yanaji da azuminsa. Shidai ya lalaɓata kawai dan yana buƙatar nutsuwa baison hayaniya.
    Tuni yasa ana bibiyar masa bayan Ɓaleru duk inda ya sanya ƙafa batare da shi ya saniba, bayason kamasa a cikin watannan mai albarka shiyyasa yay tamkar ya manta da al'amarinsa, ga jikin ɗan-fir'auna da har gidan su Shahudah suka ɗauka ya mutu na nata sauƙi da warwarewa.

______________________

       Kwanci tashi babu wahala wajen UBANGIJI azumi yakai tsakkiya, a daren sha bakwai sarki Sameer da Amaryarsa suka dawo, anyi murna da dawowar tasu sosai, dan ranar kam kowa ya shaida hakan a masarautar gagara badau, ranar gimbiya da kanta taima Takawa abincin buɗa baki a kicin ɗinta na sirri da babu mai shiga sai ita saiko Amintacciyar baiwarta. Tunda ta tafi ɓangarensa su bily basu sake jin ɗuriyartaba sai washe gari, sai a randa za'a ɗau azumi na sha takwas ne suka ganta, shima dan tasaka a kira mata bily ne.
       Cikin girmamawa na gaisheta kamar yanda na saba, fuskarta ɗauke da murmushi ta amsa min tare da kamo hannayena cikin nata. “Ɗiyata dama nasa a kiramin kene saboda zaku wuce Umrah gobe idan ALLAH ya kaimu ke da su Amaturrahman, an kammala miki komai insha ALLAH” Dama Boss ya sanarmin tun shekaranjiya, sai dai na nuna mata farin cikina sosai akan hakan itama tamkar bansan da tafiyarba, nakuma mata godiya. Ta cigaba da faɗin, “Naso ace tun farkon azumi kika tafi, sai dai mijinki ya sanarmin hakan bazai yuwuba saboda aikinki, dan akwai wata auntyna matar yayan abokin Takawa tanada makaranta ta musamman domin koyar da amare, ana gyaran jiki da komai a ciki, koya girki da dukkan dabarun zaman aure, itama ƴar nan ƙasarmu ce, dalilin ƙaddara ta shigo rayuwarmu, mun kaita domin neman magani sai yayan abokin Takawa yace shifa yayi mata, wannan shine dalilin zamanta a can itama”. Fuskata ɗauke da murmushi nace, “ALLAH sarki”. Itama murmushi tayi, “Yanzu dai yayi dukkan cuku-cukun daya dace a wajen aikinku insha ALLAH keda nan sai saura kwana biyar tarewarki, inason naga kin zama cikakkiyar mace mai amsa suna mace a fadar mijinta, mijinki babban mutumne sannan yanada wasu sirrika dake kaɗai zaki fahimci kayanki anan gaba, shiyyasa nakeso a gyaramin ke yanda ya kamata domin zukatan maƙiya su girgiza, waɗanda suke ganin baki kaiba su fahimci kin musu zarrah ta har abada kinji”. Hawayen dake ziraromin na share, bansan irin godiyar da zanma wannan baiwaba a rayuwata, itaɗin ta musamman ce a cikin jerin abubuwa masu muhimmanci da suka shigo rayuwata, ALLAH ya biyata da aljannarsa.

      Washe garima naje wajen aiki, sai dai yau bashi ya maidoni ba sawa yay sabon direbansa ya maidoni, gobe idan ALLAH ya kaimu kuma bazanje aikiba, dan ƙarfe huɗu zamu wuce, share hawayen dake zubomin nake akan abinda ya faru tsakanina dashi yanzu a office ɗinsa. Na roƙesane akan zanje gidan Dad nai masa sallama, dama tun farkon azuminan naketa masa magiyar ya kaini na gaishesa, bai taɓa kulaniba sai yau da yanema marina a office, yajamin dogon gargaɗi akan inhar na sake masa maganar Dad ALLAH sai ya fasan baki. Sake share hawayen nai zuciyata namin zafi da takaucinsa,

ni bansan mi Dad yaymasaba haka da zafi shi da ahalinsa, inason ganin koda mutum ɗayane a cikinsu amma abin ya gagara, sam yanzu bana ganin Yah Qaseem, narasa ina ya shiga baya zuwa Office, mike damunsa? Minene matsalarsa? Haka kawai bazai bar zuwa office ba ai?. Zafin boss yayi yawa, nikuma har zuwa yanzun ban taɓa jin sonsa a rainaba, nasan dai zan iya haƙurin zaman aure dashi amma badan inajinsa a raina da kalmar soyayya ba, bansan miyasa hakanba, har zuwa yanzu Yah Qaseem ne kaɗai a zuciyata, shi nakeso, shi na fara so, sai dai shikuma banajin sha'awar zama dashi matsayin miji, bansan miyasa hakanba shima. Ya ALLAH ka kawomin ɗauki bisa ruɗaɗɗen tunanina daya banbanta dana sauran mutane a yanzu.

         Har muka bar ƙasar bana cikin walwala sam, sai wata irin matsananciyar damuwa da na tsinci zuciyata a ciki, wannan dalilin yasa har jirginma ya tashi ban tuna shine hawana na farkoba, Safah na lafe a jikina tana barci har muka sauka. mun sami tarba ta musamman daga wasu manyan mutane da bansan matsayinsu ba, sai dai ina tunanin waɗanda Gimbiya taban taƙaitaccen labarinsu ne ranar, sai dai wannan nafi ƙyautata zaton abokin takawane da iyalansa ba waccan mai makarantar bace da naji nafi ɗokin gani. Ƴan uwa abu mafi ɗaure kaina shine, maimakon najini cikin farin ciki da zuwa ƙasa mai tsarki a karo na farko a rayuwata sai saɓanin hakan ya biyo baya, kallonsu nike kawai tamkar wata sakarai, ƙirjina na wani irin zafi, sai can ƙasan zuciyata kuma nakejin wani irin sanyi dake kawomin sassauci a cikin ƙirjina kaɗan-kaɗan. Darene sosai, dan haka makwanci kawai aka bamu da abinci, nikam bammaciba na kwanta.

__________________________

            Yau tunda ya tashi aiki wanka kawai yaje yay a gida ya kimtsa, sabon drivernsa mai suna Sadiq ya ɗaukesa sai gidan Alhaji Babba dan acan yake buɗa baki yanzun kullum, wataran kuma gidan Ummah babba, kokuma gidan Ummah ƙarama idan ta ishesa da ƙorafi. Haka kawai yau yakejin tamkar wani abu dake nesa dashi yana tunkarosa, minene? A ina yake? Itace amsar dakanzo masa akai-akai cikin shauƙinsa.
      Shi dai Alhaji babba kallonsa kawai yake amma baice komaiba, sai da suka dawo salla sukai zaman buɗa baki sannan, ya kai dubansa ga Jay da keta juya cokali cikin kofin kuni yana ɗan murmushi. “Wai nikam gwauron nan yau miya saka farin ciki haka?”. Kallonsa Jay yay fuskarsa ɗauke da murmushin har yanzun, yace, “Babu komai Baba, kawai dai”. Murmushi shima Alhaji baban yayi, “Kawai dai haka ka tsinci kanka kaima ko?”. Kai Jay ya jinjina masa yana lumshe ido. Alhaji babba yace, “Nima haka na tashi da farin ciki, sai nakeji tamkar wani abu dana daɗe da rasawa zai dawo gareni, sai nakeji kamar wani abuna mai muhimmanci ya haɗu da abuna mai muhimmanci, sai nakeji kamar wani abun da na daɗe ina neman amsarsane lokacin sanin amsar yayi, a daren jiya nayi mafarkin ƴaƴana guda biyu cikin farin ciki, tabbas Jawaad inaji a raina wani abu mai daraja da haske na matsowa zuwa garemu”. Jawaad  sauraren Alhaji babba kawai yake yana murmushi irin wanda ya kasance mai tsada a garesa, ya ɗora kansa a kafaɗar kakansa yana sake ƙawata murmushinsa, “Ya ALLAH ya tabbatar da wannan hasashe naka ya zama alkairi kakana”. Shafa kansa Alhaji babba yay yana murmushi da faɗin, “Amin ya rabbi jikallena, amma yakama ka dawo nan kwanaki goman nan na ƙarshe muyisu tare cikin ƙololuwar ibada, ka ajiye duk wani aiki gefe”. Jay ya tashi zaune sosai yana kallon kakan nasa, yace, “Nima nayi wannan tunanin, sai dai banason takura maka da yawa”. Ranƙwashi Alhaji babba ya kai masa bisa kai, Jay yay saurin kaucewa yana dariya da haɗe hannayensa waje guda alamar na tuba.

       Bayan sun dawo daga salla suka iske Ummah babba da ƙarama sunzo, dama sunce yau zasuzo. Jay ya zauna tsakkiyarsu yana dariya da faɗin, “Saini ɗan gatan ALLAH, Ummahs ɗina duka tare dani”. Atare sukai dariya da riƙe hannayensa, Ummah babba tace, “Ja'iri kamar ya wani damu damu?”. Karyar da kai Jay yayi ya ɗora saman kafaɗarta, murya a sanyaye yace, “Idan ban damu da kuba dawa zan damu Ummah?, kuɗin duniyatace, sannan haskena, aikine kawai ke hanani rawar gab

an hantsi”. Guntuwar dariya tayi da shafa kansa, ta sumbaci hannunsa tana mai saka masa albarka.
        Kasancewar basu da ishashen lokaci suka fara tattaunawa akan maganar lefe da dama shine ya kawosu. Da farko Jawaad yace su barsa zaiyi, amma sukace sam bazai yuwuba, na farkoma dan an nuna musu fin ƙarfine Uncles ɗinsa sukace zasuyi, to wannan kam suma sune zasuyi insha ALLAH.
       Jawaad yay shiru yana murmushi dajin ƙaunarsu mai narkar da zuciya na ratsasa, zamansa ya gyara a kujerar daya koma shi kaɗai yana kallonsu, “Nagode sosai iyayena, kun sharemin hawayen maraici tuni, bani da abin biyanku sai dai naita muku addu'oin gamawa da rauwa lafiya, idan na ganku saina manta bani da Uwa, idan kuka kalleni sai nake ganin Mah-mah har yanzu tana tare dani, ida har tabar duniya ina roƙon UBANGIJI yasa ana nuna mata dukkan alkairanku ga gudan jininta, idan tana duniya ina fatan ganinta na bata labarin alkairanku ga gudan jininta, ku......” “Ya isa haka kaji Muhammadu, insha ALLAH inaji a jikina BILKEESU tana raye, insha ALLAH kafin nabar duniya saina ganta” Alhaji babba yay maganar yana share hawayen da suka ɗan zubo masa. Ummah da Ummah ƙarama ma kuka suke, Jay gwanin dakiya babu hawayen zahiri saina zuci kawai.

____________________________

              Kasancewar nazo babu tsarki sai yau nake fatan samu lokacin da zamuyi sahur saina duba, naji wani nishaɗi ganin ya ɗauke harda tsallena a bayi, wanka nayo da brush na fito, cikin tsokana Meenal tace, “Gandiya halan yau kin musulunta ne? Naga wanka da asubar fari”. Murmushi nai mata ina zama domin busar da kaina da hand drayer ɗin dana gani saman mirror ɗakin, nace, “Oh da kafira kike kallona?”. Dariya sukayi ita da Amaturrahman dake ƙoƙarin shiga yin brush itama, tace, “Ai kima godema ALLAH ke kina zuwa yana ɗaukewa, ita tana shigowa yana zuwa”. Cikin ɗan zaro idanu na kalli Meenal ɗin, sai kuma na langaɓe kai nace, “Kai harfa kin bani tausayi babie”. Filo ta ɗauka ta jehomin ɗaya ta jefama Amaturrahman. Da gudu Amaturrahman ta shige bayi tana dariya, nikuma na cafe wanda ta tillomin. “ALLAH karkiji wasa meenal tausayi kika bani” nai maganar da ɗan mata gwalo. Ƙwafa tayi da faɗin, “Wlhy duk zan rama, ke saurama ƙiris na raman ai, zaki gane kurankine”. Murmushi nai mata bance komaiba na cigaba da busar da kaina.
         Bayan munyi sahur salla mukai muka sake kwanciya barci, mune bamu tashiba sai sha ɗaya, shima tadamu akazo akayi. shiri mukai a gaggauce na tafiya massallaci, nidai   Kasa daurewa nai na tambayi Amaturrahman Auntyn da Ummu tace tanada makaranta gidansu kuma na kusa da inda zamu sauka?.
        “Lah Bily ai yanzu bazakiga Umm-Anum ba, sun shiga ittifaqi, kinga gidansu nan, duk Ramdhan idan mukazo bama ganinsu muma sai ranar sallah”. Da mamaki nace, “Basu da yara?”. Tace, “Sunada yara biyu mana, mace da namiji, namijin ya girmemu da kusan shekara biyar, sunansa Anwar, sai macen Anum, tare suke shiga ittifaqi. Tunkan na gansu naji sun matuƙar burgeni har ina zumuɗin ganin nasu mai ban mamaki, dan tunda Ummu taban labarin matar a taƙaice saita kasa barin zuciyata. Yanda na iso da ƙuncin zuciya a yanzu sai ba hakaba, fes nakejin raina cike da nishaɗi da farin ciki da shauƙin ganina a ƙasa mai tsarki, santin da banyi a daren jiyaba sai gashi a yau inayinsa, dan har muka isa massallaci bakina bai hutaba, Safah kam bata gajiya damin bayanin komai dalla-dalla. Lokacin dana ganni gaban ɗakin ka'aba sai kawai nakejina tamkar wata sabuwar Bilkisu ce tsaye ba wadda tazo da ƙunci ba, hawaye masu ɗumi na ziraromin bisa kumatu, abinda ban taɓa tunaniba koda a mafarki, wani nauyin zuciya da ƙunci da damuwar da natsinci kaina a gaba ɗaya cikin shekarunan sai naji tamkar an yayesu an zubar tare da ruwan wankan dana samu tsarki ɗazun da asuba. UBANGIJI mai rahama, UBANGIJI mai ni'ima.

           Muna zaune a wajen mutanen kirki, larabawan usul masu ƙyawawan zuciyoyi, bamu rasa komaiba, ibada muke babu wasa dansu Amaturrahman sun horu sosai, sannan sunada ilimin addini suna kuma aiki dashi, Umm-Aban koda yaushe cikin kulawa take damu sosai, nasamu sauyi iri-iri da ha

ske a rayuwata a cikin kwanakinan goma da mukai na Umrah, babu abinda mukeyi banda ibada, duk wata shiririta mun ajiyeta gefe, a kullum safiya bayan sahur muna waya da gimbiya, hakama su Ummie duk saina kirasu, Boss kam ko filashin bai taɓa haɗamu ba, sannan dukkan numbers ɗin ƴan gidanmu bana ganinsu a wayata yanzun, bansan yaya akai hakan ta kasanceba tunda nidai ban gogeba.

        Yau take salla, sosai massalacin ke cike, bayan an idar da sallah sai na dingajin juwa, duk yanda naso dannewa hakan ya gagara, bandai sanarma su Amaturrahman ba dan karsu tada hankalinsu, miƙewa nai da nufin na ɗan samu waje inda babu yawan mutane na huta ko zanji nutsuwa sai kawai hajijiya ta kwasheni. Sama-sama na jiyo wata nutsatstsiyar muryar ta ambaci “Yah ALLAH”. Sai jina nai a jikinta. Cikin ɗan larabcin da nakeji kaɗan-kaɗan na tsinci tanama wani wanda bansan ko waneneba magana akan ya bata ruwan zam-zam dake hannunsa. Gabana yay wata masifar faɗuwa jin muryar data amsa mata, murya irin wadda wajan mutum ɗaya na santa, muryar dake sakani bugun zuciya, muryar dake saka jinina gudu cikin jijiyoyi, da ƙyar nai ƙoƙarin ɗaga idanuna dake neman rufewa na sauke a kansa dai-dai ya miƙo ƙaramar goran ruwa wa matar da har yanzu nike a jikinta.............✍

ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.

SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
        ƊAURIN ƁOYE
      ALƘAWARIN ALLAH.

HAFSAT RANO tazo muku da;
         SAUYIN ƘADDARA
        ƊAURIN GORO

MAMU GEE tazo muku da;
           BURI ƊAYA
         ƘAUNAR MU.

MISS XOXO tazo muku da;
           KAIMIN HALACCI
           IGIYAR ZATO.

BILYN ABDULL tazo muku da;
          WUTSIYAR RAƘUMI...
         GUDU DA WAIWAYE....

abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.

Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899

sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.

Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300

Sai kunzo😍😍😍😘.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[1/11, 10:48 PM] Abue Saleh AlQuyraemey: Kwai Cikin Ƙaya!!
.
Book Two
.
Bilyn Abdull 📚:
BARKA DA JUMA'A

Page 37

..................Sosai su Amaturrahman ke santin gidan Jawaad na A.Y Street, badan yafi kowane gidaba, bakuma dan an cikasa da ƙawa ba, ginine dai tamkar kowanne gini da kowa yasani, sai dai yanda akai tsarin gyaran sai ya kuma fiddo da ƙyawun gidan fiye da yanda yake a da, (masu karatu karku manta wannan shine gidan da aka haifa Jawaad, a cikinsa iyayensa suka rayu, dan shine gidannan da turawannan suka bama Abba Abdul-aziz, shine kuma sanadin wannan arziƙi daya tsolema mutane ido). Sai da suka shiga ko'ina da ina dan babu komai cikinsa sai ƙamshin sabon fenti.
     Suna tsaka da dubawa Jay ya iso gidan, zaune yake a bayan motar sai Sadiq sabon drivern sa dake tuƙi cikin nutsuwa, dan shima dai baida matsala, amma hakan bai hana Jay tuna Gimba ba a kowacce daƙiƙa ta rayuwarsa, yasan gimba bazai mantu a zuciyarsa ba, dan yawuce duk tunanin mai hasashe a zuciyar tasa. Yauma kamar kullum yana cikin gayunsa da ƙyamshi, sai dai ya ɗan rame, hakan yasakashi yin wani fayau dashi, (bamu saniba azumin da aka shane kokuma ɗokin amaryarne. lol😂).
             waya yakeyi, hakan yasa har Sadiq ya fito ya buɗe masa bai fitoba, sai da yaja kusan mintuna huɗu sannan ya fito bayan ya ajiye wayar, Safah data dage sai anzo da ita da gudu tayo kansa, fuskarsa ɗauke da murmushi harta iso garesa, hannunsa ta kama tana gaishesa. Shidai kallonta yake kawai, dan sosai ƙiriniyarta ke bashi mamaki, ko gajiya batayi, girma take amma abun tamkar ƙaruwar mata yakeyi. (Hhhhh tunda Jinin Munaya na yawo a jikin Safah ai kaga abinda yafi hakama, sarki Sameer ne zai baka labari dalla-dalla😂🤐). Cikin ɗoki tace, “Yayanmu gidanka kaida aunty B ya haɗu sosai, nima harna zaɓi ɗakina dan kasanfa nan zan dawo. Murmushi yay mata mai sanyi ya jinjina mata kai amma baice komaiba.
      Sosai mamaki ya kama Jay lokacin da suka shiga ciki shi da Safah yay arba da Munubiya, shi tunaninsa Gimbiyace da kanta, itama ɗindai kallon mamaki take masan sai dai ita bamusan kona minene ba. Su Amaturrahman ne suka katse tunaninsa da gaisuwar da suke masa, ya amsa musu da kulawa kafin shima ya gaida Munubiya cikin girmamawa. Kasa haƙuri yay dai yace, “Ummu da kanki? Su Amaturrahman ma aisun isa basai ke kinzoba”. Munubiya tai murmushinta mai kama dana Munaya, kafin ta bashi amsa Safah tace, “Lah Yayanmu bafa Ummu bace, wannan Mami ce sweetheart ɗin Ummu”. Cikin rashin fahimta yake kallon Safah amma baice komaiba. Amaturrahman tace, “Yayanmu ai Ummu ƴan biyune, Mami itace hassanarta”. Ɗan waro idanu Jay yayi waje sai kuma ya shafa kansa, “Sorry Mami ai wlhy ni duk ɗaukata Ummu ce, bansan ita ƴan biyu baneba nasan dai tanada yaya mace”. “Karka damu ƙanina, Gida yay ƙyau masha ALLAH, ALLAH yasa rai akaimawa, ALLAH yasa a cika manashi taf da ƴaƴa ko jikoki zance”. Cikin murna su Safah suka shiga faɗin, “Amin”. Shidai a saman laɓɓa ya amsa nasa amin ɗin.
         Kasa jurewa Mami Munubiya tai ta koma gefe tai kiran Munaya, tana ɗagawa tace, “Sweetheart kingako mina gani ga angon nan?”. Daga can murmushi gimbiya Munaya tai tana gyara kanta a kafaɗar takawa, tace, “Nasan ina kika dosa sweetheart, tun randa na fara ganinsa nima naga abinda kika gani, wannan ne dalilin tura matarsa can ta ɗan zauna, sai dai bamu da tabbas, amma muna fatan ALLAH yasa ta kasance hakanne”. “Kai to amin kuwa, al'amarin akwai ruɗarwa, amma gaskiya bana tantamar alaƙa a tsakaninsa da Umm-Anum Sweetheart, nifa da farko na zata Anuwar ne wlhy, sai da nai masa kallon nutsuwa na fahimci yafi Anuwar cikar zati, Anuwar kuma ya fisa haske, hatta da maganarsu kumafa babu banbanci, bara sai dai mun dawo ma tattauna”. Daga haka Mami Munubiya ta yanke wayar ta koma ciki dan baƙin da suke jira har sun iso.
           
Showing 120001 words to 123000 words out of 249282 words