rigarsa, “Ai nafi ƙarfin ramawa ta haka yarinya”. Tsayawa nai ina kallonsa fuskata a marairaice, “To gani na dawo ai, amma dan ALLAH faɗamin ta yaya zaka rama? Nifa ɗazun wlhy bansan mizan baka bane shiyyasa na kashe”. “Kin tabbatar?”. Kaina na ɗaga masa. Yay murmushi kawai batare da ya sake cewa komaiba. Hakan yasa nace, “Naje dan ALLAH? Kaga an barsu su kaɗai”. Kansa kawai ya ɗagamin. Nikam tuni nai waje. Mamakine ya kamani ganin falon wayam, na leƙa ɗayan falon har zuwa ɗakina nanma babu kowa, a rikice na fito harabar gidan saina iske babu motarsu, abinda ya sake ɗaure kaina har Nabeelah babu itama. Dawowa nai ɗakinsa danna sanar masa saina iske harya shiga wankan, da sauri na ɗauki wayarsa dan tawa babu kuɗi ciki na shiga laluben sunan Ummu. Bugu biyu kuwa ta ɗaga tamkar dama jira take. Kafin tai magana nai sallama dan karta ɗauka ko shine, ko gaisheta ban tsaya yiba nace, “Ummu.......” katseni tai itama da faɗin nasan mizaki tambaya kwantar da hankalinki, Anuwar ne ya sake suma shiyyasa nace su taho gida, yana da Asthma shiyyasa gashi basu taho dako inhaler ɗinsa ba ma, sun faɗamin komai daya faru yanzu ina mijin naki shi?”. Ya shiga wanka Ummu, ya kumace zai sanarmin da komai daya shafesa”. “Alhmdllh mu dama wannan muke jira ai, saiki nutsu sosai ki fahimci komai yanda yake, ta hakane zamu tabbatar da abinda yake gaskiya, sannan nasan zai iya cewa zai biyosu idan ya fito yaji sun taho, karki faɗa masa Anuwar ɗin yana cikin wani haline, nafiso sai zuwa da safe idan ALLAH ya kaimu inma zaizo ɗin kuzo tare”. “To Ummu insha ALLAHU zanyi hakan, amma inaji a raina wlhy abinda muke zargin gaskiyane, dan yace mamarsa bata rasuba”. “Da gaske?”. “Wlhy kuwa Ummu”. “To shikenan bara na barki karya fito”.
       Ummu na yanke wayar kuwa na goge kiran na dawo ɗakin na ajiye masa wayarsa, fita na sakeyi domin yin salla nima dan anata kira.

     Koda Jawaad ya fito a gaggauce yay shiri ya fita massallaci, bai kawo komai a ransa game da rashin ganinsuba a falon, yayi zaton sun tafi salla matan kuma sun shige ciki, yanayin da yake ciki kuma ya saka bai kula da babu motarsu a harabar gidanba.
     Ana idar da salla gida ya nufo, dai-dai Bilkisu itama ta fito daga kicin tana haɗa masa abinci a d/table. Tsayawa yay kawai yana kallonta daga cikin falon...
     Jin idanu na yawo kaina ya sakani ɗagowa nima, cikin sanyin murya nace, “Ga abinci”.
     Ɗauke kansa yay daga gareni, ya tako zuwa dani ɗin yaja kujera ya zauna, “Su suna ina?”. “Sun tafi”. Na faɗa ina ƙoƙarin zuba masa abincin, Da sauri ya ɗago ya kalleni, “Bangane sun tafi ba, miyasa?”. “Takawane ya kira yace su koma gida hakanan”.
       “Aiko dolene na nabi bayansu dan zuciyata ta kasa samun nutsuwa, inason yima yaronan  tambayoyi”. Saurin zuwa nai gabansa murya a sanyaye nace, “Kayi haƙuri zuwa safiya mana, nima akwai abubuwa da yawa dazan faɗa maka game dasu wanda tunda naga kamaninka dasu naita samowa dama dan na kawosu gareka”. Murmushi yayi ya jawoni kawai ya rungume a jikinsa batare da yace komaiba.............✍

Maganar gaskiya man kaina ya gama tsiyayewa antafi yajin aiki daga yau😓😫🚶🏻.


ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.

SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.

HAF
[1/6, 5:08 PM] Abbu Saleh Kurami: SAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO

MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.

MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.

BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....

abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.

Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899

sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.

Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300


Sai kunzo😍😍😍😘.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.

Domin samun littafin Ƙwai cikin ƙaya daga farkon ko taɓa Link ɗin da ke ƙasa.
👇👇👇👇
.
https://www.facebook.com/groups/2803452939899949/?ref=share
[1/11, 10:48 PM] Abue Saleh AlQuyraemey: 🥚Ƙwai Ciki Ƙaya🥚
.
Book Two
.
Bilyn Abdull 📚:
Page 45

..................Ganin ya nata juya spoon a abincin ya kasa kai ko lauma ɗaya yasa tausayinsa kamani. nasan yana cikin yanayin ruɗani da shikaɗai yasan yanda yakeji, sai dai jarumtar ƴan mazan ta ɓoye komai daga fuskarsa harma da kuzarinsa. naɗan rumtse idanuna ina tariyo kalamun Umm-Anum. ‘Anya zan iya kuwa?’ na ayyana a cikin raina, daga can gefen zuciyata tace zaki iya ki daure, ruɗanin da yake ciki yana buƙatar kulawarki, hakan zai bashi nutsuwa. Kaina naɗan jinjina ina danne fargabata da matsananciyar kunyar da nakeyi na ɗaura hannuna akan nasa dake riƙe da cokalin.
     Ɗago lumsassun idanunsa yay yana kallona batare da yace komaiba. daƙyar na iya danne zuciyata nabar idanuna cikin nashi daya tsareni dasu, na langaɓe kaina cikin tsananin nuna kulawa nace, “Dan ALLAH ka kwantar da hankalinka kaci abincin karya huce, kagafa harka rame, kanaso Ummah tace bana kula mata da kai duk farfesun da take sawa kullum Nabeelah tana kawowa”.       
             Lallausan murmushi na musamman ya saki har dimples ɗinsa guda biyu na loɓawa, haƙwaransa suka fito kaɗan, yaɗan lumshe idanu ya buɗe a kaina yana faɗin, “Yarinyarnan na kula wayo kawai kikeson min dan karna fita”. Ya ƙare maganar a hankali yana wani kashemin ido ɗaya da ɗage gira sama.
           Hannu na saka na rufe fuskata ina murmushi, ba ƙaramin kasheni murmushinsa yayiba, dan nikam zan iya rantsewa ban taɓa ganin kalarsa daga garesaba sai yau, fuskata a rufe cikin tafukan hannuna nace, “Ni ƴar ƙaramarnan da nice zan maka wayo?”.
          “Ba gashi ba kinamin”. Yay maganar da kamo hannuna ya miƙar dani tare da zagayo dani inda yake ya ɗaurani saman cinyarsa, ya zagayo hanayensa duka biyu kan cikina, kansa kuma na bisa kafaɗata. Jinai kamar na nutse dan kunya amma na daure kaina a ƙasa nace, “karfa kasa wani yaji ya ɗauka da gaske ne, ina ni ina yima boss wayo, bayan kai ɗin wayon ne da kansa”.
       Kansa ya ɗaura saman wuyana yana huramin iskar numfashinsa, hakanne ya saka tsigar jikina tashi lokaci guda, naɗan ƙanƙame jikina ina haɗiye yawu daƙyar. Dai-dai saitin kunnena ya ɗora bakinsa yana magana a hankali kamar mai tsoron a jisa, “Ni ina naga wani wayo tunda gashi kinamin kuwa, a wajene Jay yake boss, amma a gaban Zinaran bawane, kece boss ɗin. buɗe idonki kiga wani abu”. Sosai maganarsa ta nema fasan kai, ashe mutumnan haka yake yana magana raɗam abinsa, amma yayta mana mazurai a office. Janye hanayen nawa nayi daga kan fuska a hankali harna kaisu ƙasa sannan na buɗe idanuna dake rufe. Ina buɗewa yana ɗaura laɓɓansa akan nawa. Na zaro idanu sosai dan ba haka na zataba. Shima idanun nasa dake cikin nawa yaɗan zaro yana cigaba da abinda yakeyi.
       Nasan banida ƙarfin dazan ƙwace, kuma ma nayi alƙawarin insha ALLAH bazan taɓa zama mai bijirewa a garesaba a komai da zaizo min dashi inhar bai taka dokar ALLAH ba. Ballantana a yanzu da nake hango tsagwaron damuwa akan fuskarsa, dannewa kawai yake dankar na fahimta. Mun kwashi tsahon mintuna biyar ahaka kafin ya barni, ya rungumeni muna sauke ajiyar zuciya a tare, ya sumbaci kuncina da wuyana, acan ƙasan maƙoshi yace, “Idan nace tadaban ina nufin keɗin tadabance har ƙasan ruhina Miemaa, a kwana biyu kacal da mukai dake na fahimci ƙyawawan abubuwa masu yawa daga gareki, inason mace mai juriya da biyayya akan abu koda bai mata ba, inason mace mai tsafta da ƙamshi, inason mace mai kawaici, kunyarki tana a farkon abinda ke ƙara miki daraja da girma, inason mace mai aji, mai addini, mai kamun kai, na tsani ballagazar mace mai rawar kai, da ace ƴammata da yawa zasu zama irinki da sun zama masu darajar daraja bisa daraja a wajen maza......” ya ɗagoni daga ƙirjinsa, muna haɗa idanun nai azamar maida kaina a ƙirjin nasa.
       “Ka daina huramin kai da yawa irin haka, yanda kake lissafin nan bankai haka ba, ni macece mai rauni, maison kulawa, waɗanan makaman suna saurin sakani bama mutum yarda, ada kallon bahagon mutum nima nake maka, wanda ba damu da damuwar kowaba sai abinda ya shafesa, amma a tsakanin jiya da yau na kula kai adaline mai sauƙi ga iyalanka, ka yafemin akan gurɓataccen tunanina, idan nace k

ai na dabanne ko a cikin mazan ina nufin nadaban a cikin miliyoyi, ba dan kafi sauran maza bane dan dukiya, ba dan kafi sauran maza bane dan ƙyau, ba dan kafi sauran maza bane dan darajar da ALLAH ya baka, kafi sauran mazan dan kai ɗin mai ƙyaƙyƙyawar ZUCIYA ne”. Na ƙare maganar da ɗora yatsana akan saitin zuciyarsa ina hawaye”.
        Bilkisu ko duniya zatace ƙarya nake saina faɗa, keɗin tadabance ko acikin nadaban ɗin kinzo da banbanci mai tazarar nisa.  
        “Karfa kasa mata sumin bugun kayan wanki”. Ɗagoni ya sakeyi yana murmushi, “Su sun isa ko kallon banza ga matar Jay ma”. Dariya muka ƙyalƙyale da ita a tare saboda yanda yay da fuska kicin-kicin kamar mai shirin shiga filin daga. Na yunƙura zan sauka daga jikinsa ya sake riƙeni. Naɗan marairaice masa batare da nabari mun haɗa idanu ba, “Yanzufa za'a kira sallar isha'i, ga abincin zai huce kuma”. Siririyar ajiyar zuciya ya sauke yana sakina, “Idan bakiso na fita akwai sharaɗi”. Kallonsa nai alamar ina sauratensa. tattausan hannunsa ya ɗaura akan haɓata ya matso da fuskata gab da tashi. “Idan har bakiso na fita sai dai ki ciyar dani da hannun nan naki, inba hakaba bazanci abincin nanba, kuma saina fita, kuma yunwa nakeji, kuma nagaji barci nakeji”. Ƙoƙarin juyar da fuskata nayi dan kunya da dariyar dake tahomin dan a narke yay maganar, amma ya hanani damar hakan, saima wani sake narke fuska da yayi irin na (Aji tausayina ɗinnan😔).
          Da sauri na jinjina masa kai danya barni na tashi nidai, zuciyata sai wani zallo take cikin ƙirjina tamkar zata fito, ga kunya kamar ƙasa ta buɗe na shige ciki, dan kusani ALLAH ba ƙaramar dauriya nakeyiba yasin.
      Ɗauke hannunsa yay ya gyara zamansa, hakan ya bani damar tashi tsaye, kujerar kusa da shi ya zaunar dani da juya kujerar yanda zanyi facing ɗinsa sosai. Ya zanyi, nina taroma kaina match ɗinan ai. Abincin na fara basa idanuna a ƙasa ban yarda na kallesa ba, amma shi inajin yanda idanunsa kemin yawo a zahiri da baɗini na, koda naɗan saci kallonsa sai muka haɗa idanu. Saurin maidasu nai ƙasa, daga haka ban sake ɗagowarba harna tabbatar ya ƙoshi. Ina murnar an gama zan tashi ya riƙe hannuna, kallonsa nai ya ɗagan gira, “Malama saura ke dan baza'amin ɗuraba ni kaɗai”. Dukda da gaske yunwar nakeji saina ɗan ɓata fuska nace, “Nifa na ƙoshi”. “Idan na yarda kenan”. Yay maganar yana ɗebo abincin ya kai bakina. Dole nima na haƙura na karɓa, yana bani yana addabata da kallo, hakan yasa duk naji na takura matuƙa. Sai da ya tabbatar na ƙoshi sannan ya barni.
          Naɗan kallesa ina tattare kayan ganin bai tashiba, kuma salla akeyi. Nace “Sallafa akeyi”. “Kin karyamin alwalata ai?”. Yanda yay maganarne ya sakani barin wajen da sauri na nufi kitchen. Bayan na kammala ɗauraye kayan na fito, ban iskesaba ya tashi, ɗakina na nufa nima domin gabatar da sallar isha'i.

            Sai da nai wanka na saka doguwar riga mara nauyi sannan na fito falon dan banji motsinsa ba, zaune na iskesa cikin kujera yana waya, ga takardu ya baza saman centre table. ‘Agogo sarkin aiki kenan’ na faɗa a zuciyata ina ƙarasawa. Kitchen na wuce domin ɗakko masa ko ruwa ne. Inaji a jikina kallona yake amma ban juyaba. Harna dawo ɗauke da ruwa da lemo bai gama wayarba, naja ƙaramin copy table na ajiye tiren sannan na ɗago na kallesa, ganin ni yake kallo na ɗauke kaina, “Wanne zan zuba?”. Maimakon ya bani amsa sai ya amshi kofin ya ajiye ya kamo hannuna, zaunar dani yayi a gefensa tare da kwantar da kaina a kafaɗarsa ya cigaba da wayarsa. 
        Bai jimaba sukai sallama ya ajiye yana ɗan guntun tsaki, ɗago kaina nayi na kallesa, kafinma na tambayesa yacemin, “Inaga yarinyarnan zan taka mata birki, iskancinta sake gawurta yakeyi, aikin nan kusan sati ɗaya kenan na batashi amma sai yawo takemin da hankali”. Tsaf na fahimci da Rose yake, dan naji muryarta ta cikin wayar, amma sai nai kamar ban fahimtaba nace, “Wacece?”. Tsakin ya kuma ja da ɗaukar wata takarda yana dubawa, harma na fidda rai da samun amsa sannan yace, “Rose” a taƙaice. Ƙin cewa komai nayi dan naga kamar ya hau sama.  Sai da ya gama shan ƙamshinsa niko nai kamarma na manta da sh

i a falon sannan ya juyo ya fara sakani wani aikin muka cigaba dayi tare, sai kusan goma da rabi sannan muka kammala, munayi yanamin bayani akan abinda suka tattauna yau da yaje office, da yanda suka tsara yanda abubuwan zasu kasance, tsarin yayimin, nakuma ƙara da shawarata dana fuskanci yaji daɗinta sosai.

____________________________

              Su Abdul-raheem kuwa suna isa masarauta clinic aka wuce da Anuwar, likitan da yay aiki da rana ma har yana shirin tashine na dare kuma zaizo ƙarfe tara, dole ya dakata, taimakon gaggawa ya shiga bashi, cikin amincin ALLAH ba'a wani ɗauki lokaci ba numfashinsa ya dawo dai-dai. Hannun Abdur-raham dake kusa dashi ya riƙe yana hawaye, “Abdull  kamarmu ɗaya fa da shi, komaifa iri ɗayane, Wlhy ina cikin ruɗani Abdull, ko ku baƙwa irin wannan mugun kamar dasu Abdul-Raheem ai, inason ku maidani wajensa naji wanene shi? Idan kuma kun sani ku faɗamin Please, karkuce na rasa hankalina wlhy a rikice nake, jinake zuciyata na wani irin tsitstsinkewar da bantaɓa jin tayi ba.....”
     Abdur-raham bai samu damar bama Anuwar amsaba aka sanar da zuwan gimbiya. Kanta tsaye kan Anuwar tayi, tashi Abdur-raham yayi ya bata wajen zama, ta zauna tanama Anuwar sannu. Hawaye na shatata a kumatunsa yace, “Ummu yau naga mai kama dani kama mai ban al'ajabi da saka zukata ruɗani”. Murmushi Ummu tai masa cikin sigar lallashi tace, “Nasan da hakan Anuwar....” “Kin sani? Kenan kema kinsan shi? Kuma kinsan muna kama Ummu?”. Kanta ta jinjina masa tana sake faɗaɗa murmushinta, “Anuwar muma kamanninku ba ƙaramin sakamu a ruɗani sukai ba alokacin da muka gansa, hakanne ya saka muka tura Bilkisu wajenku, muka kuma ƙirƙiri hanyar da zakuzo ƙasarnan danmu sake tabbatarwa...”. “Ummu kin sake sakani a duhu wlhy”. “Zaka fita insha ALLAH Anuwar, amma lokacin hakan baiyi ba. abinda dai nakeso shine ka kwantarmin da hankalinka kaji, komai zai warware fiyema da abinda muke hasashe”. “To Ummu, amma inason na sake ganinsa dan ALLAH”. “Eh to banƙi ta takaban ba, amma ina ganin mubarshi basai ka koma ba, hakan zai saka ya sake zaƙuwa da ganinka kaima, dan inason ku wuce saudia goben idan ALLAH ya kaimu, lokacin da zai biyo sawunku nan ku kuma kun wuce, hakan zaisa yaso zuwa saudia ɗin, mukuma dama wannan damar muke buƙata ai”. Kansa kawai ya iya ɗaga mata danshi ta sake dulmiyasa a ruɗani, amma sai yay shiru bai sake tambayar komaiba. A take ma Doctor ya shigo ya bashi sallama suka tafi sashensu Abdul-Raheem.
           A wannan dare inhar Anuwar yayi barci to ragaggene, gashi Ummu ta gargaɗesa karya kira Umm-Anum balle sukai ga tunanin sanar mata wani abun, kuma koda komawa sukai karsu sanar mata komai har sai Jay yaje saudia da kansa.
       Washe gari jirgin safe suka bi shi da Anum cike da tsarabar biki daga Ummu, daka kallesu kasan basa son tafiyar dan ransu duk a cinkushe yake musamman ma Anuwar, har jiyake kamar ya zauna yayta kuka, sam bayason tafiya bai sake ganin Jawaad ba, baiji wani abu daga garesaba kuma.

_____________________________

                Ɓangaren Shahudah kam an sallamota itama sun dawo gida, taji sauƙi amma dukta rame ta ƙara wani irin haske maiban tsoro kamar wadda bata da jini a jiki, gashi yanzu ko yawan magana batayi sai dai ka ganta tayi zugum kamar wadda abin duniya ya dama. Koda yake ya dametan, dan Shahudah tanama Jay so mai tsananin gaske, sai dai tanaji a ranta bazata taɓa iya shearing ɗinsa da kowacce maceba ballema Bilkisu ƙasƙantacciya da tazo ƙarƙashin inuwarsu cin arziƙi. Har yanzu zatonsu na akan bilkisu asiri taima Jay ya aureta wai.
        Shi Dad harya bar ƙasar ma yau kwana biyu kenan, dan wani business ne na gaggawa yace ya taso masa, ko sallama saita waya yayma Momy ma, da yake ta rigada ta saba da irin wannan halin nasan sam sai bata damuba bakuma ta kawo komai a ranta ba.

_________________________

              Koda na kammala shirin barcina ban nema inda ya keba nai kwanciyata a ɗakina, har barci ya fara figata naji shigowarsa ɗakin, banko motsaba balle yay tunanin idanuna biyuma, gadon ya hawo yana faɗin “Wannan amaryar dai matsoraciya ce, nasan idanunki

biyu ai”. Guntun murmushi nayi kawai batare dana motsa ɗinba. Mannani da yay da jikinsa ya sakamu sauke ajiyar zuciya a tare, ya busomin numfashi a saman wuyana zuwa kunne yana sake ƙanƙameni. “Kin fasa jin labarin kenan?”. Da sauri na girgiza kai, “Naga kamar ka gaji ne shiyyasa nai shiru, amma cike dake da zaƙuwa wlhy”. Murmushi ya saki mai sanyi yana matsa yatsun hannuna daya riƙe, “To aike miskilancinki bai bari asan kinason abu”. Sosai maganarsa taso bani dariya, amma saina dake nai murmushi kawai, wai ni yake kira miskila, ai shinema ya dace da wannan sunan bawai niba. Yanzunma bance komaiba ina dai saurarensa, saida ya gama jan ajinsa da shan ƙamshi sannan ya juyo dani muna
Showing 156001 words to 159000 words out of 249282 words