin lokaci". "Babu damuwa wlhy ɗana duk sanda kake buƙatar wani abu ka kirani". Godiya muka sake masa, ya tada motar yay reverse, a wani wajen muka saukesa saɓanin inda muka ɗaukesa.
Jin yayi shiru sai na ɗan kallesa, "Hoton wanene ka nuna masa dan ALLAH?". "Zaki gani yanzun" ya faɗa yana karya kan motar muka shiga wani layi. A ƙofar wani gida madaidaici yay fakin, ganin zai fita nima sai na buɗe na fita. Mun gaisa da samari uku da alama ta nuna suke

tsaron gidan, yanda suke gaishemu cikin girmamawa nasan lallai shine ya ajiyesu. Ɗakin farko dake a gidan muka shiga, inda muka iske matashin saurayi zaune, shigowarmu ta sakashi miƙewa yana murmushi da mana sannu da zuwa. Na buɗe baki zan amsa kawai naji tass!!!.
Idanu na zaro baki a hangame ina kallon boss da ya saukema saurayin mari, ban gama fita a mamakinba naga ya hau dukansa. Dukansa yake ta ko ina, a take jikina ya fara rawar tsoro, nasa hannu na rufe fuskata ina ambaton "innalillahi....." da sauri na buɗe fuskata jin ƙarar ɗana kunamar bindiga, nai masifar sake zazzaro idanu waje ina faɗin, "Boss badai kashesa zakai ba?". Harara ya balla min ya ɗauke kansa yana huci.
A tare muka saki ƙara ni da saurayin saboda harbinsa da yay a ƙafa, zufa ta shiga rige-rigen karyo masa, jikinsa na wani irin rawa, ko kallon inda nake baiba ya ranƙwafa kan saurayin yana hure bakin bindigar dake ɗan hayaƙi da faɗin, "Kaga bindigar nan cike take taf da alburusai, kuma idan zan ƙarar dasu tas a sassan jikinka babu mai tambayata yaya nai da su?, wannan harbin danai maka na ƙaryar daka mince, idan wata ta biyo bayanta yanzun kuma wlhy saina faffasa gaɓɓanka ɗaya bayan ɗaya da alburusan nan kafin na aikaka lahira dan ubanka. Ina kakaita itama?". Jikin ɓaleru na rawa ga jini na malala a ƙasa cikin hakkin kuka da azabar shigar harsashi yace, "Bansan wacce kake maganaba oga, dan ALLAH karka kasheni, nayi kuskure a farko amma wlhy bazan sake kwatantashi ba". "wani rainin hankalin zaka sakemin?" ya faɗa a taƙaice yana sake ɗaure fuska da ɗana kunamar bindigarsa.
"A'a wlhy oga ba haka bane ba, na tuba dan ALLAH zan faɗa maka komai, bata a garin nan". "Amma ranar ca kaimin baka da alaƙa da Alhaji kokino, bama ka sanshiba ko?" ya faɗa yana ɗora masa bindigar a saman kai. a take jikin ɓaleru ya ƙara ƙarfin mazari, harya jiƙe wandonsa da fitsari, "Oga kawa ALLAH da MANZONSA karka kasheni, ka yafeni, komi kake buƙata yanzu wlhy zan makashi, harma abinda baka saniba zan faɗa maka". Ƙafa Jay ya saka ya danna ƙafar ɓaleru daya harba. Ya sake sakin wata wahalalliyar ƙara jikinsa na karkarwa.
Da sauri nazo na riƙe hannunsa ina hawaye. Janye ƙafar tasa yay ya juyo yana kallona da wani murmushi irin na tsagwaron muguntarnan, ya lakacemin hanci da faɗin, "Ki rage wannan tausayin malama". Rungumesa nai da sauri ina faɗin, "To dan ALLAH kayi haƙuri ka barshi haka tunda yace zai faɗa mana".
"To na barsa" Jay ya faɗa yana ballama Ɓaleru da keta kukan wahala harara da shafa bayan bily data lafe a jikinsa. Sai da ya tabbatar tayi shiru sannan ya ɗagota ya share mata hawayen tas da sumbatar goshinta.
Jikkata ya amsa ya buɗe, ya fiddo biro da ɗan littafi dake ciki ya jefama ɓaleru, duk da halin da yake ciki haka ya ɗauka ya rubuta masa address ɗin. Yana sharar hawaye da sauke numfarfashi yace, "Oga gidan akwai matakan tsaro sosai, hanyar da zaku iya fiddota cikin sauƙi itace kiran masu tsaronta da wayar Alhaji kokino". Uffan baice masaba, saima waya daya kira, mintuna kaɗan saiga ɗaya daga cikin masu tsaron gidan ya shigo. A daƙile yace, "A cire masa wannan bullet ɗin a tsaida jinin". Da girmamawa ya amsa da "Yes Sir" hannuna ya kama kawai muka fice, sai binsa nake da kallo da ɗunbin mamaki, ban taɓa zaton tsaurinsa ya kai hakaba, nikam tsoroma yake ƙara bani yanzun.
Sai da muka fara tafiya sannan yay magana hankalinsa nakan tuƙi, "Tunaninmu na samun wayar kokino yana a kan hanya, wannan tsoron da tausayin naki kuma dole ki cireshi dan aikinmu baya buƙatarsa". Kallonsa nayi sai naga bani yake kallo ba, yama fuske abinsa tamkar bashine yay maganarba. Nima bance komanba amma sai juya lamarin nake a rai, 'sai kace a cikin film? kai anya kuwa ban sako kaina inda yafi ƙarfina ba? Wani ƙarfin zuciyar ai sai maza dole'.
Da wannan tunanin a raina muka iso wani waje saɓanin station da nai tunanin zamu koma. Fakin yay sannan ya ɗauka waya yay kira. Yanda ya kwantar da murya tamkar ba shine ya gama hargagi yanzunba sai ya bani mamaki, jin kuma da mace yake maganar dan a hans free yasa sai naji wani abu ya dunƙulemin a ƙirji na takaici. Ƙin kallona yay ya cigaba da wayarsa,

"Kiran da nai miki yanzu ai ya tabbatar miki ban manta da ke ɗinba". Cike da yanga daga cikin wayar akace, "Kai dai kanason kare kanka, shekara biyar ai ba kwana biyar bace". Baki naga ya wani taɓe da ɗauke kai kamar yana a gabanta, a zahiri kuma sai ya sake kwantar da murya da faɗin, "Tom nayi laifi, amma nima bana ƙasar ai, yanzu ma dai akwai wani taimako da zakimin akan Dadynki". tace, "To yanzu na fahimci dalilin kiran, tunda ba taɓa kirana kayiba, inma na kira baka ɗagawa" "Humm" ya faɗa batare da ya bata amsar zancen nata ba, "Yanzu dai bazakimin taimakonba na nema wani?" "Ah haba, kaima kasan bazan iyaba ai, ko karan gidanka ka aiko da buƙata ai zan biya masa balle kai ɗin da kanka" "Yayi" ya faɗa a taƙaice, sannan ya cigaba da faɗin, "Wani ƙulli da ake sonma Dadynki mukeson kwancewa batare da ya saniba, dan haka mukeson ki ɗebo mana dukkan phones nashi a daren yau zuwa safiya insha ALLAH za'a dawo dasu ki maida masa batare da ya saniba". Jimmm tai alamar tunani, kafin ta sauke numfashi da faɗin, "Tab wannan aikin baiyi girmaba kuwa Jay, Dady fa ko Momy bai bari ta taɓa masa waya balle mu, to ta inama zan fara hakan?". "Yanda za'ai ɗin ke ya kamata kiyi tunani, inba hakaba komai zai iya faruwa da shi, idan kuma kin zaɓi komai ya farun akan ki bada haɗin kai a taimakesa kafin ya farun to babu damuwa sai anjima....." da sauri tace, "A'a tsaya-tsaya, ka bani lokaci zanje nayi tunani, nanda magriba idan da yuwuwar hakan zan turo maka saƙo, dan matsalar shine kasan shi business yake, komai dare kuma amsa waya yakeyi, to tayaya za'a ɗauka har sai zuwa safiya a maido bai fahimta ba?". "Kidaiyi ƙoƙari mugani". "Shikenan sai ka jini" ƙitt ya yanke wayar tare da juyowa ya kalleni. ɗauke kaina nai gefe batare da nace komaiba. Shima ɗin baice min ɗinba, saima sallama da naji ya sakeyi alamar wata wayar.
kiran oga Hafiz yay aka yayma su Jabeer magana su zo su samemu a office ɗin da aka buɗe na karɓar cases ɗin masu fyaɗen nan, dan yanada buƙatar sanin komai a yau ya fasa gobe, amma kafin sannan su fara turo su Ummie sannan, kafin su su biyo bayansu nanda mintuna talatin.
Duk da abin ya bama Hafeez ɗunbin mamaki sai bai tambayi dalili ba ya amsa masa da to kawai, dan yasan zai musu bayani. Wayar ya ajiye yana sauke numfashi, ya kamo hannuna cikin nashi tare da saka ɗayan hannunsa ya juyo da fuskata garesa. "Na matan ne ya motsa?". Yay maganar gab da fuskata yana wani ɗagemin gira. Fuska naɗan ɓata nace, "Miye na mata?". "Kishi mana" ya bani amsa da lakacemin hanci. Bansan sanda murmushi ya suɓucemin ba nace, "Nidai ai ban faɗaba". "Ai shi ba sai an faɗaba, a fuska ake ganoku". Mintsininsa nai a hannun da yake murzamin cinya. Ya ɗauke da sauri yana faɗin, "Ouch!, muguwa". Dariya na ƙyalƙyale da ita, dan yanda yay da fuska kamar wani ƙaramin yaro.
Murmushi Jay yay yana kwantar da kansa a kafaɗarta da lumshe idanu dan dama soyake yaga ta dawo cikin walwalarta.
Babu jimawa sai gasu Zuhrah sun iso, cayay na fita na samesu mu shiga wajen tare, shi zai jira su Oga Aliyu.
"Anacan anashan soyayya an barmu" cewar Ummie sanda na iso inda suke. "Ya ranki ne?" na faɗa ina mata gwalo. Dariya su Zuhrah suka sanya mana, Ummie kuma tace, "Fari ƙal, muma ai tana tafe garemu, a lokacin wasu sun tsufa". "Ko kuma mun zama gwanaye ba" na bata amsa ina mangare ƙeyarta.
Yanayin yanda aka tsara wajen ya birgeni sosai wlhy, ga matansu Oga Jabeer sunata aiki tuƙuru, gaisuwa mukai cikin girmama juna suna tsokanata wai har mun dawo daga Honeymoon ɗin. Dariya kawai nayi bance komaiba. Muka rungume juna da Amina ina tambayarta ya mama da yaya sule?.
Babu jimawa da zamanmu su boss suma suka shigo, bayan anyi ɗan gaishe-gaishen juna matar Jabeer data kasance shugaba ta fara mana jawabin cigaban da aka samu musamman ma ni da Boss da bamusan yanda ake ciki ba.
"Ƙasarnan danƙare take da cases na matsalolin fyaɗe, wasu sunma kai kotun amma rashin gata yasa an watsar da shari'oinsu, daga baya an saki waɗanda suka aikata laifin, wasu ko tsoro yama hanasu fitowa su faɗa. A yanzu haka dai munada ƙararraki kusan saba'in da uku a cikin kwanaki goma sha shidda kacal da shelanta ƙunyar, mun gama bincike akan ashirin da ɗaya kamar yanda muka sanar maka, mun tabbatar da gaskiyarsu kuma harma munsa an kama wasu daga cikin masu laifin, wasu kuma muna kan fakonsu, sai cases Goma sha huɗu masu kamanceceniya da irin wanda muke nema".
Kai Jawaad keta jinjinawa yanajin daɗi da ƙaunar abokan nasa, ya ajiye file ɗin hannun nasa da matar Hafiz ta bashi yana gyara zama, "Wace shawarace da ku yanzu akan goma sha huɗun da muka samu? Dan kunga idan muka haɗa da baƙwai ɗin dake ƙasa sun zama ashin da ɗaya kenan".
Aliyu yace, "Hakane, ni dai a nawa ganin shine mu fara bincike akan gidajen da duk abin ya faru, dan abinda zai baka mamaki da ɗaure kai waɗanda abin ya faru dasu dak ƴaƴan masu gidan ne, ko ƴaƴan ƴan uwa, kuma babu gidan talaka, ƴaƴan talakawan da tsautsayin ya hau kansu duk masu aikine a gidajen".
"Shawararka tayi Aliyu, yanzu zamu rarraba yaranan cikin ofisoshin waɗanda abin ya faru a gidansu a gobe idan ALLAH ya kaimu, kowacce zata lurar mana da abu biyu, na farko zobe, na biyu sana'ar mutumin ko aikinsa".
Duk kai muka jinjina masa na gamsuwa, daga haka aka ƙara ɗan tattaunawa muka fito bayan an damƙama kowa aikin da zaiyi.............✍




ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.

https://www.facebook.com/groups/2803452939899949/?ref=share
[1/21, 11:54 PM] Abue Saleh AlQuyraemey: 🥚Ƙwai Ciki Ƙaya🥚
.
Book Two
.
Billyn abdul:
Page 53

.................Bayanan da Dattijon nan na tashar garinsu gimba ya kawo masa yay dai-dai da dukkanin hasashen Jay, abin sosai ya ƙara bashi mamaki da tsoro, babban mamakin shine minene alaƙar Hajiya Safara'u (Maman yara) da gidan Alhaji kokino tunda a gidansu ta fara aiki? Sannan minene dalilin da yasa ta turo masa gimba?. Bibiyar rayuwarsa take bisa umarnin wasu ko kuwa umarnin kanta ne?. Malam shehu shine ya haɗashi da gimba lokacin yana neman driver, dan malam shehun shine drivern da aka fara nemo masa kasancewar shi mutumne da baison tuƙi, kasancewar ya gansa babba yace a canja masa da yaro, dan bayason yaga babban mutum mai shekaru kamar na mahaifinsa ace yana aiki a ƙarƙashinsa gudun watarana kar wani dalilin ɓacin rai ya shigo ya aikata abinda bai daceba a garesa. Haka malam shehu ya kawo masa gimba a cewarsa ɗan garinsu ne, shikuma sai ya samawa malam shehu wani aikin a gidan gonarsa wanda bazai wahala ba, to a yanzu dai shekarun malam shehu kusan huɗu kenan da rasuwa, dan shekara uku da wasu watanni kaɗai yay yana aiki a gidan gonar ALLAH yay masa rasuwa dama yana da hanta.
         Hannun da ya tallafe kansa da shi ya janye yana furzar da huci. Yanzu idan yace zaije garin su gimba yamma tayi, ya kalli agogon dake a tsintsiyar hannunsa yaɗan lumshe idanu, lokacin ma tashi yayi, yanason su wuce gida da wuri kodan Bilkisu, ga kuma aikin da yake son suyi ma a gidan. Yaɗan fara tattare kayansa akai knocking ƙofar. Batare da ya kalli wanene ba ya bada izinin shigowa.
       Ƙamshin turarenta da yajine ya sakashi ɗagowa ya kalli ƙofar, kallo ɗaya zakai mata ka fahimci a matuƙar gajiye take, ya ɗauke idanunsa yana murmushi a ransa. Takardun hannunta ta ajiye bisa tebirin nasa tana faɗin, “Barka da yamma Sir”. “Yarinyar nan kin fara rainani wlhy” ya faɗa yana tura takardun daya haɗe cikin briefcase ɗinsa.
        Bily dake ɗan murmushi tace, “Rufamin asiri, ina ni ina raina shugabana”. Baice komai ba ya ɗauki takardun data ajiye ɗin, “Na minene?”. “Oga Hafeez ne yace na kawo maka ka saka hannu, yace dan ALLAH yanzun”. Rufe file ɗin yay ya ture gefe, “Ku wlhy ku barni na gaji, sai dai ya bari sai idan ALLAH ya kaimu gobe danni kam nama tashi”. Agogon hannuna na kalla sannan na kallesa, biyar da minti tara fa”. “Koma babu minti tara ne bazanyi ba, kije ki shirya mu wuce, idan kuma na barki anan to?”. Ɓata fuska nai batare dana ce da shi komai ba na juya zan fita, harna kama ƙofar zan buɗe na tsinkayi muryarsa yana faɗin, “Habawa yarinya badai gida zamu ba, zakiyi min bayani ai”. Idanu na lumshe da buɗewa a lokaci guda, kafin naɗan juya na kallesa, “To nama fasa binka, gidan Ummah zanje na kwana”. Da hanzari na buɗe ƙofar na fice ganin ya taso, sai da na tabbatar na sauka ƙasa sannan na dafe ƙirjina dake bugawa da sauri-sauri ina murmushi, juyawa nai na kalli saman sannan nabar wajen zuwa office ɗin oga Hafiz dan na sanar masa abinda yace.

        
★★★★★★★★

           Muna shigowa gida ana kiran sallar magriba, ɗakinsa ya nufa nima na nufi nawa, wanka na farayi sannan nai sallar magriba, bayan na idan na zura doguwar riga kawai na fito, kitchen na nufa dan na duba abinda zan samar mana muci kasancewar ya faɗamin Sadiq yayo cefane da rana. Ina fara ƙoƙarin ɗaura abu mai sauƙi da bazai takura mana ba ya shigo kicin ɗin, kallonsa nai da masa sannu, ya amsa yana mai kallon agogon hannunsa, “Miemaa bara naje yarinyar nan ta kirani inaga an dace”. Nace, “To ALLAH ya tabbatar da hakan, sai ka dawo”. Matsowa yay ya sumbaci goshina da faɗin “Amin nagode, sai na dawo”. “ALLAH ya tsare” na ƙara faɗa ina maida hankalina ga aikina shi kuma ya fice.
      Dawowarmu gidan sai tunanin ganin wallet ɗin ɗazun ta sake dawomin cikin rai, ina aiki ina sake juya al'amarin, da yake aikin ba wani mai yawa bane dan danan na kammala, na tanaji abinda zamuyi breakfast da shi dana tashi sai haɗawa. Shirya namu abincin nai a dining na saka hijjab na fita na kaima maigadi nashi. Sannan na dawo nai sallar isha'i, na gaji hutu kawai nake buƙata, amma yaya na iya, gaskiya a kwai wahala ga mace mai aure ace kuma tana aiki, yanzu mu biyu ne ka

wai fa, to inaga nan gaba ƴaƴa sun ƙaru kuma fa? Mace daban ce a rayuwa, na tabbatar ba kowanne namiji bane zai iya juriyar da mu mata mukeyi wlhy, ki duba dasun dawo aiki wanka kawai zasuyi suci abinci su huta, mace ko kota dawo ɗin wani sabon aikinma zata taras, harma shi kansa ya ƙara mata da wani a bayan fage, hakan kuma bazai hanata tayi sammakon tashi ba da safe. (Mata kuɗin na dabanne, idan nace na daban ina nufin nadaban aduk lungu da saƙo na duniya, ALLAH ya ƙara muku martaba da kwanciyar hankali a duk duniyar da kuke. “Maza banda jealous kuma👻dan gaskiya na faɗa🙈”. lol😂).
        Bai shigo gidan ba har tara saura, lokacin harma naɗanyi barcin wasu mintuna a falon. Jin ana shafa min kai na buɗe idanuna a hankali, cikin nasa suka shige, yana tsugunne gaban kujerar da nake kwance,
Showing 186001 words to 189000 words out of 249282 words