ledar ya buɗe ya juye gasashen naman rago daketa tashin ƙamshi saboda yanda aka sarrafashi cikin filet ɗin, kofin kuma ya saka fresh milk a ciki. “Taso kici abinci” ya faɗa yana zama akan sofa. Duk da bazan cinba ban musaba na tashi zuwa garesa jikina duk babu ƙwari ga ciwo yanamin ta ko ina saboda damben da mukaci da azzalumin can, ƙasa naso zama amma sai ya riƙoni na zauna kusa da shi, murya a sanyaye nace, “Naƙoshi, da yamma mukaci abincin da Ummah ta aiko dashi da rana”. Baice dani komaiba ya miƙamin fresh milk ɗin cikin kofin, amsa nai ita na kafa kai na shanye gaba ɗaya badan tanamin daɗiba sai dan buƙatar samun sanyi a cikin ƙirjina da yaymin nauyi. Jikina ko ina ciwo yay tsamu ga barci dama inaji. Amsar kofin yayi ya sake zubawa ya miƙomin, kaina na girgiza masa cikin marairaicewa dan kar yace saina shaɗin tilas. shanyewa yay ya miƙe ɗauke da filet ɗin naman da kofin. “Ga kaya nan ki canja ki kwanta”. Kaina a ƙasa nace, “To”. Juyawa yay ya fita, harna kammala saka kayan bai dawoba, na zauna bakin gadon ina ƙara tariyo abinda ya faru awanni biyu da suka shuɗe tamkar film ko mafarki. Gittawar da akai ta gabana ya sakani saurin ɗagowa, ganin shine sai na sauke ajiyar zuciya a hankali. Kwantawa nai da sauri ganin zai cire jallabiyar jikinsa na juya masa baya. Kusan mintuna goma sannan ya hawo gadon shima ya kwanta bayan ya kashe fitilar yabar ta gefen gadon kawai. na lumshe idanuna hawayen da suka taru min na silalowa, ni kaɗai nasan irin raɗaɗin da nakeji a raina da ruɗanin abinda ya hanani tuna waɗancan kwanakin da wannan shaiɗanin yazomin. saukar tattausan hannunsa akan kumatuna ya sakani buɗe ido a hankali kan
sa, fuskarsa gab take da tawa har muna shaƙar numfashin juna, dan akan filon danake kwance ya ɗora kansa shima, idanunsa dake kallon fuskata ya lumshe a hankali cikin salon lallashi yana mai sharemin hawayen da hannunsa dake akan fuskar tawa, cikin muryar raɗa yace. “Miyasa baƙya gajiya da kuka?”. Wasu hawayen ne suka sake silalo min, nace, “Na tsaneshi ne fiye da yanda kowa zai iya tunani”. Murmushi naji yayi mai sauti, hakan yasa na buɗe idanuna ina kallonsa, kallona yake shima,, “Kinsan minene?” kaina na girgiza masa alamar a'a, yace, “Na fiki tsanarsa Miema”. Murmushin da ban niyya bane ya suɓuce min a bazata. Gani nai shima yay murmushin idanunsa da suka rine jaa na wani irin ƙyalli kamar hawaye ya taru a cikinsu. nai ƙoƙarin jan fuskata baya dan kusancinmu yayi yawa, sai yay saurin maidoni gab fiyema da farko, yace, “Faɗamin miya faru? Kozan sami nutsuwa”. Hawayen ne suka sake silalowa, na maida idanuna na lumshe inajin yanda yake murza yatsansa babba saman fuskata, sauran huɗun kuwa kan gashina daga ƙeyya zuwa gefen kunne “A wani daren daya shuɗe, wanda tunani ko hasashe bai sake dawo dashi ba gareni, ranar da ya fara zuwa gareni.........................”.
Na ƙare faɗa masa dukkan abinda ya faru har zuwa yau da fashewa da kuka mai cin rai, da ƙarfi ya jawoni jikinsa ya rungumeni tsam, jikinsa na wani irin rawar ɓacin rai, nima saina sake fashewa da kukan, dan koba komai na fahimci shima yanajin irin zafin da nakeji a cikin raina, nace, “Na rasa miyasa ban taɓa tunawa ba sai yau?, Inason nasan ko wanene shi? Miyasa duk waɗanan kalaman nasa a kaina? saina kasheshi, da hannuna zan kasheshi azzalummi maƙiyin ALLAH, sainai gunduwa gunduw.........”
Jawaad daya saki murmushin takaici mai ciwo ya ɗagota daga jikinsa, babban ɗan yatsansa da yake share mata hawaye ya ɗaura akan laɓɓanta da faɗin, “Shiiii!!. kisa a ranki zaki sanshi, bana buƙatar sake ganin kukanki, Ni Jawaad Abdul-aziz yusif insha ALLAHU zan gurfanar miki da shi a gabanki kan gwiyoyinsa, abinda yake bibiyar kuma zan tabbatar masa da yafi ƙarfinsa har abada a wannan daren”. Ya ƙare maganar da manna bakinsa saman nata batare da ya sake bata damar magana ba. Duk da yana tausayinta bazai iya barintaba, wani irin shauƙi da zumuɗin kasancewa da ita yakeji, ji yake tamkar ana ingiza zuciyarsane akanta, jiyake idan bai kasance da itaba a wannan daren kamar zai rasa komai ciki harda ita kanta, tun yana sarrafata da tunanin iya ƙaramin wasa ya barta har hakan yaji bazai yuwuba, zuciyarsa ingizashi kawai take na kaiwa ga ƙololuwar martabarta................✍
😜Saura kuma naji wani yay gulmar Jay ehe😣🤐🤣🚶🏻.
Barkanmu da dawowa.
A ranar asabar an samu kuskuren ɗakko page daga telegram zuwa WhatsApp, wadda tayo copy ɗinsa daga can bata ɗauka a jereba kamar yanda page ɗin yake, shiyyasa tallan zafafa goma ya koma tsakkiyar page, wasu sai sukai tunanin ƙwai cikin ƙaya ake talla wai. To ba haka baneba, dan ranar kam masu sai da zafafa goma saida kuka tsiyayar musu da man kansu tas🤦🏻😑 saboda kira. Waɗanan buks ɗin goma namu sune nake talla gasu ga mai buƙata dan karku bari a baku labari inhar kasan baka karantanba dan duk sunyi lagwadar daɗi aradu🚴🏼👇🏾 .
ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.
SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.
HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO
MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.
MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.
BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....
abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.
Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300
Sai kunzo😍😍😍😘.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
Domin samun littafin Ƙwai cikin ƙaya daga farkon ko taɓa Link ɗin da ke ƙasa.
👇👇👇👇
.
https://www.facebook.com/groups/2803452939899949/?ref=share
[1/11, 10:48 PM] Abue Saleh AlQuyraemey: 🥚Ƙwai Cikin Ƙaya🥚
.
Book Two
.
Bilyn Abdull 📚:
*TELEGRAM LINK ƊINMU*
https://t.me/joinchat/SBu4bmWd8skN4Zfr
WATTPAD
https://my.w.tt/TiR6HMHUNcb
Page 43
.....................A take salon wasan ya canja, bily da batai tunanin hakan daga garesaba a wannan daren duk da dai yau jinta take wani sakayau kamar an sauke mata kaya tuni jikinta ya fara tsuma, zuciyarta da jininta na wani irin tsitstsinkewa, gashi ya hanata dukkan damar da zatai ƙorafi ko magiya, juyata yake duk yanda yaso da zafafan salonsa masu rikita ƙwanya da zuciyar duk macen data mallakesa matsayin mahaɗin rayuwarta, ta rumtse idanunta da ƙarfi lokacin da yake karanto___
بِسْمِ اللهِ اللّهُمَّ جَنِّبْنَا الشَّيْطَانَ، وَجَنِّبِ الشَّيْطَانَ مَا رَزَقْتَنَا.
Bismil-lah, allahumma jannibnash-shaytan, wajannibish-shaytana ma razaqtana.
(Da sunan ALLAH. Ya ALLAH! Ka nisantar da shaidan daga garemu, kuma ka nisantar da shaidan daga abin da Ka azurta mu da shi).
Ƙanƙamesa tai da sauri jikinta na wani irin rawa cikin gigitar data risketa batare datayi hasashe ko shiyaryama zuwan wannan daren ba.
Abinda yay matuƙar birge Jay da mamakin matar tasa shine Jarumtar da bai zatoba daga gareta, ko sau ɗaya batai yunƙurin hanashi yin yanda yaso da ita ba, ta miƙa masa dukkan ragama baki ɗaya cike da juriya da dauriya da sadaukarwa, sai saukar ɗumin hawayenta kawai yake ji da ajiyar zuciyarta tamkar zata shiɗe. (Uhumm) baiji daga garetaba dangane da ɗaga murya balle akai ga kwakwazon da duniya zata fahimci ana dai-dai wajen. duk yanda yaso yin juriya wajen binta a hankali shima dan nuna tausayinta hakan ya gagara, komai ya ƙwace masa a lissafi itaɗin kawai yake gani abu mafi daraja da martaba a garesa a wannan daren dama cikin duniyar baki ɗayanta. Ƙaunarta da tausayinta na ratsa dukannin tsoka da ɓargon jikinsa da jijiyoyi yana gaurayewa da jininsa, bashi da bakin musaltawa, bashi da kalaman kwatantawa, bashi da ƙarfin shelantawa, abinda kawai ya sani shine itaɗin tadabance, idan yace tadaban yana nufin tadaban har ƙarƙashin ruhinsa. Nutsuwar da ya daɗe yana hasashenta a zahiri da mafarkinsa daga gareta yama riski fiye da hakan.......
A zahiri Bilkisu ta hana kanta kuka mai sauti, amma wahala iya wahala shanta take a hannun Jay, yanda kawai take fitar da numfashi ɗai-ɗai zai baka tabbacin baije da wasaba. Hawaye kam ai wasu basa direwa wasu ke gangarowa. shi kansa bai fahimci ya tafka ɓarnaba sai da komai ya lafa, Sosai tausayinta ya sake mamayesa, taimakon gaggawa ya shiga bata ta kowace hanya data dace. Yanda take kuka sosai sai hankalinsa ya sake tashi, amma haka ya daure ya gasa mata jiki dan yasan shine babban gatan dazai mata a yanzun. Sai da ya tabbatar ta samu ƴar nutsuwa sannan ya barta ta ƙarisa gyara jikinta shi kuma ya fito ya cire bedsheet ɗin da duk yaɗan ɓaci, tunani yake anya kuwa baiji mata ciwo ba?....... Da sauri ya waiga bayansa jin kukanta, zanin gadon daya fara jawowa ya saki ya nufeta dan bai zaton zata fito ba, tarota yay jikinsa yana magana a hankali dan shi kansa muryarsa gaba ɗaya ta wani dadushe kamar mai mura, “Miyasa zaki fito kinsan bazaki iya tafiya ba?” Yay maganar yana kwantar da ita akan sofa.
Hawayen dake ziraromin na share, dan ni kaɗai nasan azabar da nakeji, babu inda kemin daɗi a dukan jikina, dai-dai da bakina ɗaci yakemin sam babu ɗanɗano, tausayin dukkan matan da aka kusancesu ta ƙarfin fyaɗe ya kuma mamayemin zuciya, shiyyasa Amina ta koma kamar wata ƙaramar mahaukaciya a lokacin.......
“Ya isa haka kukan mana uhmyim, kinga jikinki harya ɗauki zafin zazzaɓi, ina cewa matar tawa jarumace ashe raguwace?”. Haushi maganarsa ta bani, dan haka nasa hannayena biyu ina kai masa ƙananun duka a ƙirji. Hannayen nawa ya riƙe yana ƙaramar dariya, “Oh to yi haƙuri jarumace, giwar mata, bara na duba wajen nagani bakiji ciwo ba”. Ƙanƙamesa nai ina sake fashewa da kuka, nace, “Ni dai a'a, banji wani ciwoba”.
Jay yay murmushi kawai yana girgiza kansa, miƙewa yay ya ƙarisa cire zanin gadon ya shimfiɗa wani, rigarsa mai ɗan kauri data kai mata har cinya ya saka mata, yasa towel ya tsane mata kanta sosai gudun kar mura ta kamata, dama ga
jikinta yay mugun ɗaukar zafin zazzaɓi, tausayinta duk ya gallabi ransa, cak ya ɗauketa dan harta fara barci ya maidata saman gadon ya kwantar, so yake tasha magani amma baison tadata, dan haka ya ɗakko man zafi kawai ya shafa mata a jiki kozataji ƴar nutsuwa.
Gaba ɗaya a hidimar Bilkisu Jawaad ya kusa cinye wannan dare, sai da ya tabbatar komai yayi masa yanda yake buƙata sannan ya samu shima ya kwanta, wani irin zafi yaji jikinta ya ɗauka, sai sauke ajiyar zuciya take a jajjere cikin barci, fuskarta ya ƙurama idanu yana kallon yanda ta ɓata fuska alamar dai bata jin daɗi har a cikin barcin. Yaɗan lumshe udanunsa ya sake buɗewa akan fuskarta yana wani ɗan murmushi, ƴar yarinyar nan itace ta nema zautar masa da tunani, “UBANGIJI mai hikima, UBANGIJI mai rahama da jinƙan bayinsa” yay maganar a fili tare da sumbatar goshinta da laɓɓanta da sukai jazur sosai saboda wahalar da sukasha a hannunsa. ‘Yanda take mai sanyi haka komanta yake mai sanyi’ ya ayyana a ransa yana rungumeta tsam cikin jikinsa har saida ta motsa sannan ya sassauta mata. A haka shima barci ɓarawo yay awon gaba dashi.
★★★★★★
DARE MAIBAN MAMAKI.
Dolene mutane masu yawan gaske su kira wannan dare da sunan dare maiban mamaki da ruɗani tare da tashin hankali ga wasuma maybe. Dan kuwa lokacin da Jawaad ke angwancewa a lokacin wasu cikin matsanancin ruɗani suke, dan duk wani azzalumi dake da alaƙa da wani ɓoyayyan sirri daya shafi waɗanan ma'aurata da hikimar UBANGIJI ta dunƙule waje guda wannan shine mafarkin da suka tsinci kansu a ciki a wannan dare.
(Ƙudirar UBANGIJI ta tabbata, rahamarsa ta yalwata, izzar mulkinsa ta Ƙaddara haɗewar jini dake cikin jinin da kuka salwantar, azzalumai lokaci yayi, UBANGIJI ya ƙulla rugujewar zaluncinku ta inda bakuyi zato ko tsammani ba, wannan ruɗanin shine nai muku hasashe, kuma gashi ALLAH ya tabbatar dashi, dama na faɗa muku wannan shukar saita fito da izinin UBANGIJI tai yaɗon da zata zamewa rayukanku barazana, nakuma tabbatar muku kafin kubar duniya sai kun wulaƙanta, duk wanda yaci amana dolene amana ta cisa shima, gashi kuwa ALLAH ya tabbatar da hakan, ku fara gudu maƙiya ALLAH, na ce ku fara gudu tun yanzu.......”
Dukkanin wanda keda alaƙa da wannan mummunan kalamai a cikin mafarkin a wannan dare hankalinsa a tashe ya wayi gari, domin dai wata shukace da suka binne a wasu shuɗaɗɗun shekaru take nuni da tayi tsiro da yaɗo harta saki ƴaƴa, suwaye ƴaƴan? A ina suke? Tayaya aka samesu bayan irin da suka shuka sunada tabbacin basu bar ko fure ajikin itaciyarsa ba, itaciyar kanta saida suka busar da ita balle ai tunani tayi yaɗon ɗa? Mike shirin faruwa dasune? A ina kuskuren yake? Ya akai mai gidauniya bai taɓa gano musu hakanba? Shima bai gani bane? Kokuwa ya gani ya ɓoye musu?.
Lokacine zai basu wannan amasar damu kanmu masu bibiyar labarin😵.
★★★★★★★
Rashin yin barci da wuri ya sakasu makara da asuba, dan sanda Jawaad ya farka wasu masallatan ma harsun kusa idar da salla, akan fuskar bily ya sauke idanunsa dake cike da barci, ya sauke siririyar ajiyar zuciya tare da tashi zaune da ita a jikinsa, idanu itama ta buɗe a hankali, sai dai suna haɗa ido tai saurin maidawa ta rufe tana ɓata fuska. Murmushin da bai niyyaba ne ya suɓuce masa, a zuciyarsa yake ayyana ‘sai shagwaɓan tsiya’ A fili kuwa sumbatar laɓɓanta yay, cikin raɗa-raɗa yace, “Good morning my Heartbeat”. Saurin cusa kanta tayi cikin ƙirjinsa. Iska ya hura mata cikin kunnenta yana murmushi, “Ko a ɗan ƙarane” yay maganar yana ƙoƙarin cusa hannaunsa cikin rigarta. kukan taɓara ta sakar masa da sauri jan jikinta baya. “Matsoraciya” ya faɗa yana sauka daga gadon gaba ɗaya.
Lamo nayi kwance zuciyata na tariyomin dukkan abinda ya wanzu a daren na jiya daya tara abubuwa masu yawa a cikinsa, darene da zuciya bazata iya mantashiba ta kowacce irin siga, dan yazo da abubuwa kala-kala a cikinsa. Har yanzu jikina akwai zazzɓi, ga ciwon kai da bala'in ciwon jiki, babu inda bayamin ciwo a jikin nan nawa wlhy. Ina jin motsin fitowarsa amma nakasa motsawa, tunanima nake tayaya zanyi t
afiya ni balki........? Cak aka ɗagani sama, wata nannauyar ajiyar zuciya na sauke ina ɓoye kaina a ƙirjinsa dan banaso ko ido mu haɗa, wata irin matsananciyar kunyarsa nakeji fiye da da. jina kawai nai cikin ruwan zafi, hakan yasa na ƙanƙamesa sosai. A cikin kunnena yace, “Sorry daure, kaɗan za'ayi”. Kaina na ɗaga masa ina haɗiye kukan dake neman tahomin. Yanda ruwan yaɗanyi zafi sosai sai naji daɗi dan har jikina ya gasamin gaba ɗaya dukda inata noƙewa, har aka gama hannayena suna naɗe a ƙirjina. Saida ya bani towel na ɗaura sannan na samu nutsuwa duk da dai shima bawani babba bane amma yafi dai babu. Matsowa yay zai ɗaukeni bayan na kammala alwala. kaina a ƙasa cikin dakusashiyar muryata nace, “Zan iya tafiya da kaina”. Baice komaiba ya ɗan matsa baya ya bani hanya. Cikin dauriya na fara tafiya a hankali ina matse idanu, dan zafin nakeji, sai dai ba sosai dazai cutarba, bakamar na daren jiya dana ringajin tamkar ana yayyankani da wuƙa ba.
Kallonta Jawaad yake cike da nazari harta fice, yanda take tafiyan batason haɗa ƙafafunta sosai ya sakashi jin dolene ya dubata kodai ya jimata ciwon da gaske?. bayanta yabi shima. taimaka mata yay ta saka doguwar riga da hijjab shima ya saka jallabiya ya jasu jam'i duk da garima harya waye.
Bayan sun idar fita yay daga ɗakin, babu jimawa sai gashi ya dawo ɗauke da madaidaicin kofi daketa fidda turiri. Kwance ya sameta a inda tai sallar ta ƙudundune da hijjab, tea ɗin ya ajiye ya ɗakko magunguna ya ajiye sannan ya ɗagota jikinsa harma ta fara barci, “Sorry, tashi kisha tea da magani saiki kwanta”.
Duk yanda na marairaice masa akan na ƙoshi bai saurareniba, sai da ya tabbatar nashaye tas sannan ya bani maganin nasha. Da taimakonsa na koma saman gado, harna fara lumshe idanu naji yana buɗemin jiki, sauri buɗe ido nayi da riƙe masa hannunsa ina ɓata fuska, dan nazata ƙarawar zaice zaiyi. “Na shiga uku, dan ALLAH kayi haƙuri, wlhy ka maimaita mutuwa zanyi”.
Dukda ta bashi tausayi saida yaji dariya na neman kufce masa, ya dai daure ya haɗiye kayansa yana wani binta da kallon ƙasan ido, harta fara hawaye. Ɗauke idonsa yay daga fuskarta batare da yace komaiba ya maida inda yake son ganin.Ya kuwa ji mata ciwon da yay hasashe, sai dai bamai ɗaga hankali bane, amma zaiso a dubata gudun kuskure, tsabar son ya tsokane saiya ranƙwafo kanta kamar da gaske abinda take gudun zaiyi. jiyay kawai ta fashe masa da kuka jikinta ya fara rawa kamar wadda ta hango dodo. Dole ya danne dariyar da keson ƙwace masa ya rungumta. “Wasa nake miki niba ƙarawa zanba yi haƙuri”. Da ƙyar ya samu tai shiru har barci yay awon gaba da ita saboda maganin daya bata yana saka barci, ga kuma dama bawani isashen barci sukaiba. Sai da ya tabbatar barcinta yay nisa sannan ya gyara mata kwanciya ya sauka daga gadon bayan ya lulluɓeta da bargo. Dukda shima barcin yake buƙatar yi bai kwanta ba, wayarsa dake a drowan gefen gadon ya ɗauka ya fita falo.
10:30am
Ring ɗin wayarsa ne ya sakashi farkawa daga barcin daya ɗaukesa anan falon bisa doguwar kujera, kwance yake a rubda ciki, hakan ya sakashi miƙa hannu bisa centre table ɗin dake gab dashi ya lalubi wayar batare da ya buɗe idanunsa ba, guntun tsaki yayi sannan ya buɗe idonun da ƙyar ya kalli wayar. Ganin Jabeer ne ya sakashi ɗagawa yasa wayar a kunne, cikin muryar barci ya
Showing 147001 words to 150000 words out of 249282 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50 Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71Chapter 72Chapter 73Chapter 74Chapter 75Chapter 76Chapter 77Chapter 78Chapter 79Chapter 80Chapter 81Chapter 82Chapter 83Chapter 84