Page 40
...............Sosai Nabeelah ta waro idanunta da suka cika da hawaye tana haɗe hannayenta waje guda alamar roƙo, “ALLAH yayanmu ni babu abinda zan faɗa, dan ALLAH kayi haƙuri”.
“Kinsan ALLAH idan kika bari harna miƙe kanki sai jikinki yay masifar yin tsami”. Yay maganar muryarsa babu alamun wasa. A mamakina sai naga Nabeelah ta fashe da kuka tana ɗanja baya, na kallesa da nufin bashi haƙuri duk da nima a tsoracen nake sai na ga ya miƙe, ai kafinma nace wani abu sai hango Nabeelah nai ta kwasa da gudu ta fice. Yanda yaja birki tare da riƙe ƙugu yana kallontane ya sakani kasa danne dariyata, hannu nasaka na toshe bakina tare da saurin kauda idanuna ganin ya kalloni.
Jawaad yay ƙwafa yanabin Bilkisu da kallo, “Ke kuma dariyan na miye to?”. Kallonsa nai da sauri ina ƙoƙarin haɗiye kayata amma na kasan, dan fuskata kawai zaka kalla kasan dariyar taƙi haɗiyu wa, harar daya ballo mince tasa nai niyyar barin masa falon naje nai dariyata a ciki. Caraf naji an cafkomin hannu da faɗin, “Dariya ko? To bara na huce a kanki”. Tsaf na haɗiye dariyar na koma zare idanu, cikin marairaice fuska nace, “Nifa ba dariya nayiba”. “To mi kikayi?”. Yay maganar da tsatstsareni da mayun idanunsa. Sosai kunya ta lulluɓeni nai ƙasa da kaina ina ɗan waige-waige, nima na Nabeelah nake tsarawa na fece kawai. Kamar ya fahimci abinda nake tsarawa a raina yace, “Kema guduwar zakiyi? Itama ɗin ba ƙyaleta naiba zan sameta har gida sai naci ƙaniyarta na gasa mata baki tunda ita magananniyace”. Murmushin da ban shiryaba ne ya suɓucemin, nace, “Yi haƙuri to niba baƙuwar zafi bace wlhy”. Kafin yace wani abu wayarsa ta shiga ring, kallon wayar duk mukai da mamaki, da alama ma anan ya mantata ta kwana ko?, hannuna dake cikin nasa na janye na ɗakko masa wayar da rabinta ya shige ƙasan filon kujera. Ban tsaya kallon ko wanene ba na kawo masa cikin.
Amsa yayi yana zama, ni kuma na juya na ɗauki basket ɗin da Nabeelah ta kawo wanda ko ba'a faɗaba kasan breakfast ne a ciki. Harna nufi D/table naji ya kirayi sunana, juyowa nai ina amsawa da “Na'am”. Dai-dai zai saka wayar a kunnensa alamar wancan kiran ya katse shi ya sake kira. Yace, “Kawomin tea, karki saka suga da yawa”. Da “to” na amsa kawai na ƙarisa na ajiye basket ɗin saman dani. Kicin ɗin na nufa ina ɗan murmushi da yaba ƙoƙari da sadaukarwa irin ta waɗanan bayin ALLAH, babu dangin iya babu na baba suka kashemin waɗanan kuɗin? Ba ƙaramin mutsuwar tsaye naiba da ganin yanda kicin ɗinan yay mugu-mugun haɗuwa, ni balki ɗiyar baba makaho ce da wannan gidan matsayin matar cikinsa? Sai kawai naji ƙwalla sun cikamin idanu, na shiga maimaita kalomin Alhmdllh a zuciyata ina hawayen zuci. Fasalta muku yanda kicin ɗinan yake ai ɓata lokacine, abin mamaki da al'ajab harda kayan abinci da malam bahaushe ke kira da gara, dai-dai da magi wannan sakarai an ajiye min shi. Sai dai kuma babu kayan tea ɗin da yace na haɗa masa, iya dubana banga koda lipton ba sai kayan ƙamshi kawai da abinda ba a rasaba, komawa nai da niyyar faɗa masa ban ganiba amma na iske yana waya da ransa a ɓace. “Uncle Please ka ƙyalesu ni babu abinda zanzo na musu, ina ƙoƙarin danne duk abinda suke son takalata dashi kawai amma na kula neman kaini maƙura sukeyi akan shirmensu”. Yaɗanyi shiru alamar saurare, hakan yasa na juya zan koma dan na bashi damar gamawa amma sai naji takunsa a bayana, baimin maganaba yazo ya wuceni, ganin hakan yasani bin bayansa, drawer saitin fridge ya buɗe ya nunamin. Kaina na jinjina masa na ida shiga ciki shi kuma ya fice yana cigaba da wayarsa. Bani da matsala da kayan ƙamshi dan duk gasunan a robobi harma da ganyan shayi masu daɗi da Umm-Aban dama tace zata haɗa min saboda ta lura inason shayi. Tukunya na ciro da dama an fiddata a kwalinta na ɗauraye na zuba duk abinda zan buƙata na ɗora saman gas da dama an haɗashi shima. Komawa nai na ɗauki plate da flask da kofi na ɗaurayesu tsaf, cikin mintuna ƙalilan na kammala na fito da komai na ajiye a dani ɗin, sannan na koma na ɗakko tea ɗin dana haɗa a kofi na ɗaura saman ƙaramin tire na kai masa falon dan har yanzu wayar yakeyi. Yanda yake kallona harna ajiye tiren a centre table duk sai naji na takura, nuni yaymin da in bashi, ɗauka nai na miƙa masa, ya ɗan lumshemin idanu alamar “thanks”. Bance komaiba nabar wajen dan sonake nai wanka.
Saida na gyara gadon yay tsaf sannan na shiga wankan, wanka nai haɗe da wankan tsarki dan mai jar motama ya ɗauke tunkan azhar ɗin da nake hasashen, zaton babu mai shigominne ya sakani fitowa daga ni sai guntun towel ga gashi a jiƙe, sai dai inata ƙoƙarin tsanesa da ƙaramin towel dake a hannuna. Ina ƙarasawa gaban mirror yana shigowa da sallama ciki-ciki alamar ransa a ɓace yake har yanzun, saida naji tamkar na ƙwala ihu, na ɗan wawwaiga banga wani abu dazan iya ja na rufe jikina da shiba, haƙura nai kawai na ɗan ɗago na kallesa cikin dauriya ina faɗin, “Nazo na baka abincin ɗinne?”. Shirun da naji yayi bai amsaba yasa na ɗago kaina na dubesa, idanunsa nakan gashina ko ƙyaftawa bayayi. Sake maimaita masa tambayar nayi. Ya janye idonun nasa da juyawa zai fita yana faɗin, “Ki gama nima zanyi wankan ne”. Binsa kawai nayi da kallo dan na lura ransa a ɓace yake, ‘Komi akai masa kuma?’ na faɗa a fili batare da inada mai bani amsata ba. Gudun karya sake shigomin yasa nai shiri a gaggauce cikin sket da riga na shadda orange color. Ni kaina nasan sunyimin ƙyau dan kamar an haliccesune a jikina sunmin ɗam dan telan ya iya ɗinki, kaina nakeson busarwa amma abin haushi babu wuta, a haka na gyarashi bayan na tsanesa sosai babu ruwa, ɗauresa nai da tunanin ƙila su kawo wutar anjima tunda naga anguwar kamar suna samunta sosai. Bawata kwalliya nai da yawaba amma fuskata tayi fayau, na saka ƙaramar sarka sannan na feshe jikina da turare sosai, kowa ya ganni yaga amarya da gaske, farin gyale na ɗauka shima na saka turare sannan na yafa na fito falon. Gidan tsaf yake babu wani datti, hakan yasa kawai na ɗauki fresheners da turare mai ƙamshi haɗin gida na fesa iya falon nan kawai. Ina cikin fesawar ya fito.
Jin Motsinsa a bayana ya sakani waigawa, kwalliyar tasa ta sakani shagala a kallonsa batare dana fargaba, shaddace ƴar ubansu golden color ya saka, sai maiƙo take da ɗaukar ido, ta samu nutsatstsen ɗinki na zamani da ya fiddo cikar zatinsa mai tabbatar dashi jinin hausawan usul harda su hula......
Saukar iskar da naji a cikin idanuna da ƙamshi Mouth freshener ɗin da ya saka ya sani dawowa hayyacina daga sakin layin da nayi, nai ƙasa da kaina dan naji kunya.
“Gulmammiya kinaso kina kaiwa kasuwa, na miki ƙyaune?”.
Ɗan kallonsa nai na juya ƙeya nace, “Kaɗan”. Murmushi ya saki har inajin sautinsa, ya ɗaura hannunsa saman haɓata ya maido fuskata inda yake, “In har da gaske kike ki kaleni cikin ido kice kaɗan nai ƙyau”. Hannu nasa na rufe fusa da sake juya masa baya ina murmushi. “Baki da gaskiya kenan”. Yay maganar kusa da kunnena yana zame gyalen dana yafa. “Malama niba surukinki bane ai, muje kiga gidanki”.
Shine yaymin rakkiya lungu da saƙo na cikin gidan har ɗakinsa da harabar gidan, gaba ɗaya gidan ya canjamin tamkar ba wanda na taɓa zuwa ɗin nanba, an gyarashi sosai ya canja kamanni. Sai da muka gama zagaye ko ina muka yada zango a wajen cin abinci. Nidai kasa sakewa nai naci saboda yanda yay mugun tsatstsareni da idanu, duk sanda zan ɗago sai naga idonsa a kaina. Da dai na gaji saina kumbura masa fuska, “Nifa wlhy ba television bace ba”. Bakinsa ya taɓe baice dani komaiba bai kuma bar kallon nawaba har muka gama. Ɗakinsa ya koma nikuma na tattarr wajen, na fito masa da abincin maigadi da tunkan mu fara cin namu ya sakani na zuba shima ya fito, agogonsa da links ya miƙomin tare da miƙamin hannunsa. Dukda inajin kunya haka na saka masa links ɗin sannan na saka masa agogon. “Thanks” ya faɗa a hankali yana ɗagemin gira ɗaya.
Kafin nace wani abu maigadi ya doka sallama a ƙofa, kallon ƙofar mukai gaba ɗaya amma shi ya amsa masa, ya amshi kular hannuna tare da nufar ƙofar ya buɗe.
Maigadi ya gaidasa da faɗin, “Alhaji kanada baƙone”. Da ɗan mamaki Jawaad yace, “baƙo kuma malam gambo?”. “Eh Alhaji, harzan masa ƙaryar baka tashiba saina fahimci amatse yake da son ganinka gaskiya, kuma kamar baƙon mai muhimmanci ne”. “Okey, to ga abincinka ina zuwa”. Amsar kular yay dayi godiya ya koma, Jay kuma ya maida ƙofar ya rufe ya dawo inda yabar Bily tsaye tana kallonsu. Wuceta yay ya ɗauka key ɗin motar dake kan centre table, “Bara naje na gaida Alhaji Babba daga nan na leƙa asibi wai Hudah aka kwantar”. “Ya salam” na faɗa cikin damuwa, “Miya sameta kuma? Dan ALLAH kaje dani”. Kaɗan ya kalleni ya ɗauke kansa, “Kimata addu'a daga nan ya isa, kokin taɓa ganin amarya ta fita”. Cikin shagwaɓar da bansan inada itaba nace, “Toni tsoro nakeji wlhy”. “Tsoro kuma?” ya faɗa yana kallona. kaina na ɗaga masa batare dana yarda mun haɗa ido ba. Jin yaƙi magana yasa na sake kallonsa, sai naga niɗin yake kallo ashe shima. “ALLAH na kula kinma rainani” yay maganar yana matsoni, baya nai saurin ja, amma duk da haka saida ya riƙoni. Cikin magana raɗa-raɗa yace, “Ke komai abin tsorone a wajenki halan?”. Nace, “To inason naje naga aunty Shahudah ne”. “Uhhyim shine zakimin ƙarya? to babu inda zakije, ki jira ƙawayenki na nan zuwa zan dawo bazan jimaba dan zanyi magana da ku”. Saurin kallonsa nai da mamaki nace, “Su Ummie?”. Kansa ya ɗagamin. “Miya faru?”. “dan na dawo zakiji ai, ana jirana yanzun”. Ya ƙare maganar da ɗaura bakinsa saman nawa babu zato. ‘Ya salam’ na ambata a zuciyata tsigar jikina na tashi ga yanayin da nakeji na neman tasomin dukda dai yanzuma da sauƙi sosai ba kamar da ba. Sai da yaja kusan minti biyu kafin ya saki bakin ya sumbaci goshina. “Saina dawo”. Kaina kawai na jinjina masa dan na kasa kallonsa. A hankali na furta, ”ALLAH ya tsare”. Inajin yana murmushi. Nidai ban kallesanba har ya fice.
Sassanyar ajiyar zuciya na sauke tare zubewa a kujera daɓar na dafe kaina, wlhy abun mamaki yake ban, boss fa! Kai rayuwa bata rabo da abubuwan al'ajabi. Naja kusan mintuna biyar a haka kafin na miƙe naje ɗakinsa dan na gyara. Sosai ɗakin yake ƙamshin turarensa daya fesa yanzun, tsaf na gyarashi na saka fresheners sannan na koma kicin na ɗauraye kwankina da mukaci abinci shima naɗan gyara abinda bai minba.
Koda Jawaad ya fito sai ya iske baƙonsa cikin rumfar bunun dake harabar gidan maigadi ya kawosa, ƙarasawa yay yana faɗin, “Ai bammayi tunanin kai bane Munkaila”. Baƙo mai suna Munkaila daya miƙe domin girmamawa ga Jay yay murmushi, “Nine wlhy Oga barka da fitowa”. “Yauwa sannunka da zuwa” Jay ya faɗa yana zama tare da masa nuni daya zauna shima. Cikin girmamawa Munkaila ya gaishe da Jay kasancewarsa ogansa, file ɗin gabansa ya miƙa masa yana faɗin, “Oga dukkan abinda kake buƙata gashi, harma da abinda bakaceba dukna haɗo maka”. Kai Jay ya jinjina masa da faɗi, “Sannu da ƙoƙari” yana buɗe file ɗin. Da hotuna ya fara cin karo waɗanda sukai masifar ɗaure kansa dan harda Alhaji baba tare da mata biyu wadda ɗaya a ciki takasance kakarsace mahaifiyar su Ummah da shima a hoto ya santa, kallon Munkaila yay kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya maida file ɗin ya rufe.
Munkaila yace, “Oga akwai matsala ne?”. Kai Jay ya girgiza masa, “Babu matsalan komai, yaya maganar wancan aikin?”. “Shima ina gab da kammalawa oga, saboda naga ka matsu da wannan ma shiyyasa na dakata da wancan”. “Shikenan kayi ƙoƙari shima ka haɗamin shi a satin nan, ga wannan ka saka mai nima nayi aljihun nawa yay ƙasa”. Godiya Munkaila yayi sosai sannan suka fito a rumfar. Jay ya shiga mota shikuma ya fice dan mashin ɗinsa na daga waje bai shigo da shiba.
★★★★★
Fitar jawad babu jimawa su Ummie suka isa gidan amarya Bilkisu, Ummie, Zuhrah, Rebecca, Nazifa. Duk da jiya suka rabu da juna tuni suka haukace da ihun murnar ganin juna, suka saka bily tsakkiya da tsokana kala-kala, tun tana musu shiru dai harta koma ramawa itama dan taga shirun nata bazai sa su barta ba.
_________________________
Asibiti yay niyyar fara zuwa saboda Uncle Sulaiman daya tilasta masa yaje, to amma wannan bayanan da Munkaila ya kawo masa yanzun sun ruguza komai, burinsa kawai ya dangane da gidan Alhaji Babba. A waje yay fakin motarsa ya shiga shi kaɗai, Alhaji babba na zaune a falo hannunsa riƙe da Jarida Jay ya shiga da sallama. Ɗagowa yay yana kallonsa fuska ɗauke da murmushi, cikin tsokana yace, “A lallai wannan angon da gaske bahausa ya aura, ashe ba gidan jiya ya komaba”. Jay dake murmushi ya girgiza kai kawai yana zama, “Wannan itace tarbar da zakamin ma na baro matata na taho ganinka da farar safiyar nan”. Alhaji babba yay dariya irin tasu ta manya yana faɗin, “Ja'iri kenan bakifa ya buɗe”. Gaidashi Jay yayi yana murmushin tsokanar da kakan nasa ke masa. Sai da suka kammala gaisuwar da tambayar lafiyar juna da amarya Bilkisu kafin jay ya buɗe file ɗin da Munkaila ya kawo masa, hotunan ciki ya fiddo gaba ɗaya ya miƙama Alhaji Babba shi kuma ya maida hankali ga duba bayanan cikin file ɗin.
“Sa'adatu! kuma?”. Alhaji babba ya faɗa da alamun bazata. Kallonsa Jay yayi amma baice komaiba. Alhaji babba yace, “Jawaad kana nufin matarka nada alaƙa da wannan ta hoton?”. Zama Jawaad ya gyara sosai yana maida dukkan hankalinsa ga kakan nasa, “Baba abinda bincike ya nuna min kenan, sai dai nima kaina a kulle yake musamman da ganin hotonka a tsakkiyar mata biyu bayan mata ɗaya nasan kanada ita kafin Mama Maryam”. Shiru Alhaji babba yay na wasu mintuna kafin ya sauke ajiyar zuciya, yace, “minene sunan mahaifin nata?”. “Adam makaho” Jay ya bashi amsa a taƙaice. Nanma shiru Alhaji babba yay na wani ɗan lokaci yanata faman jinjina kai da murmushi a fuskarsa kafin yace, “Abin akwai ɗaure kai da ban al'ajabi”. Jawaad yace, “Miyasa zai ɗaure maka kai bayan na fahimci kasan wani abu”. Murmushi Alhaji babba yayi mai ciwo da sake maida hankalinsa ga hotunan guda biyar, ɗaya shine da mata biyu a jiki sai jaririn yaro da alamu suka nuna ranar sunansa aka ɗauki hoton ma ƙila, ɗaya kuma matane da miji matar gurguwa sai mijin da alamu suka nuna makaho ne, sai hoto na uku jaririyace nannaɗe cikin farin showal da gani kaga sabuwar haihuwa, hoto na huɗu, mata da minjin nan ne da jaririyar, na ƙarshema dai mata da mijinne sai bilkisu a tsakkiyarsu da bazata wuce shekaru goma sha biyarba. Ya ajiye hotunan yana kallon Jawaad da ƙyau. “Akwai abinda ku baku saniba Jawaad, mahaifiyarka cema kawai zata iya sanin wani abu itama ba duka ba dan a labari ta sani. Ba Amina da Maryam kawai na taɓa aureba, na taɓa auren wata matar mai suna Sa'adatu. Kafin aurena da Amina Sa'adatu itace yarinyar da naso aura dan itace muke soyayya amma iyayena suka ƙi, bakomai ne ya sakasu ƙinba sai kasancewar Sa'adatu batajin magana, duk da yarinyace da bata wuce shekaru goma sha biyarba a lokacin mutane kan jefeta da kalmar ƙarancin tarbiyya, Sa'adatu ta tashi a gidansu bata da uwa a hannun kakarta ta tashi, hakan yasa ta tashi sangartacciya da batajin ƙwaɓa, a dalilin ɗan karatun da aka sakata na boko wanda a wancan lokacin iyakamu maza kawai keyinsa yasa idanunta buɗewa dan ita kaɗaice mace a cikinmu, Sa'adatu ji take tafi kowa a ƴammatan yankinmu dama gata ƴar gata kuma babanta shine maigari, ALLAH ya jarabceni da sonta fiye da yanda kake tunani har takai naima iyayena maganar aurenta. Amma sai mahaiyata tace sam batasan wannan zanceba tama rigada tamin mata Amina, na ɗaga hankalina matuƙa a lokacin amma dole na haƙura muka rabu da Sa'a ina kuka tanayi. Hakan ya zafi kakarta har tayi alwashin sai nayi nadamar yaudarar jikarta da nayi. Babu wanda ya ɗauki alwashinta wani abu aka ɗauramin aure da Amina ta tare. Banason Amina amma ita tana sona kuma mace ce mai haƙuri da kawaici, a zamanmu tasha wahala kafin na ɗan fara fuskantarta, aurenmu da Amina yakai shekara shida amma bata taɓa ko ɓariba, a wancan lokacin dan mace takai shekara goma ma bata haihuba babu mai damuwa da hakan balle ya zama abin magana shiyyasa nima ban taɓa damuwaba. Zuwa lokacin Sa'a itama tayi aure amma ba a wannan garin namu ba, wani ɗan uwanta mai kuɗi aka aura mata, sai dai kuma hankalinta na kaina dan haka shekararta uku ta kashe auren ta fito da yarinyarta guda safara'u, a lokacinfa na tsaya kai da fata saina auri Sa'a dan sonta na nan daram a raina. Zakasha mamaki idan nace maka Amina itace taita kai kawo ga iyayena har mahaifiyata ta amince na
Showing 135001 words to 138000 words out of 249282 words
BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....
abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.
Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300
Sai kunzo😍😍😍😘.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
.
.
Domin samun littafin Ƙwai cikin ƙaya daga farkon ko taɓa Link ɗin da ke ƙasa.
👇👇👇👇
.
https://www.facebook.com/groups/2803452939899949/?ref=share
[1/11, 10:48 PM] Abue Saleh AlQuyraemey: Typing📲
ƘWAI cikin ƘAYA!!
Bilyn Abdull ce🤙🏻
BOOK TWO

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46 Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84