labaranmu a wannan karonma, naga baƙwa motsawa😪, bayan kuma gagarumin shirin da muketa shiri dominku🤗.
ALLAH ka gafartama iyayenmu🙏🏻😭.
Page 61
...............Cike da mamaki matuƙa Aamilah ke kallon Shahudah dake zaune gaban mirror'n ɗakin Mama Atika tana tsara kwalliya, taci jan wando da farar top ƙal mai ƙyau da akaima hoton zuciya a gaba, gefe kuma madaidaiciyar jikka ce mai azabar ƙyau da aka ƙawata da zanen furrani na zuciya.....
“Sister! Wai mi kikeyi hakane?”.
Ɗago manyan idanunta tai da sukasha kwalli ta kalli Aamilah, sake maida fuskarta tai ga mirror tana dai-daita janbakinta da yay mata ɗas a baki. “Harma tambayata kike Aamilah? Kin manta yau Valentine day?. A duk irin wannan ranar kema shaidace ai ina shiryama BB wani abu, sannan muɗan fita yawo koda dakene idan shi yace bai zuwa. Tunda matsalolin nan suka fara kema kinsan hakan bata kasanceba, to amma yanda aka maida auren nan namu ai wannan ranar ni tazomin a dai-dai, koba komai zan sake tabbatar masa yana nan daram a raina, a shirye nake kuma nai waje da waccan jakar baƙauya daga garesa da baƙin asirinta”. Cike da takaici ƙarara a saman fuskar Aamilah ta girgiza kai ƙwalla na cika mata idanu, “Sister yanzu nan duk tashin hankalin da muke a ciki keta soyayya ma kikeyi? Wlhy bantaɓa sanin akwai kunyaba a duniya irin jiya, hatta da ƴan gidannan kunyar haɗa ido nake da wasu dalilin halin da su Dad suka jefa kansu da mu, amma ke tun a daren jiya nagama kin ware kamar komai bai faru ba, ga Mom can kwance yanzu haka zazzaɓi ne ma a jikinta, wlhy badan su Uncle Sulaiman sun matsa fitar nanba nasan babu inda zataje. Duk shirmen Salman jikinsa a sanyaye yake tun jiya ya kasa fita ko ina yana tare da Mom, amma ke........”
Shahudah da kema Aamilah wani banzan kallo tunda ta fara maganar taja gajeren tsaki tana ɗaukar sosan hoda da ƙara gyara fuskarta. “Aamilah kenan, harma kece kike da bakin faɗamin ban damu ba? A kaf ɗinku nafi kowa shan kunya a al'amarinnan, dannice kullum mai posting pictures ɗin Dad a kowanne shafina, kinsan kuma yanda nake da ɗunbin fans. sannan a dukanin shafukansa hotunana yafi na kowa yawa a cikinku, wlhy tsabar baƙinciki gaba ɗaya shafukana na rufesu, ke a jiya saida na karya duka layikan na fasa wayar sannan na samu nutsuwa. Bayan wannan mikikeso nayi? Na rasa Dad, nakuma rasa BB a karo na biyu? Impossible dear, dolene na tsira da ɗaya, domin ina ƙaunar mijina. Nasan duk bayanin dazan miki ba fahinta zakiyiba tunda ba auren kikayi ba, dan haka karki bari a jimu a gidan mutane”.
Baki a matuƙar hangame Aamilah da Mama Atika dake a kwance tana duk saurarensu suke kallon Shahudah data jefa Cingam a baki tana ƙara gyara zaman gashin dokin dake a kanta da siririn mayafin data yafa. Juyawa tai tana kallonsu kanta tsaye, “Kumuje. dan nifa namafi son mu fara isa dan naga Maman BB sosai naga kuma kalar tarbar da zatamin. Sannan naɗan faracin uban yarinyarcan kafin zuwa dare na tare”.
Uffan babu wanda yace mata a cikinsu, Aamilah ta taimakama mama Atika ta tashi zaune dan dama tuni ta shirya, badan tasoba zata bisu, sai dai kawai waɗanda suka bada shawarar zuwa gidan Alhaji babba a yau sunfi su da basa son zuwa rinjaye, batason kuma tace bazataje ba a fassara al'amarin da wani abu daban, ko aga kamar tana baƙin ciki da dawowar Bilkisu ne.
Sun iske mafi yawan jama'ar gidan suma duk sun fito harabar gidan, fitowarsu ta saka kowa ya zubama Shahudah idanu, dan taci wani uban dogon takalmine bayan ɗamewa datai cikin wando da riga. Uncle Sulaiman ya kalleta cikin ɓacin rai zaiyi magana Uncle Sadiq yay saurin riƙe masa hannu yana girgiza masa kai alamar karya ce mata komai, dan yasan yin maganar kan iya janyo wata fitina daban musamman ga mama Atika da tun jiya taketa datsama mutane magana a gidan tamkar ba uwace a garesu ba.
Haɗiye maganarsa Uncle Sulaiman yayi, badan yaso hakanba. A sauranma babu wanda yay yunƙurin cewa komai, sai dai sunata kallon Shahudah data toshe da baƙin eyeglasess ga cingam a baki tanata tauna hankalinta a kwance.
__________________
ZAFAFA 2021
_______________
Masoya naku taurarinfa sun sake dawowa da sabon salo a 2021.
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
Kasancewar mai martaba ya sanar da wuri zasuzo saboda yanada zaman meeting da su manyan jihar zasuyi game da abinda ya faru akan su Dad, tun daga sallar asuba bamu koma barci ba, aunty Batool da Boss suka fita suka haɗo kayayyakin da za'a buƙata na haɗa abinci, kasancewar munada yawa dandanan muka shiga hada-hadar haɗa breakfast. Koma nace dai sunayi, dan nikam bama wani aikin kirki nakeba dan sam banajin daɗin jikina. Wasu na gyaran gida wasu na haɗa abinci haka akai aikin, zuwa takwas na safe komai yayi tsaf kowa nata ƙoƙarin yin wanka. Da yake boss ya ɗakko mana kaya ni da shi tun fitar da sukai da aunty Batool sai banji damuwa da tunanin mizan sakaba, nai shirina tsaf cikin doguwar rigar lass ɗin daya ɗakko mini, sai dai bayan fauda babu abinda na ƙara, turarema kaɗan na saka na yafa mayafi na fito falo inda nake ɗanjin maganganun su Anum.
Zamana baifi da mintuna uku ba mukaji ƙarar buɗe gate, miƙewa duk mukayi, Boss da Anuwar ma suka fito tare da Alhaji babba da suka sakko a tsakkiya, yasha gayu cikin farar shadda ƙal harda babbar riga, fuskarsa fayau alamar gyaran fuska yasha a ciki, sai baza ƙamshi suke su duka ukun. Ido muka haɗa da boss mukaima juna murmushi.
Sune suka fara fita, mu kuma muna biye da su. Lokacin har motocin guda uku zuƙa-zuƙa sun gama shigowa, sauran kuma duk sun tsaya a waje alamar bazasu samu waje ba dan habar gidan batacin mota fiye da bakwai. Akwai kuma ta Batool, boss sai na Alhaji babba guda biyu.
Abu-Siddiq ne ya fara fitowa, sai Abbu. Da gudu Anum ta nufi Abbu ta maƙalƙalesa, shima ya tarba ɗiyarsa cike da ɗoki da kewa duk da shekaranjiya suka rabu. Mota ta biyu, Gombiya munaya sai mai martaba Sarki Sameer Saifudden cike da izzarnan tasa da kwarjinin girma da mulki, a take dogarai suka fara jera masa kirari tare da lulluɓe gaban motar har saida ya fito. (ALLAH ya taimaki ɗan autan jimina gagara ɗaukar shaho. Ɗawisu sarkin ado, hadari sa gabanka inda kakeso, kaga dutsen cikin ruwa bakasan ana rana ba, kainuwa dashen ALLAH. Ɗan sarki, jikan sarki, baban sarki kuma insha ALLAHU). Duk da sarauta da mulki na wannan sarki yana girmama duk abinda ya kasance a gabansa, ma'ana wanda yasan ya girmesa a shekaru, dan haka koda Alhaji babba da su jay suka ƙarasa gabansa ƙasa ya rissinar da kai alamar girmama ga Alhaji babba. Dan ya tabbata a haife zai haifesa.
Sosai Alhaji babba yaji daɗin wannan girmamawa har fuskarsa ta bayyana.
Ba'a ɓata lokaci ba akai musu jagora zuwa babban falon baƙi na Alhaji babba da yasha gyara da ƙamshi, an kuma shirya musu abincin karin kumallo.
Gambiya na riƙe dani sai faman taɓa jikina take da tambayata mike damuna. Nidai kaina a ƙasa nake faɗa mata babu komai, kawai gajiyace, da yake ita bata bi su takawaba muna tare da itane sai Ummah ƙarama ke faɗa mata ai ta samu jikane. A take Ummu ta rikice da murna ta rungumeni a jikinta kai kace niɗin jininta ce da gaske. Hakan ya ƙara saka kimarta da mutuncinta gasu Umm-Anum dama duk wanda yake a wajen.
Daga haka mukai zaman yin breakfast, inda Ummu ta saki jikinta sosai kodan dama can ta riga ta saba da Umm-Anum ne oho. Sai dai kowa yaci ya ƙoshi Alhmdllh sannan su Nabeelah suka gyara wajen, bandani da Umm-Anum ta hanani tashi, a cewarta na zauna na huta haka nan.
★★★★
Acan falon baƙi kam Abbu kasa sakewa yay yaci abinci saboda nauyin Alhaji babba da yakeji, hakama takawa da ƙyar yasha haɗaɗɗen shayin da Umm-Anum taima dahu na musamman saboda tasan shi da Abbu suna matuƙar son shayin, dan idan takawa yaje can sosai yake shansa, sai farfesun kan rago da shima yana matuƙar sonsa.
Alhaji babba babu ruwansa, mutum ne mai sakewa da jama'a dajan na ƙasa da shi a jiki, dan haka yayta jansu da hira hardai suka saki jiki da shi, musamman Abbu daya fahimci shine surukin nashi kodan nannoƙewar da yaketa famanyi.
______________
Bayan kammala cin abinci dukanmu muka ɗunguma falon baƙi inda su takawa suke kamar yanda Alhaji babba ya bada umarni, muna gama zama sai ga kira ya shigo wayar boss, tashi yay ya fita, mintuna baifi uku ba ya dawo ya sanar da cewar su Uncle Sulaiman ne. damar shigo da su Alhaji babba ya bada.
Tunda suka shigo falon idona ya sauka akan aunty Shahudah sai kaina ya ɗaure, bawai alamunta na nuna bata tatare da damuwa bane, bakuma shigartace ta bani mamaki ba dan dama nasaba ganin abinda ma yafi hakan, yanda take ta faman shigewa jikin Boss da shi hankalinsama baya kantane ya bani mamaki, inajin lokacin da take faɗa masa wai tanason magana da shi. Banji ya bata amsaba, baima kalleta ba naga yabar inda take ya nufi kusa da Alhaji babba ya zauna.
Harara ta watsomin tare da jan tsaki ta koma kusa da kakarsu ta zauna dan tsallakawa inda boss yake dai babu dama na sani. ɗauke kaina nayi tamkarma ban gantaba, dan ni bata gabana wlhy.
Sai da aka fara buɗe taro da addu'a kamar yanda addini ya koyar, kafin kowa ya fara magana Umm-Anum ta kalli Alhaji babba, cikin girmamawa ta roƙesa dan ALLAH tanason idan da hali a kawo Dad da Uncle Nasir da Alhaji kokino gidan kafin ita dai tace komai, dan tanason ta maimaita dukkan abinda ta sani a gabansu gudun karma ace ta musu ƙazafi.
Kowa kallon Boss yayi, dan ansan dai wannan aikinsane. Kansa ya girgiza yana gyara zamasa, “Bani da wannan damar, domin case ɗinsu babbane, sai dai........” sai kuma yay shiru yana ɗan kallon sashin da Takawa yake. Murmushi sarki Sameer daya fahimci inda ya nufa yayi, baice komaiba ya ɗauka wayarsa ɗaya a cikin wayoyinsa, ɗan danne-danne yay kafin ya ajiye, da alama dai text message ya tura. Babu jimawa kuwa wayarsa tai ƴar ƙara alamun shigowar saƙo. ɗauka yay ya duba, sai kuma ya ajiye yana kallon Boss, shima kallonsa ya keyi, Takawa ya jinjina kai alamar an gama. Murmushi Boss yay yana rissinar da kansa akamar girmamawa da jinjina.
Da ɗan lokacin jira ne Gimbiya tai amfani wajen basu labarin yanda akai su Takawa suka tsinci Umm-Anum, har kaita asibiti da maidata saudia, da maganin da aka nema mata, bata kai ƙarsheba aka iso dasu Dad kowanne a cikin ankwa. Gaba ɗayansu kansu a duƙe sun kasa kallon kowa dake falon saboda kunya, jami'an tsaronma dake a tare dasu basu bada damar kowa ya raɓi inda suke ba, dan cikin kuka Aamilah ta nufi Dad amma sai suka daga mata tsawa, hakama yaron Uncle Nasir autansa hanashi taɓa Abbansa akai, dole ya koma jikin mamansa yana kuka itama tanayi.
Gyaran murya takawa yay, a take falon yay tsitt, sai ƙarar ac kawai data taimakawa cinkushewar falon kakeji, dan falon yay matuƙar cika sosai. Hakan ya saka Jay miƙewa ya tada yaran da ƴammatan yace su koma falon cikin gida. badan sunso ba duk suka miƙe har bily. sai dai kuma Alhaji babba ya buƙaci Bilkisu ta dawo. a cewarsa zaman yanada nasaba da ita ita da Anum.
Dawo mukai muka zauna, dama a raina naji haushi ganin banda Shahudah aka kora sai mu, dan ƙin tashi tayi ita, duk da kuma harda ita ya nuna ɗin.
“Inaga kuka bashi bane ya dace ace munyi a wannan lokacin, haƙuri dayin amfani da lokacin zamuyi domin warware matsalolin dake a tsakkiya”. Takawa ya faɗa a hankali yana kallon kowa dake falon. Hakan yasa kowa ya sake nutsuwa aka sake maida hankali ga Gimbiya data cigaba da bada labarin Umm-Anum, bayyanar cikinta da kuma aurenta da Abbu da haihuwar Anum. Sai a yanzu Dad, Uncle Nasir, Alhaji Kokino sukama fahimci halin da ake ciki. Gaba ɗaya ganin Umm-Anum dajin ƙarin bayani game da ita daga bakin Matar sarki ya sakasu diriricewa, sai kallonta suke hawaye na kwarara bisa fuskokinsu. Uncle Nasir ne cikin kuka yace tabbas BA FARKON BA ƘARSHEN, da ace nasan da zuwan wannan rana da ban biyema yaudara ta azzalumai irinku ba Alhaji Sadi, yau gashi babu Abdul-aziz a duniya amma ina cikin tsananin kunya mai muni dako ƙaramin ɗana banason duba, mama kin bada gudunmawa, kema....” yay maganar yana kallon Mama Atika data duƙar da kai ƙasa tana hawaye. “Da baki zama mai hassada da ƙyashi ba da ban tsinta kaina a wannan halinba, da baki zama maison tafi kowaba da ban tsinci kaina a hakaba, tabbas ke uwace mahaifiya a gareni, amma tun daga jiya na farajin nadamar hakan, kaicon rayuwar da take ƙarewa da dana sani da ruɗani. kaicon jin daɗi da arziƙin da sakamakonsa yake zama wuta, inama nine Abdul-aziz...........”
“Bashi bane kai, bakuma zaka taɓa zama shiba azzalumi, mai maida hallaci da butulci”. Umm-Anum ta faɗa a harzuƙe idanunta sun kaɗa sunyi jazur da ɓacin rai.
Numfashi takawa ya sauke yana gyara alƙyabbarsa, yace, “Inaga mai makon wannan kace nace ɗin, mizai hana mutafi kai tsaye akan abinda ya taramu nan. Umm-Anum, mike faruwa?”.
Cikin soyewar zuciya Umm-Anum ta kalli Takawa da yay mata maganar tana haɗiye zafin da takeji a ƙirjinta, kafin ta maida dubanta ga jama'ar falon baki ɗaya. “Basai na maimaita ba kowa yasan wacece ni, ɗiyar wacece, sannan wanene ya kasance mijina a shekarun baya, gwagwarmayar da akasha kafin zamansa wani abu harma ya zama wani abun. Abdul-aziz mutum ne mai matuƙar son ƴan uwansa, bai haɗa sonsu da kowaba hatta ɗan da ya haifa, yanda yake ƙaunarsu al'amarin har tsoro yake bani, dan nidai nasan suɗin da wahala ace suna sonsa kamar haka. Sai dai kuma ban taɓa magana ba, dan hakan ba hurumina baneba. Halayyarsa ta samo asaline kuma da yanda mahaifiyarsa tai masa tarbiyya akan ƙyaunar ƴan uwansa da zuciya ɗaya. Abdul-aziz yanada abokai tunkan yazama wani abu, sai dai babu wanda yafi shaƙuwa da shi kamar Sadi Kokino duk da kuwa ya girmesa da shekaru masu ɗan tazara. tare sukai karatu tamkar yanda ya faɗa min, sannan kuma aminine a garesa bawai aboki kawai ba. Sadi ya taka matuƙar rawa a bikinmu dan a lokacin yafi Abdul-aziz abin hannu, saboda shi yana juya dukiyar da mahaifinsa ya rasu ya bar masane shi da ƙaninsa. Bayan aurenmu nasha zuwa gidansa wajen matarsa, hakama matarsa tana zuwa wajena sosai, a haka muka zama aminai sosai har ALLAH ya ɗaga darajar Abdul-aziz ya zama gwamna, wanda Sadi yana ɗaya daga cikin waɗanda suka tsaya tsayin daka akan hakan har Abdul-aziz ya amince duk da baya buƙata. Harga ALLAH siyasar da Abdul-aziz ya shiga bata taɓa kwantamin a rai ba, sai dai nayi shiru ne saboda su Mama maryam da Baba duk sun amince masa, kuma shima naga ya karɓa, Alhaji kokino yana ɗaya daga cikin waɗanda sukaita nunamin muhimmancin mutane irin Abdul-aziz a cikin masu mulkin ƙasarnan, tun ina ganin suna tunzurashine kawai harna yarda dasu na shiga jerin masu masa addu'a. A haka ya kammala shekara huɗun farko a gwamna aka tsaidashi takarar shugaban ƙasa a bazata. Yaso ya bijire a lokacin kam, amma muka tsaya kai da fata ni da Sadi da Nasir da wasu a ƴan uwansu wajen roƙonsa ya tsaya tunda jama'ane suke buƙatar hakan. Haka ya haƙura dan darajar roƙon da mukai masa. An shiga hidimar kamfen da sauransu har dai gwamnati ta tsaya, Abdul-aziz ya zama shugaban ƙasa. Harkokin mulki sun fara zama da ƙafafunsu yanada watani huɗu, dan anyi naɗe-naɗe ga waɗanda ya dace, ciki harda Sadi wanda ya samu muƙami mai tsokar gaske, hakama Alhaji Ali. cikin amincin ALLAH suka fara fiddo ayyuka na cigaban ƙasa wanda ina ɗaya daga mashawartan na cikin gida. Ƴan ƙasa nata murna da nuna jin daɗinsu, sai dai kuma ga Abdul-aziz abubuwa sun fara canjawa, walwalarsa da kuzari duk sun fara raguwa, idan ya zauna sai kagansa zugum tamkar wani wanda abin duniya ya addaba. Abotarsa da Sadi kokino kamar ta fara ja baya, dan yawan zuwa da ya keyi gidan sai naga ya rage daga shi har Ali. A koda yaushe ya dawo gida yana manne da Jawaad kamar wani wanda za'a ƙwace masa shi. Idan na tambayesa mike damunsa kuma sai yace dani babu komai, ko yace, “Harka mulkin ƙasarnan sai addu'a Bilkisu, babu komai cikinsa sai baƙin tashin hankali, a zahiri kawai shugaban ƙasa yake amsa sunansa, amma a baɗini ɗaure yake tamau agun waɗanda ke zagaye da shi”. Nakan nema fashin baƙi akan wannan magana a duk sanda ya yita, amma sai dai yay murmushi kawai baya cewa komai. Tun ina ƙoƙarin tambayarsa ma harna daina, sai dai inata masa addu'a. Yana wata na goma da hawa mulki nakasa haƙuri nai masa tambaya akan Sadi da Ali, amsar daya
Showing 234001 words to 237000 words out of 249282 words

Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗
Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗
Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗
Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
09033181070
Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO
TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
______________________
Gidan Alhaji Babba
_________________________

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79 Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84