hannunsa ɗaya a sumar kaina ɗaya ya riƙe hannuna dana ɗaura saman ciki yana murzashi. Murmushi yay min nima na maida masa murtani, cikin muryata da taɗan sirka nace, “Sannu da dawowa”. Kansa ya ɗagamin yana mai lumshe idanusa, kafin ya tura yatsunsa cikin gashin kaina da faɗin, “Ya kamata aima kan nan kitso Zinaraina, kar yazo ya lalace aimin asara”. Na ɗan jinjina kaina ina murmushi da yunƙurawa zan tashi, taimakamin yay na tashi zaune sosai, sai da na zauna da ƙyau sannan nace, “An dace?”. Ni kaina yanda nai maganar cikin kalar tausayi sai da na bama kaina dariya, yay murmushi shima yana miƙewa tsaye da zama a kusa dani, “Idan kika koma kalar tausayi sai ki zama wata saliha dake”. “Lah!, to ni ina da tsiwane?”. “Eh mana, sai mutum ya zauna dake yake ganewa ai, a nesa ba'a gane Fitsararriyace”. Nace, “ALLAH kana gani”. “Nima ALLAH kana gani” ya faɗa da dungure kaina da ɗoramin ƴar ƙaramar jikka saman cinyata. leƙa jikkar nai, ganin wayoyi huɗu a ciki ya sakani jin wani ɗanyan farin ciki, bansan sanda na rungumesa ba ina dariyar jin daɗi. Shima rungumeni yay yana dariyar. Ɗagowa nai da sauri, cike da farin ciki nace, “Kai amma tayi ƙoƙari wlhy, yaya akai ta samo mana?”. “Ai dama nasan zata ɗakkosu, yanda yarinyar nan ta mutu a kaina ko Alhaji kokinon nace ta sato ai zata sato min”. “Uban nata?”. “Sa wasa yarinya, nifa nan farin jinine dani garama ki ringa lallaɓani”. Yay maganar yana miƙewa, sai da yaje dining sannan ya juyi ya kalleni, “ƴammata ko dai kina jealous ne?”. Baki na taɓe ina miƙewa nima bayan na maida wayoyin a jikkar. Ganin na basar shima sai ya basar da zancen.
★★★
Tunda muka kammala cin abincin muka koma falonsa, a ƙasa muka baje, shine yake binciken wayoyin ɗaya baya ɗaya ni kuma ina copy ɗin komai na ciki zuwa lap-top ɗinsa, yanayi yana rubuce-rubuce, kasancewa dama tun daga can ta saka wayoyin a Airplane mode sai babu wani kira da yake shigowa ciki.
Ɗan kallonsa nai na ɗauke kai, “Boss!”. “Uhmyim” ya amsa min batare da ya ɗago ba. “Wai baka tsoron yasa a bibiyi wayoyin nan ne? Naga fa komai yinsa kake hankali kwance”. Shiru bai amsa minba sai kusan mintuna biyu sannan ya ajiye biron da yake rubutun yana miƙomin flash, “Basai idan mai wayoyin yana duniyar da kike ba zaisa a bibiyesun?”. A tsorace nace “kamar ya? Kashesa kukayi?”. Yanzun kam saida ya kalleni sannan ya ɗauke kansa, “Kefa wani lokacin mashiririciyace, miye na kisa anan?. Gani nai zata bamu matsala dan ta kirani akan ita dai tarasa ta yanda zatai tunanin ɗauka, shine na ɗaurata bisa keken ɓera, na saka aka kai mata maganin barci mai ƙarfi ta saka masa a drink ɗin da yake fara sha kullum idan ya shiga gida, na kuma ƙara mataa da allura”. kasa janye idanuna nai daga garesa, hatsabibancinsa kawai nake jinjinawa a raina, boss dabanne akan dabaru da ƙwazon aiki, dolene kana tare da shi ka rinƙa koya kaima....... “Kallon fa?”. Ɗauke kaina nayi na cigaba da abinda nakeyi.
Muna tsaka da aikin wayarsa tai ring, yanda naga ya ɗauki wayar a ring ɗaya babu wani ɓata lokaci, ya sakani kallonsa da mamaki, wani lokacinma da zakaga anata kiransa ya share wayar.
“Munkaila kun isa ne?”. “Eh boss gamu a cikin anguwar kusa da gidan ma”. “Okay ku saka masa wannan rigar bomb ɗin. bashi wayar”. “Okay sir, gashi”. Ɓaleru da duk ya zam
a wani kalar tausayi ya amshi wayar, cike da ladabi yay sallama. Cikin Kakkausar murya Jay yace, “Idan ka gadama kaci amanarmu, idan ka gadama kayi aikin da zaka ceci ranka, wannan bomb ɗin da kake gani a tashi ɗaya zai tarwatsa naman jikinka ko kalar ƙashinka baza'a gani ba ma balle kaiɗin”. “Oga dan ALLAH kaimin rai, komai kake buƙata zanyishi”. “Ya rage naka”. Jawaad ya faɗa yana yanke kiran.
Computer ɗin da ya haɗa a saman centre table tun ɗazun ya kunna, ya koma saman kujera ya zauna, ya jona wayarsa jikin USB sannan ya daidaita muryar Alhaji kokino da maigadin gidansa yay mana recording. cikin wayoyin da yazo da su ya ɗauki ɗaya, itama ya haɗata da Computer ɗin sannan yay kira. Nidai inata aikina ina kuma kallonsa lokaci-lokaci, da hannu yaymin nuni dana zo, matsowa nai garesa, ya miƙamin mouse ɗin Computer da faɗamin yanda zanyi da zaran an ɗaga wayar, saboda muryar Alhaji kokino yazam ita suke ji. Kaina na jinjina masa, ya saka abu a kunne sannan yay kiran wayar. Bugu biyu aka ɗaga, cikin wata buɗaɗɗiyar murya aka fara gaisuwa da tsantsar ladabi. Amsawa naji yanayi da salon da ba nasa ba, kafin ya fara magana cike da tsumewa, “Yaron da ya kawo matar nan gashi nan na turosa shi da wasu yara su uku zasu ɗauketa”. “To amma oga ya kuma zaka canja shawara? Ɗazunfa ba haka mukai da kai ba, wai miyasa kuketa canja mana aiki bakamar yanda yake a baya ba?. Kawai saboda sakacin mutum ɗaya, gaba ɗaya gazawarsa tasa komai sai rushe mana yake nemanyi a ƙungiya, a kaudashi mana”. Kallon juna mukai ni da boss, ya ƙara tsaurara muryarsa da gyara zaman abinda ya ɗaure wuya dashi, “Sabon yanka kaima kasan muhimmancinsa ai a garemu, amma ka ajiye wannan maganar zamuyita wajen taron ƙungiya na ranar bauta, a basu matar dai dan akwai matsalane zasu canja mata wajen zamane”. “To babu damuwa oga, saisun ƙaraso”. Ya yanke wayar da sauri yana kunce ƙyallen wuyansa da sauke nannauyan numfashi, saurin miƙa masa ruwa nai, ya amsa yasha yana lumshe ido da murza wuyansa. sai kuma ya ɗauka wayarsa ya turama su Munkaila saƙo akan suje komai yayi.
Daga ni har shi kowa juya zancen ƙungiyarnan da sabon yanka ya faɗa mukeyi a ranmu, ya kalleni yana miƙewa “Mikika fahimta a zancensa Miemaa?”. “Sunada wata ƙungiya, da gaji kuma bata alkairi bane, to amma wanene ya ɓata musu aikin?”. “Nima wannan shine tambayata, maganar gayen nan ta sake ɗarsamin abubuwa a cikin raina da yawan gaske, kuma insha ALLAHU saimun bincikosu. Inada tabbacin duk wani wanda muke buƙatar samu a dalilin bibiyar numbers ɗin dake cikin wayarnan zamu samesa, tsabar munafurci babu wadda akai saving nata da sunan mai ita, yanzu dai mu jira dawowarsu da maman yara, insha ALLAHU daga nan zuwa asuba nasan zasu shigo”. Kaina na ɗaga masa jikina duk a sanyaye.
Dawowa yay ya zauna muka ƙarisa aikin, kusan sha ɗaya muka kammala, muna cikin tattare komai Munkaila ya kira ya sanar masa yanzu haka sun ɗakko hanyar dawowa, amma gaskiya maman yara na cikin mawuyacin hali sosai, dan a yanayin da take ciki su da farko ma sun zata bata numfashi, sai daga baya suka fahimci tsabar wahala ce da azabar da ake gana mata.
Hankalinsa tashe ya basu Umarni akan su gaggauta tahowa kawai, su kuma ringa mata addu'a suna tofa mata.
Mun kwanta ne kawai badan muna tare da nutsuwa ba, duk bayan wasu mintuna sai ya kirasu yaji suna a ina ne? Barci gaba ɗaya ya ƙauracema idanunmu. Bamu sami ƴar nutsuwa ba sai da suka iso kusan ƙarfe uku na dare. Likitan da zai dubata isowarsu kawai yake jira, dan haka suna isowa ya duƙufa kanta kamar yanda suka kirasa video call mukaga komai.
Mawuyacin da take ciki saida nai kuka dan tausayi duk da a yaune na fara ganinta, shi kansa ajiyar zuciya kawai yake saukewa a jajjere. Barci ya sacemune kawai kasancewarsa gwanin iya sata, amma badan mun shirya kwanciyarba.
★★★★
Da asuba kiran sallar farko yay alwala ya fice gidan, na zata massallaci ya nufa, sai da najiyo ƙarar tada mota da buɗe gate na fahimci fita yay. Addu'a na bisa da ita na tashi nai alwala nazo nai zaman yin nafilfili nima har aka kira sallar sh
iga.
Koda Jawaad ya fito kansa tsaye gidan Alhaji kokino ya fara isa, ya bama baba maigadi wayoyin sannan ya wuce inda aka ajiye maman yara. Ba ƙaramin tashi hankalinsa yayi ba ganin mawuyacin halin da baiwar ALLAHr nan ke a ciki, a hakama Munkaila ya tabbatar masa tayi fasali fiye da yanda suka ɗakkota, Jawaad ji yay kamar yayta dukan ɓaleru har sai ya daina numfashi, amma ya danne ransa suka fita salla. Bayan an idar baro gidan yayi akan zai dawo zuwa anjima tare da wadda zata kula da ita.
Ina kitchen ya shigo gidan, na leƙo nai masa sannu tare da gaisheshi, a yanda ya amsa min kawai nasan zuciyar ƴan mazan a kusa take, ɗakinsa ya wuce, nikuma na cigaba da aikina dan na samu na kammala da wuri ba sai na makarar damu kamar jiya ba.
Bayan na kammala sai da na fara leƙe ɗakinsa, wanka yake, dan haka nima na fito zuwa nawa ɗakin na shiga wankan. Harna fito nai shiri bai shigoba yau, ban damuba na kammala abinda zanyi sannan na fito gaba ɗaya, ɗaura bag ɗina nayi a dani na kuma nufar ɗakinsa inajin duk babu daɗi, shi indai yanada damuwa to shikenan sai kiga duk ya ƙuntata, duk wani walwalarsa gushewa take ya koma miskilin gaske, nikam a ɗan zamana da shi ɗin nan na fahimci ga iyalinsa shi mai sauƙine, miskilancin sa sai a waje yake zubashi kamar ba shiba. A shirye na iskesa, rigar saman suit ɗinsace kawai bai sakaba sai tie..., zaune yake a bakin gado da waya a kunne alamar waya ya keyi. Ƙarasowa nai na gyara saman mirror ɗin da ya gama hargitsawa, ya riƙo hannuna ya ɗaurani bisa cinyarsa yana faɗin “Gata Ummuna, amma ki kwantar da hankalinki dan ALLAH, muna nan munata shirin dawowar ai”. Sai yanzu na fahimci da ƴan saudia yake wayar, kafin nace wani abu ya ɗauran wayar a kunnena. Cikin girmamawa da ɗoki nai sallama, daga can Umm-Anum ta amsa min cike da kulawa, sai dai yanda naji muryarta na sake fahimtar tana tare da damuwa. Bayan mun gaisa tace, “Ɗiyata wai da gaske yake kuna shirin dawowa?”. Murmushi nayi ina kallon fuskarsa, ya wani narkemin idanu da fuska, na sake murmusawa sannan nace, “Eh Ummu da gaske ya keyi”. Wata sassanyar ajiyar zuciya naji ta sauke, sai tausayinta ya kamani har ƙwalla suka cikamin ido, munyi ƴar hira kaɗan ta bama Anuwar wayan shima muka gaisa, sannan Anum ta amsa itama, ganin mun fara nisa a fira dan Anum ma dai babu laifi akwai magana tamkar Nabeelah, ƙwace wayar yay, “K sai anjima aiki zamu fita”. Ina jiyota tana kukan shagwaɓa ya kashe wayarsa bai saurareta ba. Kai ya dunguremin, “Idan kina biyema Nabeelah da Anum sai kin zama parrot irinsu, nidai nafison matata haka mara son hayaniya”. Murmushi nayi tare da miƙewa daga cinyar tasa batare da nace komaiba. Shima bai sake cewa komaiba ya miƙomin tie.. Ɗinsa, “Nifa ban iya sakawa ba”. “Sai ki fara koya daga yau” ya faɗa yana miƙewa. Ya fini tsawo, dan haka na ɗauki filon dake saman sofa na ajiye ƙasa na taka, duk da hakan ma dai ban kaiba, amma nafi ɗazun, shine ya rinƙa nunamin yanda zanyi har muka kammala, yace, “Woow kinyi ƙoƙari”. Daɗi naji sosai, nace, “Da gaske?”. “Ehum” ya faɗa da ɗan lumshe ido. “Thanks” na faɗa nima ina murmushi.
Tare muka fito daga ɗakin, ya ɗauka abincin maigadi da Sadiq tunda yana nan da safe ya kai musu, nikuma na zuba mana namu a plate ɗaya, sai tea dana haɗama kowa dan nasan shikam in bai sha tea ba akwai damuwa, ina mamakin yanda yakema tea so na masifa haka. Koda ya dawo muka zauna cin abincin sai naga bayaci sosai, ya raba hankalinsa biyu, ɗaya a aiki a tab... ɗaya ga abincin, cire nauyinsa da nakeji nayi na amsa cokalin na fara bashi da kaina, baice dani komaiba ya fara amsa, da yake hankalinsa nakan wayar sai yaci abincin sosai batare da ya fargaba. “Miemaa Please barni haka karnaje office na kasa aiki, ashe wayo kikemin kinata nausamin abinci a ciki”. Ƴar dariya nai kawai na tattare kayan zuwa kitchen, sauri-sauri na ɗaurayesu na fito, tsaye na iskesa riƙe da bags ɗinmu alamar ni yake jira. “Anya kuwa bazaki ajiye wannan aikinba ki zama matar gida kawai?”. Gabana ne yay masifar faɗuwa da jin wannan furuci nashi, dama kullum cikin addu'a nake kar wannan tunanin yazo masa a
kai, dan na kula shi mutum ne mai tsananin kishi. Yinai kamar banjisa ba na hau gyaran agogon ƙarya, “Nasan kin jini ai”. Yay maganar daɗan kallona. “Nifa banji komai ba, yi haƙuri mikace?”. Shareni yay muka ƙarisa, bayan mun gaisa da su Sadiq ya buɗe mana mota muka shiga.
A motarma bai hutaba, aiki ya keta faman yi har muka iso office, nazata zamu biya ta wajen maman Yara, amma jin baiyi maganarba saina share abina. Yauma sai da na masa rakkiya har office sannan na koma namu inda na tarar da Rebecca kawaice tazo a cikinmu, itama ta cemin nanda goma zata fita saboda aikin da boss ya raba musu jiya, akwai abinda tazo yi shiyyasa amma da sai ta kammala zata shigo kamar su Ummie, ni dama bandani ya ba shugaban ƴan kishin, dana tambayesa bayan mun fito amsar daya bani itace, yanzu duk inda nasa ƙafa yana wajen ai, duk aikina zai kasance tare da shine insha ALLAH, nidai najisane kawai, watarana ai za'a iya canjama wani wajen aiki a cikinmu ko wani abun daban, naga yanda zaiyi kuma. Tana aikin muna hira danni aikin gabana mai sauƙine, jiya nema oga Hafiz ya banishi da yamma. Goma nayi ta fice, saina maida hankali ga nawa aikin. Yau bamu da yawa a office ɗin, mafi yawansu sun fita operation, wasuma ko office ɗin basu zoba.
Wajen sha biyu na amsa kiran boss da yaymin, na iskesa shi da Jabeer, na gaishesu sannan nace masa gani. “Na ganki ai” ya faɗa yana cigaba da aikinsa a Computer batare da ya kalleni ba. Ina daga tsayen ban zauna ba, dan baibani izinin yin hakanba, yanzu a matsayin shugaba yake wajen aiki ba miji ba. Kusan mintuna huɗu sannan ya juyo gareni yana tattare takardun gabansa da yake aiki akansu. Miƙomin yay fuskarsa dai babu walwala sam, a boss ɗinsa dana sani yake. abinda zanyi ya faɗamin, na amsa ina jinjina masa kai, kafin na juya na fita.
Aikin nan daya bani shine ya jani lokaci daƙyar na turesa naje nai salla na dawo na sake cigaba, a lokacin ne su Zuhrah suma suka dawo, sam banajin yunwa, koda ya kirani akan miza'a kawomin nace masa ni banama jin yunwa, baice komaiba ya yanke wayar, bayan wasu mintuna saiga doughnut da fresh milk an kawomin. Murmushi kawai nayi nama wanda ya kawo godiya na cigaba da aikina, shine su Nazifa suka iske inaci, ƙarshe ma tare da su muka ƙarisa.
★★★★★
Ƙarfe biyar muka bar office, barci nakeji sosai a idona, dan haka naɗan jingina kaina da kafaɗarsa. Ɗan kallona yay ya ɗauke kansa yana murmushi, tun ina kallon aikin da yake a lap-top har barci ya ɗaukeni a haka. A hankali na buɗe idona jin an jamin hanci. “Sorry kin gaji ko?” yay maganar yana shafamin gefen fuska. Kaina na ɗan ɗaga masa da lumshe idanu na sake buɗewa a kansa. “Daure mu shiga, bazamu jimaba, sai mu tafi gida kinji”. A hankali nace to ina tashi.
Koda muka fito da mamaki na kallesa, “Lah! Dama nan mukazo?” na faɗa cike da zumuɗi. Ƙin tankamin yayi, sai ma nunamin gidan su Amina da yay da hannu alamar muje. A tunanina nan zamu fara shiga kafin gidan Dad, dan haka nai gaba raina fari ƙal.
Cikin farin ciki Mama ta tarbemu, sai faɗi take, “Kai masha ALLAH, lallai Jawaad kana kularmin da yarinya sosai, kaga duk ta sake canjawa, kai Alhmdllh”. Murmushi mukaita yi mudai, inata ɓoye fusaka dan naji kunya kuma ALLAH. Tunda naga banga Amina ba nasan basu taso aikiba, mama ta nuna mana ɗakin kusa da nata, “Ku shiga to, dama yanzu na gama kimtsata, mun samu yanzu taci abincin Alhmdllh”. Shine ya amsama mama da Alhmdllh, ni dai da ba fahimtarsu nai ba sai nabi bayansa kawai.
Babbar mace muka tarar a ɗakin kwance, kallo ɗaya nai mata na gane maman yara ce da nagani jiya a video call, kenan nan aka kawota ashe? Shine koma faɗamin baiyiba. Kallonsa nai irin na tuhuma ina kumbura fuska, ya ɗan waro idanu da ɗage kafaɗatsa alamar “shima babu ruwansa”. sake tura bakin nai, yaymin gwalo da ɗauke kansa daga gareni..
Shigowar mama tasa na ƙyalesa, yace, “Mama barci take ne?”. “Eh to inaga ta koma, dan tun allurar da sukai mata jiya da daddare bata gama sakinta ba, likita yace da gani ko barci bata samu a can shiyyasa ta jigata sosai”. “Humm” ya f
aɗa cikin ƙunar rai tare da matsawa gaban katifar da take ya durƙusa saitin fuskarta.
Jin motsin mutum gab da ita yasa ta buɗe idanu a hankali, ƙure boss tayi da kallo ko ƙyaftawa batayi, har zuwa wasu sakanni, sai kuma ta saki murmushi cike da ƙarfin hali, hanunta dake rawa ta ɗaga da ƙyar ta miƙo masa, babu musu ya miƙa mata nasa shima ta riƙe, murmushin ta sakeyi hawaye na ziraro mata akan kumatu.
Hawayen ba ƙaramin sake tunzura zuciyar Jay sukayi ba, ya risinar da kansa ƙasa yana haɗiyar zuciya, jijiyoyin kansa harsun fara mimmiƙewa, cikin muryarta da bata fita sosai tace, “Jawaad”. Da sauri ya ɗago idanunsa da sukai jazur ya zuba mata. “Na godema ALLAH da ya ƙaddara haɗuwarmu kafin nabar duniya, nagode
Showing 189001 words to 192000 words out of 249282 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64 Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84