yasa ƙarfi wajen janta har hannu ɗaya ya fincike yana lililo, duk dai ya ganta yiyai tamkar basan da zamantaba, baba maigadi dai tun ɗazun yana hangen Qaseem ɗin daga ɗakinsa, tsabar baison yafito ya gansa ya sakashi aikin tayashine ya sakashi maƙalewa cikin ɗakin yana leƙensa ta Window. Jikkar ya dangwarar ya sake juyawa zuwa sashensu, daga shi sai gajeren wamdo da baƙar singlet datai mugun fidda masa siffarsa ta ƙaƙƙarfan namijin dake cin ƙarfe. Saida taga ya shige kafin ta juya da gudu gulma na cinta har saura kaɗan ta faɗi, ALLAH dai ya ara mata damar dafe ƙarfen da aka ƙawata barandar ƙofar falon nasu dashi, ƙara kwasa tai a gujen ta shiga tana ƙwala kiran Momy dake sama abin duniya ya isheta ga Shahudah tsaye kanta tana ribzar kuka da mata fitsara. Sosai kiran da Aamilah ke mata ya firgitata, ta miƙe zumbur ta fito tanabi matakalar benan da gudu-gudu. “Haba auta wannan wane irin kirane haka kamar wata baƙauya, miya farune shin kikemin kiran mafarauta?”. Baki Aamilah ta cuno bayan ta murguɗama Momy kamar wata sa'arta, kafin cikin taɓara tace, “Kajimin Momyn nan, dama kika samu na taimakeki na kawo miki labarin da ɗuminsa, toga ɗankican yana haɗa kaya da alama barin gidan zaiyi”. Sosai gaban mom ya faɗi, batama tsaya saurararta wanne a cikiba ta fice daga falon da sauri, dafa mata baya Aamila tayi tare da Shahudah data fito idanu a kumbure.
Qaseem dake ta faman lodama ƙatuwar motarsa kayan yayma momy dake masa magana kallo ɗaya ya ɗauke kai batare da yace da ita ko ci kanki ba. Muryarta har zuga take na alamun ɓacin rai tace, “Qaseem wai badakai nake maganaba? Shin mikukeson maidanine a gidannan kai da Shahudah? shin bazaka nutsu kai ka fahimci uzirinmuba, Na shiga uku ni Aysha, wane irin mugun asiri wannan yarinyar ta haɗaku da shine kaida yaronan Jawaad da kuke ɗaukar kowa ɗan iska akan lamarinta?”. Cikin zafin murya Qaseem yace, “Nifa kin bala'in cikani da surutu hajiya, Please ki barni nai aikin gabana Mtsooww!!”. Ya ƙare maganar dajan wani wawan tsaki yana ɗauke kansa ya cigaba da loda kayansa a motar. Mutuwar tsaye kawai Momy tai tana kallonsa, Aamilah ta kwashe da dariya tana kallonsu, “Faɗan Uwa da ɗa abin birgewa, kucigaba da gashi guys”. Baki Shahudah ta taɓe tana mai juya manyan idanunta alamar zubama Qaseem harara, tace, “Ɗan jaraba duk bakai kaja manaba, wani iyayi da ƙwala kai a farantinne ya kaika nacema banzar yarinyarnan ƙazamiya mara gata, idan da baka maƙale matanba ta gidan uwarwa aurena da naka zasu haɗu ballema har bb ya aikata haka, asararre kawai mai baƙar zuciyar tsiy.....”
Jikake tasss!! Qaseem da babu wanda ya lura da isowarsa gaban Shahudah ya sauke mata wani wawan mari, ƙasa ta zub
e tana garsheƙ
ar kuka daja masa ALLAH ya isa, to daman zuciyar ƴan mazan a kusa take, neman wanda zai amayarwa yakeyi, gashi ya samu cikin sauƙi, dan haka ya shigar tamkar an aikosa. Duk ihun da Aamilah keyi da Momy bai sauraresuba, sai ma tsarabar mari Aamilah ta samu itama, Momy kuwa ya hankaɗeta. Qaseem yanada Masifaffiyar zuciya irin wadda idan ta yunƙuro ɗinan sam bayajin bari, dan tamjar zugasama yake, sannan shifa cinnakane baisan na gidaba. Wanna. mugun zuciyan da ALLAH ya basu shida Jawaad itace ta hanasu zama ƙarƙashin inuwa ɗaya, dan kowa yanaji da kalar tasa, kawai shi Qaseem yafi Jawaad saurin fushine, dan Jawaad na dannewa yay kawaici har saika kaisa ƙarshe, amma ga Qaseem sam ba haka bane, sha yanzu magani yanzu, ga kuma ɗanbanzan riƙo saikace dangin kutare🤦🏻.
Iya gwargwadon iko babu algus Shahudah ta daku harma da Aamilah daya koma haɗawa daga ƙarshe, dama yanajin haushinsu akan abu biyu, dukan Bilkisu da jimata ciwo, saikuma gudunmawar da suka bada akan ai masa aure da Azeema. Daƙyar da suɗin goshi baba mai gadi da kuku suka amshi Shahudah da Aamilah a hannunsa, dan yay musu kaca-kaca abinka da farar fata, Shahudah harda fasa mata baki akai jini sai ɗiga yake. Yace, “ƙananun marasa kunya, daga yau idan harku kun cika tsagerune dan ALLAH kusake shiga cikin al'amurana”. Kuka kawai suke daga su har Momy, babu wanda ya iya tanka masa har kuku da baba mai gadi suka gama loda masa kayansa a motar, sashensu ya koma ya ɗakko sauran tarkacensa ya shige mota ya fice batare da ya sakebi takantaba.
Kai tsaye gidansa ya zarce, dama harya ajiye mai gadi tun jiya, kodaga waje kasan gidan ya haɗu, ya mugun ƙawatuwa da shukoki masu ƙamshi da daɗi, ga ƙamshin sabon fentima na tashi. Dakansa yayta shiga da kayan, da yake ALLAH yayisa mutum mai hanzari da zafin nama sai gashi ya gama sakasu ciki tas.
★★★★★
Bayan barin Qaseem gidan babu jimawa Dad ya dawo, iske Momy yay zaune ta zabga tagumi, Shahudah na kwance barcin wahala yay gaba da ita ta ɗora kanta a cinyar momyn. sai Salman da Aamilah dake lido a d/table. duk sannu sukai masa, ya amsa yana zama kusa da momy tare da kamo hannunta cikin nashi. “Humairah mike faruwane?”. Muryarta na rawa tace, “Qaseem ne ya tafi?”. “Ya tafi? Ina ya tafi to?”. “Muma bamu saniba, ya kwashe duk kayansa na gidannan”. Cikin taune leɓe Dad yace, “Bari dai zamuyi magana, yanzu tare nake dasu Alhaji Nasir suna falon baƙi, mun kira yaronan ne da aka ɗaura aurensa da mamana zaizo”. Zumbur Momy ta miƙe jikinta har rawa yake ta ture kan Shahudah batare data tuna tana jikinta tana barciba, tace, “Ya yarda ɗin zaizo Dadynsu?”. Fuskarsa ɗauke da murmushi yace, “Eh ya amince, drivern Alhaji Nasir ma yaje ɗakkosa”.
____________________________
Bayan Jawaad ya dawo daga sallar magriba shiryawa yay ya amsa kiran da Alhaji babba yay masa, kansa ciwo yake masa, amma bashi da ikon bijirema kiran kakan nasa, ballema yaji muryarsa wani iri kamar yana tare da damuwa, tun da ranama ya fahimci hakan, ya haƙurane kawai ya barsa da yace masa babu komai..
Fitowa yay yanata baza ƙamshi, sai dai fuskarnan a cinkushe babu walwala. ya tsaya suka gaisa da mai-gadi har yake tambayarsa gimba bai shigo bane?. mai-gadi yace, “Aiko bai isoba Oga, ni harma na fara tunanin ko lafiya? Dan tunda ya tafi bamuyi wayaba kuma kaga har lokacin daya saba dawowa ya shige amma shiru”. Jimm Jawaad yay alamar tunani, dan shima dai tunda gimba ya tafi basuyi wayarba kam, to wannan hargitsicinne ya ɗauke masa hankali gaba ɗaya har bai ɗauki hakan komaiba. Ya ɗan sauke numfashi yana kallon mai-gadin. baba bara dai naje na dawo, idan har lokacin bai shigeba saina nemesa naji mike faruwa?”. Mai gadi yace, “To to ba laifi oga, ALLAH ya maidoka lafiya”. “Amin” Jawaad ya faɗa yana ficewa, sai dai acan ƙasan zuciyar tasa maganar gimba taƙi gushewa.
A ƙofar gida ya iske Alhaji babba zai shiga massallaci, dan haka yay fakin anan waje ya fito suka shiga tare, bayan sun fito Alhaji baba yay sallama da mutane maƙwaftansa da ragowar ƴan anguwa masu salla anan kamar yanda ya saba, ka
fin ya kama
hannun Jawaad dake masa shagwaɓan shifa fura zaisha, Alhaji babba ya bada a siyo masa. Alhaji babba dake murmushi ya tsaya yana dungure masa kai, “Kai miyasa idan rikicinka ya motsa babu wanda ka raina saini? Kaje kaima su Mariya mana”. Fuska Jawaad ya yatsine saboda ciwon da kansa ke masa yace, “Nidai ka daina sawa gaban mamana na faɗuwa a darenan, kabama Tanimu ya sayo mani inba hakaba bazan sake zuwa kwana gidanka ba”. Dariya Alhaji babba yay da jan hannunsa suka cigaba da tafiya, yace, “Yoni ALLAH na tuba aina yayeka da zuwa kwanarmin gida, matarka ta jajiba nima na huta da rigimarka hakanan”. Jawaad yace, “Basai na ɗakkota muke kwana anan ɗin tareba”. “Bana gayya, ku zauna gidanku nima aure zanyo”. Ciki dauriya Jawaad ya ƙyalƙyale da dariya, koba komai yarage nauyin da zuciyarsa tayi da tattaunawa da kakan nasa, shi kansa Alhaji baba sai yaji damuwarsa ta sassauta.
Bayan sun zauna Alhaji baba ya zubama Jawaad fura mai ƙyau da daɗin gaske da bai rabo da ita ya dubesa, cike da jin daɗi yake shan furan sanyinta na ratsa masa zuciya da ƙirji. “Muhammad kasan miyasa na kiraka kuwa?”. Kallonsa Jay yayi ya girgiza kansa batare da yace komaiba. Alhaji baba ya ɗan sauke numfashi, murya a sanyaye yace, “Akan matarkane” Saida Jawaad ya haɗiye furan daya sha kafin yace, “Matata kuma?”...............✍
Ƙyan alƙawari cikawa, sai dai wanda na ɗauka ni ya gagara cikar dalilin birkicewar wattpad, harna fara canja page ɗinma sai ALLAH ya taimakeni ya dai-dai ta🤦🏻, page ɗinnan kaɗai gareni babu nagobe saboda matsalar wattpad ɗinan ta ɗauki hankalina banyi typing ba, ƴan telegram sunce a turo muku kawai, amma da wuya kujini gobe idan ALLAH ya kaimu zan samu nayi typing ɗin jibi idan munada rabon kaiwa. Gaisuwa ga kowa da fatan alkairi😍😍😘😘.
ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.
SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.
HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO
MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.
MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.
BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....
abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.
Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300
Sai kunzo😍😍😍😘.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻
+234 909 304 4460:
SURPRISE💁🏻
Wannan page sadaukarwa ne ga iyayen yaran da suka kuɓuta, gaskiya ina tayaku murna matuƙa gaya, mungodema UBANGIJI daya maido mana dasu garemu da gaggawa cikin ƙoshin lafiya kuma, ƴan uwa wannan yana sake nuna mana mu duƙufa addu'a wa ƙasarmu, aikin bana shugabanni bane kaɗai, dan idanma munƙi addu'ar mune zamusha wahala, shugabanninmu mutanene tamkarmu, suma basu isa tsaremu ba sai wanda ya haliccemu, aduk yanda rayuwa tazo mana mu amsheta matsayin jarabawa mu godema ALLAH, UBANGIJI yafi kowa sanin halin da muke ciki, muyi ƙoƙarin cinye jarabawa sai muzama masu nasara, zage-zage marasa amfani nakasace irin ta zuciya, ALLAH yay mana ni'imomi masu yawa miyasa bazamu gode masaba sai ƙoƙarin aibanta waɗanda suke mutane kamarmu da hangen gazawarsu, sai dai taimakon addu'oinmu zamu samu tsaron da muke buƙata a yankinmu, muyi haƙuri mu duƙufa wajen faɗama ALLAH kukanmu, mu gyara mu'amulanmu ga junanmu mu kanmu, dan bazamu kasance azzaluman junaba sannan muce zamu samu shugabanni adalai, mugyara sai ALLAH shima ya gyara mana danshi mai rahamane. ALLAH ya kawo mana haske da kwanciyar hankali, ya dafama shugabanninmu suma akan ƙyawawan ayyukansu, saɓanin haka ALLAH ka magance mana badan halinmu ba😭🙏🏻.
Page 32
.................Ganin yanda ta tsume sai ta bashi dariya da tausayi, ya dungure mata kai yana miƙewa da faɗin, “Yarinyarnan ki rage tsoro”.
Ni kaina bansan na sauke wani kakkauran numfashiba tare da komawa na zauna daɓar, nai azamar cusa kaina tsakanin cinyoyina ina mai godema ALLAH daya tashi. A raina sai ayyana rashin kunya irin na maza nakeyi, suyi abu kuma su fuske abinsu tamkar basuyiba.
Jay da tuni ya koma kan aikinsa yaɗan kalleta ya maida kansa ga rubutun da yakeyi, haka kawai yanaso ya ganta a yanayin tsoro dan ƙyau take masa. Bai sakebi takantaba ya cigaba da haɗa bayanai akan case ɗin mutuwar Gimba, ya ɗaukama kansa alwashi sai yabi kadin jininsa, duk masu hannu a cikin wannan al'amarin kosu ubanwaye saiya soya musu gyaɗa bisa tafin hannu. Ganin lokaci yaja sosai Bily na a yanda take tun ɗazun ya sashi sake kallonta, muryarsa babu alamun wasa yace, “Miemaa!”.
Gajiyar dake tattare dani tasa har barci ya saceni a haka ban fargaba, a bazata naji ya kira sunana, na ɗago da sauri na kallesa, shima ni yake kallo, sai dai fuskarsa babu walwala sam. “Tashi kije ki kwanta” ya faɗa yana nunamin gado da idanu. Yanda ya tsuke fuska babu sauƙi yasa na miƙe babu musu dan nasan dai kwana anan dole ya tabbata, zuwa nai na kwanta a bakin gadon sosai, naja bargon na rufama jikina batare dana cire hijjab.
Jay daya kuma maida hankalinsa ga aikinsa yace, “Kicire wannan hijjabin tunda ba cinyeki za'ai a ɗakinba”. ‘Boss matsala’ na ayyana a cikin raina ina zame hijjab ɗin naja bargon har saman wuyana.
Duk da azabar ciwon kai da ya keji haka ya jure yana cigaba da haɗa bayanan, sai kusan ƙarfe ɗaya saura ya miƙe, kallo ɗaya yayma sashin da Bilkisu take kwance ya fahimci har yanzu idonta biyu, baice komaiba ya cire jallabiyar jikinsa yasa t-shirt fara akan boxer ɗinsa ya haye gadon shima, sai dai ba kwanciya yayba, zama yay ya jingina bayansa jikin fuskar gadon ya kashe fitilar ɗakin yabar iya ta gefen gado. Bargon yaja ya lulluɓe iya ƙafafunsa zuwa cinya, ya lumshe idanunsa yana maijin zafi da ƙirjinsa ke masa wanda yaketa ƙoƙarin dannewa, tunɗazun dannewa kawai yake dan bayason ya ƙuntata zuciyar yarinyarnan da laifin daba nataba, yana buƙatar jin wasu abubuwa daga garetane shiyyasa ya kawota nan dama. Rayuwarsa da gimba ta shiga kokawar dawo masa cikin zuciya, yarone mai mutunci da sanin mutuncin duk wanda zama ya haɗashi dashi, yasha saka Gimba manyan ayyuka masu haɗari akan aikinsa kuma yay masasu cikin ƙwazo, gimba na ɗaukarsa tamkar yayansa da suka fito ciki guda, tabbas yayi rashi wanda yasan bazai taɓa maye gurbinsaba har abada, danshi tuni yabar ɗaukar gimba matsayin drivern sa kawai jinsa yake a jininsa tamkar ɗan uwansa abokin farin ciki da baƙin ciki. Wata ƴar ƙwalla ta taru mai akan fatar idanu kaɗan, hannu yasa ya shareta yana mai jero masa addu'oin ne
man gafara a cikin zuciyarsa. Ya ɗau tsayin mintuna goma a haka kafin ya juya ya kalli Bilkisu, ɗauke kansa yayi murya cike da ɗaci yace, “Miyasa kika dawo gidan su Hudah da zama?”.
Banyi tunanin ya fahimci idona biyu ba har yanzun, na rumtse idanuna da ƙarfi ina sauke ajiyar zuciya, batare dana motsaba nace, “Ƙaddarar maraici”.
Idanu Jay ya tsurama bayanta, tsawon sakanni ya ɗauka a haka kafin ya sake ɗauke kansa daga gareta, “Ina dangin mahaifinki suke? Misa basa cikin rayuwarki?”.
Hawayene masu zafi suka silalomin, dan yau kan Boss ya taɓomin inda yafi ko'ina ciwo a zuciyata, zaune na tashi na jingina da fuskar gadon nima, hawaye na ƴar tseren fitowa na shiga bashi amsa kai tsaye, dan na fahimci so yake kawai yasan wacece niɗin kafin zuwana gidan su aunty Shahudah, batare dana kallesaba nace, “Har iyayena suka bar duniya su dukansu basu taɓa sanar dani wata matsala dake tsakaninsu da duk danginsu ba, dukda nasha musu tambaya sai dai babu wanda ya taɓa bani amsa ƙwaƙwƙwara a cikinsu, kullum amsarsu a gareni itace, (komai da lokacinsa, idan lokacin yayi zan sani) tun ina damuwa da abun harma na ciresa a zuciya, dama ba komai ke sakani kwaɗayin son jiba sai yanda nake ganin sauran yara ƴan uwana sukan shirya a ranakun juma'a da Sallah suje gidajen danginsu, sai dai ni daga gareni ba haka baneba, tunda na girma nai wayo a gidan haya mai ɗauke da ɗakuna kusan arba'in na buɗi ido na ganmu, bara dai na maka gwari-gwari zakafi farimtata.
Ni dai sunana Bilkeesu ɗiya ga malam Ado makaho, ƙwarai mahafina makahone da ko tafiya baya iya yi sai da ɗan jagora, Sai mahaifiyata Asiya.
A shekarun baya can mahaifina yana ɗan gani da ido ɗaya, amma da ga baya wahalhalun rayuwa suka ida rufe ɗayan idon yazam gaba ɗaya, mahaifiyata ma tana da nakasar ƙafa, dan kuwa gurguwace bata ma iya tafiya sai dai jan jiki. A matsayin da iyayena suke kawai zai nuna muku ni ba kowan kowa bace ba, dan kuwa muɗin talakawane irin tiɓis ɗinan da a kullum sai an nemo za'aci. Abin da zai matuƙar birgeka a rayuwar iyayena shine sam mahaifina baya bara balle aje kan mahaifiyata, duk da baba baya gani bai yarda zama maroƙi ba, dan a ganinsa UBANGIJI ya masa dukkan gata da ya bashi rai da lafiya, idaniyar ganice kawai bashi da ita. Sana'ar mahaifina itace sai da kayan ɗinki irinsu zare, allura, almakashi da dai sauran kayan nau'in ɗinki tsiraru dai-dai arziƙinsa, a gaba ɗaya jarin idan zaka dinƙuleshi waje ɗaya bazai wuce na naira dubu goma sha biyarba, wataƙil ma na zurma da yawa. Dalilin kamewarsa na janye kansa da ga ƙasƙancin bara ne ya ja hankalin mafi yawan telolin anguwarmu zuwa sayayyar kayan ɗinki a wajensa. Sai mahaifiyata da ke saida kayan kuka, kuɓewa busashshe, kayan ƙamshi harda daddawa domin kare mana mutunci itama. Gidan da muke gidan hayane mai ɗauke da ɗakuna kusan arba'in, dan irin dogon gidannan ne da akan jeranta ɗakuna reras da ga farkon baranda zuwa ƙarshe tamkar gidan karuwai, ba wani faɗine da gidan ba, amma kowa iyakar mu'amularsa a ƙofar ɗakinsa ne da bazata gaza taku goma ba, babban kicinne guda ɗaya a gidanmu dake a farkon shigowa gidan wanda ya gama cuɗewar baƙi saboda mafi yawancinmu girkin icce mukeyi, masu arziƙin cikinmu ne keda lasisin dahuwar abinci saman gawayi, can da ga ƙarshen gidan kuwa banɗakine guda biyu, na kashi da wanka, wanda suka ɗaine duk yawan mutanen gidan ke shiga, shiyyasa mafi yawanmu zaki samu kowa da fo ɗinsa na kashi a ɗaki ko ƙaramin botikin fenti, da safe idan bakai azamar tashi kai wanka ba to fa ka tabbata ƙila sai dare
Showing 102001 words to 105000 words out of 249282 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35 Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84