ya raya mana ke cikin aminci, ALLAH yasa ki zama hasken idaniyarmu da al'ummar MANZON ALLAH (S.A.W) baki

ɗaya, kizama madubi mai haska addinin musulinci a kowace irin nahiya, kizama jaruma irin Mamanki.....”
          Murmushi ya suɓucemin babu shiri saboda jin sambatun da yakeyi, hannuna nakai saman kansa na fara shafawa a hankali ina sake faɗaɗa murmushi na, shi kaɗai ya ragemin yanzu a duniya sai gudan jininmu dake a cikin ciki, muryata da ɗan rawa nace, “Nidai insha ALLAH Little Jay ne”.
       “Tab, yarinya ban yardaba”. Ya faɗa yana ɗaga kansa da sauri da hawowa saman gadon ya zauna, yunƙurawa nai zan tashi ya riƙeni, maidoni yay jikinsa ya kwantar dani saman ƙirjinsa. Sai da na shaƙi ƙamshinsa na lumshe idanu sannan na buɗesu a kan fuskarsa ma'abociya kamala da kamewa ina murmushi. Shima murmushi yay min kaɗan yana kafeni da jajayen idanunsa, ya duƙo da fuskarsa dai-dai tawa ya sumbaci goshina da laɓɓana. Sake lumshe idanu nayi da kai hannuna saman kumatunsa ina shafawa a hankali har zuwa bayan kunnensa. “Thanks you Sweet Love” na faɗa a can ƙasan maƙoshi batare dana san shauƙi ya kwasheniba nai suɓutar bakin. Idanu ya ɗan waro alamar mamaki, cikin sarƙewar halshe yace, “Mi ki ka ce?!”. Cusa kaina nai a ƙirjinsa wani masifan kunya na lulluɓeni, ya ɗago fuskata da sauri yana faɗin, “Please Miemaa sake faɗa naji”. Ƙara ɓoye fuskar nayi da ƙyau. “Pleaseeeeeeee”. Ya faɗa a wani irin yanayin daya saka tsigar jikina tashi na sake ƙanƙamesa. “Sweet Love” na sake faɗa a hankali. “Oh my God, wannan rana ta musamman ce a gareni” ya faɗa da sake ƙanƙameni yay baya muka faɗa saman gadon ina jikinsa. “Lilly kinzo da tarin sauyi” ya sake faɗa yana shafa cikina da lalubar bakina ya haɗe da nasa.
       Karan farko a rayuwata dana fara maida masa murtanin abinda ya kemin kaina tsaye babu wani kunya kojin ɗar, a take ya haukacemin jikinsa sai tsuma yakeyi, munyi nisan kiwo sosai dan da gaske neman kaiwa inda yafi ƙauna yake nemanyi, ALLAH ya ceceni a bazata akai knocking ƙofar ɗakin.
        Nice na fara ƙoƙarin zare jikina daga garesa a wale, amma duk da haka ƙoƙarin maidoni ya keyi, na sake ja baya sosai ina sauke tagwayen numfashi da sauri-sauri da gyara rigata, sake knocking ɗin akayi, sai dai narasa ta yanda zan amsa, dan inhar nayi magana sai angane halin da nake a ciki, gashi kuma bansan wanene ba. Juyawa nai na kallesa, yana kwance a yanda na barsa idanunsa a rumtse yana sauke nasa numfashin shima, nasan tabbas yanajin buga ƙofar da akeyi, amma ya share abinsa hankali kwance. Yunƙurawa nai zan miƙe naje na buɗe yay saurin riƙo hannuna, sake juyawa nai na kallesa, yanzu kam ya tashi zaune, ya zaunar dani saman cinyarsa sannan yay gyaran murya batare da ya kalleniba. Daga wajen Nabeelah tace, “Yayanmu ance kufito aci abinci”. Ajiyar zuciya na sauke a hankali, shikuma yace, “Uhhum”. Daga haka bai sake maganaba, Nabeelah ma haka saita bar wajen kasancewar tasan halin kayanta.
     Kallon juna mukayi, yaɗan kaɗamin idanunsa da suka ƙanƙance yana cika bakinsa da iska ya furzar. Bance komaiba na maida kaina na duƙar. Shima bai sake cewarba ya ɗagani daga cinyar tasa bayan ya shafa cikina. Matsawa nayi gefe ganin na samu ya sakeni, batare da yace dani komaiba ya nufi bayi.
     Ƙarar ruwa kawai na jiyo alamar wankama ya keyi kenan, na ɗan dafe kaina ina jinjina kaina, tunanin kar aga bamu fitoba ai zaton wani abunne ya sakani saka hijjab ɗina na fita ni, idan ya fito ya iskeni a can.

         Tunda na fito suketa jeramin sannu, Umm-Anum ta kamo hannuna ta zaunar a kusa da ita. Ɗan kallon Alhaji babba dake gefenta nayi na gaishesa, ya amsamin da kulawa tare da sakamin albarka da doguwar addu'a akan namijin ƙoƙarin da muka nuna a jejin can dan a cewarsa yanzu ya ga komai a labaran dare da suke sake maimaitawa. Kasa cewa komai nayi nidai, na juya na gaida Umm-Anum itama dasu Ummah babba, sai Yaya Anuwar da Aunty Batool da Aunty Haneefa, Aunty Saudah da sukazo suma babu jimawa, Anum da Nabeelah kuma na basu hannu mukai musabaha.
      Babu wanda ya tambayeni boss har aka fara zuba abinci a babban faranti kamar yanda Alhaji babba ya buƙata, muna shirin fara ci sai gashi ya fito sanye da kayan daya haɗo cikin nawa da Anum ta kaimin ɗazu

n. Ɗan kallonsa nayi ya zubamin harara, na ɗauke kaina ina haɗiye murmushin dake neman suɓucemin. Zama yay tsakkiyar Anuwar da Ummah ƙarama, shima yay bismilla kamar kowa ya saka hannu.

              Muna gab da kammala cin abincin wayarsa ta shiga vibration, da farko kalla yay zai ɗauke kansa, sai kuma ya ɗauka wayar da ɗan zafin nama yana ja baya daga gaban abincin, babu wanda yasan mi aka faɗa masa ya mike da ɗan hanzarinsa yana faɗin, “Zanje office, na manta shaf munada meeting wlhy”.
       “Meeting a daren nan Muhammad?”. Alhaji babba ya faɗa yana kallonsa.
          “To ya zamuyi baba? Akan case ɗin mutanen nanne, kasan manyan ƙasar sunyi caa akan batun, gefe kuma al'ummar ƙasar suma da zafi-zafi suke buƙatar suga hukuncin da za'a yanke, gashi a kuma a dalilin faruwar al'amarin allura na neman tono garma”.
       Murmushi Alhaji babba yayi yana faɗin, “Garmuna ma, dan ta wuce guda ɗaya. ALLAH ya bada nasarar ƙulla alkairi to, amma shiga ɗaki ka ɗakko magani kasha, wannan kan naka daga gani ciwo yakeyi”.
      Baiyi musu ba ya nufi ɗakin Alhaji babban ya ɗakko maganin, ruwa ya ɗauka a inda muke yasha sannan yay mana sallama ya fice. Muka rakashi da addu'a mukuma.

          Bayan kammala cin abincin zaman hira akai duk da gajiyar dake tattare da kowa, Umm-Anum ta fara bamu labarin rayuwar da ta tsinci kanta bayan barinta gida. Ma'ana sanda hankalinta ya dawo jikinta ta ganta a ƙasa mai tsarki, sai dai kuma ta gagara tuna komai daya danganci rayuwarta ta baya, da inda ta fito, da ahalinta.
     Kuka kowa ya keyi hawaye shaɓe-shaɓe, duk da nariga nasan duk wannan tunda mu an faɗa mana sanda mukaje saudia nima saida nai kukan. Ummah babba ma ta labarta mata yanda abubuwa suka faru bayan barinta gida. irin neman da akaita mata da tashin hankalin da Mama maryam da Alhaji babba da Rahmah dasu kansu suka shiga, harma da ƴan uwan mahaifin boss. Rasuwar Mama Maryam da Auran Rahma.
           Sai dai bayan wasu shekaru kuma sai kowa ya haƙura aka cigaba da binta da addu'a dansu tunaninsu koma ta rasune. Itama taci kuka, muma muka tayata.
       Har kusan ƙarfe biyu na dare bamu kwanta ba. dan da ƙyar Anuwar dasu Aunty Haneefa suka lallaɓa Alhaji babba ya yarda zai kwanta ya huta daboda jikinsa, gashi Doctor yace ya samu isashen barci.
     Muma duk tashi mukai mukaje muka kwanta kowa zuciya babu daɗi. cikin amincin ALLAH ni dai inama kwanciya barci mai nauyi yay awan gaba dani.

_______________________
Tafida family house
__________________

               Lokacin da labari ya isa kunnen mama Atika akan ganin Umm-Anum sai tahau surutai tamkar wadda ta zare, tun su Uncle Uwaisu na ɗaukal al'amarin matsayin ruɗani harya koma basu tsoro. Dan sosai neman fita take daga hayyacinta.
       Sake ruguntsumewa gidan yayi da tashin hankali, babu mai iya fahimtar yaren wani. Batun yunwa kuwa ai an manta da sunanta a wannan gida yau, dolefa aka danƙarama Mama Atika allurar barci ta ɓingire, har dare basa tare da nutsuwarsu, barema da Qaseem suka iso gidan Mom da itama take a jangwaɓe, ta tada hankalintane akan a maidata gida batason kwanan asibitin shiyyasa Qaseem ya kawota nan dan can gidan zamansa tashin hankali kawai zai ƙara mata.
        Itama dai Mom maganar dawowar Umm-Anum ta nema maidata ruwa, dan ruɗani ta sake komawa ciki fiye da tunani, al'amarin sai ya sake bama su Uncle Sulaiman da basu san komaiba mamaki, a ganinsu dawowar Bilkisu cikin ƙoshin lafiya abin ayi murnane bawai tashin hankaliba, amma yarasa miyasa abin ke neman zama wani iri ga wasu daga cikin ahalin nasu?. Bashi da mai bashi amsa, dan haka yay gum da bakinsa kawai.

       Saboda meeting ɗin da za'ayi shima dai Qaseem baro musu gidan yayi, sai da ya fara zuwa gidansa ya watsa ruwa yay sallar isha'i sannan ya nufi station batare da yay tunanin neman abinciba ma, dan shi sam a yinin yau bama abinciba ko ruwa sai ƙishirwa ta kaisa maƙura yake nemansa yasha.

__________
STATION
________

                  Ɗakin meeting ɗin yay tsitt, tsumayen shigiwar oga kwata-kwata (Director General) daya iso garin a yammacin yau kawai sukeyi, kusan mintuna go

ma sai gashi ya fito tare da wasu manyansu. Duk miƙewa sukai tsaye domin girmamawa a garesu, suka ƙame tare da sara musu.
      Shima murtani ya maida musu sannan ya zauna da nuna musu alamar suma su zauna. Zama duk su Jay sukayi, bawai matsayin rank ɗin Jawaad ya kai ai zaman wannan meeting ɗin da shi bane, kawai ƙwazo da suka nuna akan aikin ya kai shi ga shiga wannan tawagar, dan gaba ɗaya gurin manyansune nacan ƙololuwa, sai su Sir Ahmad dasu Qaseem, sai dai shi Qaseem ma gaba ɗaya yama kasa shigowa ɗakin meeting ɗin, koda yazo sai ya maƙale a office ɗinsa ransa duk a dagule.
           An buɗe taron da addu'a a ɓangarorin addinan biyu, kafin D.G ya nuna kujerar data rage babu kowa cikin alamar son sanin wanda ya kamata ya zaunata. Sir Ahmad ne yay masa bayanin Qaseem, an ɗaga waya za'a kirasa Jawaad ya miƙe tsaye yana ɗaga hannu, damar magana Oga kwata-kwata ya bashi. “Sir ina neman alfarma”. “Muna saurarrnka”. “Sir Qaseem yana cikin tsananin ruɗani, inaga zamansa tare damu a wajen nan kamar zai ƙara tunzura tunaninsane ga wani abu daban, a ɗazun har mummunan hukunci yaso yankema kansa. mizai hana ai masa alfarmar barinsa kawai”.
     Tsit ɗakin yay alamar jiran amsa daga bakin Oga. Sai da yaja kusan mintuna biyu kafin ya jinjina kansa yana gyara abin maganar gabansa. “Maganar Cpt gaskiyane, kasancewar abinda zamu tattauna ɗin yanada nasaba da mahaifinsa akwai damuwa, kuma shi jami'inmu ne daya taka rawar gani a wannan hukumar, ya cancanci koda sau ɗayane a nuna masa hallacin hakan”. Duk kawuna suka jinjina, inda wasu kuma a cikinsu hakan bai musu daɗi ba, dan su kam basuƙi ama kori Qaseem ɗinba daga hukumar gaba ɗaya.

         Jawaad ne ya fara bayani akan matakan da sukabi dangane da kamasu akan dukanin bayanan sirri da suka samu, sai abubuwan da suka samo a gidan kama daga mutane zuwa wasu abubuwan daban, sai kuma adadin su Dad da suka kasance su 22 idan aka haɗa da shugabarsu data kasance mace. Sai ayyukansu da muƙaman wasunsu a cikin siyasa da kasuwancin wasunsu.
    Bayan ya kammala ya miƙa takardar da dukkan bayanan suke ciki ga Sir Ahmad, wanda shi kuma ya miƙama D.G.
         Amsa yay ya duba na tsahon wasu mintuna kafin ya ɗago yana kallonsu. “To duk kunji bayanai ga jami'inmu, mi zaku iya cewa ku?”. Hannu wani ya ɗaga aka bashi iznin magana.
      “Sir ina ganin kawai mu miƙasu kotu mana, dan dukkanin bayanan da Jay ya bayar an samu mutanen nan dasu a zahiri kuma duniya duk ta gani, a ganina bama buƙatar wasu hujjoji kuma”.
      Jin jina kai D.G ya shigayi, amma baice komaiba. Wani ya sake ɗaga hannu shima aka bashi izini.
       “Ni kuma Sir a ganina kamar kaisu kotu ba mafita bace, dan za'a iya amfani da siyasa wajen kuɓutar dasu, ƴan ƙasa kuma su cigaba da kallonmu da laifin daba namuba, kawai mu riƙesu a wajenmu har iyakar rayuwarsu”. Nanma dai kawuna kawai suketa jinjinawa, wanima ya sake miƙewa shima ya faɗi ra'ayinsa. Haka sukaita faɗar ra'ayinsu ta kowanne fanni, inda maganganun su duk suna akan turbar gaskiya da kuma muhimmanci mai ƙarfi, shi dai Jay baice komaiba ganin duk manyansane keta magana, saida kowa ya lafa sannan D.G ya kallesa da kulawa. “Bakace komaiba Jawaad, bayan kuma kaine jami'in dayasan sirrin case ɗin nan fiye da kowa a cikinmu”.
    Iska Jay ya zuƙa ya fesar, kansa a ƙasa yace, “Sir ai kune iyayenmu, zaku hango abinda mu sam bamu iya hangosa ba, duk hukuncin da kuka yanke muma zai zama dai-dai a garemu”.
      “Hakane Jawaad, amma kuma da kuke ƙasanmu zaku iya bada shawara mai amfani da zatafi wadda mu zamu kawo, domin ku a yanzu kuke ganiyar ƙuruciyarku da kaifin tunani, sannan kuke shiga lungu da saƙo akan kowacce matsala, kune kuke ganin komai dangane da al'umma, kune kuke fita farautar masu laifi cikin kowanne irin runtsi da ƙalubale, mu muna office zaune, idan kun bada shawara ai bazai zama kuskureba”.
       “Hakane Sir. To nidai idan har shawarata bata sauka a layiba ina ganin kaisu kotun shine babbar mafita, amma kafin hakan ya dace a faɗaɗa bincike dangane da masana'antunsu, da wajejen ayyukansu, akwai business da wasu a cikinsu ke gudanarwa a cikin ƙasa da wajen

ƙasa, mizai hana musan mi suke fitarwa da shigowa ne? Masu ayyuka a gwamnati musan wane irin aiki suke gudanarwa a ofisoshinsu suma, daga haka mu basu damar neman lauyoyi muma mu samu namu ƙwararren lauyan. Hujjata anan itace dukansu waɗanan mutanen akwai zargin fyaɗe akansu wanda sam bama asan adadinsaba, sun lalata yara da yawa da mummunan aikinsu, ciki harda ƴaƴan ƴan uwansu. Duk yanda muke tunanin kare kanmu ga al'umma bazamu fitaba sai anyi komai akan idanunsu.........”
      “Tayaya za'ai komai akan idanunsu?, fili kakeso a ɗiba a tara duka talakawa ai zaman kotun a gabansu komi?”. Wani ya faɗa aɗan fusace yana kallon Jay ɗin.
     Murmushi Jawaad yay yana mai girgiza kansa, “Ba haka nake nufiba yallaɓai, abinda yasa na kawo wannan maganar ta al'ummah saboda idanma muna gudun manyan ƙasar zasubi ta ƙarƙashin ƙasa wajen saye alƙalan da zasu gudanar da wannan shari'a muryoyin ƴan ƙasa zai daƙile hakan, sannan suma manyan zasu tsorata domin inba waɗan nan jama'ar ai babu su, musaman idan mukai dubi da mafi rinjaye a cikinsu wannan shine hawa na farko da sukayi. sunason komawa na biyu, bazasu so sunansu ya ɓaci ba ai kodan mulkin da suka ɗanɗana suke kuma ƙulafuci da ƙwaɗayin komawa”.
      Sir Ahmad dake murmushi ya kalli D.G, “Sir Jay yazo da maganar hankali, dominfa wannan faɗan sam ba namu baneba, faɗane tsakanin al'ummar ƙasa da waɗanan mutane, idan kuma har mukai tunanin shiga ciki wajen kare mutuncinsu to lallai zamu fuskanci ƙalubale harma a ringa zargin muma da namu dalilin mara ƙyau a ƙasa, amma idan min fidda komai ga al'umma muka kuma nuna musu suma sunada ƙarfin iko akai su kansu alƙalan zasu shiga hankalinsu sosai, sannan ƴan siyasa bazasuyi wani tasiriba wajen yaɗa farfagandar da suka saba. Kaga mun jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, mun kuma ƙarama hukumarmu kima da daraja a duniya baki ɗayama ba wanan ƙasar kawai ba”.
      “Wannan gaskiyane wlhy” wani ya faɗa cike da goyon baya akan zancen su Jawaad da Sir Ahmad.

         D.G yace, “Okay, inaga to zamu tsaya a wannan matsayar, zuwa gobe sai mu yanke hukuncin daya dace ko ya kukace?”.
      Duk kawuna suka jinjina masa cike da gamsuwa. Daga haka taron ya tashi. lokacin ƙarfe kusan uku na dare.
            Jay baibar station ɗinba saida yaje office ɗin Qaseem ya fiddosa, shine da kansa ya kaisa har gida sannan ya wuce gidan Alhaji babba, ya iske duk sunyi barci, dan haka ya wuce ɗakin da yake tunanin Bilkisu na a ciki. Kwance ya sameta ita kaɗai a saman gado ta cure waje ɗaya kamar maijin sanyi, yay ɗan murmushi da cire kayansa sannan ya raɓa ta gefenta ya kwanta tare da turata cikin jikinsa. A take ta shaƙi ƙamshinsa, sai ta gyara kwanciya kawai ta lafe tana mai sauke tagwayen ajiyar zuciya kamar wata mage.
      Murmushi ya sake saki mai sanyi, ya sumbaci kanta yana sauke tasa ajiyar zuciyar a jere.

____________
WASHE GARI
________________

               Washe gari ta kama Lahadi, tunda safe Jay ya samu kira daga Gimbiya Munaya akan takawa da kansa zai yoma su Abbu rakkiya gidan Alhaji babba.
    Hakan ba ƙaramin mamaki ya bama Jawaad ba, dan haka ya sanarma dasu Alhaji babba halin da ake ciki, su kansu sunyi mamaki, to amma idan akai dubi da matsayin su Abbun a wajen Takawa hakan ba komai bane face girmamawa.

★★★★★

         A family house ɗin su Jawaad ma sun wayi gari da shirin zuwa gidan Alhaji babba wajen Umm-Anum kamar yanda Uncle Sulaiman ya bada shawara shi da wasu a cikin sauran ƴan uwa.

★★★★★

          Ɓangaren su Firdausi ma tun da farar safiya suka kammala nasu shirin na nufowa birni, sai dai su saɓanin ƴan masaurata da familyn Jay ne, su gidan Jawaad sukai shirin zuwa tamkar yanda Muktar mijin Firdausi yay ƙoƙarin sama musu adireshi a daran jiya ta dalilin wani abokinsa ɗan sanda.

★★★★★★

           Maman Amina ma sun tashi ne da shirin nufar gidan Alhaji Babba kamar yanda Jay ya kirasu ya sanar musu suje dan Mama Safara'u ta gana da Umm-Anum.............✍


“Hummmmmmm!!!!! Wannan shine ake kira da ga wuri ga waina, to masu karatu, idanfa bakusan gariba to ku saurari daka, dan yanzu zamusan ma'anar ƘWAI CIKIN ƘAYA. su wanen Ƙ

AYOYIN? su wanene ƘWAYAYEN?. Amsoshinku na'a page 61, saiku shirya kuma domin yin gangamin tafiya gidan ALHAJI BABBA mu gani wace wainar za'a toya shinnnnnnn?🚴🏼🚶🏻😢.



Masoya ZAFAFA 2021 fa sunata gagarumin shiri da yafi rukunin farko dana biyu da suka kawo muku a baya, mun shirya shiri na musamman domin ƙayatar daku da nishaɗantar daku da daɗaɗan
Showing 231001 words to 234000 words out of 249282 words